Free chapter · Read without an account

58

by Fareeda Aliyu · KOWA DA ƘADDARARSA

BAYAN WATA HUƊU

Zuwa wannan lokacin an kammala komai na restaurant ɗina har ma an buɗe. Nu'uman da kan shi ya zauna yayi interviewing ma'aikatan wurin tare da yanke albashin su, duk da yake ban manta masu aiki na kitchen ɗin gidan mu ba, har da su aka ɗauka. Sannan kafin mu buɗe, tare da shi muka yi market survey, tun daga farashin kayayyakin abinci zuwa gidajen abincin su kan su. Duk lokacin da yake Kano (tunda aikin shi ba wai weekends yake bi ba, ya danganta da lokacin da off ɗin shi ya faɗo), sai ya zama ba mu da aiki sai ziyartar gidajen abinci, aim ɗin mu ba wai cin abincin ba ne, a'a, mu ga menene a menu ɗin, kuɗin abincin, kazar-kazar ɗin wurin har ma da lura da abinda mutane suka fi buƙatar siya. Wani sa'in kuma na ɗauki Hussein mu tafi idan Nu'uman baya gari, sai dai na ba shi labarin komai da na gani. Hussein ya fi kowa murna da wannan yawon, balle ma ba kuɗin shi ake kashewa ba, ina ga mai cin kuɗin Hussein daga Mama sai wannan budurwar ta sa Nafisa mai bala'in wayo.

Lokacin da aka buɗe kuma an gabatar da intercontinental dishes, Umma ce ta taimaka mana da wannan, wani professional chef ta biya ya zo kafin a buɗe wurin ya koyar da mu wasu girke-girken masu yawa, kawai ni nayi twitching abubuwan ne saboda ina buƙatar namu ya ɗan fita daban, kuma da aka buɗe sai abun ya karɓu. An ajiye dukkan abin buƙata a restaurant ɗin, kai hatta NAJNINO SPICES (***) shelf guda aka zuba su, kana doso restaurant ɗin mu yawu zai fara gudana a bakin ka.

Ɓangaren girke-girken biki ko taro ba mu daina ba amma an canza masa fasali, muna da masu kai maka abinci, su kuma raɓa idan haka kake so. Kuma Nu'uman yayi reviewing prices ɗin, don idan ka san ni daa ina maka girki, yanzu cewa za kayi na ƙaro wulaƙanci saboda kuɗin ba irin na baya ba ne amma ai shi kan shi salon sarrafa abincin ya sauya. Papa ya haɗa ni da kwastomomi har ban san yawan su ba. A taiƙaice zan ce Alhamdulillah, gidan abincin mu ya karɓu don kullum daɗa haɓɓaka ya ke. Na yi kuma matuƙar sa'a Manaja na mai riƙon amana ne, ko bana nan da wuya ya cuce ni, shi yasa koyaushe cikin kyautata masa nake, don bahaushe yace ka gaishe da mai gaishe ka ko da ba zai amsa ba.

A makaranta kuma mun kammala jarabawar zangon farko na aji huɗu, abinda yayi mun saura babu yawa yanzu. Project ɗina ma ya kammalu, kuma aikin Nu'uman ne. Duk da irin aikin da yake kan shi, shi ya zauna yayi mun aikin, ɓangaren field ne muka yi liason da class rep, shi ya fitar mun na biya shi. Abinda kawai nasan na yi shine idan na kai wa project supervisor ɗina aikin ya duba, to nice nake yin gyaran da yayi mun.

Lokacin da muka fara ɗan yin nisa a zango na biyu ne Nu'uman ya samu wani short break, wannan karon Umra ya kai mu. Karon farko da idanuna suka sauka kan Ka'aba, naji hawaye ya cika mun ido. Na tsaya ina kallon ta ina kwatanta girman Allah da hikimar sa a zuciya ta, sai kawai na fara kukan da ban san dalilin sa ba. Nasan Allah yayi mun alkhairai masu ɗimbin yawa a rayuwa ta da ban isa na ƙirga su ba. Na dinga godewa Allah akan kowacce ni'ima da yayi mun. Nace Ya Rabb ka bani lafiya, Nagode maka. Ya Allah idan ka ba ni wata ni'ima ban gode maka, ba saboda butulci ba ne, saboda tawaya ta ce ta ɗan'adam. Alhamdulillah ala kulli ni'ima. Na riƙo hannun Nu'uman nace Allah Nagode da wannan kyautar da ka yi mun, zan cigaba da gode maka har ƙarshen rayuwa ta. Allah ka wanzar da zaman lafiya, fahimtar juna, soyayya, riƙon amana tsakani na da bawan nan naka har ƙarshen rayuwar mu. Allah ka sa ya so ni fiye da kowacce mace a duniya in dai ina raye, Allah ka sanya ni ma na so shi fiye da kowanne namiji in dai har yana raye, Allah sanya auren mu ya zamo mutuwa ce kaɗai za ta raba. Ka sanya zaman mu tare ya yawaita alkhairin mu duniya da lahira, ka ba mu zuriyya ɗayyiba, Allah ka ba mu ikon da damar da za mu yi masu tarbiyya bakin iyawar mu, ka sanya su zamo sanyin idaniya a gare mu da al'ummar da zasu rayu da su. Addu'a har bansan yawan wadda nayi ba. Abu ɗaya na sani, kukan nan da nayi ya yi matuƙar sanyaya mun zuciya. Alƙawarin Allah ya cika, bayan Kowane tsanani akwai sauƙi. Alhamdulillah.

Bayan mun dawo babu daɗewa aka sanya bikin Jamila nan da wata biyar, kuma ina ji na kamar mai shigar ƙaramin ciki amma dai ban tabbatar ba. Ranar da kuwa Oba ya bugo waya ya haɗu da wata kuma ba ɓata lokaci za'a yi ba, za'a yi auren, gidan kamar zai ɓalle don murna. Dukkanmu mun yi video calls da shi muna ta taya shi murna. Har ma yana tsokanata wai ya ya ya ga nayi ƙiba, haka ma Nu'uman, to ko me muke ci mu tattara a turo masa U.S. Matar ta shi 'yar asalin Kaduna ce, karatu ta je America amma a gidan kawun ta take zaune a chan, kuma shi ne zai aurar da ita. 

Papa ne kaɗai ya samu sararin zuwa ɗaurin auren, don a lokacin ma Nu'uman baya ƙasar amma tafiyar ta ɓangaren aikin sa ne, ni ma kwanakin nan wahalar gani yake mun. Amma na ba wa Papa dambun nama mai yawa a tafi wa Oba da shi, sannan na aikawa su babyn gidan Anty dambun kifi, su kam ban san ko sau nawa nake yi masu irin wannan aiken ba, suna matukar son shi. Har ma akwai direban da muka saba da shi a tasha da yake kai masu Kaduna kuma har gida in dai har nayi aiken. To finally Oba has tied the knot! Sannan naji Papa yana cewa gabaɗaya za mu tattara mu je U.S ɗin ganin amarya kwanan nan in shaa Allah.

Lambu na yayi albarka, ba na siyan kayan miya a girkin gida na, kawai zagayawa nake na tsinka domin amfani na. Irin yalwar da yayi ya sanya mun sha'awar yin lambu babba for business purpose. Na fara research akan green house, so nake na kammala makaranta gabaɗaya na ga ta yaya zan farawa abun, in shaa Allah.

Ranar wata Laraba da na taso daga makaranta gida na wuce wurin Mama. Yanzu ita kaɗai ce a gidan, dan ma Yaya Muntari ya kawo 'yar shi makaranta Kano, ita ce take ɗan ɗebe mata kewa idan tana gida. Wurin ƙarfe uku sai ga wayar Nu'uman ta shigo "Ummu kina ina?" Na amsa ina gida wurin Mama, daga makaranta na taho nan kawai. Yace "Shine ba notice sai yawo ko?" Nace Allah na kira wayar ka ɗazun a kashe, sai na rage murya nace na kuma ɗauka har na koma ba za ka samu time din da za ka kira ni ba balle ka sani. Yayi dariya mai sauti "Zan yi maganin ki ne, gani nan zuwa gidan Maman." Na yi zumbur na tashi daga kwanciyar da nake yi a gadon Mama nace wait, what? Kana gari ne? Murmushin sa kawai na ji sai ya kashe wayar. Ina ajiye wayar na ga Mama ta faɗo ɗakin cikin sauri ta doshi wardrobe ɗin ta tana neman abu, amma fa kuka take yi. Hankali na ya tashi na miƙe tsaye na je kusa da ita ina tambayar ta menene? Tace Hajiyar ƙofar Na'isa ce ta rasu, yanzu Abba (baban Yaya Rufa'i) ya kira ta.

Nu'uman da ya ƙaraso ya iske mu a falo ne, don Baba yace ga shi nan akan hanyar dawowa gida domin su tafi gidan rasuwar. Yana shigowa falon ya gan ni cikin damuwa har ma da alamun nayi kuka, bai ƙara cewa komai sai kusa da ni da yazo ya zauna, tambayata yake "what's wrong Ummu?" Ko Mama da ke gefe bai kula da ita ba, ya ƙanƙame hannu na duk hankalinsa ya tashi. Da ya san me ya faru kuma, Mama yayi wa gaisuwa amma bai tashi daga kusa da ni ba bare ya saki hannu na da ya riƙe.

A na kai Hajiya kuma lokacin magriba tayi yace na fito mu tafi gida tunda ba daɗin jiki na nake ji ba. Da na fito nace masa yayi haƙuri ya bar ni na kwana, 'yan kwanan kuma muna da yawa bai kamata a ce ni kaɗai na tafi ba. Bai ƙara kallo na ba ya juya ya fice daga zauren gidan, da alama kuma tafiyar sa gida yayi. Tunda na koma ciki na rasa me yake mun daɗi, sai na samu Yaya Zainabu na faɗa mata Nu'uman yace na koma gida, kuma tunda nace anan zan kwana yayi fushi ya tafi. Tace "Ai kowa ya kalle ki ya san ba kya jin daɗi, tunda ma muna da yawa da za mu kwana anan menene na son kwanan na ki? Ba gobe sai ki zo ba? Kuma addu'a na ga ko a ina kike za ki iya yi mata. Bari na ga ko baban su Najwa na kusa ya sauke ki gida, don shi ma tafiya zai yi da su Al'ameen." Shi ya sauke ni gida.

A falo na iske shi zaune yana aiki akan MacBook ɗin sa, falon ma bai kunna dukkan fitulun ba akwai ƙarancin haske. Har na shigo bai ɗaga kai ba, babu wata alamar da ta nuna ya san na dawo gidan. Ni kuma na kunna ragowan fitulu, bai ɗago ba. Na taku buguzum-buguzum duk don na shaida masa na dawo amma bai ɗaga kan sa ba. Na wuce ciki don na samu na yi wanka, nasan ba ya wuce tayin wankan dare tare da ni, amma har na gama ban ga alamar zai ma shigo ɗakin ba. Akan gado na iske wasu sabbin lingerie, da alama zuwan shi ɗazun ya kawo mun su. Ai kuwa kai tsaye na saka mai kalar ja, abin ka da farar fata sannan ƙaramin cikin da nake tunanin ina da shi ya sanya nayi ƙiba at the right places. Na fito yana kan aikin da yake har yanzu uffan bai ce mun. Na wuce kitchen na ɗauko roban Nutri milk na dawo, bawan Allahn nan ya ki kallo na. Abinda nayi kawai zuwa nayi gaban shi na ajiye abun hannuna a table mafi kusa, na sauke laptop ɗin na shi na haye kan ƙafarsa tare da sanya kaina ta wuyan shi wurin ƙarƙashin haɓar sa sannan na riƙe shi da kyau ma fara juye-juye ina daddane shi ina faɗin wai ni wai ni wai ni....... Ita kawai nake ta maimaitawa. Kafin daga bisani yayi ajiyar zuciya ya riƙe ni da kyau. Duk muka yi shiru, shiru ne da ake cewa 'comfortable silence', da yake kuma nasan yana matuƙar so idan nice na fara neman shi, sai kawai na sa hannu na riƙo haɓar shi don yo wa ƙasa da kan shi na fara kissing ɗin shi. Ya sha mun gori har ba iyaka akan kullum ni ina jin daɗi idan ya zo mun, shi ma mutum ne fa. Ranar da na gaji da gorin na gwada kuwa, irin farin cikin da yayi ya sa once in a while ina karya bille na nayi initiating moment ɗin. Make up ... bayan faɗa is always the best!

Ina zan iya bari yayi mun fushi a halin yanzu? Fushin Nu'uman azaba ne a gare ni. Babu duka babu zagi kai faɗan ma ba yayi amma azabar da zai gana maka sai ka gwammace ya zane ka a wuce wurin kawai. Tunda na gano 'mumu button' ɗin shi, shi ke nan sai na samu sauƙin abubuwa. But babban sauƙin bai wuce na gudun ɓacin ran na shi ba gabaɗaya. Kuma yawan gudun ɓacin ran na shi ya sanya shi yake mun abubuwa tamkar bawa na, don haka shi ya fi kama da mijin kan tace ba wai tace ba. Amma fa idan na sa ƙarfi na ce dole ga abinda za'a yi mun to kuwa ba zai yi ba. Lallashi ne kawai hanyar samun galaba akan shi.

Washegari ma hana ni zuwa gidan rasuwar yayi, shi ya je da rana, ya kuma sa a aka yi abinci mai yawa daga restaurant aka aika. Yace masu bana jin daɗin jiki na.

**************

A satin da na kammala jami'a ina ɗauke da ciki wata shida da satittika amma girman shi kamar ya kai wata tara, da ƙyar nake tashi idan na zauna. Ganin Nu'uman ya gaza zama wuri ɗaya saboda halin da nake ciki, kullum akan zirga-zirgar zuwa Kano duba ni yake, hakan ya sa Umma ta ɗauko mun wata mata daga Kabo, domin take kulawa da ni kafin na kammala makaranta ya ɗauko ni daga Kanon. Kuma muna gamawa ya zo ya wuce da ni Legas, a cikin main gidan su muke zaune, amma ta bayan ginin ainihin gidan an yi babban wuri mai parts uku, ɗaya daga ciki namu ne, akwai komai a ciki tunda falo, ɗakunan bacci, kitchen da komai da gida yake buƙata. Na koma dawo Lagos ɗin daidai satin bikin Jamila.

Tunda aka fara bikin, duk wurin da nayi idon Umma na biye da ni. Idan nace a ba ni aiki na taya su sai tace a'a, a samo mun kujera doguwa yanda zan zauna na kalle su kawai kuma ba zan wahala wurin tashi ba sosai. Sannan tana sa Nu'uman ya fita zagaye da ni, wai na tattaka ƙafa ta. Don haka cikin unguwar muke zagayawa kusan koyaushe ya samu dama.

Sati biyu da kammala bikin Jamila, gabaɗayan mu watau Umma, Papa, Anty da su baby, Nu'uman, Ni da Asmaa muka tafi America wurin Oba da amaryar shi. Sati ɗaya jal za mu yi mu dawo, Papa kuma daga can Egypt zai wuce wurin matarshi da su Tamim. Mu baro Jamila tana jin haushin mun tafi mun bar ta, ni da Asmaa muna tayi mata dariya.

Tun ina jirgi nake ji wata irin gajiya, duk da hira muke tayi da su Umma. Labarin zaman su a America take ba mu ita da Daddy (babansu Nu'uman), zaman ne silar zaman Oba a chan. Da ta gangaro kan yarintar Nu'uman kuma ba wanda ya kai ni dariya, su baby da suke bayan kujerun mu suna taya ni. Shi dai mammatsa mun ƙafa yake yi saboda ta fara kumburi saboda zama, bai ce komai ba, kafin daga bisani yayi mun adjusting kujerar na fara bacci.

Tun a ranar da muka isa na fara jin wani iri, dukkan mu kowa ya ɗauka jetlag ne sannan ga yanayin halin da jikina yake ciki, cikin jiki na ya shiga wata na bakwai yanzu. Ashe wasa farin girki kafin wasu awanni na fara fita daga hayyacina, bayana, mara ta kai komai nawa ciwo yake mun. Nu'uman ya kasa barin ɓangare na, a haka aka kwashe ni sai asibiti.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol