Free chapter · Read without an account
Chapter 43-44 Zubar da ciki
HAFSATUL-KIRAM
©Mai ƙosai
FCW
Babi Na 43-44
"Ban ce ni ma ki aureni ba, amma ki sani ko ki yarda ko karki yarda soyayyata na cikin zuciyarki, kuma da sannu wata rana za ki aure ni."
Ina shirin yin magana baba Iro ya katse ni ta hanyar furta,
"Ya isa haka! Don Allah ku daina takurawa 'yata, mijinta dai sai wanda ya ciri tuta ne zai aureta."
Duk yadda kaka taso naƙi amincewa da ɗanuwana a matsayin na aure shi. Yalsha da Dije ma sun sha fama amma naƙeƙashe, na turbuɗawa idona kwallin rashin arziƙi naƙi.
Wata biyu tsakani, kullum na kwanta bacci sai na yi mafarki da inna tana roƙona na yafe mata, takan zo mini a wani hali mara kyan gani. Jikinta duk ƙuna fatar wani wajen ta ɗaye.
Na sanar da baba Iro, nan ya sake roƙata a kan na yafe mata, ban yi wata-wata ba na yafe mata har abada.
Rayuwa na ta gwarawa, ganin bana komai kuma naƙi aure ya sa yaya sama mini makaranta, nan na shiga na soma karatun abin da ya shafi shari'a. Dije ma ta shiga makaranta in da take karantar likitanci. Yalsh kuwa bata komai, ta ce sai ta sake hutawa za ta ɗora akan karatunta da ta yi na baya a kan fannin kimiyar na'ura.
BAYAN SHEKARA BAKWAI
A waɗannan shekarun Dije wacce ta sauya sunanta zuwa Dija ta kammala karatunta, ni ma haka. Yayin da Yalsha da muke kira da Nisha kuma ta koma Dubai don yin digiri na biyu a kan karatunta.
Dija ta sami aiki a asibiti, ni kuma na kafe zan zama lauya mai zaman kanta ne ba ƙarƙashin kowa ba.
Wata rana, muna tare da Dija a wajen aikinta. Cikin marasa lafiyar da take dubawa sai ga wata ta shigo.
"Meke damunki?" Dija ta tambayeta.
Matar ta soma silalar da ruwan hawaye kafin ta ce,
"Don Allah so nake ki taimaka mini, ki cire mini cikin nan da ke jikina."
Sororo muka bita da kallo, ina danne-danne a wayata sai na ajjiye na fuskance ta, tare da jin irin amsar da Dija za ta bata.
"Me ya sa baiwar Allah? Kin san kuwa illar da ke tattare da zubar da ciki? Me ya sa bakya so kika je kika yi shi? Kin san kina gudun a ce kin haife shige amma kika yi cikin?"
Ta kalli Dija, ta ɗan taune leɓanta na ƙasa kafin ta ce,
"Cikina ba na shege ba ne likita."
"To me ya sa kike son zubar da shi?" cewar Dija.
"Saboda bana so na haife shi ya taso a cikin maraicin uba. Mijina baya sona, baya ganin ƙimata da darajata. Kullum cikin dukana yake yi, abinci ba na samun isasahen, wata ranma sai na yi sati ban saka komai a cikina ba face ruwa, idan kuwa maƙota suka kawo mini to a ranar dukan kawo wuƙa yake yi mini, baƙin halinsa ya sa duk masu taimakona suka janye, bana ganin kowa cikin gidana. Shi ya sa da na sami ciki nake shan magani na zubar da shi. Wannan ma ban fargaba sai da ya kai wata huɗu, shi ne nake so ki taimaka ki fitar mini da shi."
"Amma baki da iyaye ne da ba za ki sanar da su ba?" Na yi karaf na jefa mata tambayar.
"Ni ba 'yar nan ba ce ba, daga kamaron ya auro ni ya kawo ni nan, ya ƙwace komai nawa wanda zai iya sada ni da 'yanuwana, gidan da suka san ni da shi ma ya canza wani mun baro can."
"Amma yana sonki ya auro ki ko kuwa?" Na sake furtawa.
"Gaskiya ba auren soyayya muka yi da shi ba. Saboda babana ne ya aura masa ni, don sake ƙulla zumuncin da ke tsakaninsa da shi, kasancewarsa yaronsa tun bayan zuwansa ƙasarmu wacca ya yi karatu cikinta, sai ya haɗu da mahaifina. In da shi kuma ya ɗora shi kan kasuwancinsa, ganin riƙon amanarsa ya sa ya damƙa masa ragamar kasuwancin gaba ɗaya, har takai ya yi masa kwaɗayin aurena ya yarda ya amsa. Bayan auren da watanni biyu ya sanar da mahaifina zai dawo gida Nijeriya gaba ɗaya, saboda rasuwar babansa ga shi mahaifiyarsa babu mai kulawa da ita, shi ne ya taho da ni. Allah na gani, daidai gwargwado ina yin abin da zai faranta masa." Ta ƙarasa tana kuka.
"Ki yi haƙuri, amma babu batun zubar da ciki, baki san abin da Allah ya nufa ba shi ya sa ya bai baki ikon gane cikin ba sai yanzu. Yanzu dai ki koma gida ki ci aba da addu'a tare da neman taimakon ubangiji." Cewar Dija.
"Ba zan iya ci gaba da zama da shi ba, matsawar na koma gidansa to na yi alƙawari sai na kashe kaina."
"Subhanallahi! Ke kuwa me ya yi zafi. Yanzu shi mijin naki yana ina?" Na ce.
"Yana wajen sana'arsa, sai dare yake dawo wa, da safe kuma wajen goma ya fita."
"To shi ke nan, ki daina kuka, ki yi shiru. Zan miki wani taimako guda ɗaya, matsayina na barista mai son nemawa mata 'yancinsu. Za muje wajen mijin a yi masa magana."
Ta so turjewa, amma sai na tausheta kana ta amince.
Na kira yaya a waya na buƙaci taimakonsa. Wajen tara muka je gidanta har da yaya. Muka shiga nusar da shi a kan abin da yake aikatawa. Bamu bar gidan ba sai wajen goma da rabi, na kuma bata ƙaramar wayata, da sabon layi a ciki na ce ta riƙe wajenta tana amfani da ita. Kuma gobe zamu dawo in sha Allahu.
Sai dai bamu koma ba, sanadin kiranta da na gani cikin dare, na ɗaga na kara a kunnena. Sai na jiyo numfashinta na fita da ƙyar, na tashi zaune zumbur! Ban ji me take cewa ba na katse kiran na yi wa ɗakin yaya tsinke, nan na taso shi, a daren muka isa gidanta ni da shi, da Dija. Nan muka isketa cikin jini faca-faca ba ta numfashi. Ba mu tsaya jinkiri ba muka ɗauketa sai asibitin da Dija ke aiki. Ta sami ɓari, har ta kai ga mahaifarta ta raunata, wanda binciken da Dija ta sa aka yi ya nuna haka.
Bata sami kanta ba sai a washegari. Dija ce ta tasata a gaba ta soma yi mata faɗa da kuma gaya mata illolin da ta janyowa kanta saboda zubar da cikin da ta yi.
"Sai da na ce kada ki zubar, amma kika ƙi ji. Yanzu kin san me kika janyowa kanki kuwa? To bari kiji kin sami rauni a mahaifarki yadda nan gaba ba lallai ne ciki ya iya zama a cikinta ba, wanda sai dole kin dage da shan magungunan da zan ɗoraki akai.
Daman shi illar zubar da ciki ke nan, domin yakan janyo matsaloli da dama. Shi ya sa ba a san yawan Misscarrage(ɓari)."
Hawaye ta soma silalarwa, cikin kuka ta ce,
"Wallahi ban yi ƙoƙarin cire cikin nan ba. Jiya bayan tafiyarku, wajen ɗaya na dare har na soma bacci sai kawai na ji saukar waya a jikina, ya shiga dukana ta ko'ina, yana kai mini bugu. Ƙafarsa ya sa ya dinga naushin cikina, duk ƙoƙarin kare cikin ban sami nasara ba, dukan da ya kai mini da ƙarfin gaske shi ya haddasa mini zubar jini, take jini ya ɓalle mini bai saurara ba sai da ya ga numfashina na neman ɗaukewa ya shuri sawayensa ya yi ficewarsa, da ƙyar na samu na iya ɗaukar wayar da kika ba ni na kiraki."
Raina ya ɓaci sosai, me ya sa wasu mazan ba su san darajar mata ba? Yaushe ne mata zasu sami 'yanci? Yaushe ne maza za su samar mana da adalci?
"Ki yi haƙuri, ki ci gaba da juriya wata rana sai labari" Dija ta ce mata.
"Bana son shi, bana son ci gaba da zama da shi, ina so kai shi gaban alƙali domin a raba aurenmu da shi, don Allah ki taimaka mini matsayinki na barista." Ta yi maganar rana kallona.
"Kada ki damu, in sha Allahu zan tsaya miki a kan ganin kin sami haƙƙinki."
Na duƙufa sosai don ganin na maka shi a kotu, duk da Dija na son yaƙata a kan haka, ni kuma na kafe, don na yi alawashi sai an bi mata haƙƙinta. Yaya ya tsaya mini a kan lamarin. Har gida muka kai masa takardar sammaci ni da yaya, inda nan da kwana biyu za a shiga kotu.
Dija sosai take fushi da ni a kan lamarin, har sai da na warware mata manufata a kan ba wai auren nake so a raba ba, ina so ne a ganar da shi kuskurensa, sannan ta sakko.
BAYAN KWANA BIYU
KOTU:
Kotu ta cika maƙil da mutane, shigowar alƙali ta sa kowa nutsuwa tare da miƙewa tsaye, mutane na ambatar "kuto!" Alƙali ya zauna tare da buga gudumarsa kowa ya zauna.
Nan magatakarda ya miƙe ya soma koro jawabi,
"A yau ranar laraba, wadda ta yi daidai da ranar shida ga watan satumba, shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu, kotu za ta saurari ƙara tsakanin Bahijja Hassanu da mijinta Mahrazu Yusif, inda take ƙararsa a kan cin kashin da yake yi mata, har ta kai ga ya yi mata dukan da sai da ya zubar mata da ciki wanda ya janyo mata matsalar samun rauni a mahaifa, tare da neman kotu da ta raba aurensu."
Ya zauna, alƙali ya ɗan muskuta.
"Kuto na buƙatar ganin Mahrazu Yusif da Bahijja Hassanu a gabanta."
Suka fito, kowanne ya tsaya cikin abin da ake tuhuma.
"Lauyoyin kowanne sashi su gabatar da kansu." Cewar alƙali.
"Sunana Barista Hafsa Abdallah Makafi, ni ce mai kare wacca ke ƙara." Na ce ina mai zama.
"Sunana Barista Hafiz Mahmud, lauyan wanda ake ƙara." Wani ɗan lukutun mutum ya yi maganar.
Alƙali ya yi rubutu, kana ya kalli Mahrazu ya ce,
"Ka ji abin da Bahijja ke ƙararka akai, me za ka ce game da haka?"
"Ni ban san maganar ba, sharri kawai take yi mini. Kuma ina sonta babu abin da zai sa na rabu da ita."
"Malama Bahijja shin kina da hujjar bayyana gaskiyar abin da kike tuhumarsa da shi?"
"E, ya mai shari'a. Lauyata za ta gabatar da komai."
"Lauyan wacca ke ƙara, ko kina da abin cewar da zai bayyana gaskiyar tuhumar da ake yi masa?"
"E, ranka ya daɗe." Na ce ina miƙewa tsaye. Gaban Bahijja na fito na tsaya na dubeta na ce,
"Ko za ki iya gayawa kotu sunanki, da alaƙar ki da wanda kike ƙara?"
"Sunana Bahijja Hassanu, shi mijina ne."
"Za ki iya taimakawa ki faɗawa kotu labarin alaƙarki da yadda zamantakewarku ta kasance da shi?"
"Ba zan iya cewa komai ba, saboda alaƙa ce da zamantakewa mai muni. Sam! Baya sauke mini haƙƙoƙina da ke kansa, idan na ce haka. Ina nufin ciyar da ni; domin na kan shafe twason kwanaki ban ɗora tukunya a kan wuta ba, sai dai na sha garin kwaki da tsuran ruwa zalla, wanda shi ma ba ko da yaushe ba. Tufatarwa da lafiyata, duk ya ɗauke wa kansa su. Babu abin da ke haɗa ni da shi sai duka, baya bari kowa ya raɓe ni, nan da can bai yarda naje ba, kullum ina cikin gida, ya mayar da ni saniyar ɗaure. Dalilin da ya sa nake so kotu ta raba aurena da shi ke nan."
"Ya mai girma mai shari'a, ko da iya wannan ma ya isa ya zama hujja a kan abin da ake tuhumarsa da shi."
Alƙali ya gyara zaman gilashin fuskarsa, ya yi rubutu kana ya ce,
"Barista Hafiz ko kana da abin cewa?"
Barista ya miƙe tsaye, ya isa gaban Bahijja ya soma magana,
" Malama Bahijja, abin da kika yi ƙararsa akai, akwai togaciya cikinsa. Domin mijinki ya shaida mana ke ce kika yi yinƙurin zubar da cikin, wanda har asibiti kika je a kan kina so a cire miki. Haka ne ko ba haka ba ne? "
"Tabbas na je asibiti domin a cire mini ciki, amma likitar ta hane ni, ƙarshe ma ban sami biyan buƙata ba na koma gida."
"Me ya sa kike so a cire miki ciki?"
"Saboda ba na so na haihu tare da shi."
"Ke nan saboda ba kya son haihuwa da shi, ya sa kika yi masa sharrin yana takura miki, har kike so a raba aurenku?"
"Objection ya mai shari'a Bai kamata barista na shigo da abin da ba shi ba." Na miƙe da sauri ina faɗin haka.
"Ƙorafi bai karɓu ba" Alƙali ya ce, yana rubutu.
Barista Hafiz ya yi wani murmushi ya sake jefa mata tambayar a gadarance.
"A'a " Ta ba shi amsa.
"To me ya sa?"
"Saboda ba na so na haihu, abin da zan haifa ya taso cikin rashin kulawar mahaifi."
"Wannan ba hujja ba ce, kin ga ke nan shi ma zai iya makaki a kotu a kan kina yunƙurin zubar masa da ciki."
"To ai shi ma baya son cikin, don ya shaida mini da ya haihu da ni gwara ya ƙare rayuwarsa babu ɗa."
"Ya mai shari'a! Idan aka yi la'akari da bayanan Bahijja, ya isa ya nuna itama mai laifi ce, kuma ƙage kawai take son yi masa, ina fata wannan kotu za ta kori tuhumar da take yi masa."
Alƙali ya yi rubutu, kana ya ce,
"Barisat Hasfa ko kina da wani abin faɗar?"
"E, ya mai shari'a. Ina so kotu mai alfarma ta bani damar gabatar da malam Tajuddin matsayin shaidata ta farko."
"Kotu na buƙatar ganin Tajuddin a gabanta."
Wani mutumi da ke zaune gaban layi, ya miƙe ya fito.
"Ko za ka iya gabatarwa da kotu sunanka."
Gyara ko sharhi ƙofa a hangame take, *** whtsapp only
Mai ƙosai