Free chapter · Read without an account

60

by Fareeda Aliyu · KOWA DA ƘADDARARSA

Makaranta littafin Kowa da Ƙaddararsa Nagode da irin ƙaunar da aka nuna mun, Allah ya yi albarka, ya bar zumunci tsakanin mu. Na sha motivation da encouragement har babu iyaka. Allah ya nuna lokacin da zan fara sabo, nasan ba za ku gaza da ba ni goyon baya ba. Nagode ƙwarai. Allah ya saka da alkhairi.

Sannan kar mu manta komai aka jarabce ka da shi saboda Allah ya san za ka iya ɗauka ne. Domin yace ba ya ɗorawa rai sai abinda za ta iya ɗauka. Haka abinda haƙuri bai ba ka ba, wallahi rashin sa ba zai taɓa ba ka ba. Sirrin shine addu'a tare da yaƙini, fawwala Allah komai da kuma haƙuri. Sannan akan kan ka learn to support your sibling, friend or family, it can go a long way. Allah ba mu ikon ɗaukar ta mu ƙaddarar ba tare da mun gaza ba. Ameen Ya Allah.

*******************


Na tashi domin bin shi banɗakin ina yi wa kaina faɗa cewa ya kamata idan akan gaskiya ta nake, na daina barin fushin Nu'uman na damu na. A kulle ƙofar take, ya kulle ta ciki. Sai na ƙyale shi kawai na zo na tattare kayan da ya zubar a nan na kai laundry basket, na ware boxers ɗin na shi ina jira ya fito daga wanka na wanke masa shi a washing machine.


Ya ɗade ƙwarai kafin ya fito daga ciki, kuma ya fito kamar yana cikin nishaɗi don har waƙa yake yi ta fi-to. Kamar yanda na sani, ba zai kalle ni ba, hakan kuma yayi. Shiryawa yayi ya fice daga ɗakin. Raina babu daɗi na wanke masa ƙaramin wandon tare da busarwa a machine ɗin. Da naga baƙin ciki yana neman kassara ni sai na kwashi ƙafafuna na tafi wurin Umma, ko ba komai hidimar yara za ta ɗauke hankali na in shaa Allah. Ina shiga na gan shi a falon, kamar ma cikin farin ciki yake sai kawai na juya na wuce ɗakin baccin Umma na haye kan gadon ta na kwanta kawai.


Ban san tsawon lokacin da na ɗauka a haka ba, da yake ɗakin da duhu sai ban kunna wuta ba nayi kwanciya ta a haka. Shigowar Umma ce ta dawo da ni cikin hayyacina. Tace "Amma kina jin Khalifa na ta kuka tun ɗazun? Kin san bai cika son madaran nan ba, ai tunda kika jiyo kukan shi yanda bai cika kuka ba ai dole da dalili. Bari a kawo shi ki ba shi nono mu gani, idan bai daina to tabbas ba shi da lafiya sai mu bazama asibiti yanzu babu ɓata lokaci." Ta fice daga ɗakin da sauri, kafin ƙofar ta ƙarasa rufewa naji tana cewa "ashe tana cikin ɗa....."


Tare da Nu'uman suka shigo ɗakin, Umma ta miƙa hannu ta karɓe Khalifa daga hannun shi ta zo waje na ta ɗoro mun shi a hannu na. Sai kuma ta janye hannun ta da sauri tana cewa "Subhanallahi! Haba Ummu. Yanzu duk muna gidan nan ki kasa cewa wani ba ki da lafiya? Kin ji zafin da jikin ki ya ɗauka kuwa?" Ban kalli kowa ba, na daɗa gyara zama na yanda zan ji daɗin ba wa Khalifa nono nace Lafiya ta ƙalau fa Umma, wannan kwanciyar da nayi ce, ƙila ma don yamma ta yi ne. 

Tace "A'a, wannan ba ɗumin jiki ba ne. Zazzaɓi ne. Bari na nemo maki paracetamol, idan bai ki ji dama-dama ba, anjima sai mu tafi asibiti. An ce maki ana dauriyar ciwo ne?" Tana mita ta fice daga ɗakin.


Nayi kamar ban san ta bar shi a ɗakin ba, ban ma ɗaga kai na kalle shi bare na san me yake yi. Shi kam Khalifa tunda ya kama nono yayi shiru sai zuƙa kawai yake yi. Ƙoƙarin gyara filo nake ta baya na domin na samu na jingina don na fara jin jiri sama-sama haka, kasancewar da yaro a hannu na sai abun yake neman yi mun wahala. Jin shi nayi kawai tsaye kusa da ni yana gyara mun pillows ɗin tare da jingina ni a jiki. Na jingina na rufe ido na, sai da naji muryar Umma tana cewa "Ba dai bacci kike a haka ba ko? Ga maganin, kawo Khalifan. Kamar ma bacci yake son yi." Na cire shi daga nonon, na sa shi kafaɗa don ya samu yayi gatsa. Ta ɗauke shi ta fice daga ɗakin tana jijjiga shi domin ya samu yayi baccin da ya fara. Maganin da ta ajiye mun a gefen gado da robar ruwa mara sanyi na sha, sannan na zame na kwanta, jiki na gabaɗaya yayi la'asar.


Ban daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗauke ni amma sai tsananin sanyi ya farkar da ni, a take zazzafan zazzaɓi ya lulluɓe ni. Ba zan ma iya tashi ba, bare naje na samu su Mama a falo. Waya ta kuma ina hango ta a chaji da na saka ɗazun, ita ma ba zan iya ƙarasawa na ɗauko ba.


Cikin ikon Allah sai ga Nu'uman ya shigo zai ɗauki abu a gaban madubin Umma. Cike da rashin ƙarfi nace don Allah ka kira mun Umma. Ya dakata da tafiya, don har ya ɗauki abinda zai ɗauka ya juya zai fice, sai juyo ya dawo wurin da nake kwance yana kallo na. Sai ya sa hannun shi ya dafa goshi na, da saurin gaske ya zame hannun yana cewa "Ya Salam." Sai kuma ya fara tarairayo ni yana cewa "tashi mu tafi asibiti, You are burning up!" 

Cikin murya mara amo nace ba yanzu ba, sanyi nake ji. Don Allah ka ɗauko mun bargon Umma na rufa. Jiki na zuwa lokacin ya fara karkarwa. Ya janyo duvet ɗin Umma ya lulluɓeni sannan ya fita, babu daɗewa suka dawo tare da Umma da Mama. Da ƙyar suka haƙura sai zuwa bayan isha sai mu tafi asibitin, sun bar ni a kwance akan na samu nayi bacci ko yaya ne yanzu.


Kusa da ni ya dawo ya zauna, ni ina cikin duvet ɗin shi kuma yana saman shi ta ɗayan ɓangare na. Da ya gama kiran waya akan cewa ba zai samu zuwa ba yanzu ba, sai ya kwanta a wurin da yake zaunen. Har bacci ya fara ɗauka ta sai naji alamar yayi magana, na buɗe ido na, sai na gan shi ya kwanta a gefen shi, ya kafe gwiwar hannun shi tare da tallabo kan shi a tafin hannunsa yana kallo na. Sai na ƙara mayar da ido na zan rufe sai na ji yace "Gaskiya mata kun ji daɗin ku, drama upon drama. Ke ce fa kika yi mun laifi, amma ke ce mai yin zazzaɓi. Watau an dake ni kuma shine za'a hana ni kuka. Ni nace maki ba ni halin ɗaukan yara ko nawa kika haifar mun ne? A je ma bani da shi, ai ko Asmaa da take ƙarama muddin tana raye za ta iya ɗaukar nauyin su balle ga Oba ga Papa."


Na mirgina tare da juya masa baya na fara hawaye, watau ba ni da lafiya amma baya tausayi na ko? Sai naji ya matso kusa da ni sosai, ya haɗe bayana da ƙirjinsa a salon kwanciyar 'spoon', ya sa hannun sa ya ƙara ja na jikin sa sosai yace "Yi haƙuri Kulsum, ba zan ƙara ba. Shikenan ko? Bar kukan to." Hakan sai ya zama kamar ya ƙara kunno mun kukan. A tsakanin wannan rarrashin zuwa baccin da muka yi tare, a nan na rasa zazzaɓin. Kenan da gaske fushinsa ne ya jawo mun haka? Oh ni Ummu.

**********

Satin da muka koma Kano gabaɗaya har Umma, na iske ɗakin yara an shake shi da kaya kuma duka aikin Oba ne, shi yayi shipping kayan daga can zuwa nan. Da na kira shi godiya ma cewa yayi kar na manta zancen lambu da muka yi, da zarar na nutsu na kira shi da shawarar da na yanke.


Batun suna kam Nu'uman ya dage ba za'a yi ba, Umma kuma tace sunan ne zai rage yawan zuwan mutane barka. Gara kawai a zo a lokaci guda a gan su ko zan dinga samun hutun da ya kamata. Ya yarda amma da sharaɗin ba za'a bari a yi ta ɗaukan su ba. Ƙarshe dai a hall aka je aka yi taron sunan, sai wani cin magani yake. Ni dai kawai lallaɓa shi nake yi, so nake a ƙare lafiya mu rabu da kowa lafiya.

*****************


Jarabawar mu ta fito, kuma alhamdulillah da first class na kammala, an ma yi mun tayin lecturing idan mun kammala service amma da sharaɗin fara masters immediately, sai dai Nu'uman yace gaskiya ba yanzu ba tukunna, gara na fara masters ɗin, daga baya bayan na yaye yara sai a san me za'a yi. 


Na fara bautar ƙasa a nan cikin gari, makarantar polytechnic aka kai ni. Kuma akan ɓangaren harkar lambu na, online classes na biya na shiga. Karatun ba ƙaramin ganewa nake yi ba, ina yin classes ɗin muna magana da Oba. Oba is my go-to in dai akan kan shawarar business ce, ba ya lanƙwasa magana, yana faɗar abu a yanda yake.


Ranar da na kammala classes ɗin i'm more than ready to start. Tare da Nu'uman da Papa muka je gonar. Daskarewa nayi saboda girman ta da na gani, amma shine Oba yake cewa wai tana da girma babu laifi? A take na yi masa waya ta FaceTime, yana ɗauka nace haba my motivational speaker Oba! Ka ga girman wurin nan kuwa? Ta ina zan fara? Na taho da ƙwarin gwiwa amma ina ganin girman gurin nan naji inaaaaaa.


Ya fara dariyar rikicewar da nayi sannan yace "Heyyyyyyyy, listen, shhhhhh. Kina ji ko? Ai ba wai gabaɗaya za ki yi yanzu ba. Ba gwaji za'a fara ba? Ɗan wurin kaɗan za'a yi setting maki greenhouse ɗin, idan kin yi nasara a shukan farko sai a fara ƙara yawan space ɗin." Na katse shi da sauri, idan ban yi nasarar ba fa. Ya amsa "sai a zauna a duba menene ba ki yi daidai ba, sai a gyara a sake gwada wa. Kuma Papa ya samo mana supervisor, ƙwararre ne ta ɓangaren, zai dinga zuwa kuna haɗuwa har sai kin gama fahimtar komai, an yi first harvest sannan sai mu sake shi."


Wani daɗi ya rufe ni, watau ni 'yar gata ce. Lokacin da nake tasowa sai Allah ya ba ni yayye masu tsayuwa akan matsala ta a kodayaushe, ba sa taɓa gajiya. Yanzu kuma sai aka bani another set of brothers in my in-laws. Alhamdulillah ya Rabb. Dole na gode wa ni'imomin ka Ya Allah.


Bayan Baaba wadda aka ɗauko mun daga Kabo lokacin da nake da ciki, ta dawo bayan dawowar mu Kano. Sai aka ƙaro wasu masu aiki har guda biyu domin taya ni raino. Ga shi daga Mama har Umma kusan koyaushe a tafe suke su zo su ga yaran.


Ba abu ba ne ɓoyayye cewa Nu'uman ya fi son Adawiyya. Daga nace yana nuna son kai sai yace ai ita ce mace, sannan tafi 'yan'uwan ta rigima nesa ba kusa ba. Yana da wata ƙa'ida, in dai ya dawo gida dole a bar komai a saurare shi, ko da kuwa hidimar yaran ce. Idan ya dawo ban baro su ba, ranar irin fushin da za'a yi mun sai ta Allah. Amma don son kai, yana shigowa zai ɗauko Adawiyya, sai dai idan da wani dalili babba ne zai haƙura da ita sai daga baya. Gabaɗaya ta ma saba, in dai yana gida, wannan ɗan zaman nan da muke a tare kujera ɗaya, ko kuma na kwanta a jikin sa sai ta fara kuka sai na ɗaga mata baban ta. Yanzu shekarar su biyu da ɗan watanni.


Cikin wannan yanayi ne na samu sabon ciki, sannan ya zo mun da salo irin wanda ba abinda nake so irin na gan ni kwance jikin Nu'uman. Sai a lokacin na lura da irin fili na da Adawiyya take hayewa. 


A wannan yanayin nawa na mai ƙaramin ciki bikin Asmaa ya kama. A kano aka yi bikin. Ranar yini na gudo daga gidan bikin na dawo gida don na huta, kuma da ƙarin cewa nasan Nu'uman na gida. Khalifa da Deen suna can gidan Mama, sun bi ta ɗazun da ta zo gidan yinin, da wuri ta koma gida saboda Hassana na jego a gida. Ita kam sai yanzu Allah ya kawo mata haihuwar. Nasan kuma Adawiyya na tare da su Ihsan (ƙanwar baby, 'ya'yan Anty).


Wankan na fara yi sannan na saka rigar da zan sha iska na dawo falo wurin da yake zaune, na haye jikin shi na kwanta. Gyara zaman sa yayi tare da gyara mun kwanciyar yanda zan ji daɗi, sannan ya fara daddana mun jiki yana cewa "sai da nace ki yi zaman ki kika ƙi, su 'yan sarauta bikin su baya ƙarewa (mijin Asmaa yake nufi), kalli irin gajiyar da kika yi." Ƙara gyara kwanciya ta kawai nake yi, na samu abinda nake so kuma nake nema a daidai wannan lokacin. Ban daɗe ba sai kawai na ga Adawiyya ta fito daga ɗakin sa ta doso mu tana kiran sunan shi 'Daada', cikin mamaki na kalle shi nace au ɗauko ta kayi daga wurin su Ihsan ɗin? 


Ya miƙa hannu ya ɗauko ta zuwa kafaɗar shi yana cewa "To ta yaya za'a bar wa su Ihsan ita? Kan su na rawa hankalin su na wurin kiɗa, ai sai su manta da ita. Kuma ba ni nace su bani ita ba, tana gani na ta sa masu kuka..." Bai ƙarasa ba ta sa ƙafar ta tana ture ni tana kuka tana ihun "tashiiiiiiiiiiii".


Sai ya fara ƙoƙarin janye jikin sa daga gare ni yana cewa "bari na samu tayi bacci, idon ta ma duk baccin ne."


Na miƙe cikin ɓacin rai nace yanzu kana nufin sai abin da take so za'a yi? 

Ya yi sauri magana "Haba Ummu, wannan yarinyar me ta sani? A hankali duk za ta bari fa."

Na ƙara fusata nace haka kullum kake faɗa, amma ni ban ga wani abu da yake raguwa ba. Hatta brothers ɗin ta ba ta bari su kusance ka fa, suna zuwa sai ta fara kuka. Komai daga tayi kuka sai a yi mata? Wannan ba salon ɓata yaro ba ne? Khalifa yana da ƙulafucin uwa, saboda gudun ɓacin ran ka in dai kana gida haka na kai shi wurin su Baaba da masu rainon su, amma komai akan Adawiyya naka daban ne. Allah ya sani enough is enough. Yanzu ma miƙa ta za kayi wurin su Baaba, ai suna ciki, sai a goya ta tayi bacci.

Ya ɗaure fuska "Kin ga....dakata mana. Ba fa zai yiyu ki dinga ba ni command kamar wani Deen ko Khalifa ba...."


Ban tsaya sauraron shi ba, na tashi a fusace na wuce ɗaki na na zumbula hijab har ƙasa na ɗauki purse ɗina da waya ta na fito. Idan na tsaya muna cigaba da magana da shi akan wannan abun, rayuka ne zasu ɓaci. Gidan bikin na koma, amma sai na shige ɗakin Umma na side ɗin baban su marigayi, babu kowa a ciki. Da ta shigo ɗaukar abu ma ta gan ni cewa tayi "Gara da kika gudo nan ki huta ai, ki daina biyewa su Jamila."


Har dare ban koma gidana ba, a nan nayi bacci. Da safe ma da aka tafi kai amarya gidan ta a Bauchi ban bi su ba, Umma ce ta hana. Waya ta kuma duka kiran da Nu'uman yayi mun ba wanda ba'a kan ido na kiran ya shigo ba, amma ban ɗauka ba. Ni dai ban san ko yaji nayi ba, amma in dai na koma gidan to tabbas na huce gabaɗaya ne.


Da azahar ma ina jin su da su Umma da ragowar mutanen da suka yi saura a gidan. Ina jin ya ɗauka na bi 'yan kai amaryar ne, sai da ya ji Umma tana cewa a zo a kai mu fruit yogo, ni ce nace shi nake sha'awa shine ta aika aka siyo fruits ɗin aka yi mun, don sam na kasa cin komai tunda na tashi yau. Shine ma ya karɓa yace bari ya miƙa mun kawai.


Da ya shigo ma na kalle su shi da 'yar sa, ban ce uffan ba, hannu na kawai na miƙa na amshi bowl ɗin hannun shi ma fara sha, don tuni yunwa ta ci ƙarfi na. Yace "Ina wayar ki?" Na nuna mashi wurin da take da ɗan yatsa na. Ya cigaba da magana "Ki na ganin kira na kika ƙi ɗauka?" Nayi masa shiru.

Ya ce "Sai ki tashi mu tafi. An gama biki kuma kowa tafiya yake yi, ga wasu can ma Malam Sa'adu zai mayar da su a falo duk sun fiddo kayan komawa." Nayi banza da shi. Yana daga tsaye yana ƙare mun kallo, ita kuma Adawiyya tana ƙoƙarin ya sauke ta ƙasa ta zo ta sha abinda nake sha, ya matso ya sauke ta kusa da ni sai kawai na tashi da bowl ɗin a hannu na na fara ƙoƙarin barin masu ɗakin. Cikin hanzari ya riƙo gwiwar hannu na yace "ina kike niyyar zuwa? Ba ki ga ta fara kuka ba? Yogo ɗin take so."


Ban san lokacin da na galla masa harara ba nace ai ba baban ta ba ne ya siyo bare a ƙafa mun ƙa'ida. Ni fa ka ɗauki 'yar ka ku tafi, na zo nan ne saboda bana son tashin hankali.


Ya juyo da ni da sauri "What? Me kike nufi?" Na amsa da murya ƙasa-ƙasa nace ko ma mene ya zo ranka. Adawiyya ta kara fashewa da kuka ganin kaman muna faɗa tana kuma miƙa hannu ya ɗauke ta, na juyo na daka mata tsawa "Dallah malama rufe mana baki. Mts!" A take ta ƙame saboda ba ta saba da haka ba, sai kuma ta saki wani irin ihu da kuka na gigicewa. Shine abinda ya jawo hankalin Umma zuwa ɗakin. Ta gama raka baƙin ta sun shiga mota, ta dawo ciki shine ta jiyo ƙarar.


Ta shigo ta ga har ya ɗauke ta ya saba a kafaɗa yana girgiza ta na lallashi. Da Umma ta tambayi me aka yi mata, buɗar bakin shi sai cewa yayi "Wallahi Umma, Kulsum ce. Na rasa dalili, ta tsani Adawiyya...."

Umma ta katse shi "Auzubillahi! Kar ka kuma faɗar haka, ai babu uwar da take tsanar ɗan da ta haifa." Ta juya ɓangaren da nake tsaye tace "Ummu me ya faru?" Kawai na fashe da kuka na hau yi mata bayani, komai a gidan mu idan Adawiyya ba ta so, to ba za'a yi ba. Idan ana taƙamar cewa yarinya ce su 'yan'uwan ta fa? Ina ce lokaci ɗaya aka haife su? Wannan wariyar yana tunanin za ta haifar da ɗa mai ido ne? Ni ban hana ya nuna mata so ba, amma ya dinga kwaɓar ta, idan ba haka ba sai ta tashi a sangarce. Kuma ni zai bari da aiki tunda ba shine yake tare da su kodayaushe ba. Kuka nake har da su face hanci. Umma tayi masa faɗa sosai sannan ta koma nasiha da ba shi misalai. Sai kuma a ƙarshe dukkan mu ta ba mu haƙuri ta kuma ce na tashi na koma gida na. Har wannan lokacin zuciya ta tafasa take ban sauka ba. Nasan ma har laifin hormones.


Tunda muka koma gidan mu na shiga ɗaki na na rufe, ban ƙara ko leƙowa ba. Dama da za mu taho Umma ta haɗo ni da fruit yogo a babban roba, tace naje nayi ta sha. Shi yasa ban ƙara fitowa waje ba. Sannan na sa a raina dole na zama jaruma, jikin na shi na bar wa Adawiyya, sai su ƙarata chan.


Washegari ma a cikin gidan nan ko ya mun magana, uh ko um-um ce take raba mu, idan kuwa amsar maganar ta kalmomi ce to ba zan amsa ba. Yana zama kusa da ni nake tashi. Da naga bana jin daɗin gidan sai na wuce gida wurin su Mama. Sai da naje gida sannan nayi masa text cewar naje duba Hassana, zan kuma ɗauko su Deen.


Muna cikin ɗaki muna ta hayaniya ni da su Hussein, wai zaɓar gudunmawar da zan bashi a auren sa yake yi, ni kuma ina cewa ban taɓa ganin wurin da wanda za'a ba wa abu yake zaɓa ba. Shi kuma ya dage wai yanzu ni fa mai kuɗi ce, ko da gona ta kaɗai aka bar ni ai an san na haɓaka, balle yanzu Ummu's kitchen har ma da branches. Muna cikin hayaniyar nan sai ga Najwa ta shigo wai na zo Mama na kira na.


Tare da Nu'uman na gansu. Na kuwa ɗaure fuska, don da na shigo dariyar maganar Hussein nake yi. Mama tace "Ummu ni da ɗa na Nu'uman muna neman afuwar laifin da muka yi maki..."

Na katse ta, to Mama ai abun ne.....

Ta katse ni "Shi ma nace masa ba na son naji komai, ke ma ba sai kin faɗa mun ba. The most important thing a nan shine an san an yi laifi kuma an nemi afuwa. Idan na isa ki yi mun alfarma ai zan gani daga yanzu ko kuwa? Yanzu ai kin girma ba sai nayi faɗa za kiyi abu ba, ko?" 

Nace shikenan Mama. Ya wuce.

*****************


'yan uku shekarar su uku cif na haifi 'yan biyu mace da namiji. Har Yaya Muntari na tsokana ta "Ummu so kike yi ki wuce mu yawan yara ne?" Dariya kawai nayi.


Kuma babu daɗewa da haihuwar na kammala masters ɗina, kuma kamar koyaushe da first class ɗin shi ma. PhD nake shirin yi, kuma Oba yace na taho can nayi zai ɗauki nauyin komai. Ban dai san Yaya za ta kaya da Nu'uman ba, saboda shi yanzu ya ƙi jinin ya ji mun yi nisa da shi. Ya ma fara dagiyar na zauna a BUK ɗin na yi kawai, shi kuma Oba yace idan naje can sai na fi saurin kammalawa kuma at least zan samu different experiences da irin karatun mu na gida da muka saba. Amma yanzu kam na ci ɗa marar in shaa Allah sai an kira ni da Dr. Ummu Kulsum Aminu kafin idan da rai na koma Professor Ummu Kulsum Aminu don ina shirin karɓar lecturing ɗin nan da zarar na kammala PhD na dawo. Ba zama na saci ɗan ɓarawo.


Goyon baya da soyayya tare da tattali irin na mijina uban 'ya'ya na, Nu'uman, shi ne yake ba ni kuzari da ƙwarin gwiwa ba tare da fargaba ba. Sannan ga support daga family ɗina da in-laws ɗina a kodayaushe. 


Lallai kam! Kowa da Ƙaddararsa!

Tammat bi hamdulillah.

Faddabanan ce!




Mu haɗu a littafina na gaba BA NI DA MASANIYA and it's going to be a paid book.


Idan ka karanta liitafin nan ko page ɗaya ne yayi maka daɗi, don Allah a taimaka da yi wa 'yar'uwa ta addu'ar Allah ya jiƙanta da Rahma😭😭😭. Next month February za ta cika shekara ɗaya da barin mu. Allah ya jiƙan ki SADIYA UMAR ALIYU, Allah ka haskaka ƙabarin ta, ka sanya ya zamo daga dausayin aljanna ne. Ameen ya Rabb.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol