Free chapter 路 Read without an account

Chapter 22

by Ramlat Abdulrahman Manga 路 BA茦IN HAURE..........

*BA茦IN HAURE....馃惥馃惥*


  {Greed for Money is the roots of all evils馃珋}

 Arewabooks:maidambu41

Wattpad:Mai_Dambu

Mallakar:Mai_Dambu

   *022*

"AURE!!" ya furta da karfi, yana me toshe bakinshi. "Eh aure zaka yi, aure nace zaka yi ko ba zaka yi min biyayya ba ne?" Idanuwanshi suka yi jawur ya kalli Aryan da Mahdi, mikewa Aryan yayi ya cewa Nabeeha. "Tashi muje cikin gida." Shima Amaan tashi yayi da Matarshi, domin kuwa ya fahimci maganar ta manya ce. Yadda fuskar Majid ya koma kamar zai nufi filin yaki, yasa kowa ya mike suka fita daga falon. "Hajiya ba zan iya aure ba." Cikin fushi ta ce mishi. "Wacce karyan kake tunanin zaka min kuma? Duk duniya kowa gani yake nice na rike maka kan maciji kake wasa da jelarshi, karewa har cewa ake ina zaune zaka kwaso min abin kunya duk wannan bai isa ka fahimci yadda nake rayuwa akanku bane? Majid ina son rayuwa ina son farinciki, amma na zabi na zauna da ku domin kuyi farinciki. Domin ku rayu cikin salama sannan ku zame min ribar hakurina na zauna daku, Ashe ban cancanci ka kyautata min ta hanyar yin auren ba?" Ta fada muryarta na rawa, kanshi a matukar sunkuye duk maganar da take yasan gaskiya ce kuma duk abinda ta fa蓷a gaskiya ne, amma kuma shi ba zai iya fa蓷a mata cewa bai da lafiya ba, ba zai iya cewa ga halin da ya tsinci kanshi ba, sai dai a shekarun baya .


  A ban蓷akin gidan horan yara marasa jin magana, wannan tashin hankalin ya same shi. Jikinshi ya tafi baya da wani amfani sai fitsari, bata wani motsin sai dai yayi fitsari kawai. Sannan yanayin rayuwarsa bai bashi damar kallon wata mace da sunan soyayya ba, ya kasa sakin jiki ya yi soyayya domin idan ya ce zai yi soyayya me zai bawa mace? Saduwa tana daga cikin shika -shikan aure, shi tashi tazugen bazata iya amfanar shi ba balle wata. Sannan har yau baya jin zuciyarshi tana da wata shauki akan mace, abin da ya sani ko aiki ne ya ha蓷asu da mata yana tsayawa yaga sun yi nasara, haka yasa Umaima ta makale mishi. "Kuna gani ina magana ya bawa iska ajiyata? Abdul Majid ba zan kunshi bakin cikin mahaifinku na kunshi naka ba." Mikewa yayi zuwa gabanta. "Hajiya ki min uzuri, don Allah." "Na maka uzuri fa kace min? Na hana kaina farinciki na gina ku shine zan maka uzuri? Gaya min Meye matsalarka?" Hadiye yawu yayi yana kallon yadda take cikin b'acin rai. "Hajiya duk matar da zaki aura min, karshe wahala zata sha, domin idan ta zauna dani."

  "Maza kake so kenan?" Inji Alhaji Abubakar Abzin, da sauri ya juya kanshi yana kallon Alhaji Abubakar Abzin, idanunshi har wani shekin kwalla yake tsabar tashin hankali. "Abba da ace zan so mazan da nayi farinciki,tunda a karshe dai na fahimci inda zuciyata take amma abin bakinciki babu maza da matan da suke iya burge ni ko shiga rayuwata. Duk wanda na zauna da shi don aiki ne da wani halin rayuwa"

  "Ita yarinyar da kace a nimo maka fa?" Hajiya ta kara watsa mishi tambaya. "Yarinyar nan hatsari ne ya had'a mu, domin na bugeta da motana ne, kuma nayi mata jinya Hajiya ki fahimta auren idan nayi karshe."

  "Abba ka zama shaidana idan Abdul Majid bai yi aure ba, tow kuwa sai dai ya zab'a ya hakura ya ajiye aikin shi ya zauna anan." Da sauri ya kalleta yana jin kamar kanshi zai bu蓷e wani irin sara mishi yake yana jin jiri. Harshensa yayi wani irin nauyi, so yake ya fada musu ba zai iya rike mace har ya mata kome ba, haka yasa shi jin wani irin jiri-jiri kafin ya ankara duhu ya mamaye mishi idanu, haka ya zube a gaban Hajiya a sume. Sai gashi ita tafi kowa shiga damuwa. 

   Salatinta ya shigo da Amaan, da yake makale. Lauya Sulaiman ya watsa mishi ruwa yana kwance jikin Alhaji Abubakar Abzin da ya rike shi yana tofa mishi addu'a. "Ba zance lallai kada kiyi yadda kike so ba, amma yana da kyau mu hakura da al'amarin auren nan." Wani irin kuka ne ya kwacewa Hajiya tayi ta yi ta kuma yi, muryarta yana rawa ta ce. "Abba don Allah kada ka hana ni yimishi aure, domin kuwa ina matu茩ar son yayi aure. Duk wannan shiri ne."

"Ba shiri bane, tun ranar da Mamman ya gaya min ya bar shi a gidan horan kangararun Yara, ban kara yarda na zauna ba. Lokaci zuwa lokacin ina kai ziyara naji halin da yake ciki. Yaron nan ya sha wahalar rayuwa, idan kika ji abinda ya same shi ba zaki kara barci ba. Don Allah ki kyale shi ki mishi fatan Allah ya bashi lafiya."

     Wani irin sanyi ta ji ya lullubeta, bata ta蓳a kawowa da gaske bai da lafiyan ba, domin a tunaninta zai tsarewa auren da zata kakaba mishi ne, amma kuma anya zata yarda da su? Tunda ya iya ajiye mata takardar sallama, babu abinda ba zai aikata ba don kada Alhaji Abubakar Abzin yaga kamar tana da bala'in taurin kai ta share hawayenta, amma a kasan ranta sai anyi auren nan ko zai mutu ne idan aka yi auren don ubanshi ba zata yarda ta ganshi haka babu aure ba, don haka ta dauke kai tana share hawayen da yake zubo mata.


    Ganin yadda yake barci yasa baki daya aka yi shiru, babu wanda ya kara tada zancen. Asalima kowa tausayin Hajiya suke ji hatta Amaan da yake ganin duk wani abinda ya faru da laifin Hajiya tun farko. "Tow ki daina kuka mana, ba gamu a raye ba, idan mutuwa aka ce zai yi ai kowa ya huta." Juyawa Aryan yayi yana kallon shi. "Dadina da kai baka boye waye kai? Gab'o kawai." "Kai waye gab'o." Ya taso a fusace. "Idan bakincikin Mamman Ba'are bai kashe ni ba, bakincikin abin da kuke aikatawa ya isa ya kai ni kabarina, don Allah ku bari." Ta fada tana kuka. "Hmmm Alhaji meye kuskurena akan Yaran nan? Jama'a su jefe ni, suma su koma gefe suyi dariya, Alhaji idan nace maka bana jin dadin rayuwata zaka dauka rashin godiyar Allah ne ko? Tow wallahi bana jin dadin rayuwata." Ta fada tana kuka, "sun mai dani mahaukaciya, basa jin magana ta, basa son junansu kamar su kashe kansu suke ji don Allah ya ake son nayi?" Baki daya sai jikin kowa yayi sanyi. "Alhaji da zaka Duba zuciyata, Yarana ne a cikinta,, ina son su hade kansu ina son na gansu cikin farinciki. Ina son nayi alfahari da haihuwarsu, sai dai idan na cire maka Aryan da sauransu, Amaan zai kashe ni. Bakincikin shi zai kai ni lahira ban shirya ba. Amaan ya zame min wake daya me kona gari." Yadda take kukan kawai xai saka kaji kamar ka tayata. "Ban san meye nayi mishi na kuskure ba, ya tsani yan uwanshi mata da maza ba, Alhaji Abubakar na hakura da kome na zauna da mutumin da ya haife ni kasan ba karamin al'amari ba ne. Mace ta zauna da namijin da tasan bata sonshi. Kuma ta zauna akan babu yadda zata nime hakkinta. Alhaji amsar 茩addarata da nayi hannu bibbiyu shine laifina ko zama da nayi nai ta haihuwarsu!" Yadda Hajiya take kuka yasa baki蓷aya tashin hankalin da suke ciki ya nunku. "Idan da ace Amaan yana da adalci ba zai tab'a had'akai da makiyana ba, nawa zasu bashi? Nawa suke da shi? Bana son nadama tazo mishi bayan ya ha蓷akai dasu sun kashe ni."

  Yadda take kuka yasa Majid ya tashi da matsanancin ciwon kai, wanda yasan baya raba daya biyu jininshi ne ya hau. Hajiya bata fasa fadar abin da yake damunta ba, tana ganin idan bata fada ba, tabbas kafin su koma Niamey ta mutu, shi yasa ta hakura ta fadi abinda yake damunta ko zata samu sauki. Kuma bata fasa fitar da abinda yake ranta ba, domin taji sauki kuma Allah ya taimaka tana fa蓷a tana jin kamar ana zare mata k'ayar da yake ranta, ruwa Aryan ya mika mata, ta amsa ta sha sannan ta sauke ajiyar zuciya. "Allah kagani na fita hakkinsu, saura su ya rage su futa nawa."

   "Kiyi hakuri Hajiya, Indai aure kike so nayi zan yi in sha Allah." Inji Majid yana dafe kanshi, "A'a Majid kayi yadda kake so, ba sai kayi auren ba, tunda baka da lafiya." Ta fada tana share hawayen da yake zubo mata, "Aryan don Allah kai ni, asibiti kada na fadi don zan iya samun shanyewar b'arin jiki." Ya fada kamar zai fadi, da sauri ya tare shi, suka bar falon Hajiya tana me bin su da idanu, don a tunaninta shirinsu ne suyi wasa da hankalinta. Sai da ta ga sun tafi baki daya, sai Amaan ka蓷ai ya rage, yana son ya hada rigima. "Ba wani ciwon da yake damunshi, kawai renin hankali. Fisabilillahi Hajiya kina ji kina gani wai board director aka bani?" Sai kuma yayi kasa da murya yana fa蓷in. "Hajiya Chairman bai yiwa Aryan girma ba? Ki ga fa Yaro ne? Sannan."da

  "Duk da Yaro ne bai saka dukiyarshi gaba ya lalata ba, har yau bai tab'a kaso biyar na dukiyar shi ba, kai ina naka dukiyar? Wai me kake yi da kudinka?"

 Shiru yayi yana kallon yadda take tsare shi da idanu. "Wato Hajiya " "ya isa haka! Kada ka kara kawo min sukar kowa sannan da na san board director za'a a baka wallahi da sai na hana a baka, domin ba zai yiwu a dauki jahili a bashi abin da ba zai iya rikewa ba " 

"Allah ya ba茩i hakuri Hajiya, naga kamar ranki ya b'aci "

"Hakuri shi ya kashe Uwar jaki." Yadda tayi maganar yasa shi kame kanshi kada Hajiya ta kara fusata. 

----

  A can Asibitin kuwa, Mahdi shi ya musu jagora aka kwantar dashi bayan an saka mishi ruwa. Likitan da ya duba shi ya fito yana kallonsu kafin ya ce su same shi a office 蓷inshi. Bayan sun shiga ya zauna yana ta rubuce-rubuce. Kafin ya d'ago kai domin har Aryan ya gundura da zaman ya ce musu. "Gaskiya jininshi ya hau, don Allah a bashi lokaci ya huta, idan kuma yana da mata tow a dan janyeta daga gare shi, a nisanta shi da hayaniyar mutane." 

"In sha Allah!" Suka fa蓷a, kafin ya ci-gaba da cewa. "zamu sallame shi nan da kwanaki uku, domin jikinshi yana 茩ar茩ashin kulawa ne. In sha Allah zuwa nan da wani lokaci zamu sallame shi." Haka suka yi ta godiya, sannan suka fito. 

"Hajiya Sa'adatu tayi hakuri da maganar auren nan, Yaron nan yana bu茩atar nutsuwa."

"Abba me yasa ba zai yi auren ba?" Kallon shi suka yi ta window, Alhaji Abubakar Abzin yana tuna ranar da ya kai mishi ziyara da yadda aka fito dashi baya iya tafiya. Sai riko shi aka yi. Idanunshi ne ya cika da kwalla. "Ya hadu da hatsari ne, bayan an kai shi gidan horon, Yaran da suka fi karfinshi suka mishi duka tare da doke mishi gabanshi. Wanda sanadin haka gaban ya mutu."

   Rufe baki Aryan yayi da karfi jikinshi yana rawa, hawaye na zuba mishi kamar mace haka yake kuka yana kallon dan uwanshi. "Hammayo ba xai tab'a zama da mace ba kenan?"

  "Gashi nan dai, bamu sani ba ko Ubangiji zai yi ikonshi, amma Abdul Majid yana cikin jarabawa." A hankali ya fashe da kuka, yana jin wani irin tausayin dan uwanshi. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Ubangiji mun gode!" Ya fada Aryan akwai karyayen zuciya, haka yake ga saurin kuka kamar mace, gani yake kamar dan uwansa zai mutu da damuwar lalurar. 

  Shi yasa yake nisanta kanshi da mutane, baya yarda ya zauna da kowa rayuwarshi cikin duhu, akwai wani irin shakuwa tsakaninshi da duhu tun yana Yaro, gashi ya girma da wannan trauma 蓷in. A rayuwar Abdul Majid bai san soyayya ba, bai samu soyayya ba, ita kanta Hajiya ta haifi Majid ne amma bata damu da damuwarshi kamar yadda ta damu kanta da yayi aure ba.


 Duk laifin abinda ya same su, laifin Alhaji Abbati ne, da bai saka Hajiya a cikin caca ba da babu yadda zata hadu da mahaifinsu ya kashe rayuwar dan uwanshi haka,. Sai yanzu yake fahimtar me yasa Majid ya tsani dukiyar Mamman ba'are, asalin don a gina duniya da dukiyar aka lalata musu rayuwarsu. Cikin shashekar kuka yake fa蓷in. "Saboda hab'aka dukiyarshi ya lalata rayuwar wanda babu ruwanshi."

"Asibiti muke kayi hakuri ka bar wannan zancen." Haka suka cigaba da zama har wani lokaci kafin Alhaji Abubakar da lauya suka bar asibitin tare da Mahdi,. Suka tawo da Hajiya tare da abinci, mika mata kome Aryan yayi sannan ya koma gefe yana kallonta, ajiye takardar tayi ta zauna tana kallon Majid. A hankali hawaye yake zuba mata, wannan wacce irin rayuwa ce? Me yasa kome yake zuwa mata haka? Me yasa daga wannan sai wannan? Shin anya bata yi wani laifi Ba tare da ta saninta ba.

 Su da suka zo da zimmar kwana 蓷aya, sai gashi sun kare da dibar kwanaki har sama da biyar, a na shida aka sallami Majid din, ba laifi ya 蓷an samu sau茩i. Kuma dama yanayinshi ba mai yawan walwala bane, sai abin ya kara yawa. Ita kanta Hajiya ta damu sosai kamar ta cire ciwon. Haka suka tawo Niamey zuciyarta babu dad'i. 

    Lokacin da suka isa gidan A tsakar gida suka hadu da Nanah, tana jin rigima. "Ya zamu yi da wannan tsohuwar?" A hankali ya fito yana tafiya, kamar ba zai taka kasa ba, saboda rashin karfi da kuzari. "Kai Alhaji!" Ta fada tana mikewa tare da dogara sanda har inda yake ta ce mishi. "wallahi ka sake ka mutu sai Allah ya mana hisabi. Kai ma mutuwa zaka yi?" Ta fa蓷a, yadda tayi maganar zaka fahimci bata cikin nutsuwarta. "Munafukan can ne suka kaika zasu kashe min kai ko?" Kasa magana yayi yana kallon yadda take fada. "Nana likita yace a barshi ya huta." "Muje daga yau ni zan yi jinyar shi " duk da bata kaunarsu amma a lokacin da takira Hajiya take fadan ba zasu dawo bane, an barta kamar ba a damu da ita ba, gashi kayan abincinta ya kare, babu nama babu kome Haladu da Kamilu sunki saya mata, me take nufi na dauke mata Aryan shi ko zata mishi meye baya fasa saya mata kayan abincin.


    Shi ne ta bata hakuri da gaya mata ai Majid bai da lafiya ne, bata san lokacin da ta rikice ba, tayi ta sumbatu tare da dorawa Hajiya laifin abinda ya faru gani take kamar Hajiya ta kaishi aka mishi wani abu, sannan ga Amaan da dama can tasan munafuki ne. "Ina gaya maka kada ka sake kana yarda da mutane, domin kuwa wasu ba imani a cikin zuciyarsu. Sun sayar da imanin su ga duniya, Gara ka yi nisa da su domin kada a wayi gari babu magajin Abdul Majid ba'are. Sannan kasaka ayi ta maka addu'a da saukar Alqur'ani domin nasan makiya ba zasu Barka haka ba, li'ilafi aniyar kowa ta bishi daga yau har Sa'a ban yarda da ita ba. Domin dankareren dukiyarka yawa ce da ita a tow zamani na masu iya kashe mutum, waye ya sani ko shima Muhammad kashe shi aka yi!" Zama yayi a daya daga cikin sofa, yana haki yana kallon agogon hannun shi. "Nana zan huta kiyi shiru." "Alhaji duk abinda kace ai shi zan yi." Ta zauna tana kaskantar da kanta tana fa蓷in. "Ahtow nayi shiru, amma ina ga hatta Salamatu ban yarda da ita ba, waye ya sani ko har da ita ake shirya maka kitimurmura." "Nana jeki gida, an jima zan shigo duba baki." Ya fada yana daure fuska, domin idan ba haka yayi ba, ba zata kyale shi ba.

  Sannan ya san halinta sarai sai ta kara mishi wani sabon ciwon kan. "Tow Allah ya baka lafiya, zan damo maka kunu na kawo maka." Yasan sarai idan yace mata ba zai sha ba, zata yi tsammanin bai yarda da ita ba ne. Haka yasa shi rufe idanunshi ya d'aga mata kai, domin kuwa baki daya bayan son magana. "Sa'adatu ki saka idanu akan shi domin ba zan yardaba idan wani abu ya same shi." Ta futa tana fa蓷in. "A kula da shi don wallahi zan iya shiga kotu da kowa." Tana fita ya kalli Hajiya ya ce mata. "don Allah a gyara min dakina." Daga haka ya juya musu baya, don baya son magana, Hajiya da kanta ta wuce dakin, ta gyara baki daya, sannan ta fito tana fa蓷in. "Na gyara maka" dakyar ya mike ya haura sama, koda ya shiga kashe wutar dakin yayi ya kwanta.


 A hankali labarin matsayin da Abdul Majid ya bawa su Aryan ya zagaye cikin gidan, baki蓷aya suka taru a falon Nana suna mitar abin da ya faru, da akan me Majid zai yanke hukuncin babu shawara da su, musamman su da suke Yan uwan Babanshi. Yadda ake masifar Nana ta zuba musu idanu, can da suka ishe ta mike tana fa蓷in. "Yayi yadda yake so kamfanin nasu ne ba na wasu ba. Don Allah ku sakar musu mara na gaji da fitinarku, kada na kuma jin wata magana." Ta wuce dakinta bata kuma kula su ba, haka ta shiga ta bar su nan suna mita.


    Wannan fitinar ta dame ta, kowa yasaka musu idanu. Kowa ya saka buri akan abinda ba na shi ba, sannan baki daya kowa burinshi ya mallaki abin da yafi na dan uwanshi, a kan wannan zasu iya kashe junansu akan abin da ba nasu ba,

***

*Zahrah*

 Bana ce rayuwa tana da sauki a wurin Uwa irina ba, domin baki daya na susuce akan Babyna, zamowa uwa ba abu ne mai sauki ba. Haka na nakoma kome kamar mahaukaciya, bana barci da zarar naji motsinta duk barcin da nake na daina Kenan xan tashi daga barci har sai ta koma, wani abin da na kasa sabawa da shi, shi ne, da zarar na saka abinci a gaba Baby zata fara kuka, ba zata kuma shiru ba sai na hakura da abincin............

#Mai_Dambuje

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol