Free chapter · Read without an account
Page 05
by Safiyya Haruna · Page 01
ZUCIYAR REEMA
©Mrsjmoon it
ADABI WRITER'S ASSOCIATION.
Page 05.
11:30am
Motar Sagir ya sanyo kai gidan yana gyara parking su Ahlan da Aslam 'yan biyun Momy suka kewaye motar suna tsalle cike da murna, hayaniyarsu ya janyo hankalin Reema da ke bitan wasik'ar jaki ta nufo harabar gidan cikin sar-sarfa, tana isowa dai-dai sun fito ta rungume Momy tana cewa "Barkanku da dawowa daga wurin mai cikakken tsarki."
"Yawwa my Dear dafatan mun sameku lafiya?"
"Alhamdulillah."
"Masha Allah."
Sai ta saketa ta koma kan Ummie dake dubanta cike da farin ciki. Kamo hannunta tayi ta sumbata sannan ta ce "Ummiena sannu ya ibada."
"Yawwa l, alhamdulillah Kharimatuna."
"Ummiena kin cika min alk'awari kuwa?"
"Wannan wajibi ne domin abinda na soma ambata kenan sadda na tsaya gaban Ka'aba kuma ina da tabbacin Allah ya karb'a."
Wani tsalle ta daka kamar yarinya sai kuma ta sunkuya ta kai goshinta ƙasa ta jima a haka sannan ta d'ago cike da farin ciki suka haɗa ido da Sagir ta d'age masa gira cikin cewa "Yallab'ai Ummiena ta gama min komi domin ta kaimin kukana a inda hawayena zai k'afe saboda addu'ar bakin mahaifiya na dabanne dana bakin kowa."
Tana rufe baki ta juya da gudu zuwa cikin Falo ta faɗa saman kujera ta kife fuskanta a hannun kujerar tana cigaba da murna a lokaci ɗaya kuma natsuwar ruhi na samuwa gareta wanda batayi tazo ba. Jikin Sagir ya yi sanyi, yana kallon su Ummie suka rufa mata baya suma cike da walwala sai ya koma cikin mota ya yi mata key ya fice daga gidan na jin matsanancin fad'uwa gaba.
"Me yasa na aikata?"
Shi ne kawai abinda ya iya ambata, bai ankara ba ya ji saukan hawaye a saman kumatunsa a rikice ya yi parking gefen hanya ya tsirawa fuskansa ido ta mirror wanda har lokacin hawaye ne ke zubowa.
"Me hakan ke nufi? Kenan Reema na daf da yin nasara akan k'udirina?"
Girgiza kai ya yi tare da kaiwa steary duka ya furta "No! Bata isa ba, ni ke da nasara, wallalhi in har ina numfashi sai na aureta na rayu da ita koda hakan na nufin mutuwarta ne saboda tsanar da tayi min."
Ya jima zaune kafin hawayen ya ɗauke sakamakon zafin da zuciyarsa ta ɗauka dama raunin da tayi ne hawayen ya sami daman fitowa, ya gyara fuskansa tare da mood d'insa ya kunna motar ya nufi super market da ke kan layinsu ya digowa Reema kayan zak'i wanda ya san tafi so tare freesh milk ya nufo gida cikin walwala domin nuna mata ya fita murna da farin cikin da take ciki.
Duk suna kan dining har da Abbie domin sai lokacin kowa ke gabatar da break fast, ya yi sallama suka amsa ya iso ya gaida Abbie ya amsa sannan ya ja kujera da ke fuskantan Reema ya zauna na kallonta wacce tayi tamkar bata san da shigowarsa ba amma fuskanta cike fal ya ke da murmushi.
"Hy R..
"Keep silent Sagiru."
Saif ya amabata a hankali.
"Very good Saifullahi."
Abbie ya ambata na kallon Sagir, sai ya haɗa hannayensa alamun ban hak'uri Abbie ya motsa kai, daga nan wurin ya sake ɗaukan shiru. Bayan sun kammala, su Momy d'akunarsu suka shige dan huce gajiya, Reema ta rufawa Ummie baya tana mai cewa "In taya Sweet heart d'ina barci saura wasu su kirani da bindin Ummie."
Dariya suka sanya tare da furta sunar a tare, tura baki tayi tare da watsa masu harara cike da tsiwa.
"Eyee lallai yarinya ta ga su Ummie sun dawo dole ta dawo da halin raina kowa."
Saif ya ambata cike da tsokana.
"Aikam faɗa mata dai Habibi kuma ba shi ne zaisa a murje bakin mutun ba."
"Ban da lokacinku ku, ki jira zuwa anjima madam Nafi."
Daga haka tayi gaba Sagir ya rufa mata baya tana jin takunsa a bayanta ta juyo tana sauke masa wani mugun kallo ya murmusa tare da juyowa yaga hankalin 'yan uwa na kansu sai ya buɗe murya ya ce "Hy ku shaida Sagiru ya fi kowa farin ciki da farin cikin da yau Masoyina ta samu kanta ciki dan haka dole ta zo ayi matsakaici party, a gwangwaje."
Ihun murna su Ahlan suka saka tare da soma rawa sai Reema ta dawo ta tsaya a tsakiyan Falon tana doka murmushi, Sanaaya ce ta soma yin tafi sai kowa na Falon ya ɗauka ta jinjina kai tana kallon cikin idanun Sagir wanda hakan yasa shi jin fad'uwar gaba amma da ya ke namijin duniya ne sai ya tako ya iso gabanta tamkar zai rungumeta tayi saurin ja baya Nafi ta yi fito suka saka ihu ita da su Twins ya yin da Saif da Sanaaya ke nazarinsu.
"I love You with all my heart Reema."
Sagir ya ambata cikin sanyin murya wanda kai tsaye Reema ta bashi suna da na yaudara.
"Please ambatamin hakan my Reema."
"Daram!!!."
K'irjinta ya bada sauti, ta ware idonu a kansa ya gyaɗa kai cike da marai-raita, ta tsuke fuska sai suka haɗa ido da Saif wanda ta hasko kallon tuhuma a fuskansa, dole ta aro walwala ta ɗora saman fuskanta inda ta saukewa Sagir kallon ƙauna ta hard'e hannayenta a k'irji tana wani lumshe idanu lamarin da ya sanya Nafi tafawa cike da yabawa salon ƙaunarsu.
"I really love you Reeman Ummie."
Ya sake furtawa muryansa na ɗan rawa.
"Ina son aurenka Masoyi wanda shi ne matakin ƙarshe na cikar so da ƙauna."
Ta ambata cikin sauti mai amo da ya ratsa cikin kunnuwar kowa da ke Falon.
Tsira mata idanu ya yi ita kuwa ta sunkuya ta soma buɗe chocolate tana sakawa su Aslam a baki suna ihun murna.
"Sagir and Reema."
Sanaaya ta ambata suka amsa da hanzari gami da maida hankalinsu kanta, ta motsa yatsunta suka bada sauti sannan ta soma magana "Ina sonki, zan aureka duk wad'annan kalaman sun wuce a tsakaninku yanzu domin Fatiha ya rage a shafa wanda nan da 'yan kwanaki zai tabbata dan haka bama son sake jin shiririta irin haka, oya ayi maza a bamu daɗin mu saka a bakin salati.
Ta kai ƙarshen maganar cikin raha, aka sanya dariya ya yin da Saif ya murmusa na son aminta da zancen da Abdul Basit ya yi masa akan masoyan.
'Zan kuwa maida hankali akansu dan gano abinda suke b'oyewa, musanman Reema da gano karatun ruhinta abu ne mai wahala.
Saif ya ambata cikin ransa na sake nazarin Reema dan zuciyarsa yafi aminta matsalar daga ita ne.
'Zan iya takona Barrister Saif.'
Reema ta ambata itama a ranta tana kallonsa a fakaice dan ta gano hankalinsa ya dawo kanta.
Cikin lokacin kaɗan Reema da Nafi suka k'ayata tsakiyar Falon da kayan k'walam din da Sagir ya siyo, suka zubawa kowa a gabansa tare da cup d'in fresh milk, suka soma ci da sha suna nishad'i duk da cikinsu a cike ya ke. Sanaaya freesh milk din kawai ta dauka saboda bata cin kayan yaƙi, Nafi ta kwashe ta haɗa da nata Saif ya dubeta na jinjina kai tare da cewa "Kubi dai a sannu kada baƙonku ya zo ku cika mana gida da ihu."
"Faɗama mara dauriya kam Yaya Barrister."
"Oh sabon sunar da akabani yau kenan matar Sagiru?"
"Kai Yaya wato karama kenan dai da wayau."
"Eh mana kinga anyi one-one kenan."
"Kana jinsa ko Masoyi?"
"Sunar ya dace da ke My love."
"To na bada kai tunda ka saka baki."
Harara Saif ya cilla mata ta kama kunni alamun ban hak'uri, Nafi ta rank'washi kanta aikam ta zabura zaka rama Sanaaya ta riƙeta tana cewa "Wai me yasa ba kwa girma da shiririta ne yanzu a gaban mazajen naku zakuyi dambe?"
Duk sai suka sunkuyar da kai, aikam Sagir ya fashe da dariya suka kalleshi ya nuna bakin Reema da ya ɓaci da cake suka sanya dariya ta dubesu cikin daure fuska.
"Sorry Reeman Ummie."
Ta murmusa tana kallon Sagir da ke ta doka murmushi sai taji ɓacin rai ya ziyarceta ta kauda fuska tana nemo abinda zatayi masa murmushin ya koma fuskan shanu.
"Ya isa haka nan tsokanar Sagir, yanzu dai kowa ya ci ya kuma sha amma kai komi baka ci ba me hakan ke nufi? Alhalin kai ka tara wannan zaman nishadin?"
"Banjin daɗi ne Aunty, wallahi kaina ciwo keyimin tun daren jiya."
"Ayya sannu ɗan uwa."
Saif ya ambata ya yin da Sanaaya ta k'i aminta da kalaman.
"Haba masoyi ai an wuce wannan babin na ɗorawa kai cuta, kawai ka fito ka sanar mata ni ka ke da buƙatar in baka a baki, dan haka Aunty Sanaa bari kigani."
Reema ta ambata cike da samun cikar burinta, ta mik'e da sauri ta shige d'akin Ummie ta fito riƙe da serchet na Sodrex ta balle guda biyu ta watsa cikin freesh milk da ke gabansa ta soma matsawa tana kallon cikin idanunsa wanda tuni ya gano manufarta lamarin da ya bashi mamaki, bai dawo tunanin da ya afka ba ya jiyo muryanta na cewa "Ka tuna da rana tamkar irin haka?"
Bata jira amsawarshi ba ta kafa masa cup d'in a baki tana cewa "Open your mouth my Baby, drink it all, it's so Sweet my dear Baby, drink mana, yawwa."
Samun kansa ya yi da soma sha amma ta yana jiyo kalamanta sai ya furzar da shi ya ko b'ata mata fuska ta runtse ido Nafi tayi saurin goge mata da tissue ta kalle shi ya langab'e kai sai ta murmusa tare da kama hannunsa ya mik'e ta ja shi zuwa kodido din da zai sadasu da d'akinsa tana mai cewa "Affuwan ku bari In kaishi ya kwanta ko ciwon kan zai sauka."
Suna b'acewa ganinsu ya matse mata yatsu tana jin sadda Zoben ya soketa sakamakon mai bud'ewar baki ne, ta ja yaji ya sake matsewa sai ta kai masa kyakykyawan cizo a kafad'a ya saketa ba shiri ta nuna masa hannunta da jini ke zubowa ya ware ido ta cije lips tare da zare Zoben ta d'aga sama ta ce "A hannun yaya AB na zareshi a she zai zamo sanadin famamin raunin da ke zuciyata, to ka sani kamar yarda naji zafin ciwon nan haka nake jin zafi a zuciyata a duk sadda naga fuskanka dan haka bakomi ba ne dan kana yimin mugunta ta hanyar fasamin jiki, kamar yarda ka fara da illatamin abinda yafi komi muhimmanci sai ido, rannan baki yau kuma yatsa, aikinka na kyau Sagiru Ummarul Faruq, wallahi bashi kad'auka ranar ramawa na nan zuwa."
Ta juya zata tafi ya fizgota ta fad'o k'irjinsa tayi saurin janyewa tare da hankadashi ya bugu da kofan shiga d'akinsa wanda hakan yasa ƙafor buɗewa ya afka ciki bashiri, sai ya nufota a fuska ce ta dage ta zabga masa mari wanda ya sanyashi komawa da baya cike da mamaki kafin ya dawo hayyacinsa ta nuna shi da yatsa tamkar zatayi magana sai kuma ta bar wurin da sauri, ta dawo Falo ta yagi tissue ta haye sama a hanzarce suka rakata da kallo cike da tuhuma.
"Me ke faruwa?"
Saif ya ambata cikin jiran amsa daga bakin Sanaaya, kauda fuska tayi tare da yin miƙa mai nuni da jin barci, kafin ya sake magana ta mik'e ta nufi d'akin Ummie tana cewa "Tambayesu ɗaya bayan ɗaya amma ni kaga inda na nufa sai mun haɗu anjima ka bani labarin."
"Da matsala kam."
"Habibi babu komi domin kasan jujun Reema wata k'ila faɗan masoya ne ta ɗauki zafi ko shi yayan ya ɗauka domin a bayyane Reema tafisa hak'uri."
"Kina da tabbacin hakan ne ya kasance?"
"Ban da shi amma ina son ka sharesu idan ba haka ba zasu baka kunya dan sunsha bawa Momy akan shiga irin wannan faɗar tasu a ƙarshe ta ce ba ruwanta da shiga sabgar shiriritan su."
"Ina haka ne nima babu ruwana."
It's better."
"Tafi ki sanyo hijab ki rakani wani wuri."
"Ok."
Ta mik'e shi kuma ya yi saurin nufar d'akin Sagir domin soma gano abinda suke b'oyewa.
***
Sai kai da kawo keyi na nushin iska gami da cije leb'e saboda tsaban fushin tozarcin da Reema tayi masa cikin bazata, sam ya kasa furta kalma ɗaya, jin motsin ana taɓa k'ofa sai ya haye saman gado ya kulle ido tamkar mai barci dan ya tabbatar ba Reema ba ce. Shiru Saifullahi ya yi na kallonsa kafin daga bisani ya isa gefen kansa ya taɓa wuyarsa ya ji d'umi sai ya janye hannunsa yana mai furta "Allah ya ƙara lafiya."
Ya fice cike da wasi-wasi.
'Hak'ak'a Brother AB ba zai sanar da ni abinda baya da tabbacinsa ba, amma koma meye zan gano kafin zuwar ranar bikinku domin ayiwa lamarin tubka kada ayi kitso da k'wark'wata, garin haɗa zumunci a b'ata zumunci.'
"Hy Habibi wai nazarin me kakeyi ko kana da wani case ne mai cike da sark'ak'iya?"
"Ko ɗaya kawai halin rayuwa nake nazari."
"Ko dai aurenmu kake burin a saka lokaci kamar yarda na aka tsaida na su Yaya Sagir?"
"Kusan haka ne Malama Aku."
Dariya Nafi ta sanya tana fari da ido, ya ja hannunta suka fice a Falon domin kawo ƙarshen zance ya san in ya biye mata ba zai san sadda zasu zauna ba saboda Allah ya bawa Nafi ilimin zak'ulo zance masu cike da hikima shi yasa ya kan kirata da Parrot kamar yarda yaji Reema na ambatar mata musanman idan ta sanyota gaba da tsokana.
***
Waiwaye.