Free chapter · Read without an account

GUGUWA BIYU

by Aysha d fulani · GUGUWA BIYU

*GUGUWA BIYU*



Aysha D Fulani





BABI NA BIYAR



بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ






Dariya Hajiya tai mata tana fadin

"Sudin yarana ne, su biyu nake da hotonsu yanzu, itama wannan Allah ya amshi abinsa, a hanyarsu ta dawo daga Abuja sunanta Iman, ba anan suke da zama ba suna zaune a Abuja, Babban sunansa shine Habibu ita kuma macen sunanta Iman, Habibu shine babba yanzu yana da shekara talatin da biyu a duniya, ya yi karatun sa, Abuja, ganin haka da ƙanwarsa tayi tana gama nata karatun itama tace mana chan zata nema nata admintion din, kuma ba'a sha wahala ba Ya'yanta ya neman mata.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara karatunta tana zaune a inda yayanta yake zaune gidan yayata a chan. Itama chan ta zauna daganan take zuwa makaranta Yayata yaranta biyar maza uku mata biyu babban shi sa'an Habibu ne ita Iman sa'ar Suhaima ce a chan suke da zama, lokacin da sukai hutun na kusa da karshen zango ta kirani a waya tace mun so take tazo gida ta ganni hankalinta duk yadawo kaina, nace ya take haka tana zaman zamanta zata bullo da wannan al'amari ta bari cikin weekend sai ta zo, sam taki yadda dole muka a jiye maganar akan washegari zata zo.

Washegari munyi waya akan tana hanyar zuwa lokacin karfe shaɗaya na safe, tashi nai domin girka mata abinci, ina kicin na daura duk wani abu da nasan zata bukata naji wayata sai ringing take, fitowa nai da sauri don kiran kusan na uku kenan, kanga wayar nai a kunne ina fadin "Ya kuma akai ɗiyar mama. A tsaye na maƙale da jin furucin da har na koma ga Allah bazan manta shi ba, mai wayar nan ce sukai hatsari Allah ya amshi abunsa don Allah a nemo wani mafi kusa yazo, babu abin da ya iya fitowa daga bakina sai salati da sallami kwatanta mun inda abun yafaru ya yi ya ajiye wayar. Aysha nashiga matukar tashin hankali amma haka najure na kira mahaifinta da yayanta suka karasa wurin suka taho da gawarta ashe daman zuwan da take so taimun kenan, nashiga damuwa sosai su sauran yarana da ƙananun shekaru Allah ya amshi rayuwarsu ita kuma wannan da girmanta sosai domin ta kai shekara ashirin da biyar a duniya, hakika sai dai ince Allah yai musu rahma baki ɗayansu amma kam abun babu sauki.

Kinga wannan shine ya ragemun kuma yanzu haka baya kasar shekaran jiya ya tafi Sudan yin digirinsa na biyu, dalilin nemo mai tayani zama kenan saboda da yanan yana zuwa mun hutun mako, so yanzu ya tafi shida gida ba yanzu ba sai Allah ya yi dawowarsa".

Jikin Aysha ya yi mugun sanyi da jin labarin yaran Hajiya, jajanta mata tai tare da yimata ta'ziyya addu'a sosai ta ma yaran sannan ta gyara zamanta tana sake kare ma Habib kallo tai wanda yake dauke da dogon hacin ga sajensa ya sakko ya zagaye fuskar inda ya sakin mai ƙasumba, cute lips dinsa sun matukar ƙawata fuskarsa mussaman yadda ya yi dasu a cikin hoton, lumshe ido tai tana jinjina ma Ubangiji da ya ƙagi wannan kyakkyawan bawan.

Aysha! Hajiya tai kiran sunanta ta daura da fadin "Ki tashi ki zuba abinci sai kizo in nuna miki saura wuraren na gidan, yanzu ni zan dan kwanta idan kingama sai ki kunna kallo kafin in tashi idan kuma kema baccin zakiyi to shikenan idan na tashi mayi duk abinda ya dace a yi".

"Toh! Ta bata amsa ta daura da fadim

"Amma don Allah zan roƙi alfarma a gurinki, ina so in dena kiranki da Hajiya so nike in dinga kiranki da Amie domin kin maye mun gurbin da na ɗade ina nema a doron duniya, hakika inaso in san ɗadi uwa, amma ban samu haka ba, ina jin ciwo mai matukar kona zuciya a duk sanda na tuna cewa wacece ni, na kanyi kuka a duk sanda na kalli uwa na walwala da ɗanta babban abin da nake tambayar kaina shine shin yaushe zanga tawa uwar, tana raye ko ta mutu shin wani daliline yasa suka wurgar dani, ko dai ni ɗin banda ubane kamar yadda ake kiran wasu da 'ya'yan gaba da Fatiha ko dai nima irinsu ce, a duk lokacin da na nutsa ni ka dai nakan yi kuka sosai watarana in rarrashi kaina watarana kuma ina yi bacci ya kwashe ni a haka, Ubangiji shine yasan dalilin haduwarmu don Allah Amie kiyimun alfarma in zauna dake har lokacin da Allah ya yanke zan hadu da iyayena".

Gaba ɗaya jikin Hajiya Fadilah ya yi mugun sanyi mussaman yadda taga ruwan hawaye na tsiyaya a idon Aysha, kusa da'ita ta dawo ta zauna ta riko hannunta tana fadin. Na amince miki kirani da duk sunan da yai miki, kuma ki dena kuka haka komai mai wucewa ne watarana ko ina raye ko ban raye a jikina inaji zakiji farin ciki mai matukar yawa hakika ɗanginki masu arzikine domin babu wanda zai jefar dake da wannan uban kudin, ke dai abin da zakiyi shine duk rintsi duk wuya kadda ki yadda mutuncin ki domin matarbar ƴa mace itace mutuncinta duk rintsi ko a wani hali zaki tsinci rayuwa kadda ki sake duniya ta ruɗeki, yanzu bari in shiga ciki zuwa anjima zan fito Allah ya yi miki albarka ɗiyar Amieeta".

Murmushi Aysha tai tana goge hawayen fuskar ta mike Hajiya Amiee tai ta shige ɗaki cike da tausayin Ayshatu.

Gyara zama Aysha tai bayan ta gogen hawayen idonta, ta jawo kulolin abincin ta zauna taci wanda zai isheta, Tv ta kunna ta zauna tanakallo, bacci ne yai awon gaba da'ita kiran sallah da ake yi ne ya tashe ta, bakinta dauke da salati ta mike daga kan kujerar agogon da ya mamayen bagon ɗakin ta kallah taga karfe ɗaya har ta gota, saukowa tai ta shiga daki alwalah tai ta gabatar da sallah ta mike ta fito falo, a zaune ta iska Hajiya Amie gaishe ta tai ta zaune nesa da'ita kaɗan.

"Taso muje kiga yadda gidan yake."

Miƙewa tai suka fito a bakin kofar shiga taga Camera a maƙale ta jikin bangon wurin, bin bayan Amie tai suka fito babban tsakar gidan wanda akai ma ado da fulawoyi masu kyau, gidane mai dauke da bangare uku, ɗaya na Amir ɗayan kuma na kishiyarta Bilkisu sai wanda ke chan gefe na maigidan.

Nunnuna mata cikin gidan tai suka jiyo zasu koma bangaren Amie a bakin kofah suka iske Bilkisu tsaye ita da wata yarinya kyakkyawa wacce a kiyasin shekaru bazata wuce shekara ashirin da biyu ba, sunanan Aysha Amie ta kira suna gabda zuwa inda Bilkisu ke tsaye tana fadin. "Iya gaisuwa ce tsakanin ki da matar nan bayanan ban lamunce miki komai ba, muna zuwa wurin ki gaisheta ki wuce ciki kadda ki tsaya sauran abubuwan da zata ce miki don Allah".

Gyada kai tai suna zuwa ta gaisheta kamar yadda Amie ta bata umarni, tunda suka doso wurin Bilkisu ta kafe Aysha da wani irin miyattacen kallo, ko da Aysha ta gaisheta amsawa tai amma idonta na kanta, tambayar take bakuwa mukai ne ganin ta wuce ciki yasa ta dawo da kallonta ga Amie tana fadin "Barka da fitowa bakuwa ki kayi ne".

Amsawa Amie tai tana fadin "Tazo ta zauna ne na kwana biyu, kafin Habib ya dawo daga school, ya gidan ya kwana biyu".

"Lah kice nan zata kwana biyu toooo ai shikenan, gida Alhmdulih nima bakuwa nai na rakota kin ganta ɗiyar ƙawata ce gatanan sunanta Surayya".

Jiyowa wacce aka kira da Surayya tayi tana gaida Amie, amsawa tai a takaice tai musu sallama ta shige shashinta.

A tsaye ta barsu Bilkisu sai leƙen bayan Hajiya take ko zata sake hango Aysha, kudin dake hannunta ta mika Surayya ta na fadin "Ga wannan kiyi anfani dashi babyna zamuyi waya zuwa anjima".

Karamin tsaki taja ta galla ma kudi wata uwar harara tana fadin "Banso ki bawa wacce yarinyar danaga kina ma kallan kwalama, wai don Allah meyasa ki ke haka ne ke da kinga yara hankalinki sai ya tashi, wallahi muddin ki ka shigo mana da wannan cikin rayuwarmu to sai na aikata lahira."




Comment fisabillilahi.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol