Free chapter · Read without an account
Na ashirin da biyu
ƘADDARATA CE A HAKA
©Maryam Abdulaziz
Maiƙosai(Matar Abdul)
P 22.
Farinciki ahlin suke ta kwasa. Yayin da a ɓari guda dangin Idris suka shiga kwasar takaici na abin da suka aikatawa danginsu Nuriyya.
***
Satittika na ta shuɗewa yayin da watanni ke rufawa. Yanzu kowa cikin farinciki yake. Sun sake zama abu guda tsakaninsu.
A gefe guda kuma soyayya mai ƙarfi ce ta ɓalle tsakanin Munira da Ahmad. Nuriyya kuwa babu abin da take yi musu sai tsokana.
***
Zaune suke a fatfajiyar falonsu, gaba ɗaya cikin takaici da baƙincikin abin da suka aikata suke yi. Mahaifin idiris babu abin da yake sai takaici da baƙinciki, tare da tunanin da wane ido zai kalli baffan Nuriyya har ya yi masa magana.
"Ina ga daddy mu tattara muje har gidan nasu mu ba su haƙuri" faɗin idris.
"Haka za a yi kam alhaji domin ba a bori da sanyin jiki" cewar hajiyar idris.
Shawarar da suka yanke ke nan, tare da nufin cire rana suje su ba su haƙuri.
Zaune yake bayan motarsa, abubuwa da dama sun dagule masa, yanzu aikin da yake tutiya da shi ma an kore shi saboda ya gaza baya yi musu yadda suke so. Tabbas ya sani alhakin Nuriyya ne ke binsa. Ba zai taɓa mantawa ba da sharrin da suka ƙulla mata shi da Nusaiba , wanda suka ɗauki hotan fuskarta suka ɗora akan wata sura tsirara, suka turawa Nasir, idan ba zai manta ba ranar sai da ya ji Nusaiba ta ce masa Nuriyya a gidansu ta kwana ba gidan Nasir ba, wanda kwananta biyu kafin da dawo gidan Nasir ɗin. Tabbas ya zalunceta zalunci mafi muni dole ya je ya ba ta haƙuri ya nami yafiyarta ita da Nasir ɗin.
Tamkar a mafarki ya ji murya Nusaiba na ratsa magudanar jinsa. A wani irin yauƙi ya kai dubansa gareta kana ya ce.
"Ina so ki yada makaman yaƙinki ki tuba ki koma ga Allah! Kuma a shirye nake da na tonawa kanmu asiri akan abin da muka aikata musu, zan je na nemi yafiyarsu ko Allah ya dube ni da idanun rahma."
Jikinta a matuƙar sanyaye take duban shi tamakr wacca aka yi wa dukan tsiya.
"Tabbas na gane kuskurena, domin a jiyan nan naga iftila'i kala-kala, na yi mafarki wai gani an shigar da ni wuta tare da wata sarƙa mai kauri wacca aka ɗaure ni da ita, na yi na yi na kwance kaina na kasa, wannan kaɗai ya sake tsorarta da ni, tabbas a shirye nake ni ma na je na bawa Nuriyya haƙuri na kuma nemi yafiyarta."
"Alhamdulillah! Da har ya sa mu ka dawo kan tafarki na gaskiya."
***
Yau gidansu Nuriyya dangin Idris suka yi masa tsinke, cikin ikon Alllah sai ga shi Nuriyyan ma tana gida, ta zo gaida iyayen nata.
Sun ga karamci iya karamci tamakr babu wani abu da ya haɗsu na tarzoma wanda har sai da ya saka su zubar da hawaye sosai.
Alhaji ne ya soma magana da ƙyar. "Haƙiƙanin gaskiya mun ga jarrabawa sosai saboda abin da muka aikata muku, a yanzu ga mu gurfane gabanku ku dubi girman zatin Allah ku yi mana afuwa." ya ƙarasa murya a rauna ne.
"Mu ba ku yi mana komai ba, domin ba mu riƙe ku da komai ba. Duk abin da ya faru daga Allah kuma mun karɓa ga shi a yanzu ya wanke mu, Allah ya yafe mana baki ɗaya" cewar Inna.
Yayin da gwaggo, Nuriyya da Baffa suma duk suka nuna babu komai. Sun ji daɗi sosai kafin su yi sallama da su, su wuce gida.
***
Cikin ikon Allah yau watansu Nasir da Nuriyya huɗu da tarewa, an saka ranar Munira da Ahmad nan da wata biyu masu zuwa idan Allah ya kaimu.
Yau alhamis Nuriyya ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazzaɓi wanda har sai da ya dangana su ga asibiti. Bayan dubata da likita ya yi da 'yan tambayoyin da ya mata haɗi da gwajin juna biyu ya tabbata tana ɗauke da juna biyu na sati takwas wato wata biyu. Murna wajen Nasir kuwa ba a cewa komai. Ji yake kamar ya haɗiye Nuriyya ya mayar da ita cikinsa.
Kullum idan suka zauna babu hirar da suke yi sai sunan da za a sakawa babyn idan ya zo. Nuriyya kuwa ta yi ta masa dariya.
Sannu-sannu sai ga shi an shafe wata biyu, bikinsu Munira ya matso sosai aka shiri, Nuriyya kuwa tamakr babu cikin wata huɗu jikinta haka take gudanar da al'amuranta. Wanda har sai da ta kwanta ta ɗan yi jinyar kwana biyu.
Nasir kuwa ya so hanata sabgar bikin amma ta saka masa kuka wiwi, yayin da gefe guda Ummi ta ce ya barta kawai dai ta kula da kanta. Ai kuwa ta ji daɗi sosai.
Biki ya yi biki kasancewar an haɗa bikin da na Hamza wanda ya fito da sahibarsa wacca zai aura, ganin tazarar babu yawa ya sa kawai aka haɗe bikin tare tare da amaryarsa Maryam(mami). Munira aka fara kaiwa gidanta, kana aka miƙa Maryam ita ma na ta ɗakin.
***
Nuriyya zaune a falo ta yi ɗaiɗai da ita, sai faman gwaigwayar goruba take yi, yayin da gefe guda kuma bayanta ke amasawa amma tamkar tsohowar mayya taƙi yarda gurobar.
Cikin shirin haɗaɗɗiyar shadda wacca ta sake bayyana kyahunsa ya shigo falon bakinsa ɗauke da yalwatacciyar fara'a. Cike da tsokana ya shiga tsokanarta da duk ta yi muni, hancinta ya sake bajewa tamkar faifai.
Haɗe fuska ta yi ta sha mur tamkar damammiyar fura, kafin ta mayar masa da raddin.
"Ai dai duk abin mutum na fi shi kyau dai eh!"
"Wannan gaskiyar babyna ce. Kin ga mai da wuƙar ni ma tsokanarki na ke yi, inda sabo ya ci a ce ki saba ai wai an zunguri mai ciki"
Ai kuwa ta sake haɗe fuskar.
"Ai ba dai na kusa haihuwa ba in sha Allahu sai ummi tazo ta tafi da ni." ta ce tana murguɗa masa baki.
"Cab! Lallai ma yarinya ai kuwa ki sauya tunanin tun da wuri don babu inda za ki wani wanka kina gidan sahibinki Nasir."
"Ai kuwa sai na tafi, tunda dai ta hanaka tsokanata kai kuma kaƙi. Bari ma ka ga na je na sanar mata." ta ƙarasa tana mai miƙewa tsaye da ƙyar.
"Yauwa. Ɗan yi sauri kada ƙuda ya rigaki" faɗin Nasir.
Ai kuwa ta koma ta zauna tana sakin kukan kissa da kisisina.
Haka rayuwa ke ta tafiya wajen masoyan yau da daɗi gobe babu, kasancewa rayuwar dole haka take, ba kullum ake kwana akan gado ba. Cikin Nuriyya ya shiga wata tara har da sati guda.
Yau ta tashi da wani irin matsanancin ciwon baya, yayin da mararta ke murɗawa tamkar injin markaɗe.
Ganin halin da take ciki ne kasancewar yau babu aiki yana gida ya saka shi kinkimarta zuwa asibiti, yana zuwa aka amshesu, nan ya ciro waya ya kira ummi ya sanar a ita abin da ke faruwa, kana ya kira gidansu Nuriyya suma ya sanar da su abin da ke wakana.
Ba su jima da zuwa ba Allah ya sauketa lafiya, inda ta santalo 'yan biyu duk maza gwanin sha'awa. Murna kuwa ba a magana wajen ahlin ganin yadda Allah ya yi musu wannan kyautar ba tare da sun biya shi da komai ba. Kwananta guda aka salllameta, nan fa ummi ta ce za ta wuce da ita gida har sai ta yi arba'in. Zo ku ga Nasir yadda ya yi fificin-fifcin sai faman ƙunƙuni yake yi, ita kuwa Nuriyya gwalo kawai take yi masa.
Har gidan su Nasir idris yaje ya yi wa Nuriyya barka tare da sake roƙonta afuwa akan laifin da ya yi mata, ta kuma yafe masa. Nusaiba ma taje ta sake neman afuwarta. Gefe guda kuma soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin Nusaiba da Idris, inda magana ta kai gaban manya aka tsayar da rana shekara mai kamawa.
Ranar suna yara suka ci sunan mahaifan Nasir da Nuriyya, sai dai ana ce musu Hassan da Hussain. Kwanan Nuriyya takalin da biyu cif a gidan Ummi, inda ummi ta sake zage damtse tana gyara ɗiyarta ta don yadda taga Nasir ɗin babu wasa.
Kamar yadda Ummi ta ce sai Nuriyya ta yi kwana arba'in ai kuwa sai da ta yi sannan ta shiryata ta mayar da ita gidanta. Bayan mako guda kuma Nuriyya ta cale zuwa gidansu, kwananta goma ta dawo. Saban shafin soyayya aka buɗe a gidan ma'aurtan.
***
A kwana a tashi yau shekara huɗu da haihuwar su Hassan. Alamu suka fara bayya ga Nuriyya wanda ta soma hasashen tabbas tana ɗauke da wani cikin, babu shiri ta ziyarci likita gwajin farko ciki ya bayyana inda aka yi mata scaninig don ganin kwananinsa, wanda ya nuna wata uku har da sati.
Rainon cikinta take yi ita da sahibinta Nasir, kwanci ta shi babu wuya a wajen Allah sai ga shi cikinta ya cika wata tara cif. Lokacin da naƙuda ta taso mata asibiti suka garzaya sai dai wannan karan ta sha wahala kafin ta haihu don har an soma tunanin yi mata aiki, sai kuma Allah ya sauketa lafiya inda ta sintilo kyakkyawar yarinta gwanin sha'awa.
Ranar suna yarinya ta ci sunan Suhaima ƙwanwar Nuriyya wanda Nuriyyan ce ta roƙe alfarmar haka wajan Nasir, shi kuma ya yi amanna ya sakawa yarinyar sunan.
Bayan Nuriyya ta yi wata huɗu da haihuwa Allah ya azaurta matar hadi da samun ita ma nata rabon, inda ta sintulo baby boy.
Shekara guda, tamkar haɗin baki sai ga Munira da Nusaiba sun haihu yayin da Munira ta haifi ɗiya mace, Nusaiba ma haka. Inda Idris ya saka sunan Nuriyya ga 'yarsa yayin da ɗiyar Munira aka saka mata Fatima ana ce da ita 'Zuhra'.
Tana kicin tana hada-hadar haɗa musu abin da za su sanya a cikinsu ya shigo. Rungumota ya yi ta baya yana faɗin. "Sannu babyna du kin ga ji ko?"
Murmushi ta yi tana sake jin ƙaunarsa cikin zuciyarta kafin ta ce. "A kanka ba zan taɓa gajiyawa ba."
Sumba ya kai mata kan kuncinta kafin ya ce. "Allah ko, ki ce ni ɗan gata ne."
Far ta yi da idanuwanta kafin ta ce. "Sosai ma, kai da ba ka sani ba? To bari ka ji kai ɗan gata ne gatan ma da ba a san adadinsa ba."
Wani daɗi ya ji ya ƙume zuciyarsa, ya ɗan ja karan hancinta kafin ya kai ga cewa. "Tabbas na yi sa'a da samun mace ta gari, duk da cewa na sha gwagwarmaya kamar zan mutu akanta. Sai dai na ɗau hakan a matsayin ƙaddara domin kowane bawa da irin ƙaddararsa to ni tawa ce tazo mini a haka, kuma alhamdulillah! Sai ga shi na cinyeta, yau ga shi ina tare da farincikin raina, muradin zuciyata."
Wata ƙwalla ce ta kawo mata tunawa da irin jarrabawoyin da suka tsallake, tabbas ƙaddararsu ce a haka, ga shi kuma ta haɗa su sun zama abu guda.
Ganin tana neman ɓarke masa da kuka ya saka shi saurin furta. "Yaushe ne za a samawa Suhaima ƙanwa ne, so nake ki sake haifar mana 'yan tagwaye, ina so ki yi ta haifa mini yara ki cika mini gida da yara domin ina son abin da zai fito daga tsatsonki, ni in ta ni ne ma a haifo mini 'yan biyar." ya ƙarasa yana ɗan sakin murmushin dariya.
Ta shagwaɓe fuska tare da furta. "Biyar kuma haba dai?"
"To uku" ya ba ta amsa yana dariya.
Fahimtar tsokanarta yake yi ya sakata waskewa gami da furta.
"Shi ke nan duk sanda ka shirya, ni ma a shirye nake."
"Haka kika ce?" Ta gyaɗa masa kai alamar i.
Tuni ya miƙa dogwayen hannyensa biyu ya sunkuceta, tana wutsil-wutsik amma ina sai da ya direta kan gado yana kai mata cakulkuli a gefen cikinta. Dariya ta shiga ƙyaƙyatawa kafin ta yaki ce da ƙyar ta fice daga ɗakin.
Sai da ta kwashi kimanin mintina talatin kafin ta dawo, sanye da wata riga shara-shara babu maraba da babu kaya a jikinta, kowane lungu da saƙo na jikinta ƙamshi yake yi, Nasir kuwa tuni ya ruɗe har bai san sanda ya sunkuceta ya direta a kan gado ya soma sarrafata ta ko'ina.
Alhamdulilla! Abin da na yi daidai Allah ka karɓa, ka sa ya zamo gyara ga al'umma, wanda na yi kuskure daga gareni ne Allah ka yi mini afuwa.
Note: Ayi haƙuri ba haka na so labarin ya yi saurin tsinkewa ba, saboda ido da nake fama da shi ya sa na gajar ce shi, na gode da bibiyata da kuka yi har na yi nasarar kammala muku shi.
Taku real mai ƙosai.