Free chapter 路 Read without an account

Episode two

by Aisha Umar 路 馃實 DUNIYA MAKARANTA!!馃

馃實DUNIYA MAKARANTA!


    Arewabook

https://arewabooks.com/u/nanabmb


   Wattpad

  

  My novels


 RABON KWADO...!!


 JARABTAR MU!!


 RABO!! 


 AND NOW


DUNIYA MAKARANTA!!


   

 Page two


Cikin kissa meenal ta soma kuka tana yarfe hannayen nata ta kuma rintse ido gam kamar wadda kunama tahau wa jiki, a kidime kuwa Daddy yay kanta yana cewa. 


 " My daughter lpy? Meya sameki ne?" Ay Meenal tanajin muryan nashi ta soma laluba hannun nata a iska tana son riko Daddy din don kam kam taki yadda ta bude idon ta, koda yaga haka Daddy din seya riko mata hannuwan nata cikin damuwa yake cewa.


 " Menene a hannun naki Meenal? Ki nutsu kinjee babu komai a nan!" 


 Cikin muryan kuka Meenal tace. " is something that is on my hand!please Daddy remove that from me banason sake ganin sa " 


 " Mtssss!! Aikin banza tama tsorata mutane! Wlh Daddy karya take karka bata time din ka akanta, kawai so take dama tayi abinda ta aikata yanzu, zata wani wayance don ta maida mu kananun yara mara mutum cin yarinya kawai!" 


 Cikin takaici Aseem yay maganar yana aikama Meenal din harara, Husna kuwa hawayen bakin ciki ne ya taru a eyes dinta ba yadda zatayi ta dauke cup din daga kan cinyan Bilal ta dauka tissue zata goge masa lemun ya dakatar da ita da hannun sa ya mike batare daya kula kowaba, yay upstairs fuska a murtike, cikin fushi auntie Lubna ta kalli Aseem tace.


 " Ni ban haifi mara mutum ciba ka gane Koh!! So kake kace tana sane ta zubawa Bilal lemu? Saboda ka hada rigima Koh! To idan bazaka rarra shetaba karna kumajin bakin ka anan gurin!"


 Da mamaki Aseem ya kalle ta yana cewa." Yanzu Mami goyon bayan ta zakiyi?" 


 " Na goyi bayan nata seme! Kasan meta ganine dazaka fara mana wani zance! Kayi min shiru na gaya maka "

 

 Sunkuyar da kansa yayi yanajin kamar yay kuka don bakin ciki ya rasa wani irin sangar tane haka mahaifiyar tasu takema wan nan autar tata to shi kuwa muhseen don takaici kala be tanka musu ba don yasan ransa ne ze baci a banza, sam baya tsayawa dogon magana akan kanwar tasu, tanayi ne zataji a jikin ta, duk abinda ake mummy na zaune kala batace ba abincin ta kawai take ci ta kwace kunnen ta, Meenal ranta fess ta batawa Bilal rai, daddy dama cikin parlour ya jawota suka zauna yana duba hannun nata seda taga wucewan Bilal tana murmushin a kasan heart dinta ta kalli Daddy din tace. 


 " Duka nakejin ana bina a jiki Daddy room dina zanje nayi wanka"


 Cikin gamsuwa Daddy yace." Ok kin koshi ne my daughter bazaki kara abincin ba ko kadan?" 


 " No Daddy bazan iya ciba se anjima, please ka gayama Mami tasa maids servant tayi min farfesu na opals akai min daki!" 


 " Yanzu kam za a kai miki uwar gida na maza jeki wanka ki huta abinki karma ki Kuma saukowa se anjima tunda baki son damu Koh!"


 Cikin murmushi Meenal ta daga kai itama ta dauka wayan ta, ta nufi tsagin Daddy don saboda matsayin tama dakin ta yana part din Daddy, shida kansa yaje ya bada umarni abinda za a dafa ma uwargidan tashi kamar yadda yake cewa.


 Bayan sallan Isha 9 ma yadan gota, Meenal tana tsaye a bedroom dinta ta dan bude window dinta tana leken Bilal shida Husna suna zaune a garden ka system a tsakanin su, yana danna wa Sara na masa tadi sunata nisha di abinsu, seda ta kare musu kallo Meenal har tana taune lips din ta na kasa kawai ta jawo ta rufe window din tana cewa. 


 " Wlh ya Bilal so nake na maka abinda zesa ka tsaneni da hujja harka fita daga sabgan life dita ka dena kulani kona huta da cin zalin ka" 

  

  Sleeping dress ne a jikin ta kawai ta zira shoe dinta da dan karamin veil dinta ta taje ta bude store ta bulla ta kitchen tai waje ba tare data bi ta parlor ba, koda ta isa garden din daga can nesa dasu yadda bazasu hange tabama ta tsaya kawai ta kai hannu ta soma mintsinin lallau san chicks dinta, tana hadawa da mari hakika tanajin zafin abinda take amma saboda iya hada tuggu taki denawa seda ta tabbatar face din ta yay ja tukunna ta koma cikin gidan a guje direct tai parlour tana kuka har da kururu wa ta rike face din ta gam Su mummy shiru sukayi suna jira suga ta ina me kukan ze bullo ne, garam ta banko kofa ta shigo harda barin jiki ita ta firgita din nan taje ta fada jikin Mamin tasu tana wani irin kuka, ai kuwa cikin tashin hankali auntie Lubna ta dago ta tana cewa.


 " Meenal menene? Meye ya sameki?" 


 Tana maganar tana jijjiga ta, amma ina Meenal kara kan kameta takeyi dadi ma dai hankalin sa a tashe yake, Dole ya ture tulin papers din dake gaban sa ya taso ya rikota ya zaunar yana cewa.


 " My daughter gaya mana meye ya faru dake!"


 Tanajin muryan Daddy ta bude ido cikin kuka tana cewa. " Daddy Ya! Ya! Ya!" Yadda take ambaton ya Bilal din kamar zata shide da kyar ta furta. " Ya Bilal ne yay min duka, ya yaringa marina yana ran kwashi na saboda sabo... Saboda na zuba masa lemu dazu wai!! Ina ta bashi hakuri yaki saurara ta! Please ka bashi hakuri Daddy bada gangan nayiba, idan ya kuma dukana mutuwa zanyi! Yeee!!" Ta cigaba da sharban kukan ta 馃槀 ( Nidai kam yau ina ganin lukatan makirci a gurin wan nan diya ) 


 Ran Daddy idan yayi dubu toya baci, har wani gumi ne ya soma tsatsafo masa saboda tsananin bacin ran daya shiga, kawai seya nemi guri ya zauna har yana wani huci ya kalli mummy yace.


 " Kira minshi a waya!" 


 Ba musu kuwa mummy ta dauka wayan nata don bin umarnin mijin nata, Meenal tana ganin hakan ta mika hannu ta rike hannun Daddy din cikin kuka tana cewa. " Please please Daddy karka bari ya sake dukana!" 


 " Sha kurumin ki Amina! Yau zakiga matakin dazan dauka akansa!" 


 Cikin wani irin yanayi auntie Lubna ta soma cewa. " Ni abubkar na rasa me yasa Bilal ya tsani yarinyar nan! Ada idan ya kamata da duka a gidana abin har mamaki yake bani, se kace ba 'yar war saba! To saboda ina masa magana kan autata ya dena zuwa gidan nawa tunda Mahmoud ya bar kasar nan inba wani abu ba Bilal ya dena zuwa gidana, ya maida Meenal kamar makiyar sa! Nida nakeso mu hade kanmu amma zena ma diyata wan nan izaya! To abin nasa kuma ya dawo kenan yanzu C'mon saboda ta zuba masa lemu by mistake shine ze mata wan nan dukan! Kalli yadda yamai da min fuskan yarinya ta haba Bilal me yasa hakan take kasance wane banason ganin kanku a rabe banaso!!" 


 Sharrr sega hawaye ya soma bi mata fuska, cikin wani irin takaici mummy tace. " Meenal ay bama musan kin fitaba! Kema kinsan halin sa meye ze kaiki gurin sa?"    Cikin tura baki gaba, Meenal tace." To ayni bansan yana garden dinba da meye ze kaini ma!" 

    Adai dai time din kuma Bilal ya shigo shida Sara tana rike da laptop din tashi, tunda yaga yanayin da iyayen nashi ke ciki yaji gaban sa ya fadi amma ya daure yaje gaban mahaifin nasa, ya zauna yaname tankwshe kafafun sa a gaban sa jiki a sanyaye ya dago yana shirin yin magana.  Tasss tassss!! Daddy ya dauke shi da mari masu zafi, wanda ya matukar gigita tunanin Bilal bama shi kadai ba, duka mutan parlour din seda suka shiga wani yanayi don ba wanda ya taba tunanin abinda zeyi kenan, cikin wani yanayi Bilal ke kallon mahaifin nasa eyes dinsa sun ciko da hawayen da yakasa tan tance na miye, kamar a mafarki yake ganin wai Daddy ya mareshi yau abinda be taba kwatan tawaba, cikin fushi Daddy ya gyara zaman sa yana cewa.


 " Kaima ka dan dani azabar daka ganama baiwar Allah! Ashe Bilal baka da tausayi baka da imani ban saniba se a yau!! Yanzu kiyayya da kakema Amina harta kai haka Ashe!! Me yarinyar nan ta tsare ma a rayuwa ne? Koda baka duba meye a tsakanin kuba, bakaga ita yarinya bace da zaka saki jiki ka ringa yi mata irin wan nan dukan? Wai yaushe ka zama haka ne ban sani ba Bilal?" 


 A mugun kidime Sara ta mike tsaye tana cewa. " Daddy waye ya daka wai?" Dakatar da ita mummy tayi da hannu fuska ba annuri dole ta koma ta zauna Sara zuciyan ta na wani irin bugu bare kuma shi Bilal din, koda Daddy yaji meta fada seya juya gurin Meenal dake gefen sa tana ta sharan hawaye yace. 


 " Amina fadi abinda ya aikata miki yaji idan ya isa seya karya ta!" 


 Zumbur Meenal ta gyara zama ta kalli Bilal din wanda shima a yanzu ya zuba mata nasa na mujiya hakika taga zallan kaduwa a cikin eyes dinsa da kuma tarin bacin rai to duk don ta yi katangar karfe tsakanin ta dashi dole ta kwatar ma kanta yan ci, kasa tayi da nata idanun cikin muryan kuka ta soma cewa. " Daddy ni bansan suna cikin garden dinba naje, yana hangoni se tsintar sa nayi a gaba na ya soma marina yana ran kwasan min kai wai banida kunya ina sane na zuba masa lemu duk da inata bashi hakuri. Be saurari roko naba har seda yay wurgi dani a kasa kuma yace idan na fada maka seya sumar Dani!" 


  Sosai Daddy ya kara hassala kamar ze kuma kwada masa Mari cigaba da cewa. " To don Allah inka sake kamata karka barta da rai kajee! Tunda wulakan cin naka harya kai haka karka fasa, kodan yadda take da sunan mahaifiyar kama baka kyale rayuwar taba taji dadi!" 


 Cikin wani irin kallo da Bilal yakewa Meenal yace. " Wlh Daddy ina bakin cikin sunan mahaifiya ta da yarinyar nan taci, don wan nan ba mutum bace face annoba! Wan nan ta sake kwanaki a gidan nan bansan iya masifan da zata haddasa min ba a gidan nan!" 


 Ai duka se sukai poster Daddy da auntie Lubna suna kallon sa ba tare da yabi takan hakan ba, ya cigaba da cewa. " Ina kuma baku hakuri Daddy bazan sake shiga sabgan taba in Sha ALLAH daga rana irin ta yau hakan baze sake faruwa ba kuyi hakura!" 


 Ay kuka auntie Lubna ta saki tana cewa. " Yanzu Bilal a gaba na kake kiran yata da annoba!! INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI UN! inaji ina gani kana muzan tamin yarinya a gabana wan nan waca irin kiyay yace kake nuna mata haka kiri kiri?!" 


 Cikin tsananin fushi Daddy yace. " Bilal baka taba batamin rai irin yauba! Ka bani kunya wlh indai wan nan halin zaka daukar wa kanka tirr dashi wan nan halin! Kana shekara 30 amma don abin kunya kana biyewa karamar kanwar ka yar 17 years, ta bari kajee in gaya maka, daga rana irin ta yau ka sake gwada irin abinda kama yarinyar nan yau, to wlh seka gamu da mummu nar bacin raina! don tunda ka mata haka yau gaba waya san meza mata, don haka nama ka iyaka da ita daga yau tun wuri kasan me kakeyi kakuma bawa mahaifiyar ta hakurin cin fuskan daka gamai mata yanzu!" 


 Kallon mamaki Bilal kema Daddy nasa don haka bata taba kasance wa a tsakanin sa da mahaifin saba se yanzu, jiki a sanyaye yace. " Mamy kiyi hakuri don Allah! ban fadi magana ta donna bata muku raiba, kaima Daddy kayi hakuri ka gafar ceni in Sha ALLAH bazan sake aikata laifi makaman cin wan nan ba"


 Daddy yace." Dadai ka samawa kanka lpy kuwa, ya kamata kaja girman ka, kana shirin yin aure amma kana neman bata rawar ka da tsalle kaida zaka jagoran ci iyali wan nan hali ba naka bane dama" 


 " In Sha ALLAH Daddy ku yafe min bata muku ran danayi bazan sake ba da yardar Allah" 


Daddy baya iya jurewa fushi da dan nasa shiyasa nan da nan ya saki fuskan sa dayaga jikin dan nasa yay sanyi, yace. " Ba komai Bilal ka ringa kiyaye abinda ze bata min rai dai da auntien ka" 


 " In Sha ALLAH Daddy!" 


 Mikewa yayi yaje gaban auntie Lubna ya tsugunna ya sake marai raice fuska yana cewa. " Mamy na please kiyi hakuri banida burin bata mika rai akoda yaushe koda wasa ban tsani 'yarki ba ina fata zaki fahimce ni!" 


 Fuska ba yabo ba fallasa tace. " Ina fata dai anan gaba na fahimce ka Bilal!" 


 Sam beyi mamakin jin hakan ba daga gareta in dai kan Meenal ne shiyasa yace. " To Allah ya fahimtar dake da wuri Mamy" mikewa yay ba tare daya kuma sauraren kowaba yaje ya dauka laptop dinsa dake gefen Husna tanata matsan kwallah na takaici abinda akema masoyin ta batada ikon saka baki bare ta wanke shi a gunsu, sedai ta rakashi da idanu harya haye sama haka mummy da sam tai kamar batasan meke faruwa bama, itama Meenal da idanu ta rakashi babu alamun risina a tare da ita sema dadi da takeji an musu iyaka, Daddy kallon ta yayi yace. 


 " Meenalyn Daddy kiyi hakuri kinji ki kwantar da hankalin ki baze sake dukan kiba kinga dai yadda mukayi dashi komai ya wuce daga yau ina fata bazaki rike yayan nakiba zaki yafe masa Koh?....鉁嶏笍

  

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol