Free chapter · Read without an account

Page 03

by Safiyya Haruna · Page 01

ZUCIYAR REEMA

©Mrsjmoon


Page 03


Tare suka fito da Abbie wanda tamkar haɗin baki kowa ya soma fitowa a ka cika Falon, Abbie ya umurci Sagir ya yi addu'a bayan anshafa ya dubi Abdul Basit ya ce "Allah ya tsareka gami da kariya akan duk kan abin k'i na fili da b'oye ya kuma baka nasara a abinda kaje nema sannan ya dawo mana da kai gida cikin k'oshin lafiya."


"Amin."


Falon ya ɗauka. Daga nan ya dubi 'yan uwansa cikin sakin fuska yana mai cewa "Saduwar alkhairi Brothers and Sisters, kada a manta da ni wurin Addu'o'in ku nima bazan manta da kowa ba musanman Ango da Amarya."


Dariya aka sanya cike da nishad'i daga nana suka soma yi masa fatan sauka lafiya gami da dawowa cikin amincin Allah. Yana murmushi ya fice suka rufa masa baya, Reema ce ta ƙarshen fita domin ta tsaya wurin Abbie inda tayi masa bayanin ita zata sauke Abdul Basit a Airport, ya yi mata fatar dawowa lafiya.


Sai da Reema ta shiga driver sit sannan ya shiga ya zauna gefenta na d'agawa 'yan uwansa hannu, ta mirror ta hasko fuskan Sagir kamar gobara ta murmusa tare da lek'o da kai saitinsa ta ce "Hy Hubby taho mutafi tare mana."


Ba yabo ba fallasa ya furta "Tafi kawai kaina na ciwo barci bai isheni ba."


"Ok take care, i love you."


Ya gyad'a kai gami da huro mata iskan bakinsa ta maida masa da martani, aikam su Nafisat suka saka shewa, iyayensu mata kuwa murmusawa sukayi. Ta ja motar tana yiwa Nafi dak'uwa, suna hawa saman Titi Abdul Basit da ya tsare gira ya ce "Gidan dake cikin Mall d'ina zaki kaini."


Kallon time tayi ya motsa kai tare da cewa "Sai 11:30 am jirgin zai tashi."


"Amma kacemin 6:30am?"


"Eh ko kina son cewa nayi miki ƙarya ne?"


"No."


Ta furta fuska a haɗe, ya ja tsaki mai sauti ta kalleshi ya nuna mata kan Titi a mugun hasale sai ta maida hankali kan tuk'i tana sake cin magani, daga haka bata sake magana ba shima haka har suka isa ɗan madai-daicin Mall ɗin wanda a cikinsa wani gate ne da ke ɗauke da babban gini da ya haɗa komi nabuk'ata tundaga filin motsa jiki zuwa matsakaicin swimpool da shuke shuke sukayiwa rumfa.


Horn tayi aka buɗe gate ta shiga ta gyara parking a gefen wata farar mota sabuwa dal, sai shek'i takeyi, sai ta tsaya kallonta shi kuma ya fice tare da tsayawa jiran ta fito.


Tare suka jera zuwa babban Falon gidan ya zauna na lumshe ido wanda ke nuni da barci bai isheshi ba.


"Have a sit Amarya."


Ya ambata cikin murmushin gefen baki.


Zama tayi gefen kujera tana tura baki gaba.


"Ba dodo ba ne ni balle ya cinyeki dan haka kin gama kwanciyata, 10:00am dai-dai nayi ki tasheni."


Daga haka ya baje saman Cushing ko takalma bai cire ba, sai ta mike ta ƙara masa gudun ac ta fice bakin swimpool ta zauna gami da soma latsa wayarta. Kiran Sagir ne ya shigo ta ɗauka ta kara a kunni ba tare da tayi magana ba.


"Kina ina ne?"


"Inda ka san na tafi."


"To gani a Airport ɗin ban ganku ba."


"Ok."


Tana ambatar haka ta kashe wayar baki ɗaya tana jan dogon tsaki. Ganin tunanin banza sai dameta sai ta fidda doguwar rigan jikinta ta koma daga ita sai legis da bra ta faɗa cikin ruwan ta soma iyo cike da kwarewa, hakan kuwa ya ɗauke mata hankali inda ta riga kai da komo cike da nishad'i.


Abdul Basit dake tsaye bakin window a d'akin barcinsa dake sama sai kallonta yakeyi na doka murmushi zuwa can ya furta "Aljanar ruwa kenan dama na san can zaki nufa, sam bakya jin tsoron ruwan sanyi duk kuwa da wuyan da mura ke baki." 


Sai ya soma ja da baya cikin runtse idanu har ya isa bakin makeken gadonsa ya kwanta na kallon ceilling cike da damuwa a saman fuskansa, a haka barcin da ya ke ji ya ɗaukesa.


***

Sagir kuwa turirin baƙin cike ne ya nashe ruhinsa tunda ya fahimci Reema kashe wayarta ya yi, sai ya gyara zama a cikin motar na cewa "Ina nan zaune har sai naga ta inda zaku ɓullo 'yan rainin hankali kawai, ai wallahi na zame muku ciwon ido hak'uri da ni dole tunda Reema dai nawa ce mai rabani da ita sai ikon Allah wanda bana fatar zuwarsa yanzu wato Mutuwa."


Ganin lokaci na ja har matafiya sun soma hawa matakalan jirgi amma baiga Abdul Basit ba sai jikinsa ya yi sanyi ya ja motarsa zuwa wajen Airport ɗin ya gyara parking a gefe inda duk wanda zai shiga ciki sai ya gansa, sai cika ya ke na batsewa na ayyana rashin mutunci da zaiyi mata a bainar jama'a.


***

Ta sami kimanin awa ɗaya tana kai da kawo a cikin ruwan sannan ta fito tana girgiza sumarta na fesar da ruwa, kujera ta d'auka a bakin swimpool ɗin ta kai wurin da hantsi ya soma fitowa ta zauna tana cigaba da girgiza kanta, nanma ta jima dan saida sumarta ya bushe sannan ta taso ta sanya riganta gami da d'aure sumarta da ribom ta ɗauki wayarta ta kunna ta shige cikin Falon ta zauna saman doguwar Cushing inda k'amshin turaren Abdul Basit ya mak'ale, lumshe idanu tayi tare da zamewa ta kwanta cike da jin barci amma tunowa da ya ce ta tashe shi ƙarfe goma sai ta kalli fuskan wayarta sai taga har tara da rabi ya yi sai ta fasa kwanciyar ta mik'e ta haura sama ta tura d'akinsa kai tsaye, ta hangosa ya baje na barci cikin kwanciyar hankali komawa da baya tayi ta soma kwankwasa k'ofar bata jima ba ya iso ya buɗe na murza idanu tare da furta "Har time ya yi?"


Kai ta gyaɗa masa tana kallon gefe saboda daga shi sai gajeren wando kirjinnan nasa ya cika da suma luf-luf.


'Suna kama da ɗan rainin hankalin can fa.'


Ta ambata a ranta.


"Kingama wankan kenan?"


Da sauri ta kalle shi ya watso mata harara sai ta tura baki tare da nufar hanyar sauka ƙasa, girgiza kai ya yi ya koma ciki ya sakarwa kansa ruwa a gaggauce ya shirya cikin suit Arsh color ya fito na zuba k'amshi, a fakaice ta kalle shi suka haɗa ido ta murmusa tare da mik'ewa tana cewa "You look gorgeous."


Bai tanka ba ya fice ta rufa masa baya, sai da ta iso jikin motar sannan ya miƙa mata keys ya ce "Tafi ki kulle Falon tare da tofa addu'a a bakin k'ofar."


Amsa tayi ta kulle ta dawo zata shiga gaban motar da suka iso ya ja hannunta zuwa wurin farar motar da ta tafi da imaninta d'azun ya ce "Buɗe da Bissimillah ki shiga mu tafi."


Hakan tayi sai da ta kunnata tayi worming sannan ta ja suka fice mai gadi nayi musu fatan sauka lafiya. Sai da suka hau saman Titi sannan ta tsinkayi muryansa na cewa "Tayi miki kuwa?"


"Me fa?"


"This car."


"Sosai kuwq, na yaba mala da iya zaben kala mai kyau da d'aukan hankali."


"Thank you."


"Your welcome."


Daga nan ba su sake magana ba sai da suka iso daf da Airport ya zuge glasses din motar tare da ƙara gudun ac na cewa "Sagir baida yarda, wai hala mantawa ya ke ni da shi Uwa ɗaya Uba ɗaya muke? To zan tafi na barshi da Amaryansa in ya so ya dafata ya cinye ba ruwan Abdul Basit bini Umarul Faruq."


Siririyan dariya ta sanya ya kaiwa kanta rank'washi sai ta fashe da dariya shima samun kansa ya yi da yin murmushi, ta shige cikin Airport ɗin tana cigaba da dariya lamarin da ya sanya fuskansa kasa yankewa da murmushi.


"I'll miss you."


Cak ta tsaya da dariyar.


"Gyara parking lokaci na k'urewa."


Ya amabata na kallon agogon dake d'aure a tsin-tsiyar hannunsa.


"Yaya me kake nufi da zataki kewata?"


"Abinda zuciyarki ta fassara miki."


"Please Yaya AB na yau dai kayimin maganar da zan fahimceka."


"Bana son ki fahimceni Reema, kiyi ta d'aukana a yarda zuciyarki ta baki."


Daga haka ya buɗe k'ofar ya fito ya soma takawa ta biyo bayansa da sauri suka shige wani wuri suka tsaya suna kallon cikin idanun juna shi ne ya soma janye nasa yana cewa "Amincin Allah ya cigaba da lullub'eki tare da danginmu baki ɗaya."


"Amin ya Rabbi."


"Khareematu zan tafi ban san kuma ranar dawowana ba, sai dai zan cika da kewarki tare da na kowa na gidan, idan Momy da Ummie sun dawo ki fahimtar da su domin ban san tafiyar ya matso ba shi yasa banyi waya da su ba sai in na isa can."


"Ok dan wannan kada ka damu zasu fahimceka."


"Bazakiyi kewana ba kenan?"


Shiru tayi ya kafeta da idanu ta kauda kai gefe tana mai cewa "Ambata da fatar baki bata lokaci ne, na barwa Zuciyata kawai, ina yi maka fatan samuwar nasara gami da samun kariyar Allah daga sharrin k'adangarun bariki masu sanjawa nagartattun Mazaje irinka ra'ayi daga mai kyau zuwa kishiyarta." 


A bazata taji saukan lips d'insa a saman goshinta sai kawai ta sami kanta da ware hannaye ta rungume shi, sun sami seconds a haka sannan ya janye jikinsa yana cewa "Amin ina godia da wannan shed'an. Ga mota nan taki ce ki ajiyemin keys d'in gidana idan kina da ra'ayin zuwa ki huta zaki iya, sai wata rana, saduwan khairan Hajiya Reeman Ummie."


Ya ƙarasa zancen cikin jan cheek d'inta, ita dai idanu kawai ta zuba masa, ya girgiza mata kai yana mai cewa "Banda dogon tunani k'anwata."


Daga haka ya shige inda ake da buƙatar su, sai ta ji hawaye sun zubo mata ta juya da sauri ta koma cikin motar ta kife fuskanta a kan steary ta saki kuka mai sauti.


"Bai kamata kyawawa na barnar hawayensu ba."


Da sauri ta d'ago ta kai duba inda muryan ya fito wani dogon saurayi ne wanda a kallo ɗaya ta gano dan gayu ne.


"Amincin Allah ya tabbata a gareki ya ke mai kyau."


Kauda kai tayi ta amsa da "Amin, tubarkallah."


"Masha Allah."


Ya furta na gyara tsayuwarsa sai ta janyo murfin motar zata kulle ya riƙe ta kallesa a kasalance ta ce "Da mallakin wani kake magana."


Da sauri ya ja baya na cewa "Affuwan Madam ban sani ba ne."


Motsa kai tayi tare da kulle k'ofar ta gyara zaman tana kallon jama'a domin sai ta ga tashin jirgi su sannan zata bar wurin. Kamar almara ta hango Sagir na ta shawagi a harabar wurin sai ta kafe shi da ido dan ta san ba zai ganta ba sai dai ita ta ganshi. 


"Wato Yaya AB ya gansa a waje kenan shi yasa ya ambaci sunarsa d'azun tare da kulle glasses."


Ta ambata tana auna masa mugun kallo tamkar na ganinta. Kimanin mintoci goma sha biyar girjin ya soma haramta tashi sai ta fito ta tsira masa ido har saida ya d'aga sama sannan ta koma cikin mota ta fice inda taga Sagir zaune saman motarsa na raba ido ta ja tsaki tayi gaba ba tare da ya gane itace ciki ba. Mai makon ta koma gida sai ta koma gidan da suka baro sai da ta zo fita sannan ta ga wata bak'ar bag, ko bata duba tasan computer ce a ciki ɗauka tayi ta fice zuwa Falon ta zauna a kasan carpet tana dafe gefen cikinta dan sai a lokacin ta tuna bata karya ba, tashi tayi zuwa kitchen ta samu kayan buƙata cike, nan da nan ta dafa jalof din shinkafa da kifin gwangwani kana da dafa Lipton da ya ji kayan ganshi ta fito ta ci tayi nak ta kwashe sauran ta kaiwa mai gadi ya amsa na zuba godiya ta dawo ta wanke kayan da ta b'ata sai ta haye saman Cushing barci ya ɗauke ta wanda ba ita ta farka ba sai karfe uku saura ta gabatar da Sallah sannan ta janyo bag din ta bud'e sai dai saɓanin tunaninta file ne ɗauke da tajardun ƙaddararorinsa ciki har na Kamfaninsu da gidan Ummiensu. Tagumi ta zabga tana mamakin irin yardan da Abdul Basit ya bata haka, sai ta maidasu inda suke ta mike ta fito ta kulle gidan ta fito zuwa bank dan bada ajiyar su sakamakon ganin note da tayi ya bata umurnin da ta kaisu can ta ajiye da sunarta. Daga banki gida ta dawo lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar magriba dan haka tana gyara parking ta fito da gaggawa, sam bata lura da shi ba sai jin saukan mari tayi a bazata tayi baya zata fad'i ya tareta na mazurai, ranta ya yi mugun ɓaci amma sai ta shanye tare da janye jikinta zata wuce ya fizgota ta dawo baya bashiri, ya jijjiga hannunta na cewa "Gidan uban wa kuka tsaya kuma me kuka aikata a can?"



Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol