Free chapter 路 Read without an account

Five

by Aisha Umar 路 馃實 DUNIYA MAKARANTA!!馃

馃實DUNIYA MAKARANTA!!馃


Arewabook

https://arewabooks.com/u/nanabmb

My novels


RABON KWADO...!!


JARABTAR MU!!


RABO!!


AND NOW


DUNIYA MAKARANTA!!


Page Five


A yadda Ridwan yaga maman tashi ta fito ne yasashi boye yanayin sa ya sakin musu murmushi yana cewa.


" Auntie bashariya kece ashe a gidan namu! Haba shiyasa tunda na soma hawowa naji anama mama na fada, zan shigo kenan se gashi kin fito lpy dai ko! Mama bade tafiya zatayi bah?"


Wani sanyi Mama taji a zuciyan ta haka auntie bashariya koda taji furucin sa seta dan ci magani tana 莽ewa. "Wato yaron nan iya shegen ka kullum karuwa yake nice kenan sarkin fada ka harma kasan nice tunda kaji ina fada! To daga maman taka har Papa din naka basu wuce duka a guri naba, bare kuma kai karamin kwaro!" Zaro idanu Ridwan yay yana dariya yace. " Ai kuwa tunda suka aje kamata sun wuce fada bare kuma duka! Ni din nan fa bana yau bane! Bare kuma su!" " Ah lallai na yarda wuyan ka yayi kauri Ridwanu tunda kasami bakin mayar min da martani! Don iyayen ka nawa kake?"


Itama mama seta murmusa gami da cewa. " Wlh kuwa auntie duka nawa yake! Saboda yaga dukan mu ya kere mu tsayi ne da wan nan murdadden jikin nasa shiyasa yake dauka wani babban nan ne! har yake jin kansa, toka kiyayar min auntie nah!" Dole kam na kiyaye ta! Mama bama fa ki gaya min zatazo ba, dana dawo da wuri gashi yanzu har zata tafi!" Ya karashe maganar ne cikin shagwaba hankali kwance kamar basa cikin wani matsala, " karka damu Ridwanu tunda Allah ya dawo dakai seka maida ni gida muna fira" mama tace. " Kawai ba nima na huta da mita maza kaje daga can ma ta shirya muku abincin dare kaci ka koshi abinka!" " OH!! Mama kamar kinsan nayi missing ya Allah yau sena cinye miki abinci gaba daya auntie bashariya!" Yadda yay maganar da farin ciki ne harda shaking ya aje jakar aikin sa anan parlour ya fita abinsa dama suna maganar ne suna saukowa har suka iso parlour din, da idanu suka rakashi harya fice san nan Mama ta matso cike da damuwa zata cigaba da mata magiya ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu ta fice itama abinta, ba yadda zatayi ta dawo kan sofa ta zauna tana sauke ajiyan zuciya me nauyi ta rasa wani irin tunani ma zatayi ne jakar Ridwan din ta tasa a gaba tanata kalla tana shafa jakar,


" Ridwanu ya batun su Jawaheer? Yaushe ne ranar da zakuyi zaman kotu na karshe?"


Ridwan yana driving batare daya juya saitin taba yake cewa. " Nan da 2 weeks ne auntie bashariya! Al umma sunyi mana zuru da yawa jira suke suga matakin daza a dauka, akan su Jawaheer bansan meyake damun Papa ba! Yaki goyon bayan gaskiya Abbah idan yaki gaskiya bazan ga laifin saba tunda diyar sace shiya haife ta dole zeji zafi idan yaga yadda makomar diyar tasa zata kasance Papa ne ya kamata ya kwantar masa da hankali ya rarrashe sa, ya bashi hakuri tunda fari shine ya lalata Jawaheer batajin magana bata dau doka abakin komai ba! Sam bazan taba yadda hakan ya cigaba da faruwa ba, ay tarin dukiya ba hauka bane! Komai matsayin ta dole ta fuskan ta hukun ci!"


Cikin gamsuwa auntie bashariya tace. " Kayi gaskiya yarona, kuma nima ina goyon bayanka, karka sake ka goyi bayan rashin gaskiya gaskiya itace babban mataki na nasara a rayuwa da kuma tsoron Allah! Kome zeyi mahaifin ka ka kyaleshi nina baka umarni karka fasa tsayawa ka jajir ce akan gaskiya, jiki na yana bani wan nan al amari shine sabon babi daze bullo cikin rayuwar ka Ridwanu! Sede na tayaka Addu'ah Allah ya baka juriyar daure duka wani kalube dazaka fuskan ta!"


Murmushi Ridwan yay duk da be fahimta me take nufiba a yanzu yace da ita.


" Haba auntie bashariya! Tsayay yen jarumi dayake bauta don al umma banajin akwai abinda ze sameni na karaya! Mu yan gwagwar maya ne har zuwa sanda zamu kwanta dama, zamuyi aiki tukuru don yaki da gurbatat tu" Itama murmushin tayi cikin gamsuwa da maganar sa ta mika hannu tana dan shafa kansa alamun jin dadi da maganar da yayi.


********** ***********


BAYAN WASU YAN KWANAKI


ABUJA


Meenal tana kwance kan lun tsumemiyar sofa dinsu, suna a parlour suna watching TV tayi matashi da cinyan Mamee tanata tsula tsiyan ta kamar yadda ta saba, yadda aketa shirye shirye a gidan kadai zakasan akwai wanda zezo duba da yadda ma aikata aketa zuwa dining room ana decorations dinsa da cima mara adadi, auntie Lubna tana cikin farin ciki sosai saboda babban danta daze dawo daga UK ya kammala hada degree dinsa na uku, cikin wasa da jelan gashin ta datake Meenal tana daga kwancen tace.


" Mamee! Ina farin ciki ya Mahmoud ze dawo bana farin ciki!"


Da mamaki tace. " Miyasa kikace haka auta?"


Cikin shagwaba ta turo bakin ta gaba ta cigaba da cewa. " To ay ya Mahmoud yana dawowa wan can ya Bilal din ze soma mana zarya a gida, ze cigaba da zuwa yana hayyata min bayan nida gidan mu!"


Dariya auntie Lubna tayi gami da cewa. " Lallai ma auta! Wato keda gidan ku! Shiba gidan su bane? Kinfa iya fadan rashin gaskiya fa auta! Ke kyama ce haka tunda kina zuwa nasu gidan kiyi abinda anan ma bakyayi!"


Cikin tabe baki tace. " Mamee aini ba gunsa nake zuwa ba gurin Daddy nake zuwa ni ba ruwana dashi, na kagu ma yayi yay auren yatafi ya bar mana gidan mu shida matar tasa!"


Dariya ta kuma auntie Lubna gami da cewa. " To kuwa ki dena murna yarinya Bilal koyay aure a gidan su ze zauna bakiga ana kera dayan part din dake kusa dasuba, ay gurin sune!"


Cikin jin haushi ta mike tana me cewa. " Aini dama nadena zuwa gidan yaje yayta zama abinsa base ya kara ganina ba bare yaci zalina"


Sallama da Daddy yay ne yasa auntie Lubna fasa maganar da zatayi cikin farin ciki ta amsawa mijin nata sallama itama Meenal tana shirin hawa sama ne ya shigo parlour seta dawo harda gudun ta tana masa oyoyo taje tai hugging Daddy din nata cikin farin ciki da kauna, haka zalika shima cikin soda kauna na diyar tashi yadan shafi kanta gami da sumbata tsakiyan kanta ya dago ta tana ta murmushi ta amshi kayan dake hannun sa se a time din yace.


" Auta autares! Cakusawan me kikeyi ne keda Mamee din taki?"


Murmushi ta masa kawai ba tare data amsa maganar ba ta soma cewa. " Dad yaushe zamuje mu taho daya Mahmoud din?"


" Yanzun nan zamu tafi shalele! Jirgin su nasan ya kusa sauka yanzu!"


Ayseta buga wani tsallen murna taname zubar da ledojin data amsa hannun Dad din tai gaba a guje taname cewa.


" Bari nayi maza na canza kaya nazo mu tafi!"


Yadda tayi watsi da ledojin ne ya kalla Dad kawai seya girgiza kai yaname cewa. " Allah ya shirye minke auta!" Yana maganar ne yaname zama a gefen auntie Lubna din yana ceda ita. " Lubna! Alia batajin dadi ne tace na baki hakuri bazata sami zuwa taro Mahmoud ba, amma gasu Nabila da Nadiya can tace mu tafi tare dasu!" Fuskan auntie Lubna ba yabo ba fallasa tace. " Allah ya bata lpy! Bari naje na dauko mayafi mu tafi!" Mikewa tayi ta haye sama tabar shi anan yana binta da kallo cikin rashin jin dadi har besan sanda ya furta. " Ya Allah ka kawo min sauyi na alkhairi a cikin gida na! Ya Allah ka hada kan iyali na kona sami kwanciyan hankali" yana cikin tunanin ne yaji yaji Meenal ta amsa car key din hannun sa cikin barin jiki take cewa." Yau sonake naba ya Mahmoud mamaki! Dakaina zanyi driving dinsa har zuwa gidan nan!" Ay tunkan yay magana ma ta fella tayi waje abinta, da shigar nan nata yar kullum veil dinma a kafada aka rataye shi.


Da farin cikin ta ta isa gaban motan Dad din nata ay kuwa tayi turus ganin Nabila da Nadiya datai zaune a cikin motan, kamar taga kashi haka ta yamutse face suna kallon kallo, cikin rashin kunya data kware akai ta soma cewa.


" Wlh Yaya Nabila sede ku fito daga motar nan don bazan yi driving dinku ba kuje ku shiga naku motan tunda kuna dashi dagani se Mamee da Dad zamu tafi kuda zakuyi rakiya ma miye naku na wan nan shishigi!"


" Keee! Meenal wlh respect your tongue akaina!! If not wlh sena dakaki a gun nan na fito, mara kunya fitsarariya kawai idan banda an mana dole ma uban waye ze biku toh! Kuma idan bakije kin mayarwa da Dad key dinsa ba se ranki ya baci sena hanaki hawa motar inga yadda zakiyi! Baga motar uwar taki canba kije kihauta mana! Ai motar tata kike da iko da ita ba wan nan ba! Kin gane Koh!"


Wani banzan kallo Meenal take watsa mata tana wani gatsi na baki cikin wulakan ci tace. " Kaf gidan nan babu wanda ya isa yamin iko da kayan Daddy na! Babu shi wlh!"


" Ke dallah mara kunya matsa daga nan gurin! Inba hakaba na fito sena jinya taki! Tunda naga har yanzu uwarki taki miki tarbiya, ko kuwa mu sa annin kine? Ko yayan naki da kike takama dashi sede ya kalle mu wlh!"


Cikin harare harare Meenal ta soma cewa. " Wlh ki tabanin! Kinsan me zaki tabowa kanki aikin banza kun nane mana a gida kunkiyin aure kowa ya gajee daku!"


Murfin motar dama a bude yake kawai Meenal se tsintar Nadiya tayi a gaban ta zata cafketa batayi wata wataba ta kwasa a guje, tayi cikin gida ay kuwa sukai kicibus da Daddy ya fito ayseta soma kururuwa ta dafe shi tana cewa. " Daddy su yaya Nabila suna shirin kasheni zasu rabani da rayuwa ta!"


A dai dai time din auntie Lubna itama ta fito, cikin damuwa Daddy yace. " Me kuma sukayi miki Meenal?" " Dad saboda nace zanyi driving ne suka soma zagina wai sena mayar maka da key dinka donna ce bazan kawo maba ne yaya Nadiya ta fito ta soma dukana, wai sesun kashe ni kosa huta!"


Kama hannun ta yay suka tafi gurin motan nasa da auntie Lubna tanata matsar kwallah Meenal kamar gaske tunkan su Nabila suce wani abu yace. " Ku fito ku shiga motar ku! Ay gaskiya ta gaya muku tunda bakuda mutum ci kullum bakuda aiki sena daukar magana dacin mutum ci to wlh abin ya isheshi dole na dauki mataki akanku!"


Nabila baki ta bude zatayi magana ya dakar da ita yana cewa. " Karkice min kala tunda kin zama babbar banza ku fito min a mota bansan maganar kowa a cikin ku!" Babu yadda suka iya dole suka fito a motar yadda auntie Lubna taga suna cin maganine yasata cewa. " Kunga idan anyi muku dolane ku koma ciki abinku rakiyar aiba dola bace ku koma donni banason rigima!" Ko inda suke su Nabila basu kuma kallaba ta dauka nata key din motan a handbag dinta suka shiga, zuciyan Meenal fess fess ta shige motan Dady aka bude musu gate suka tafi.

********** **********

Bilal da Sara ne sukasa mummy a tsakiya sunata rarrashi taki yin shiru sakamakon daddy da akawo hospital ba lpy ciwon sa na diabetes daya motsa Mai, duk da Bilal shima yana cikin matsanan ciyar damuwa be hanashi rarrashin mummy tashi ba yana cewa. " Please mummy kada muma ki karyar mana da zuciya, Daddy in Sha ALLAH ze sami lpy kidena kukan nan haka kina sake daga mana hankali har idan zakina kuka haka mu sede mu sume kenan! Kiyita masa Addu'ah mummy ba kuka ba duk time din da Daddy bashida lpy sede kiyi ta kuka! Addu'ah zaki masa please mummy kinji!"


Cikin jan majina ta rike masa hannu tana cewa. " Wlh Bilal duk time din da Daddy ku ciwon sa ya motsa hankali nah tashi yake se naga kamar mutuwa zeyi yabar mu!" Saurin girgiza mata kai yayi yaname cewa. " Ba haka bane! Kidena wan nan tunanin mummy in Sha ALLAH Daddy yanada sauran kwana a duniya ay ciwo ba mutuwa bane kiyi hakuri kinji mummy!"


Cikin damuwa ya karasa maganar kamar zeyi kuka, seta sauke ajiyan zuciya tana cewa. " Bilal Daddy ku ya mutu wlh nashiga uku nikam.... saurin dafe mata baki yay yaname cewa. " Haba mummy se kace baki yarda da kaddara ba!" " Haba mummy keda zaki rarrashe mu amam munata fama dake muya kikeso muyi kenan?" Shiru tayima Sara baa kuma ce musu kalaba ta koma zancen zuci har Dr ya fito ya basu umarnin zuwa ganin Daddy din, jiki har bari yake mummy tayi ciki suka shiga room din dayake, lokaci daya harya rame, fuska tayi fayau yana ganin iyalan nasa ya soma musu murmushi jiki a sanyaye ta zauna kusa da dashi cikin nuna kulawa yadan muskuta saitin mummy din, muryan sa a sanyaye yace.


" Gaba daya kun tashi hankailn ku Koh! Saboda kuna tunanin zan tafi in barku, to bayan zuba tafiyan da saura ina nan daram ku kwantar da hankalin ku!" Sosai mummy taji dadi managar nasa ta rike masa hannu tanata juyawa cikin nasa yadda yaga jikin Bilal yay sanyi ne sosai seya Mikawa dan nasa hannu ay kuwa a hanzarce suka taho shida Sara a gaban sa ya tsugunna ya rike mai hannun dayake miko mai cikin tausayawa yace. " Sannu Daddy! Allah ya baka lpy!"


" Ameen gudan jinina in Sha ALLAH senaga yayan ka tukunna kafin na tafi jikoki na senayi wasa dasu naga naka iyalan kaima yarona!"


Sosai kunya ya kama Bilal seyay kasa da eyes dinsa yace. " Allah yaja kwana Daddy" Ameen ya Allah " shine abinda mummy tace kasance wa allura da akayi wa Daddy dinne bacci ya soma fisgan sa shiyasa Bilal ya gyara masa kwanciya ya maida kansa kan pillow....鉁嶏笍

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol