Free chapter · Read without an account

12- The Plan

by Azizat Hamza · TSOHUWAR SOYAYYA

12

*The Plan*

*........Sa'eed........*

Na fara samun karaya ne gameda soyayyar mu lokacin da mu ka dawo daga Cambridge.

Ina zaune a kan benchi kusa da Baffa Manu mu ka ji horn ɗin mota. Baffa yai sauri ya tashi zai je ya buɗe ƙofar na yi wuff na rigashi. Motar Alhaji Badamasi Bulama ne ta shigo cikin gidan. Ina gama rufe gate ɗin na ji muryan Baba Umar wanda ya ke tsohon dreban Alhaji Badamasi ne yana kirana. Na ƙarasa wajen sa da sauri ina gaida shi.

" Alhaji ya ce ka sameshi a falon sa yanzu" abinda ya faɗa min kenan. Ban kawo komai a raina ba na bi bayan Alhajin.

Ina shiga falon sa na zauna ƙasan kujera ina ƙarewa falon kallo ganin yadda falon yai kyau saboda furnitures da aka sake. Shekaru shida kenan rabona da shiga falon, tun ranan da Aaliyah ta kawo ni na zo na nuna ma sa admission ɗina.

Na yi aƙalla minti Ishirin zuwa ishirin da biyar a wajen kafin Alhaji ya sauƙo ƙasa, lokacin ya yi wanka ya chanja kaya zuwa jallabiya ta shaƙatawa.

Daga inda na ke zaune na duƙa na gaida shi. Cikin fara'a ya amsa mini tareda jinjina mini bisa ƙoƙari da na yi a makaranta.

"Sa'eed sai ina yanzu?" Ya sako tambayar bayan dogon shiru da ya karaɗe falon.

"Bautar ƙasa Alhaji" na faɗa kaina a ƙasa.

"Minna ko?" Ya tambaya bayan ina da tabbacin ya san amsar tambayan.

Na amsa ma sa da eh

"Ka na da ƙwazo da hankali, ga kuma tarbiyya" yai shiru yana nazarta na duk da ƙasa na ke kallo amma ina ji ajikina yadda idon sa ke yawo a kaina.

"Sa'eed na yiwa Aaliyah miji"

Da sauri na ɗago ido na kalleshi wanda hakan ne karo na farko a tarihin rayuwata da kalleshi ido cikin ido.

"Ba sai na maka dogon bayani ba,na san ka fahimci abinda na ke nufi"

A wahale na saukar da ido na ina jin maganar Alhaji na tsatstsafomin da wani zafi daga dukkan jijiyoyin jiki na. Abubuwa dayawa su ka fara yawo a kwanya ta. Duk wani tsari, shiri, buri ko mafarkina a kan Aaliyah su ka fara min yawo a ƙwaƙwalwa ta.

Ina sane da banbancin da ke tsakanin mu, ina sane da cewa abu ne mai wuya na samu Aaliyah. Sai dai na watsar da komai saboda na yarda da soyayya ta kuma na yarda da Allah. Ban fito daga gida ma su arziƙi ba amma arziƙi na Allah ne hakanan ban cire rai da samun sa ba. A duk lokutan da na yi tunanin rana irin wannan, na kan yi ƙoƙarin janye tunanin da cewa Allah shi ne ke tsara komai, kuma duk abinda ya tsara wa Bawan sa ba makawa sai ta auku gareshi. Soyayyar da na ke wa Aaliyah daga Allah ne haka nan kuma ko da mun rabu ma daga Allah ne. Tawakkali da na yi da wannan ya sa ban taɓa ɗaga hankalina ba sai ma na sawa kai na samun Aaliyah fiye da rashin samun ta.

Sauran bayanan da Alhaji yai duk ba wanda ya wuce fatar kunnena balle har su shiga su samu mafaka a cikin ƙwaƙwalwata har ma na fahimci abinda ya faɗa...

Ina son komawa wajen Baffa Manu amma kuma ba zan iya zuwa na sameshi a yanayin da na ke ciki ba. Na dinga takawa a hankali har na kai ɗakina, duhu na ga ɗakin ya mun lokacin da na shiga duk da kuwa hasken rana da ya karaɗe ɗakin.

"Sa'eed na yiwa Aaliyah miji" maganan Alhaji ya dinga dawo min. Na tsugunna a tsakiyar ɗakin ina dafe da ƙirjina, farat ɗaya soyayyar Aaliyah ya shigeni ba tareda na shirya ba, gashi yanzu ma farat ɗaya ake son raba ni da ita.

Na jima a durƙushe a wajen ba tareda na san minene mafita a gareni ba. Tabbas rashin Aaliyah a rayuwata tamkar rasa nawa rayuwar ne gaba ɗaya. Na dinga maimaita Innalillahi saboda na samu sauƙin ƙuncin da na ke ciki, ban iya barin wajen ba sai da Jiji ta shigo ta sameni a haka. Ganin yadda ta shiga ruɗu da yanayin da ta ganni ya sa na daure na tashi na yi murmushin da ko makaho ya san ba ta kai zuci ba. Masallaci na nufa bayan na nunawa Jiji lafiya na ƙalau kawai gajiya ce da kuma ciwon kai.

Ban dawo gida ba sai ƙarfe goma na dare duk da kuwa na san Aaliyah za ta yi ta ziryar nema na. Ban ma tsaya a masallacin ƙofar gida ba saboda kar ma ta aiko a kirani. Masallacin da ke chan cikin anguwa na nufa ina mai neman samun nitsuwa idan na je chan.

A ƙofar gida na samu Aaliyah da Baffa su na hira.

Ganina ya sa ta miƙe tsaye tana faɗin " Sa'eed are you Ok? lafiya ka yi dare yau?"

Na sani ba dan Baffa na wajen ba ba abinda zai hana ta rungumeni. Ina ganin tsantsar kewa da damuwa a ƙwayar idonta duk da kuwa hasken farin wata ne kaɗai ya haska wajen.

"Lafiya Aaliyah, na tsaya karatu da wani malami ne"

Na sani ba ta gamsu da bayani na ba, dan Aaliyah tana da saurin gane ƙarya musamman idan ni na faɗeta.

A hankali ta furta "amma dai ka san zan jira ka ko"

"Ki yi haƙuri Aaliyah, mantawa na yi"

Fiskarta sam babu alamar yarda sai ma fushi, ta yiwa Baffa sai da safe ta wuce ɓangaren su.

"Barka da dare Baffa" na faɗa ina ƙoƙarin shiga gida

"Lamiɗo zo ka zauna"

Ya faɗa yana nuna min gefen tabarma kusa da shi.

Ban musa ba na ƙarisa wajen na zauna ina sauke ajiyar zuciya.

"Ina son barin nan, ina son komawa cikin 'yan uwana, Shekaru sun jaa. Sabo da mutanen gidan nan ya sa na kai har iya tsawon wannan lokaci ban tafi ba. Amma idan mu na da rai ƙarshen shekaran nan zan koma gida"

Har ya ƙarasa maganar sa ban ce ƙala ba domin ba abinda zan ce ɗin.

"Lamiɗo" ya sake kira wannan karan da sigar jan hankali.

"Na'am Baffa" na amsa ma sa tareda yaƙinin magana zai min makamancin na Alhaji.

"Na san ka na son yarinyar nan sosai, amma ka yi haƙuri ka janye jiki daga gareta, ba na fata a samu matsala a iya zaman da ya rage min a ƙarƙashin Alhaji. Ka yi haƙuri Lamiɗo na"

Hannuna da ke rawa Baffa ya kamo ya riƙe yana faɗin "ka cigaba da addu'a Lamiɗo, har Allah ya sawa zuciyar ka nitsuwa. Rashin masoyi akwai ciwo"

Mun jima da Baffa a wannan dare yana lallashina. Kafin mu ka shiga ciki dan bacci, ni kam bacci ƙaurace mini yai gaba ɗaya. Ina son Aaliyah, ba na tunanin zan taɓa son wata bayan ta...

Cikin kwanakin da na yi kafin na tafi bautar ƙasa zuciyata ta yi laushi. Ba zan iya furtawa Aaliyah halin da na ke ciki ba, ina so ko da na ƙarshe ne to na kasance da ita, ina kallon murmushin da ke shimfiɗe a kyakykyawar fiskarta, murmushin da domin Sa'eed kawai ta ke yin sa.

Ban yi mamaki ba da na samu tafiya amma Aaliyah ba ta samu tafiya tareda ni ba, na san shirin Alhaji ne dan kar ma mu tafi tare. Lokacin da ta samu tafiya ma maimakon Minna da ta sa a farko sai a ka sa ta Maiduguri bayan kuma ba ta cika da Maiduguri ba.

Ranan da zan tafi kallon ƙarshe na yiwa Aaliyah domin ni kam na san daga lokacin Aaliyah ta yi min nisa.

"Sa'eed ka ga muna gama bautan ƙasa sai aure. Za mu fara zama a Durum kafin mu tafi duk inda aiki ya kai ka. Na missing ƙauyen ku"

Yadda ta ke maganan hakanan na ke jin zafi a zuciyata. Ina ma nima wani ne ko kuma ɗan wani ne a ƙasar. Ina ma Aaliyah ba 'yar kowa ba ce. Ina ma muna duniyar da babu haramci tsakanin auren talaka da maikuɗi.

"Beloved ba ka ce komai ba?" Ta katse tunanin da na ke yi.

Na yi murmushin yaƙe na ce "duk abinda ki ke so haka za ayi"

Da na ɗau jaka na zan tafi ta riƙe hannuna. " ba goodbye kiss ne?"

Na yi seƙeƙe ina kallon ta, ba wai dan ba na son yi ba ne a'a sai dan ina gudun haƙurin da na ke ta yi na tsawon lokaci zai iya ƙarewa.

Ta matso kusa da ni sosai ta  yi ɗegel da ƙafafuwanta saboda ta yi daidai da ni.

Ta sa hannu ta shafa fiskata ta ce " na kusa zama mallakin ka duniya da lahira masoyina" ta yi murmushi sannan ta fara kissing ɗina....

Tunda na tafi na ke cikin ƙunci amma a hankali ina addu'a abin ya fara min sauƙi. Sai da na yi wata ɗaya kafin na rubutawa Aaliyah wasiƙa amma har wani watan babu amsa, na sake kai wani wasiƙan shima shiru. Da bincike na gano abinda ke faruwa, jin mahaifiyar Aaliyah ce ta hana kai wasiƙuna ya sa na haƙura na fawwalawa Allah lamarina ina neman ya taimaka min kafin rashin Aaliyah ya ja min matsala a ƙwaƙwalwata...

Bayan mun samu mafitar aikawa juna wasiƙa Aaliyah ta aiko da wasiƙar da ta rikita ni.

*Sa'eed ka zo gida, idan ba ka zo ba zan kashe kai na, Ba zan iya auren wani bayan kai ba*

Iya abin da ta rubuta kenan. Na san halin Aaliyah na san za ta iya aikata abinda ta ce shiyasa tun farko na ɓoye ma ta abinda Alhaji ya faɗa. Ba ni da niyyar komawa Maiduguri har sai na ƙare bautar ƙasa ta amma wasiƙar Aaliyah ya chanja min ra'ayi. Ba ɓata lokaci na nemi a bani hutun kwana biyu amma hakan bai yiwu ba dole sai dai na haƙura zuwa ƙarshen sati...

Ranan Jumu'ah da yamma na hau mota sai Maiduguri, ba mu isa ba sai ƙarfe huɗun Asuba. A park na kwana sai da safiya na nemi taxi na wuce gida.

Baffa da Jiji sun yi mamakin ganina da sassafiya haka, na nuna mu akwai abinda na zo yi ne kuma kwana biyu zan yi na koma. Baffa bai yi magana ba amma Jiji ta ritse ni a ɗaki tana neman tabbatar da zargin ta.

"Saura kwana shatara auren Aaliyah. Lamiɗo Dan Allah duk abinda ka zo yi ka yi ka tafi ba tareda tashin hankali ba"

Na kalli Jiji wanda ita ta zame min uwa a yanzu na ce "Insha Allahu ba tashin hankalin da zai faru"...

Ban samu ganin Aaliyah ba sai bayan Azahar. Tana shigowa ɗakin ta faɗa jikina tana kuka.

Tsikar jikina ya tashi saboda yadda wani ƙanshi ke fita a jikinta, duk da Aaliyah ma'abociyar ƙanshi ce amma wannan ƙanshin daban ya ke.

"Sa'eed wai aure za'amin, wai ƙarshen wata aurena da Ahmad Wamako. Ka taimakeni Sa'eed ba zan iya auren sa ba, mutuwa zan yi"

"Shhhhhh" na sa yatsata na rufe bakin ta.

"Ban da zancen mutuwa Aaliyah, kin san hukuncin kisan kai kuwa?" Na faɗa ina ƙoƙarin danne duk wani raɗaɗi da na ke ji a zuciyata.

"Laifin ka ne ai, da ka amince da ni tun a makaranta da yanzu babu yadda za'ayi su raba mu"

Ina ƙoƙarin shawo kan ta amma ta ƙi saurarena. Ta riga ta tsarawa kan ta mafita wanda duk ciki babu mai daɗin ji.

"Ka amince mu gudu mu je mu yi aure Sa'eed. Its the only way we can be together"

"Aaliyah" na faɗa a hankali

"Kar ka ce a'a, domin zan aikata abinda ba ka yi tsammani ba"

"Please Aaliyah, mu yi haƙuri, Allah ya...."

Dariyan da Aaliyah ta fashe da shi ya sa na kasa ƙarasa maganar da na ke yi.

"Mu yi haƙuri fa ka ce. Sa'eed son da ka ke min har ya yi raunin da za ka sadaukar da ni ga wani banza. Har za ka iya rayuwa babu ni? Har za ka iya haƙura da ni a rayuwar ka? Ta ya zan fara zama da mutumin da bayan sunan sa ban san komai game da shi ba?. Ta ya zan manta da soyayyar ka da ta riga ta zama jinin jiki na?. Ta ya za ka ce Aaliyah ta sadaukar da farin cikin ta saboda son zuciya irin na iyaye na, ba su damu da ni ko farin ciki na ba, abinda aurena zai haifar su ke hangowa. Sa'eed ban shirya biyayya wa auren dole ba tunda addini ma ya hana hakan"

Shiru na yi ina nazartar maganganunta. Nima daurewa na ke yi amma na san rashin Aaliyah zai iya jawo min matsala a sauran rayuwata. To ya zan yi? Ban taɓa burin na auri Aaliyah ba tareda yarda da amincewar iyayen ta ba.

"Aaliyah albarkar iyaye ta fi komai" na faɗa murya na rawa saboda yadda hawayen Aaliyah su ka sa na ji jikina yai sanyi.

"Ka zaɓa min halaka kenan Sa'eed?"

Na zaro ido ina girgiza kai.

"Idan ba ka amince mu gudu ba kashe kai na zan yi"

Na cigaba da girgiza kai ina ƙoƙarin magana amma na kasa saboda wani abu daya toshe min maƙoshi.

Ta ɗan ja baya kaɗan kafin ta ce " ka yanke shawara daga yanzu zuwa dare, duk abinda ka yanke shi zai tabbatar da rayuwa ta a duniya ko kuma mutuwa ta"

"Aaliyah"

Ta fice daga ɗakin da gudu tana hawaye. Nima ɗin hawayen baƙin ciki su ka samu damar zubowa daga ido na...

Duk inda na je na dawo zancen ɗaya ne, na amince da buƙatar Aaliyah.

Tsoro na ka da na ƙi amincewa Aaliyah ta kashe kan ta kamar yadda ta faɗa. Idan haka ta faru zan ƙarasa rayuwata cikin nadama da ƙunci ina dana sanin ƙin amincewa da buƙatar ta da na yi...

Da dare ta zo jin abinda na yanke na kuma tabbatar ma ta na amince mu gudu amma da sharaɗi ba za mu yi aure ba har sai iyayen ta sun amince.

"Ka na ganin ko shekara nawa na yi ban dawo gida ba idan na dawo Baba zai yarda ka aure ni?"

"Ina da yaƙinin zai amince Aaliyah" na faɗa duk da kuwa na san da kamar wuya.

Aaliyah ce ta shirya komai ita ta tsara tafiyar mu da inda za mu je. Lafiya zamu je, a nan za mu zauna har iyayenta su haƙura da maganar auren ta da Ahmad Wamako. Duk da kuwa ban taɓa zuwa garin ba amma na amince da hakan. Acikin rai na ina fatan idan mun je a hankali na nutsar da Aaliyah da maganar kisan kai da ta ke ta iƙirarin yi saboda yanzu na san tsoron auren ya ke sa ta ke wannan batu.

Bayan tafiyar ta na yi alwala na yi sallah ina roƙon Allah ya kawo mana mafita ya kuma sa kar tafiyar da za mu yi ya jawo ma na sharri maimakon alkhairi da mu ke fata..

Washe gari da safe kusan ƙarfe goma ina zaune a ɗaki ina saƙe-saƙe a raina sai ga Musa ƙanin Aaliyah wanda su ke kira da Kalim ya shigo ɗakina.

"Hamma Sa'eed wai ka je in ji Baba" ya faɗa lokacin da ya shigo ɗakin ba ko sallama.

Na kalli yaron wanda shi ne autan Alhajin na ce " Baban yana ina?"

"Yana Garden" ya faɗa yana cusa yatsar sa a hannu yana tsotsa.

Na yi mamakin ya aka yi har Alhaji ya san ina gari bayan ko haɗuwa ba mu yi da shi ba, asalima ba kowa ya san ina gidan ba. Na tashi na sa rigata na bi bayan Kalim wanda ya fita daga ɗakin ba jimawa...


*........Aaliyah.......*

Tunda na samu Sa'eed ya amince an wuce wajen maganar ma idan mun je ba aure za mu yi ba jin sa na ke yi kawai. Idan har zan dawo gida to sai dai idan da auren Sa'eed zan zo. Na san halin Baba na, ba zai taɓa amincewa da aurena da Sa'eed ba kuma ko da ban auri Ahmad Wamako ba wani ɗan maikuɗin za a kuma jajuɓomin. Idan da auren Sa'eed akai na kuwa duk fushin sa ƙarshe haƙura zai yi ya bar ni na yi rayuwata da masoyina. Ko Sanah ban faɗawa shiri na ba saboda tsoron kada ta faɗa duk da kuwa na san za ta riƙe min amana amma Sanah tana da tsoro idan Amma ko Baba ta dage akan ta gaya mu su inda na ke za ta faɗa.

Ba kasafai na ke fita ba saboda gyara da aka fara yi min. Idan na fita to na je wajen aiki ne. Kwantar da kai da na yi tun daga ranan da na yiwa Amma magana ya sa ta ɗan sake min ba kamar da ba. Ko da aka fara min gyara ban yi gardama ba, duk abinda aka bani na ci ci na keyi hakanan wa ni turara jiki da sauran shafe-shafe duk ina zama ana min. Ni kam duk tanadin nan Sa'eed na ke hangowa ba Ahmad Wamako ba.

Safiyar ranan da za mu gudu na samu Amma a ɗaki akan zan je gidan ƙawata Daula da ba ta da lafiya ba ta musa ba ta ce na je amma na dawo da wuri. Dreban ta ne ma ya kai ni gidan su Daula. Zuwan da na yi kuwa rufa ido ne dan daga gidan na chanja kaya na fita ta ƙofar baya. Dreba na nemo na ma sa bayanin inda zai kai mu da kuma inda za mu haɗu da shi. Kuɗin da ya buƙata na ga sun yi kaɗan na ƙara ma sa ninkin sa tareda alƙawarin indai ya kai mu garin Lafiya zan bashi wani kuɗin adadin wancan. Dreban mai suna Bdliya yai godiya ya kuma nuna min lallai zai cika alƙawari. Na koma gidan su Daula daga nan Dreban Amma ya mai da ni gida...

Kuɗi da hotuna da sarƙoƙi, ɗankunne da awarwaro na gwal kawai na saka a sabuwar Jaka ta, wanda daga Cambridge na taho da ita kuma ban taɓa amfani da ita ba.

Kuɗin da na sa zai isa mu kama gida a chan sannan mu fara wani sana'a kafin abubuwa su dai-dai ta, idan ma kuɗin ba su isa ba za mu iya siyar da jewelries ɗi na. Bayan na haɗa komai na sa jakar a ƙarƙashin gado na cigaba da hidima ta...

Ƙarfe shaɗaya da rabi na dare na fito daga ɗaki ɗauke da jaka ta. Amma ke da girki dan haka tana sashen Baba. Ta ƙofar kitchen na fice daga ɓangaren mu ina sauri har na tafi wajen katanga.

Lokacin da Baba ya sawa yayana Aliyu dokar kulle ta baya wajen katangar gidan ya ke haurawa ya fita. Duk da katangar akwai tsayi amma ya riga ya yi rami ta inda zai taka ya hau. Da yamma sai da na zago ta wajen na tabbatar ramukan na nan ta yadda zan iya hawa...

Jaka ta na fara jefawa kafin na diro ƙasa, sosai na bugu dan har ina tunanin gwiwowina sun kukkurje amma ba matsala ta ba ce, matsalata na bar gidan mu, matsalata na bar garin mu, matsalata na auri masoyina Sa'eed.

Gudu- gudu sauri-sauri haka na dinga tafiya har na kai inda na ce Bdliya Dreba ya jirani. Da mamakina sai ban ga Sa'eed ba, tun a daren jiya na gaya ma sa plan ɗina, sannan yau da yamma da na je ɗakin sa na ajiye ma sa wasiƙa mai ɗauke da ƙarin bayanin inda za mu haɗu da sunan dreban da kamannin sa. Dole ne idan har ya shiga ɗaki sai ya ga wasiƙar saboda na ajiye ne a ƙarƙashin pillow kuma muddin Sa'eed zai kwanta to dole sai ya gyara gado. Balle ma na gaya ma sa idan na zo ban same shi a ɗaki ba zan bar ma sa saƙo.

Amma da ta sani a gaba tana nuna mi ni hotunan wa su kaya ya sa ban samu sararin sake zuwa na duba shi ba.

Ina rungume da jaka a cikin mota ina jiran zuwan Sa'eed amma babu shi babu dalilin sa. Ba ni da agogo a tareda ni amma na yi hasashen a ƙalla zan kai minti talatin a wajen.

Ina cikin mota sai ga wata mota ta hasko mu, na sa hannu na kare ido na saboda ƙarfin hasken. Motar ta yi parking aka buɗe ƙofa, tunanina Sa'eed ne dan ban gani sosai saboda hasken fitilar motar da har yanzu ba a kashe ba.

Sai da mutumin ya kusa isowa motar mu na ga ba Sa'eed ba ne. Maimakon Sa'eed yayana Bukar na gani. Na yi wuff na fito daga motar na ranta da gudu, shima ɗin ya bi bayana da gudu yana faɗin na tsaya. Gudu na ke yi kamar rai na zai fita hakanan kuma shi ma Bukar bai bar bina ba daga ƙarshe ma maimakon gudun mutum ɗaya sai ji na yi kamar mutum biyu ke bina. Ina cikin gudu Bukar ya damƙoni ta baya.

"Ka sake ni, ka sake ni in tafi" inaaaa, duk ihu da kuka na Bukar bai sarara min ba haka ya saɓani a kafaɗa har lokacin ina damƙe da jaka ta ina kuka ina kiran Sa'eed.

Haruna ne a gefen Bukar ɗin, shi ne wanda ya biyo Sanah wanda tsakanina da shi wata goma ne cur na bashi, amma saboda shi namiji ne yadda yai girma ka ce ya girmeni da shekara biyar ne.

Motar su su ka sani ta ƙarfi, gefen dama na Haruna gefen hagu kuma Bukar.

Ina jin dreba ya ja mota na ƙara sautin kuka na ina kiran " SA'EED"...

***

Anan na kawo ƙarshen free pages na littafin TSOHUWAR SOYAYYA.

*Shin ya labarin Aaliyah Badamasi Bulama bayan wannan dare?*

*Ya rayuwa ta kasance wa Sa'eed Aliyu Modibbo bayan ya saɓa alƙawari*

*wai ya za ta kasance tsakanin Zaid, Zarah da Aaliyah?*




Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol