Free chapter · Read without an account
Page 07
by Safiyya Haruna · Page 01
ZUCIYAR REEMA.
©Mrsjmoon.
Page 07.
"Nayi miki alk'awari Reema, bazan taɓa kauda kai daga gareki ba, ina rok'on Allah ya taimakeki a duk abinda kisa sanya gaba ya kuma baki nasara bisa Amincin mai badawa ba tare da wayon mutum ba."
"Amin ya Rabbil Alamin, godiya nake Uwata alfaharina."
Jinjina kai tayi tana tsare Reema da kallo wanda ita kanta ta rasa gano ko na menene.
"Ki yarda da ni Ummie, bazan aikata abinda baida manufa ba haka kome zanyi hankalina ne akan gaba tare da tuna tarbiyanki ganeni na hak'uri da abinda zaka iya tare da neman 'yancinka akan wanda ka kasa hak'urin."
"Ki zamo mai hak'uri da yafiya domin wannan shi ne tsanin da na taka har na cimmma nasarori."
Shiru bata da niyyar sake magana sai Ummie ta shafi sumarta da ya sha gyara tana cewa "Ta shi kiyi wanka dan ni da kaima zan shiryaki ki fito a Amaryanki."
Kauda fuska tayi tana murmushi.
"Oya tashi ki gani."
"To Ummie kayan wankan na d'akinki ai."
"Oh haka ne fa bari na kira a kawomin su nan, ina ganin wankan ni zanyi miki."
"No Ummie na wuce wannan matakin yanzu."
"Ai nan bada jimawa ba zaki dawo matakin, idan kika haihu."
"Wayyo Ummie ki bari mana."
"To na bari Reeman Ummienta."
Ta sanya dariya tana sake lafewa jikin Ummie cike da shagwaba'a.
A yammacin dai Ummie da Reema tare suka yisa a cikin d'akinta cike da farin ciki, sai bayan sallar Isha'i suka fito Reema ta gaisa da dangin mahaifinta 'yan matan da suka zo bikin wanda suke sa'anninta suka tasata da tsokana zamowarsu abokanan wasansu. Sanaaya ce ke kareta dan ta fita sakewa da su, yayin da ita kam murmushi take binsu da shi.
***
Sun shirya gabatar da Lunching ana jibi biki, Fulani day ana gobe biki, dinner bayan an d'auki amare zuwa gidajen mazajensu. A yau Alhamis da misalin ƙarfe hudu na yammaci motocin alfarma suka riƙa ɗaukan k'awayen Amare suna kaisu BASIT GARDEN wanda ya ke mallakin Abdul Basit. Wuri ne da 'ya'yan manya ke kamawa dan gabatar da shagalin biki ko birthday. Wurin ya tsaru iya tsaruwa, yanzu kuma an sake k'ayata shi saboda bikin k'annin mamallakin wurin za a gabatar.
Amare sunyi shiga iri ɗaya cikin tsadajjen lace mara nauyi, Maroon mai d'auke da Golden patten. Angwayan suma shigar su iri ɗaya ne cikin had'add'en kayan india, milk color har da yin rawani irin nasu maroon, sai suka fito tamkar Indiawan sakamakon suna da hasken Fata duk da bai cika haske sosai ba amma sun fita daga layin baƙak'e.
Tun tsaida lokacin bikin sai a wannan lokacin Sagir da Reema suka zauna inuwa ɗaya inda ya shagala da kallonta har sai da Saif ya mintsilesa sannan ya dawo hayyacinsa, suka haɗa ido ta tsuke fuska gami da motsa baki inda ya gano zarginsa tayi sai yaji ɓacin rai ya kawo masa ziyara amma kyawun da tayi masa gami da kwarjini ya hana masa jin zai ɗauki mataki.
Kamar yarda suka tsara manyan abokansa ne zasuyi driving nasu zuwa wurin shagalin dan haka kowa ya zauna a bayan mota da Amaryansa, babban aboki ya ja su.
K'amshinta ya cikawa Sagir k'ofofin hanci har ya kasa controlling d'in kansa saida ya kamo hannunta mai laushi ya sark'e da nashi yana matsawa a hankali wanda take jin sak'on na shiga b'argonta amma tak'i yin ko gezau, sai ya sake matsowa ya matseta jikin kofa ta kalleshi cikin tabarau din da ta sanya mai dan duhu dan kaucewa tuhumar jama'a tambayar ba'asin jan da idanunta ya yi wanda kukan baƙin cikin zata zama matar Sagir ya haifar da shi.
"Ka kama kanka tun kafin na kama maka shi."
Ta ambata masa hakan a hankali yarda shi kaɗai ne zai iya jiyota.
Sake matseta ya yi na jin tamkar ya tsotsi mitsi-tsin bakinta wanda ke burgeshi tun tana ƙarama amma yana jin shakkar yin hakan duk da yana da damar aikata hakan tunda sadakinsa ya jima da isa hannun magabatanta.
"Baka ji ba ko?"
Ta sake ambata a hankali.
Gyaɗa kai ya yi kamar sauna sai ta ja siririn tsaki tana cewa "Ko me kakeyiwa rawar jiki bayan kafin kowa sanin gonar."
Janye jikinsa ya yi ya tsare gira ɓacin rai ya bayyana saman fuskansa sai taji sanyi ya ratsa ruhinta ta saki murmushi mai sauti wanda kowa na motar ya jiyota, ta kai hannu ta manna masa mintsili a cinya ya saki ihu tare da kai mata duka ta riƙe hannun tana dariya ƙasa - ƙasa, Khalid ya waigo shi da budurwarsa Mubaraka, suna tambayar ba'asin ihunsa, Reema ta amsa da "Angona matsoraci ne."
Suka kuwa sanya dariya har da shi wanda ba haka ta so ba.
"Zan rama ne wallahi kome kikayimin saina fanshe har da gyara."
Ya furta mata a daf da kunni.
"Za kuwa ka rame, ina mai tabbatar maka."
"To mu zuba mugani shege ka fasa."
Shiru tayi masa ya kai hannu a waist d'inta na shafawa zuwa ƙasan mazaunanta, ta zabura ya ƙara k'aimi akan abinda ya keyi tayi biris da shi duk da lamarin ya soma shan ƙarfinta, ganin na son jik'a mata aiki sai ta kai masa duka da guiwar hannunta ya tare da ɗayan hannun na furta "Oh ya rabbi."
Khalid ya latsa horn na cewa "Easy Mr Sagir yarinya ce kada ka saka mata tsoronka mana tun kafin a shafa Fatiha ɗin."
Murmushi ya saki mai sauti tare da gyara zamansa na kallonta ya yin da ta ƙi motsin kirki saboda ɓacin ran taɓa mata jiki da ya samu damar yi.
"Namijin duniya ya wuce wargin mara kunya irinki wallahi ki bini a sannu ko na baki mamaki kafin d'aurin auren nan."
"Sai dai ka ƙara a kan wanda ka gama bani, mai son zuciya kawai mara imani."
Matse hannunta ya yi ta rintse ido ya sake matsewa sai ta fashe da dariya tana cewa "Wallahi idan baka bari ba sai na sanarwa Ummie cewa kana son lalatani tun kafin a kaini gidanka."
Me su Khalid za suyi in ba dariya ba,Mubaraka ta waigo ta ce "A gaskiya Oga Sagir ka barmin K'awa ta huta ko jibi mu nahaka ganinta akan lokaci."
"Na tuba."
Ya furza cikin hura mata iskan bakinsa a saman fuska.
Daga nan bai sake taɓa ko yatsarta ba har suka iso BASIT GARDEN inda Khalid ya sami abinyi ya tasashi da shak'iyanci na bashi amsa cike da nishad'i, ya yin da Reema taji tamkar ta d'ora hannu aka ta kwarma ihu saboda baƙin cikin ganinsa cikin walwala.
A tare suka jero dan isa mazauninsu, wurin ya cika ya batse, 'yan gayu masu ado da ilimin Boko gami da na addini sai kai da kawo sukeyi, harabar a jiye motoci kuwa da gani ba tambaya ƴaƴan masu hannu da shuni ne suka halarci taron domin tamkar ana gasar hawa manyan motoci haka suka k'awata wurin. Maza da Mata kowa ka gani cikin nishad'i ya ke ganin haka sai Reema taji natsuwa na sauka a ruhinta zamowarta mai son Jama'a, fuskanta ya sake cika da Annuri fiye da na basajan da tayi.
"Kinfi kyau a haka Dear domin murmushi na ƙarawa fuskanki kyau."
Sagir ya ambata mata a hankali.
"Ba dan ka yaba nayi ba dan haka ka riƙe shirmenka bana da muradin jinsu."
Matse yatsunta ya yi wanda ke riƙe da su suna takawa a hankali dan isa wurin zamansu.
"Mugunta ya gama zame maka d'abi'ar da kafi samun natsuwa a cikinsa, kai tir da wannan baƙin hali naka mai fuska biyu kawai."
Sassauta riƙon ya yi mata tare da jin ba daɗin shaidan da tayi masa akan zalinci duk da yasan a wani babin gaskiya ta faɗa sai dai yana ganin bai kamata a irin wannan lokacin ta jefeshi da kalamai marasa daɗi ba.
"Wow Yallab'ai Sagir kunsha kyau har ma kafi Amaryan haɗuwa."
Muryan wata matsakaiciyar budurwa ya doki kunnin duk wanda ke wajen, sai duk aka tsaya ana dubansu, wani malolon baƙin ciki ne ya tokarewa sagir wuya na ganin Nawwara amma ya hana bayyanarsa a kan fuskansa illa kallon su Saifullah da ya yi ya ga Nafi na auna mata kallon banza sai ya maida kai gefe cikin iya tako inda ya nuna tamkar ba da shi take maganar ba, ita kam Reema daga cikin tabarau d'inta take ƙare mata kallo, a take kuwa ta ganeta duk kuwa da shekarun da ta ɗauka basu had'u ba.
"Ashawo ta zo ganin abin ƙaunarta, lallai ina tayaka murnan soma nunawa dangi kaidin waye, abin b'oye na daf da bayya, munafunci doka kuma kan ci mai shi."
Ta ambata masa a cikin kunninsa inda ta sauke fuskanta saman kafad'arsa cike da son turawa Nawwara haushi aikam ta shak'a domin fara'ar da ke fuskanta take ya ɗauke, Reema ta kalli Mubaraka dake gefenta ta lumshe ido sai ta murmusa gami da gyada mata kai tana mai cewa "Kishiyar kalaminki dai domin kowa ya shaida Amarya Reema Sarauniya ce a tsakanin duk taron matan nan da mazajensu kuma haka ake muradi mata tafi miji kyau, su gayyan sodi a bamu hanya masu matsayi zasu wuce."
"Yes!!."
Sautin mutane ya amsa gami da fitar sautin tafi. Ja baya Nawwara tayi tana jin takaicin halartanta taron da ba'a gayyaceta ba amma da yake 'yar bariki ce ta bugawa a jarida sai ta wayance da cewa "Lallai haka zancen yake kuma nayi mubaya'a, Sarauniya Khareematu barka da isowa, Allah ya sanya khairan."
"Amin."
Nafi ta amsa cikin kaushin murya.
Kallon kallo sukayi Reema ta jinjina kai tare da sake nammewa a jikin Sagir ta rad'a masa "Ko da wasa banji kishin ganinta ba sai dai ina yin komi ne dan kare martabata dan haka kada wani tunani da ba zai amfaneka ba ya shiga kanka dan Reema tana nan kan bakanta, na baka yi mata ba haka baka cikin tsarin mazajen da zata zauna dan biyayyan iyaye balle ta zauna a ƙarƙashin ikonka ko ba so da kauna."
"Yes na fi kowa sanin inda kika dosa dan haka nayi farin cikin bayyanar Masoyiyarta na gaskiya a wurin taron aurenmu kuma zan baki mamaki domin daga yau dangi zasu gane me ke zuciyarki, munafukan banza da wofi kawai."
"Karya kakeyi Sagir Reema bata fito duniya ba sai da ta shirya domin tare take da kariyar Allah gami da addu'ar Uwa ta gari dan haka kayi kaɗan ka sanya na muzanta sai dai komi ka taro ya ƙare a kanka wannan haka zancen ya ke idan kuma kace wasa ka buga game ɗin kaga wanda zai fad'i."
Shiru ya yi na nazarin kalamanta sai kawai ya sami kansa da jin shakkar abinda ya yi nufin aikata mata domin b'ata mata rai da tona asirin zuciyarta dake hasashen ya sani. Ganin haka sai ta murmusa tare da yin ƙasa da murya ta ce "Wuyar aiki ba a fara ba Yallab'ai domin yanzu ka soma nazarin mafita indai Reema ce matarka."
Jinjina kai ya yi ba tare da ya sake furta mata kalma ba.
Suna soma hawa matakalan da zai sadasu da wurin zamansu Sanaaya ta soma fesa nasu turen Good Golden, k'amshi mai sanyi na ratsa ko ina jama'a na ta lumshe idanu, Reema ta kalleta cike da murmushi ta ce "Thank you my second Ummie."
Jinjina kai Sanaaya tayi tana sake wadata fuskanta da murmushi gami da jin daɗin ganin annuri a fuskan 'yar uwanta. Sai da suka zauna sannan ta dakata sa feshin turaren, kowa ya natsu ana sauraren kid'an taushi da ke tashi a hankali, zuwa can MC ya soma baje kolinsa da waƙoƙin kauna masu tada tsohon zuma ga masoya, aikam suka soma fitowa suna cashewa, Sagir da ke motsa kai a hankali ya take ƙafan Reema ta kalleshi ya sakar mata murmushi ta maida masa da martani domin ta fahimci so yake karatun ruhinta ya bayyana, inda zaka gaza hak'uri za karta masa rashin mutunci.
"Mawak'in can ya iya tsara kalaman ƙauna."
"Haka ne shi yasa na hango Masoyiyarta nata tiƙan rawa kamar 'yan gidan Gala."
Kauda kai ya yi na jin tamkar ya tashi ya shiga filin su cashe da Nawwara zamowarsa mai son duk abinda ya shafi kid'a da wak'a musamman wanda ake fitar da kalaman ƙauna. Reema kan na lura da takonsa sai lamarin ya bata dariya ta kalli gefen da Nafi ke zaune suka haɗa ido suka murmusa, haske ɗaukansu photo ya fito sai suka sake kallon juna aka sake ɗaukan photo, Reema ta sunkuya dan duba wayarta da taga alamun shigowar sak'o.
'Ki cire glass din idonki ina son ganinki kamar yarda nake kallon Nafi.'
Kallon number tayi sai ta sami kanta da murmusawa kana ta maida masa da amsa kamar haka "Idanuna ba lafiya ka san da haka."
Ba jimawa wani sakon ya shigo 'I know but mene kike b'oyewa mutane Amaryan Sagiru?"
B'ata rai tayi tamkar tana gaban shi sai kuma ta d'ago tana kallon Jama'a ba tare da ta bashi amsa ba, taji saukan hannun Sagir a kan nata ta kalleshi ya kai hannu ya zare madubin ta sunkuyar da kai da sauri ya sunkuya daf da kunninta ya ce "Ko ba komi kya yi masa alfarman ganin fuskan naki kamar yarda ya buƙata tunda har ya iya sakaki murmushin gaskiya ba na munafunci ba."
D'agowa tayi tana kallonsa cikin wani yanayi, shima kallon keyi mata cikin murmushi, aikam masu photo suka soma ɗauka ya yin da wurin ya kaure da tafi, numfashi ta sauke tare da lalibo maganin ciwon ido ta b'oye fuska a bayansa ta d'iga ya sake sunkuyawa daf da kunninta ya ce "Sorry da na zamo sanadin ciwon nan."
"Ciwon ido kaɗai nake da buƙatar ban hak'urin sa?"
Bai amsa ba illa kamo kafad'uta da ya yi da hannu biyu ya juyo da ita ba tare da jin kirin komi ba ya haɗe fuskansu ta nemi janyewa ya hana mata na cewa "Shin ba yana son ganin wani kalan kulawa nake baki ba? To ya shaida ina sonki sama da shi, ina kishin naga walwalanki a sanadinsa and I hate him a lot because of you, haka daga yau ki sani nayi komi ne dan rabashi da ke wanda kika riƙeni a matsayin mugu to na sanar da ke dalilina na yin hakan da fatan zan sami tsira daga kalaman bakinki masu mugun dafin da suka fi na saran kumurcin maciji."
Daga haka ya saki fuskanta tare da bata sumba a gefen kumatu, sai sowa ya kaure dama tunda ta maida fuska bayansa komi ya tsaya tsak ana kallonsu inda mafi yawansu sun burgesu yayin da k'alilan ke jin haushi makar irin Nawwara da masu burin ganin sun sami irin kulawan daga ababen ƙaunarsu, sai kuma Su Sanaaya dake kiransu marasa kunya, sun kasa kame kansu sai sun nunawa duniya.
Duk yarda ta so maida komi ba komi ba ta kasa sai kawai ta ɗauki madubin ta maida a fuskanta tana murmushi wanda kai tsaye Sagir ya bashi suna da na yak'e, haka ya kasa daina jin fad'uwar gaba abin da baiyi zaton afkawa ciki ba shi yasa ya zaɓi sanar da ita gaskiyan ta wannan sigan.
Kalamansa sun jefata cikin tutani amma sai ta watsar sai ta natsu tayi bitansa sad'ara bayan sad'ara. Wayanta ta kalla taga hasken shigowar sak'o ta duba, shi ne dai ya sake turo mata cewa "Jinjina ga Masoya idan kun koma gida zan kiraki dan nayi miki fatan alkhairi da soma hawa matakin cikar kamala."
Jinjina kai tayi dan ta tabbatar yana kallonta, ta maida wayar gefe tare da maida hankali kan abin da a ke gudanarwa inda kafin ta tantance me akeyi tajiyo ana buƙatar ganinsu a fili dan taka rawa. Da sauri ta kalli Nafi ta ko ɗauke kai gefe ta matsa tanayiwa Saif rad'a.
'Ban son rawar nan da akayi, zanje idan kin tabbatar ba zamu fito yin rawa ba.
'Ko kadan babu wannan zancen domin yaya Saif ya gama rarrashin mazarin mijinki ya amince ba batun taka rawa dan shima ra'ayinku ɗaya.'
'Nafi na san waye ke akan iya tsara zance.'
'Wannan ba tsari ba ne ki yarda da ni sister Reema.'
Numfashi ta sauke tuno yarda sukayi da Nafi sai gashi taga saɓanin haka. Hannun Sagir da taji cikin nata yasa ta kalleshi gami da zare glass d'in, shima ita yake kallo sai ta murmusa tare da motsa kai suka mike suka rufawa su Nafi baya wanda kafin su iso tayiwa Saif rad'a inda ya tafi wurin mc ya sanar da shi wani zance aikam a take sautin kid'a ya sanja, Sagir ya soma takawa tun kafin su iso cikin filin, aka soma tafi ganin haka ya soma juyawa da Reema cike da k'warewa, ta so janye jikinta sai ya d'aga cak na sauya kalan rawar tamkar mazari tare da bin wak'ar, aikam wuri ya hautsine da sowa tare da soma tasowar jama'a daga inda suke zuwa filin sunayi masu lik'i cike da nishad'i.
Kunya ta cika Reema sai ta kai hannu ta kama wuyarsa cike da tsoron kada ya jefar da ita dan ta san zai iya, bata dawo daga hasashenta ba ya ko sauketa a ƙasa da ƙarfi ta sai hannu zata kamashi ya janye na sakar mata murmushi, Nafi ce tayi hanzarin riƙota dan ta fahimci jiri ya kamata, jin ta soma dawowa natsuwarta sai tanemi hanyar ficewa a filin, Sagir ya sake riƙota ya soma rawa a hankali dan an sanja kid'a zuwa na taushi a hankali, dole rawar ya koma a natse, sai lokacin Saif da Nafi suka tsaya a filin suma suna rausayawa, 'yan uwa da abokanar arziki suka riƙa tururuwan zuwa yin lik'i.
"Please I want sit."
Reema ta ambata ma Sagir a hankali tana lumshe idanu mai nuni da gajiya tsan-tsa.
"Sai naga kin fad'i tamkar mai aljanu zan kyaleki wanda wannan shi ne cikar burina kinga ko da kinje gidana kina yimin hauka dangi zasu fahimci ba yin kanki ba ne daga nan sai a danga naki da Asibitin mahaukata."
Ware idanu tayi cike da mamakin furucinsa ya gyaɗa kai na cigaba da juyata cike da mugunta wanda ba wanda ya lura sai ita kad'ai wacce a ke yimawa.