Free chapter · Read without an account

4

by Sadiyamuhammadnasir · IYALAINA


    Murmushin jin dadi Falmata tayi, A ranar haka suka kusan raba dare suna zancen yanda zaman Falmata zai kasace A gida Alhaji Goni, da irin ukubar da Jidde zata fuskanta idan Falmata ta shiga gidan.


Alhaji Goni kuwa sai da yayi sallar isha'i kafin ya dauki hanyar gidan sa, Jidde da Yaranta suna Palo tana koya musu karatu yayi sallama ya shigo, gaba daya hankalinta ya tafi ga Abinda takeyi ko Alamar shigowar sa bata jiba.


  "Masha Allah" Ya ambata ya nemi waje ya zauna, Murmushi sukayi gaba dayan su Yaran su kayi Sannu da shigowa wa Abban nasu suka cigaba da bitar karatun su. Jidde tace.



 "Sabriya kina kula da Abinda Amaan yakeyi ina zuwa ko?" 


"To" Sabriya tace Jidde ta mike Alhaji Goni yabi bayanta zuwa dakinsa. 


Da shigarsu hanyar toilet Jidde ta nufa "Akwai Abinda za kiyi ne?"


"Aa wai naga ka dawo ne zan hada maka ruwan wanka"


"Bari Abinki dazu dana shigo na sake wanka, zo ki zauna muyi Magana"


"To" tace ta dawo gefensa ta zauna, dago ido yayi ya dubeta.


"Jidde?" ya kira sunanta.


"Na'am?" ta amsa murya A sanyaye.


 "Kamar yanda na faɗa miki yanda mukayi da Hajja yanzu daga gida Gwaggo Hajara na fito, na kai wa Falmata Sadaki kamar yanda Hajja ta Umurceni, ina mai kara baki hakuri kinji Jidde?" Murmushi mai cike da ciwo tayi.


 "Bakomai Abban Abie Allah yasa muna Raye za'ayi, ya kuma bamu zaman lafiya a tsakani".


"Ameen ya rabbi 'Yar Aljanna"


"Ya kamata kaci abinci ko?"


"Eh to Amma gaskiya Akoshe nake, ko zanci sai Anjima"


"To shikenan barinje mu karasa karatun?"


"Ba matsala, nima Akwai lissafin da nake son yi, sai kin dawo" Fita tayi a dakin ta koma Palo, Sabriya da amaan suna cigaba da karatu kamar yanda ta barsu, waje ta nema ta zauna.


 "Ke Sabriya?"


"Na'am Mummy?"


"Kuje maza ku kwanta gobe zamu karasa insha Allah" Da sauri suka mike dama sun gaji da karatun, tana ganin kulewarsu ta mike tayi dakinta tasa key. Wayarta ta dauka ta kira Saratu, tana dauka suka gaisa ta sanar da ita Ankai Sadakin Falmata.



 "Bakomai kiyi hakuri kinji Jidde? Komai zai wuce kamar ba'ayi ba, yanzu ya kamata ki sanar wa gida zancen Auren ko Akwai wanda zasu zo?"


"Zuwa kuma Saratu? Ba kisani ba? Nifa ce mishi nayi ya biya min Umra bana so Ayi bikin ina nan Idan yaso ina dawowa Nigeria na sauka A Kano"


"Laaa Haba Jidde? Ya kike so ki bata wayonki? gaskiya ba kiyi tunani mai kyau ba, Ai wallahi matukar kika bar Qasarnan Mutane za suce Kishi ne ya Addabi zuciyarki zaki gudu, kinga shikenan Falmata da sauran 'Yan-uwansa sun sami nayi, kuma ita dadi za taji, za tace kin tsorata da ita"


"Amma Ai...



"Ke Jidde kin san Allah ki Ajiye batun zuwa Saudi A satin bikin Ko za kije to ki bari Falmata tazo tayi koda Sati guda A gidan sai ki tafi, amma ni Saratu ban goyi bayanki akan Abinda za kiyi ba, kuma wallahi duk mai kaunarki kika sanar mishi kudirinki shawarar dana baki ita zasu baki, don haka ki nutsu kiyi tunani" Ajiyar zuciya Jidde ta sauke.



 "Yanzu kina nufin na samesa da Maganar kenan?"


"Kwarai kuwa A yau dinnan"


"Shikenan Nagode Saratu, Insha Allah yanzu zan kira Yaya Zainaba na sanar da ita zancen Auren".


"Yauwa zance kenan, Allah yasa mu dace ki kara hakuri"


"Bakomai nagode. Tana katse kiran number Yaya Zainaba ta kira, ita ce tamkar Mahaifiyarta A yanzu, domin ita ce Auta a dakin su, kuma Mahaifiyar su ta rasu tun Jidde nada shekara biyar A duniya, shiyasa Zainaba ta dauketa ta riketa hade da Yaran data Haifa tamkar itace Mahaifiyarta. Yaya Zainaba tana dauka tace.


 "Lafiya kuwa Jidde?" 


Dariya Jidde tayi "Kai Yaya ke kullum idan na kiraki bayan Sallah isha'i sai kice Lafiya?"


"Huhmm to ya zanyi Jidde? Kina can wata Uwa duniya kullum kina raina, baki da kowa naki A wajen dole na rika tsorata"


"Laa Yaya ki kwantar da hankalinki bakomai ina lafiya sosai, ya Mutan gida ya labarin Baba?"


"Lafiyansa kalau shekaranjiya naje na dubasa yake tambayata ke nace kina lafiya"


"Allah sarki ina so muna waya da Baba, Amma wa'innan Kannen Matarsa Mazan ba zasu bar wayar ba, da sun ga ya kauce zasu dauke, Allah ya kyauta".


"Ameen Jidde"


"Aunty dama na kira na fada miki Alhaji Goni zai kara Aure nanda kwanaki Goma, shine nace ko Akwai wanda za suzo?"


"Ikon Allah Aure kuma?"


"Eh wallahi Yar Uwarsa zai Aura, Ansa bikin A kurarren lokaci shiyasa ban sanar dake da wuri ba"


"Allah sarki to Allah ya Baku zaman lafiya A cigaba da hakuri Jidde, zama da kishiya ba kamar zama keda Mijinki bane, dole sai Ankai zuciya nesa, Insha Allah A cikin Yaranki za muyi shawara wacce zata zo"


"To Yaya Nagode Allah ya kara lafiya da nisan kwana"


"Ameen ya rabbi kice ina gaishe da Alhajin"


"Zaiji insha Allah" Tana gama wayar ta sauke ajiyar zuciya ta mike tasa kayan barci ta nufa dakin, Yana zaune yana latsa system ta shigo, zama tayi A gefensa "Sannu da Aiki?"


"Sannu da shigowa?"

Kura wa system din idanu tayi, ganin haka yasa ya cigaba da aikin yana Mata bayanin Abinda ya keyi, a haka har ya kamala, yana shirin Mikewa tace "Alhaji ina son Magana da Kai?" Dawowa tayi ta zauna "Ina jinki Jidde?"


"Yauwa batun Umra ne, wata shawari na yanke, kawai a bari sai bayan biki na tafi, naga kamar hakan zai fi" Murmushi yayi Domin yaji dadin zancenta "Ko meyasa haka Jidde?"


"Kawai Alhaji ya kamata Ace Anyi bikin ina gari"


"Hakane nima hakan naso amma sabida kwanciyar hankalinki yasa nayi shuru, Allah ya kaimu kamar da kwana nawa?"


"Eh ko sati guda da Auren"


"To shikenan Gobe ina so zanje Abuja na duba Abie, Amma zan dawo da wuri sabida Jirgin safe zanbi"


"Allah yasa zamu kai" mikewa yayi zuwa Toilet.


  Washe gari da safe kuwa haka ya dauki hanya zuwa Abuja, bayan ya isa haka ya hada Abie da Jidde A waya su kayi magana sosai, Nan take sanar wa Abie Abban sa zaiyi Aure ga kuma wacce zai Aura, yana shirin korafi tace mishi koda wasa idan ta sakeji zata saba masa, haka ya bata hakuri suka danyi hira ya kashe wayar, Kudi sosai Alhaji Goni ya bayar wa Abie ko Akwai Abinda zai bukatar zuwa Ayi Hutu, sosai yayi murna. Sai karfe biyar kafin Jirgin da zai koma gidan ta tashin.


Kafin ya iso gida Jidde ta tanadar mishi komai da zai bukata. Yana isowa yayi wanka yaci Abinci yasa kai ya tafi gidan Hajja, Nanma wani kudin ya kashe a gidan sabida Hajja tace mishi tana son su Kubra su hada walima wa Falmata. Haka dai ya biye mata ya mata Abinda take so, bayan abunda ya turawa kubra na lefe da sauran al'ada. sai wajen karfe tara kafin yabar gidan.


Gidan su Falmata kuwa kamar yanda Gwaggo Hajara tace haka ta tura Falmata wajen Kawarta A Maradi Aka fara gyarata da kaya masu inganci, banda kayan Mata har dasu gyaran jiki Ake mata, kafin kwana biyu fatar jikin Falmata tayi kyau shining kawai take, wani karin fitinar harda dinki akayi wa Falmata sabida taci Amarci da kyau.


  Ana saura kwana hudu biki ta dawo, Falmata tayi kyau matuka, farin fatar nan sai sheki kawai take, ita kanta Gwaggo Hajara bata gajiya da Kallon Falmata yanda tayi kyau Abin dai ba'a cewa komai, wani Abin takaicin da yake damunsu ita da Gwaggo shine, tun ranar da Alhaji Goni yazo gidan bai sake dawowa ba, sannan ba waya sukeyi ba, sau biyu tana kiransa lokacin tana Maradi yace Mata yana Aiki idan ya gama zai kirata, amma shuru ba zai kira ba, shiyasa tsanar Jidde ta kara karfi A zuciyar su, A tunaninsu wani Mugun Abin tayi musu, shiyasa Falmata ta dauki Alwashin gasa wa Jidde Aya A tafin hanu.


 Ta bangeren Jidde kuwa kamar yanda Saratu tace da ita haka takeyi, sosai ta danne damuwarta tana kula da Mijinta yanda ya kamata, Amma ko wace rana idan ta farka daga barci sai taji gabanta yana faduwa sabida Falmata ta kusa zuwa. Ana saura kwana biyu biki Hafsa Yar Yaya Zainaba da Karamar Yarta suka iso garin Maiduguri, zuwan Hafsa Maiduguri shiya ragewa Jidde damuwar da take ciki.


Tun A ranar da Hafsa tazo ta fahimci Autyn nata tana jin Auren A ranta, Kayan gyaran Jiki Hafsa tazo mata dashi daga Kano, haka ta karba ta fara Anfani dashi, domin Saratu ta fada mata yanzu dole tayi himma sabida Kishiya za'ayi Mata.


 Ana gobe Aure Halima da Zara'u da Kubra kannen Alhaji Goni suka zo gidan, ko wacce fuskarta A turnuke tamkar hadari ya hadu, Jidde suna zaune A Palo suka shigo bbu wata cikekkiyar sallama dan su kansu sukaji idanma sunyita Kallon sama da kasa su kayi wa Hafsa kafin suka juya kan Jidde haɗeda yatsine fuska ga dukkan alamu nemen fitina ya kawosu. Aikuwa hakanne dan zara'u tadubi jidde tafara magana.



 "Abu daya zuwa biyu shiya kawo mu wajenki Jidde, gobe dai Yar Uwar mu zata shigo gidan nan, wacce zata wanke mana zuciya ta samu farin ciki, gargadi mai cike da Jan kunne? matukar kikace zaki takura wa Falmata a gidan nan wallahi wahala za kisha, don sai ki koma inda kika fito ita kuma ta zauna" Halima ce ta juya ta dubi Hafsa.



  "ke kuma daga ina? Kinzo cin Arziki babu A gidan Mahaifi ko?" Harara Hafsa tayi musu.


"A tunaninku kenan Ai duk cikin ku wancan karamar Yarinyar ce kawai ba taje gidan Mahaifina ba, kuma idan Akwai talauci kun sani, Ku gayara kalamanku idan kunsan na faɗa baku san na mayarwa ba, wani darene jemage bai ganiba don Allah? Mu kuma har Akwai arzikin da za'ayi mana gadara? Allah na tuba yaushe Alhaji Goni ya shahara da har za'ayi Mana gor...  Wani irin Mari Jidde ta wanke Hafsa dashi jikinta harna rawa.



  "Koda wasa Hafsa babu ruwanki?" Kama kunci Hafsa tayi ta wuce daki da gudu. Tsaki su kayi.



  "Jaka kawai , kin rufa wa kanki Asiri da kika hukunta ta, Yau da Yarinya taci Uwarta. Zamu tafi idan kunne yaji gangan jiki ta tsira" Cike da Izza suka bar Palon. Da sauri Jidde tayi daki hankali a tashe, zaune ta sami Hafsa ta hada zufa sai Ajiyar zuciya take saukewa, zama Jidde tayi A gefenta ta kama hanunta, sai a sannan hawaye masu zafi su fara sauka akan hanun Hafsa.


 "Don girman Allah Hafsa kiyi hakuri? Ki rufamin Asiri kar ki fada wa Yaya Abinda ya faru? Wallahi lafiya kalau muke da Mijina yana sona ina sonsa, wa innan kuma ki manta dasu don Allah? Masu Neman haddasa fitina a tsakani ne, kinsan Auren dangi ne Don Allah Hafsa?" Ajiyar zuciya Hafsa ta sauke 



"Huhmm Aunty haka kike rayuwar Aure A gidan nan? Da Mutuncinki da kimarki wa innan suna ci miki Kashi Akai? Kuma kiyi shuru? A inane akace ki zauna Kannen Miji suci miki kashi Akai? Tabdijam"


"Aa Hafsa ba haka bane" Jidde ta fada murya na rawa, domin tabbas Hafsa ta sanar wa Yaya wannan Magana shikenan zata dauki damuwar duniya tasa wa ranta, yanzu sai ta fara ciwo.


 "Kinyi shuru kince ba haka bane to Yaya ne?"


"Hafsa wallahi Miji na yana sona, haushin soyayyar dake gwadamin yasa suka kulleceni har suna tunanin asiri nayi mishi, duk wani farin ciki da Mace take bukata wajen Miji ina samu Hafsa, ko wannan Aure da za'ayi biyayya ce Amma baya wani so, yanzu idan kika sanar wa Yaya zata kullaci Alhaji a rai, sannan zata rasa kwanciyar hankali, don Allah Hafsa ki rufamin Asiri mubar Maganar Anan?"


"Huhmm shikenan sai a zuba idanu suna ci miki kashi Akai? Ai sabida baki da hayaniya shiyasa zan sanar wa Mama, kar watarana kawai muji sun miki duka" Dariya Jidde tayi.



 "Haba Hafsa, ai suna tsoron Yayan nasu, kuma ai ba jaka Aka kawo musu ba, kawai Abinda yasa su kazo sukayi wannan Abin, haushinsu daya ne? Naki na gwada musu Auren ya dameni, Amma sukan jima ba suzo ba"


"Huhm Allah ya kyauta" haka Jidde tacigaba da kalallame Hafsa da dadin baki har tayi mata Alkawarin ba zata fada wa Yaya wannan zancen ba.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol