Free chapter · Read without an account

8

by Sadiyamuhammadnasir · IYALAINA

     "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'um na shiga uku. Jidde ta Ambata ta yasar da wayar jikinta harna rawa, kalaman Falmata ce suka fara yi mata yawo A kwantar Kai, take ta fara ganin jiri! zuciyarta ta soma kitsa mata abubuwa barkatai marasa kyau. Runtse idanu tayi hawaye masu zafi suna saukowa bisa kuncin ta. Tun A ranar farko kenan Abban Abie zai fara cin zarafina sabida yayi Amarya? Ashe duk Maganar da yake fada min da Alkawarin daya dauka min a banza ne tun ba'ayi nisa ba?" Kuka ta fashe dashi sosai tuno Kashedin da Alhaji Goni yayi mata Akan wayar sa, ya fada mata ko da wasa duk Abinda za suyi karta kusanci wayar sa, shiyasa tsakaninta da wayar sa idan ankirasa ta mika masa, ko baya kusa aka kira bata gigin daukar masa waya, Amma yau sabida dadi Amarya har bata wayar yayi? Kenan ya samu wacce ta fini iya kwanciyar aure shine zai bata wayar sa ta fada min sako sabida ya kara Jin dadi da ita?. Sosai take kuka tana jin Kuna a zuciyar ta.


Saddiqa ce ta fito da niyyar zuwa kitchen hada wa yara Abin kari taga Aunty nata durkushe a kasa tana kuka, Abinda bata taba gani ba tun zuwanta gidan "Subhanallah! da sauri ta karasa Aunty lafiya? Rasuwa akayi ne? Innalillahi wainna ilaihi raju'um". Ko Uffan Jidde bata ce da ita ba ta cigaba da risgar kuka, ganin taki magana yasa Saddiqa haurawa sama da sauri tayi dakin da Hafsa take kwana, sai gashi sun fito da sauri zuwa kasa. A rude Hafsa tayi kanta ta jawo ta jikinta "Aunty Lafiya na shiga uku, ba yanzu kika fito a dakina ba? Meye ya faru? Don Allah ki fada min?" Cikin yanayi na kuka Jidde tace "Abban Abie ne Hafsa"


"Yayi me Alhajin yana ina bai dawo bane? Wani Abin ne ya samesa A hanya?"


"Aa ta lafiyar sa kalau Hafsa"


Ke Saddiqa je kiyi Abinda za kiyi ina ce Yara zasu je Islamiya ne?"


"Eh Aunty" Ta Anbata da sauri tayi hanyar kitchen. Gyara zama Hafsa tayi "Aunty don Allah ki fadamin meye ya faru? Ki dubi yanda kike kuka tamkar ranki zai fita? Ni wallahi kin sani a damuwa! Wani irin kuka haka? Allah na dauka mutuwa Akayi mana?" Ajiyar zuciya Jidde ta sauke ta mike ta zauna da jajjayen idanu tana share kwalla "Hafsa Ashe Abban Abie yana gida ko masallaci baije ba sabida dadi Amarya?Tun fitowa ta daga wajenki nake zaune A Palon nan ina dakon Abban Abie, ganin bai dawo ba yasa na kira wayar sa, kawai Falmata ta dauka ta cakka min magana, yana zaune kuma yana jin ta? Kinga kenan Tun a ranar farko Hafsa zai fara juya min baya sabida yayi amarya?"


"To kiyi hakuri ita Falmatan meye tace miki? Share kwallah tayi ta kwashe komai ta fada mata. Ajiyar zuciya Hafsa ta sauke, Lallai Aunty da sauran ki, ni da nake kasa dake nasan makirci ne wannan, har ki zauna kina zubar da kwallah? To inda itace ta fito ta sameki a haka fa? Kinga shikenan ta samu kanki, a lokaci kankani tasan Makircinta zaiyi tasiri Akanki, meye a cikin Kalmar data fada da har zai sakaki kuka haka? Idan Miji ne cikin Ku wacece ta fara sanin dadin sa? Da har wata Mace za tazo ta nemi wasa da hankalin ki? Ina rabaki wallahi Aunty? Idan Falmata ta fahimci makircin ta zaiyi tasiri Akanki shikenan zata cigaba dayi tana hadaki da Mijinki. In banda ke Aunty da rudewa ke kinji muryar sa yana Answer mata maganar?"


"Ban jiba Hafsa Amma Ai ko bai Amsa ba yana ji tunda daki daya suke kwance"


"To ke baki tsammanin yabar wayar a dakin yaje Masallaci?"


"Yana gida Hafsa, jeki duba kofa ki gani yana rufe yanda ya rufe jiya, wallahi yana kwance a dakin ta"


"Huhmm to idan yana gidan ai sai kiyi tunanin ko yana barci ne ta samu ta dauki wayar, kina ganin Mata Bazawara idanunta A wangale! ai da makirci idan ba kiyi wasa ba zata nemi fitar dake A gidan nan, Alhali kece wacce kike son Alhaji tsakani da Allah ba sabo da dukiya ba, gwara ki farka daga wannan barcin da kike na mutuwar Rai da ruwan ciki".


"Hafsa ta yaya za kice makirci ne wannan? Yana dakin fa? Ba wasu dakuna bane A ciki bare ace ta shiga daya daga ciki ta Amsa waya".


"Uhum Aunty kenan, idan ma so kike ki gane gaskiyar Abinda na fada cewar makirci ta miki Ai Abban Abie ba bakon ki bane, sai ki bari idan ya fito ki tambayesa ya Akayi haka? Ina ce dama kiran da kikayi sabida kisan meye za'a hada musu breakfast ne? Toki kyale shegiya barta da yunwa idan sun gama cinye junan su sai ta fito ta dafa tunda Abinda tace kenan, Don Allah ki share hawayenki, Allah raina yana baci, akan kishiya ki wani zauna kina kuka? Wacece ita da baza kici ubanta ku zauna lafiya ba?"


"Shikenan Hafsa naji nagode, sam bana son kina wannan zafin rai? Bashi da anfani, idan anciza hurawa Ake, idan muka taru muka zamo daya ta yaya gidan zai zauna lafiya? Babu yanda zanyi ne Hafsa dole nayi kuka, Abin akwai ciwo, musamman idan Mace tana son Mijinta akayi Mata haka, Amma insha Allah zan daure wa zuciyata"


"Allah sarki, ina miki addu'a Allah ya sassauta miki, ki tashi muje daki sai mu karasa hiran, ina kan shiri ne?" Haka Hafsa ta jata suka shiga daki tana mata hira don hankalin ta ya kwanta.


Falmata kuwa tana gama waya tayi sauri ta goge kiran ta fito ta Ajiye masa wayar sa inda ta samu, A hankali ta haura gado ta kwanta A gefensa, murmushin mugunta ta soma tana kare wa Alhaji Goni kallo... 'A hankali saina mallake zuciyar ka da dukiyarka ka zama tawa ni ka dai' ta furta a zuciyar ta tare ta runtse idanu tuni barci ya dauketa.


Kafin karfe takwas Saddiqa ta gama shirya Yara har sunyi breakfast, suna daukar jakar su sukayi dakin Mummy su, zaune suka samesu Jidde tana cire wa Hafsa wasu kayanta da suka kwana biyu! Akan ta dauki wanda take so sauran ta kai gida Abayar wa mabukata "Mummy zamu tafi?"


"To Aman Adawo lafiya Allah ya tsare muku hanya ayi karatu da yawa" 


"To Mummy" Suka anbata gami da sa Kai zasu fita "Sabriya da Amaan wai baku iya gaisuwa bane? Dariya sukayi suka juya suka gaida Hafsa, to Aunty Hafsa zasu tafi Anjima kuyi mata Addu'a "Laa zaki tafi Amma zaki bar mana Nanah? Cewar Amaan". Zaro ido tayi " Amaan Idan nabar muku Nana kuyi Yaya da ita? Idan ankwana biyu zan kawota"


"To shikenan mun tafi" Suka sa kai suka fita a dakin "Nikan Yaushe Abie zai dawo Aunty? Nifa rabona da Abie Ankwana biyu?"


"Hakane ni kaina ina so muje kano dashi, to yanayin makaranta, yanzu haka sai nanda wata daya kafin yazo Hutu, Amma insha Allah zan turosa yaga gida"


"Hakan yana da kyau don wallahi wasu basu San Abie ba"


"Bakomai zasu ganshi da yardan Allah" Haka dai suka cigaba da hira daga bisani suka fito zuwa dinning lokacin karfe Tara da kwata. Kwala wa Saddiqa kira Jidde tayi, da sauri ta fito "Aunty gani?"


"Ki soya min kwai guda biyu, sannan ki hadomin Lipton da kayan kamshi ki kawo min, sai kiji meye Hafsa take so ki hada ki kawo". To Aunty ta Ambata ta juya Hafsa ta fada mata meye take so. Tazarar mintuna 30 Saddiqa ta bayar kafin ta baiyana da tire a hanunta ta jera komai A dinning gwanin sha'awa. Kurba biyu Jidde tayi wa Lipton din ta Ajiye cup din ta zuba tagumi, kallonta Hafsa tayi "Lafiyanki kuwa Aunty?"


"Humm Hafsa karfe Tara ta wuce Amma Alhaji bai fito ba? Aiko gaisuwa ya kamata ya fito muyi saiya koma"


"Hakane Aunty dole wani Abinda hakuri za kiyi, ki bashi zuwa karfe goma mu gani, karfa ki manta Amarya yayi, duk son da Alhaji yake miki dole Akwai Aloft of change da zaki gani, Amma idan ki kayi hakuri zai wuce ki daina sawa kanki damuwa don Allah? Zaman nan yanzu fa Aka fara?"


"Uhumm Hafsa kenan, Saratu ce ka dai zata fahimci Abinda nakeji domin ta dan-dana taji"


"Ikon Allah? Wato ba zaki iya watsar da komai zuciyarki ta samu farin ciki ba? Shiyasa keda Jiki sai dai kiga Anayi, Kannen da Mahaifiyar sa su sakaki a gaba, yanzu kuma ki bata tsallenki da jawo kiba kishiya dama Akanki? don wallahi tana gane Abinda baki so magana ya kare, don haka ki daure?"


"Shikenan insha Allah zanyi kokari" Tabe fuska Hafsa tayi ta cigaba da cin Abinci. Bayan sun gama Breakfast palo suka dawo suka zauna suna kallon tauraron dam Adam tare da hiran rayuwa, knocking din kofa Akayi da Dan karfi "Waye?" Jidde ta Ambata daga zaune, shuru Akayi aka cigaba da bugun kofar, wannan karo da karfi sosai "Wai waye ana magana kunyi shuru? To sai kuyita tsayawa har ku gani" Hafsa ta Ambata cike da takaici, daga ta waje su kaji ance "Idan gidan na Uban Mutum kenan" Jin muryar Kubra yasa Jidde furta "Na shiga uku wata masifar? Mikewa tayi da sauri ta nufi kofar ta bude. wani irin mangari Kubra takai wa kofar ta shigo tana hura hanci hanunta rike da madai-daicin basket dauke da food flask a ciki. Kallon Raini tabi Jidde dashi ta wuce cikin Palon tare da zama a daya daga cikin kujerun dake wajen. jiki a sanyaye Jidde ta biyo bayanta ta zauna a gegen Hafsa " Mtsaw ke wallahi Aunty kina da matsala, gidan ki Aka zo fa? ya zama dole kisan waye A kofa kafin ki bude, idan masu cutarwa ne suka shigo shikenan fa? Gaskiya ki gyara idan Mutum zai shekara A jikin kofa inhar baiyi magana ba kada ki sake ki bude masa".


"Wow so nice, har dasu kaza Acin danko ? Ke asuwa? To ba za'a fadi waye ba, idan kina da gado a gidan ki fitar dani kofa na fadi waye saina shigo, ko daga yau ki hanani zuwa gidan, Mtsww" Taja tsaki ta fito da Wayar ta ta danna kira wa number Falmata.


Ringin din wayar Falmata ce ta farkar da Alhaji Goni daga barcin da yake na gajiya "Auzubillah ya Ambata ya mike ya zauna yasa hanu A jikin ta, Falmata? Falmata? A hankali ta bude idanu ta zuba cikin nasa, wayarki Ake kira?" Hanu tasa ta jawo a hankali ta dauka shi kuma ya shiga toilet. "Hello Kubra ya Akayi?" Tayi magana da muryar barci "Aunty Falmata gani A down step na kawo miki Breakfast inji Hajja"


"Alright gani fitowa please" Ajiye wayar tayi ta mike zuwa drower din kayanta ta dauko duguwar rigar Atampa ta Ajiye a bed site. Alhaji Goni yana fitowa ta shiga toilet don tayi wanka. Wayar sa ya jawo ya duba miscalls din da Akayi mishi, nan ya fara kiran wanda suke da mahimmaci A kiran, A haka Falmata ta fito ta samesa, jikin mirro ta nufa ta tsala kwalliya ta dauki kayanta ko kunya babu tasa A gaban Alhaji Goni, shi kuwa idonsa yana kanta harta kammala shiri, gefensa ta dawo ta zauna "Yaya barinje wajen Kubra tana kasa, Hajja ta aikota da Breakfast" Jin haka yasa ya katse kiran ya dubeta "Breakfast kuma Falmata? Hajja ta mance Akwai Jidde A gidan? Ga Saddiqa? To yanzu wanda su kayi Ayi yaya dashi?" Dan turo baki tayi "Haba Yaya haka akeyifa? ina mutum yana da gata, duk Abincin da Hajja zata aiko dashi na tsawom kwana uku ne".


"Duk da haka Falmata wannan bayi cikin tsarina"


"Amma.....


"Ya isa kar kice komai. To tace ta mike ta fara kada jiki ta nufi kofa, Falmata? taji ya kirata, dawowa tayi a nutse tace "Gani Yaya?"


"Zauna mana? Zama tayi ya kama hanunta yana shafawa a hankali "Kinji haushin maganata ko? Akwai Abinda Hajja hakuri za tayi dashi musamman abinda ya shafi *IYALAINA* Ina da tsari na a matsayina na Da na Miji, dole tunanina ya banbanta da naku, wannan hanyar data dauko! Hanya ce ta wargaza min gida, shiyasa ban zan dauka ba, zanje na sameta anjima" Ganin babu wasa a fuskarsa yasa tace "Shikenan Yaya barin isa gareta?" Sake mata hanun yayi ta fice ya bita da kallo.


Tun daga sama ta hango Jidde dasu Kubra babu Wacce take ma wata magana. Kubra kanta yana jikin waya Jidde da Hafsa suna kallo, shu'umin Murmushi tayi ta sauko A hankali "Barka Kubra Sannu, ai bansan zaki zo ba? Yanzu nake tambayar Yaya meye za muci, da har yana tunanin ya fita ya mana take away, ashe kina tafe?"


"Kai Haba Aunty wannan Babban gidan sai anyi muku take way? Aiko ba Hajja duk Abinda kike so Akwai cookers zasu hada miki kamar yanda kike bukata" Dan murmushi tayi "Hakane  Amma kinsa dake ni Amarya ce dole kafin akai matakin haka in dan more duniyata, kuma idan banda abinki Ai so ne ya jawo haka, ba sai kiga ya goyeni ba?"


"Kina sha'aninki Aunty na! ina Yayan mu gaisa na wuce ina da lectures Anjima so bazan jima ba?" Yana ciki yanzu zai fiyo na barsa yana waya"


"Falmata Antashi lafiya?" Muryar Jidde ta katse musu hira, da mamaki Falmata da Kubra suka juya, murya ciki-ciki Falmata tace "Lafiya". Mamaki da Al'ajabi shiga hana Hafsa yin magana, domin Jidde ta bata mamaki matuka, da kyar ta Aro jarumta tace "Ikon Allah Aunty Jidde? Cike da bakin ciki ta mike tabar palon.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol