Free chapter 路 Read without an account

002

by Auntysis 路 SADAKI

SADAKI...!


AuntySis 馃挏


002



Sunana Muhibba Hamza Akilu Malumfashi. An haifeni na kuma tashi a garin Katsina wanda shine state capital na jihar Katsina baki daya. Mahaifina Alhaji Hamza Akilu Malumfashi cikakken bahaushen garin Malumfashi ne inda family house dinsu kenan unguwar Kofar fada da kenan cikin garin Malumfashi. Malumfashi na daya daga cikin manyan manyan local governments din dake jihar Katsina. Mutanen garin kuma an shedesu da jajircewa wurin neman ilimin both boko da islama,iya mu'amala da mutane, wayewar kai gakuma kyawun halitta da Allah ya azurtasu dashi. Mafi yawan yan Malumfashi zaka samesu farare ne kyawawan gaske kamar fulani, duk da yawancinsu ma fulanin ne. Wadannan halaye nasu yasa duk inda ka shiga a kasar zaka samu ana damawa dasu kama daga kan harkar siyasa,aikin gwamnati kai harma da kasuwanci. Toh familyn mahaifina ma ba'a barsu a baya ba. Duk inda ka shiga a cikin garin Malumfashi kace familyn Alhaji Akilu Malumfashi ba wanda bai san suba duk da kuwa yawancinsu ba mazauna garin bane hutu kawai ke kawosu. Wasu na Lagos, Abuja,wasu na kano,Kaduna,porthacort dadai sauran manyan jihohin kasar tareda iyalinsu ana gwagwarmayar rayuwa dasu. Mahaifina da kanninsa mata biyu ne kawai kenan jihar Katsina. Daya na aure acikin garin Malumfashi(Aunty Laraba) a yayin da dayan kuma ketare damu acikin garin Katsina(Aunty Hassana). Mahaifina yayi aiki a wurare da dama ya kuma rike mukamai daban daban a jihar katsina bayan ya kammala karatunsa dan kuwa shi din mutum ne me basira da dole duk inda yashiga se an dama dashi. A yanzu haka mahaifina shine Director Ministry of chieftancy and religious affairs. Muna zaune a unguwar GRA dake nan cikin garin katsina. Gidan mu hadadde ne ginin zamani hakanan kallo daya zakama gidan da ahalin cikin shi kasan cewa muna cikin daula daidai gwargwado. Kuma ilmin boko da na addini ya ratsa ahlin gidan baki daya.


Matan mahaifina biyu Hajiya Asma'u(Mama) wanda itace mahaifiyata sai kuma Hajiya Kilishi( Umma) wanda itace uwar gida. Daga Mama har Umma dukansu yan asalin Katsina ne duk dama ita Umma ba yar asalin cikin garin katsina bace, Batagarawa ne tushenta. Mama da Umma zaman lafiya suke babu wani kishin hauka se dan abunda ba'a rasaba,kunsan dai zaman tare. Dole wataran a saba ma juna wannan dalilin yasa mu Yaran gabaki daya kan mu a hade yake.

A dakin mu mu takwas ne Yah Hadeeza,Yaya Al'amin,Yaya Farouq,Yaya Khalid,Yah Aseeya sai ni who's the 6th born to my mother and 13th to all sai Amatu da Isma'il. A dakin Umma kuma su goma ne Yaya Ibrahim,Yah Hauwa'u,Yah Ameena,Yaya Abubakar,Yah Maimuna,Yaya Ahmad, Yaya Abdulqadr, Fahad,Azeeza and Aliyu.


Kamar yanda na fada dazu duk da yawanmu babu abunda muka nema muka rasa a rayuwa. Mu ci mai kyau,mu sha mai kyau,mu kwanta a mai kyau,mu sa sutura mai kyau mu kuma je makaranta mai kyau harma Ya'yan wasu ma su samu dan kuwa Daddy nada wannan kokarin. He loves helping the less privileged regardless of ya hada dangi dasu kobai hada ba. Musamman abunda ya shafi neman ilmi baya wasa da shi ko kadan, daddy ba mutum bane da zaka je kayi banbadancin ya baka kudi don kaji dadin rayuwa, daddy mutum ne wanda zai iya kashe ko nawa ne ga iyayenshi, yan'uwanshi da al-umma don su samu ilmin addini dana zamani, a kullum zancen shi shine iya gadon da zan iya bar maku kenan da duk wanda na taimaka ya samu ilmi saboda ilmi bai karewa, dukiya kuwa tana karewa ta bar mai ita.

Dukanmu Kindergarten and primary school dinmu anan wata hadaddiyar private school da akeji dashi acikin garin Katsina mukayi mai suna Saldefi, a yayin da Secondary school kuma mukeyin ULUL ALBAB. Jami'a kuwa mu na kasa kasan ALQALAM UNIVERSITY ake nema mana even though Mazan Daddy na barinsu su nemi makaranta outside Katsina suyi in suna so. In zasu yi masters ko PHD kuwa dakanshi yake hobbasa wurin sama musu scholarship su tafi kasashen waje suyi bawai don bashida hanyar biya musu ba sai dan yana da dalilin sama musu su ci moriyar gwamnatin ne suma. Saboda yanzu komai sai da hanya, kuma dukkan mai dama yana damawa ne a lokacin da yake da damar.


Yanzu haka ina level 3 a ALQALAM inda nake karantar literature in English. Ni fara ce, tsawona ba mai yawa bane ba, bani da kiba sosai amma duk wanda yasan jikin dan Adam da ya kalleni ya san gaba zan iya kiba sosai saboda yadda komai nawa yake a cike, ina da yawan gargasan gashi da yawan cikar gira sosai ga gashin ido, shiyasa ko shafar zamani ake yi baa taba mun gira ba'a kara min eye lashes, Allah ya zuba min kyaun da in kamin kallo daya sai kaso kasake daga ido ka kalleni. Gani da son gayu da iya daukar wanka. Gayu na is very simple, saboda ina son komai simple, unique and classy, atamfa is my favourite a cikin suturar da nafi kauna, Burina inga na samu simple atamfa very unique ta sha stonework, wanda yawanci Asmee kawata ita ke da kokarin yi mun irin dinkunan da nake so, sai kuma lace mai taushi yaji embroidery ko beadwork, wanda shima duk aikin Asmeen ce, Jefi jefi ina dinka shadda musamman if I want to look outstanding. Duk wani latest kaya, dinki, designer bags and shoes kafin yafara yawo a gari nagama rocking dinshi saboda yawanci yayuna ke aiko mun daga kasashen da suke karatu musamman yayan dakin Umma don munfi dasawa dasu, wannan dalilin yasa na keda farin jini a wurin mutane suke kuma yimin kallon irin kema kinkai dinnan,barin ma mazan katsina da suke da nasu kalar son matan, harta Ya'yan manya anma sai dai duk basa gabana dan kuwa ni mutum ce that is not easily swayed. Abunda zaiyi saurin burgeku ni bashi zai fara catching attention dina ba. Ina da faran faran da saurin sabo da mutane, shiyasa tashi daya nake da shiga rai, amma ina da son girma da gudun raini, na tsani raini da wulakanci a rayuwata.I always keep it simple and low key. My spec is always top notch.


Ina da kyakyawar mu'amala da mutane wanda wannan din wani value din da Mahaifiyata da Umma sukayi installing mana duka Ya'yan gidan. Duk da mun taso cikin gata hakan bai taba sawa mun kaskantar ko mun kyamaci na kasa damu ba. Kowa namu ne hannun mu kuma a koda yaushe bude yake musamman ni da ko yan aikin gidanmu mutane na ne, ina da wani hali daban da sauran yan'uwana, ina son mutane da faran faran, gani da kyauta saboda ta nan fannin kamar gado mukayi, amma bani son ana yawan shige mun, duk da ina da surutu sosai amma kuma bani son a dinga shige mun physically kuma ba don rowa ba ko don kada in bada abun hannuna, aa kawai dai ko mai zai kasance tsakanina da mutane nafi son nesa nesa, tun mama na mun fada har ta gaji ta dena. Am news freak musamman abunda ya shafi siyasa da labaran dunia, shiyasa daddy ke mugun shiri dani, idan yana gida sai mu dade muna labarin abunda ke faruwa a kasar nan dama dunia baki daya, I always update him and he always do so to me, I love football, shiyasa muke shiri da wasu cikin mazan gidanmu masu son ball, I love wrestling too, shi dai bani da abokin hira sai yaya Farouk, fina finai kuwa bani da choice cos I watch anything watchable. Reading is my hobby, I read anything readable, I don't mind even if its newspapers or magazines, novels kam su Yaya Aseeyah na cemun uwar karatun novels and I love all genres. Infact it's my way of relieving stress....

Wannan features din yasa na zama very unique and outstanding a cikin yan'uwana saboda duk inda aka taboni ban rasa ilmi akan abun. haka kuma am active a social media but I hardly follow trend.


Wannan kenan.......

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.