Free chapter · Read without an account
Ilimin Boko
*HAFSATUL KIRAM*
©Mai ƙosai
Babi Na 19-20
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar mana, yau da daɗi gobe babu daɗi. Tun da, daman ai ba kullum ake kwana akan gado ba.
Da daɗi da babu daɗi, na shafe kimanin sati biyu ina kwance ina jinyar jikina. Sai dai babu laifi Alhamdulilla! Jikin nawa da sauƙe sosai kam. Har lokacin ina gidan kaka ban koma gida ba, tun da babu damar komawa, uwa uba tsoro ma nake ji yadda idan na warke zan koma gidan na ci gaba da rayuwa da Inna a gidan. Kullum Dije sai ta zo ta taya ni hira ta ɗebe mini kewa, haka yana saka ni cikin nishaɗi.
Sakanni, awanni, tare da kwanaki na wuce wa, yayin da sati ke bayar da baya. Na cika wata biyu cif! Ina jinya. Alhamdulilla! Na warke tas da ni.
Kowa murna yake yi, kasancewar yaya Lawan, babban ɗan baba Iro ya dawo. Wanda yake karatu a cikin gari, ya kanzo hutu jefi-jefi.
Kaka ta taɓa shaida mini cewa, 'Rana ɗaya da babana aka yi bikinsa da baba Iro. Sai dai matar baba Iro ta haifi yara har biyu, yaya Lawan da kuma Dije, kafin Allah ya bawa Innata ni. Lokacin da samuwar cikina ya bayyana kowa ya yi murna ciki kuwa har da ita kanta Innar tawa. Kasancewar iyayenta duka ba sa raye, kuma bata da kowa. Domin iyayenta zuwo ne, sunzo ƙauyenmu a matsayin 'yan gudun hijira.
Inna ta taso hannun kaka, saboda lokacin da iyayenta suka rasu ta sanadin gobarar da ta kama gidansu, sai aka rasa mai ɗaukarta, har dagaci ya ce yana so zai riƙeta sai babansu babana ya amsheta.
Nan ta taso tare da su baba, shaƙuwa sosai ta shiga tsakaninsu, wanda har takai Inna ta bayyana soyayyarta ga baba, ba tare da ya juyawa muradinta baya ba ya amsa aka yi aurensu. Bayan aurensu da kwana biyu mahaifinsu baba ya yi wa duniyar sallama, sakamakon ciwon cikin da ya shafe kwana biyu yana yinsa.
Baba yana da ilimi daidai gwargwado, kasancewarsa mutum mai neman ilimin addini duk nisansa. Takanas yakan wanke ƙafafuwa ya shiga cikin gari ya nemi malamai su warware masa abin da ya shige masa duhu. Wani lokacin kuma rediyo ita ce hanya ta biyu da yake samun tarurrukan ilimi.
Tun ina da shekaru shida ya soma jiƙani da ilimi, shekarata goma na sauke alƙur'ani tare da haddace shi.
Sai ya kasance tun zuwan yaya Lawan nake ta sintiri a gidan baba Iro, kasancewar sa mutum mai son karatu. Kullum na je yakan sanar da ni wasu ilimin na zamani.
Nakan yi mamaki yadda yake sarrafa harshensa idan yana turanci, ba za ka taɓa rantsewa cewa shi ɗin ɗan ƙauye ne ba.
Yau ma kamar kullum, ina gefensa a zaune. Ya tasa wasu litattafai gabansa.
"Uhm! Kai kam yaya baka gajiya da karatu kamar wani alhuda-huda"
Ya murmusa kafin ya ce,
"Ina na ga ta zama, ina so ne na yanke duhun da ke lulluɓe akaina da na ƙannena."
"Cab! Da karatun yahudancin da yake haramun?" Na ce ina taɓe baki.
"Waya ce miki karatun yahudanci haramun ne?"
"To ba ance sune suka kawo shi ba, kuma duk abin da suka kawo ai abin ƙi ne, tun da su ba musulmai ba ne."
"E! Tabbas su suka kawo shi, domin kamar yadda kowane ilimi ke da tushe haka shi ma ilimin bokon ke da tushensa. Turawan ƙasar ingila sune suka kawo mana boko. Yayin da suka fara ƙaddamar da tsarin ilimin boko a sashen kudancin Nijeriya, kafin su gabatar da shi a Arewacin Nijeriya.
Duk da a lokacin sun sha wahala sosai, har da yaƙe-yaƙe kafin su sami nasarar ƙaddamar da shi a yankin Arewacin Nijeriya, inda kuma suka amshe shi hannu bibbiyu.
Ilimin boko ne ke da tsare-tsare kafin, bayan da kuma lokacin da ake koyar da shi. Akwai tsare-tsare kafin a koyar da ilimin boko, hukumomi daban-daban na ilimi sun tsara abin da za a koyar a shekara-shekara, zangunan karatu da kuma sati-sati. Wanda ake kira (SYLLABUS) a harshen turanci, sai kuma (SCHEME OF WORK) da aka fitar da shi a jikin syllabus.
Sannan shi kansa malami yana da tsare-tsaren da zai yi kafin shigarsa cikin aji, wanda ake kira (LESSON PLAN) da kuma (LESSON NOTE)."
"Cab! Ashe idan mutum zai yi karatu sai ya sha wahala? Wannan tsari haka?" Na ce da shi ina kallonsa.
"Babu wata wahala a karatun boko. Daga matakin firamare har zuwa jami'ar, sai dai kawai ƙalubale na karatu da za ka tarar. Ki dage ki yi karatu ki zama abar alfahari, kada ki ɗau aƙidar mutanen ƙauyen nan na ƙin ganin sun bawa yaransu da kansu damar yin karatun zamani."
"Ni da nake mace ta yaya zan iya yin karatu, ai dariya za ayi mini."
"In ji waye ya ce miki baki da 'yanci yin karatu a matsayinki na 'ya mace? Shi karatu babu ruwansa da jinsi, inma mace ko namiji duka ya zama wajibi su nemi ilimi. Ki yi karatu zan tsaya miki har sai na ga kin ga ƙarshen biro." Ya ƙarasa yana 'yar dariya.
"Ni ban san me zan karanta ba ko da ace na tilastawa kaina yin karatun."
"Ki zama likita" ya ce mini.
"Likita kuma?"
"E! Mana ko bakya so."
"Ni so nake na zama mai taimakawa yaran da mahaifiyarsu ta watsar" Na ba shi amsa.
Sosai na ga tausayina a kan saman fuskarsa. Ya shiga shafa kaina ba tare da ya ce mini komai ba.
Ina zaune a kan kujerar tsakar gida, na tasa kayan wankina a gaba ina saɓesu. Kamar daga sama na ga shigowar Inna tamkar wacca aka jefo.
Ganinta gabana ya bawa zuciyata damar harbawa da sauri da sauri, bugun numfashina ya sake ta’azzarar fiye da yadda yake yi a da, tun lokacin da ta watsa mini tafasasshen ruwan kokon da ta ce na ɗora mata nake ɗar-ɗar da ita, sam ko kaɗan ba na son abin da zai sake haɗa hanyata da ita, balle har na shaƙi numfashinta, kai ko daidai da inuwarta sam ba na so na raɓa ko na yi tozali da ita balle ita kanta. Na ajjiye zanin da nake kan ganiyar cuɗawa da sauri na arci na kare izuwa ɗakin baba, ina mai garƙame ƙyauran ɗakin tare da danna masa alhargar(sakata) da ke saƙale jikin ƙofar, na jingina jikina da jikin ƙofar ina mai sauke wani gauron numfashi da ke fita a miliyan.
'Wai Allah ya kuɓutar da ni' Na ce ina mai sake numfasawa. Ban san adadin tsawon lokacin da ta kwasa a wajen ba ni dai na jima jingi ne jikin ƙofar kafin daga bi sani na yi wata ƙatotuwar gingimemiyar shahada na zare alhargar na ziro da kaina don san ganin tana wajen ko kuwa ta bawa wajen sarari. Cikin takakkiyar sa’a na hangi wajen fantal da shi babu ko da kwatankwacin inuwarta balle ita kanta, na ja wani siririn dogon numfashi kafin na ƙarasa buɗe ƙofar gaba ɗayanta na fito da jikina daga inda na fake, kai tsaye na nufi sashen hanyar ɗakinta, na sauke ajjiyar zuciya bayan na cikaro da danƙameman kwaɗo a saƙale da jikin ƙofar. Na yi hamadala tare da godewa mahaliccina da ya kuɓutar da ni daga kaidin ta, na koma bakin aikina wato wajen wankina na ci gaba daga inda na tuƙe.
Na jima kafin na kamala wankin kana na bar wajen bayan na shanya kayan da na saɓe jikin katanga kuma har lokacin Inna ba ta dawo cikin gidan ba.
A ka ce wai, 'Baƙar rana mai wuyar sha'ani ce'
Muna zaune ni da Dije a tsakar gida, mun shagala sosai akan bitar karatun da yaya Lawan ke yi mana. Don ya dage akan lallai sai mun yi karatu, yayin da ni ma na ji soyayyar karatun cikin raina, domin baba da kansa ma yakan nunar da ni muhimmancin ilimi, yakan yawan gaya mini na tsaya kai da fata na yi karatu don gobena.
Yaya Lawan ya shigo hankalinsa a tashe. Kalaman da na ji yana fesawa baba Iro ne suka haddasa mini miƙewa da azama, na yi wancakali da littafin da ke gabana, ba tare a jin sauran zantukan ba na fice daga gidan na nufi hanyar gida.
Ina shiga, na wuce ɗakin baba kai tsaye. Baba na iske kwance kan tabarma, na ƙarasa da hanzarina kamar walƙiya na isa gabansa. Cikin sauri na kamo hannunsa cikin nawa na riƙe gam!
"Me ya sameka baba? Me ya faru da kai babana?" Na ce hawaye na ƙoƙarin zubowa daga cikin idanuna.
"Ki kwantar da hankalinki Hansatu. Babanki zai tashi da izinin Allah" Muryar kaka ta doki dodon kunnena.
Sai a lokacin na lura da cewa tana kusa da baba a zaune. Na kai dubana da sauri gareta.
"Me ya sa mi babana ki faɗa mini kaka. Bana son rasa shi, don Allah ki ce ya tashi."
"Ki kwantar da hankalinki. Babu komai damuwa ce kawai ta yi masa yawa. Hansatu Innarki ba ta da kirki sam ko kaɗan. Burinta kawai ta tozarta mahaifinki, ta kuma ƙuntata masa. A jiya da dare ya shaida mini ta kwashe kaf takardun gonakinsa ta siyar. Ina kyautata zaton damuwar haka ce ta haifar masa da wannan ciwon, in sha Allahu kuma zai farfaɗo." Cewar kaka.
'Me ya sa Innata ke yi mana haka? Wane laifi mafi muni muka aikata da har take yi mana wannan hukuncin mai tsauri haka?' Na yi maganar cikin zuciyata.
Zubar ruwan hawayena ya sake gudu, tausayin baba da soyayyarsa na sake dukan zuciyata.
Sai wajen magriba baba ya farfaɗo, nauyayyeyan numfashi ya sauke, na matsa kusa da shi ina mai tallafo kansa tare da miƙar da shi zaune, na jinginar da shi jikin filon da na jingina jikin bango.
A hankali na miƙe na ɗebo ruwa na kawo masa, babu musu ya sa hannu ya amsa. Ni kam babu abin da nake aika masa face sannu.
Satin baba guda yana jinyar jikinsa. Inna ko da wasa ba ta tausaya masa ba, sannu wannan kawai ba ta ratso fatar bakinta ta fesa masa ba.
Tsanarta ta sake mamaye ƙalbina, ina jin duk duniya babu wacca na tsana sama da ita.
Yau da lafiya gobe babu, haka baba yake ta fama da jikinsa. Ga shi yaƙi yarda akai shi asibitin cikin gari.
Da wata ranar juma'a yamma sakaliya, yayin da garin ya yi hazo, iska mai sanyi na kaɗawa.
A wannan lokacin na isa da sassarfa zuwa kan baba.
Sassarfa da hauhawar da numfashinsa ke yi ya ƙara ingiza ni kusa da shi, na yi azamar ɗago da kansa da ke kan curin ƙullin kayan da na haɗa masa, wanda ya zame masa matashi na ɗora kansa bisa cinyata.
Muryata na rawa na shiga tambayarsa, "Baba lafiya kuwa?"
Har lokacin numfashinsa bai saitu ba, balle ya ba ni amsar tambayar da na gindaya masa, sai ma wata ƙullalliyar shaƙuwa ce ta hau sarƙafe shi da iyaka gunjin ƙarfi, tari mai ƙarfi ya yi masa ƙawanya inda ya mamaye ilahirin bakinsa ya gaza furta komai domin ba ni amsar tambayata. Ban daddara ba na sake jefa masa wasu tambayoyin nawa.
"Baba jikin ne? Na samo maka ruwa?"
Har lokacin da bakina ya dire lafazaina, bai ba ni amsa ba. Ganin babu sarki sai Allah ya sa na fice da sauri bayan na mayar da kansa kan curin ƙullin kayan. Wanda ya yi daidai da fitowar Inna daga bayi, hannunta ɗauke da buta. Na tare ta da sauri cikin sarƙewar harshe na furta,
"Inna Baba!"
Ta watsa mini wani gigitaccen kallo, mai cike da gargaɗi, gami da kashedin da har ya yi sanadiyar da ya sa na haɗiyi wani kakkauran yawu.
"Uban me zan yi miki?" Ta tambaye ni cikin tsawa.
Ban ji zafin kalamanta ba, domin so nake na ga ta taimaki baba. Na janyo akalar kalamaina ta hanyar furta,
"Babana! Inna ki taimaka masa, ki taimaka min ka da na rasa shi a wannan tsukakken lokacin da ya zame mini..."
Ta katse ni ta hanyar jan dogon tsaki "Mits!"
Wanda ya tafiyar da linzamina, take na ji hanjin cikina ya soma nannaɗewa.
"Mu je ni! Ka da ki siɗi ne, gaba ɗaya kin wani kafe ni da na mujiya."
Ban tanka mata ba, na wuce gaba tana mai take mini baya, har mu ka isa ga baba da ke malelekuwa.
Ƙofar sharhi ko gyara a buɗe take.
Mai ƙosai✍️