Free chapter · Read without an account

9

by Sadiyamuhammadnasir · IYALAINA


     Tsaki Falmata tayi ta dubi Kubra "Wan din wacece?" Dan murmushi Kubra tayi ta dubi Jidde da kanta yake jikin TV "Yar maula ce, kinsan gidan Mahaifi babu shine akazo a kalato Anan a samu Akai musu, so karki damu kanki da ita, kiyi kamar baki san tana existing ba" Dariya Falmata tayi "Iko Sai rabbi, shine ta samu damar sakewa haka? Lallai Yaya yana da hakuri! Yaushe zanba irin wa'innan matan dama suna shigo min gida har cikin side dina? Akwai gyara idan ba zai iya ba nikan zanyi, haka kawai?"


"Uhumm da kamar wuya Aunty Falmata, ko daya ke Amarya ce Ke bakya laifi, da sai ince miki kar ki soma, domin haushi kasheki zaiyi, don ba Abin mamaki bane ya gwada miki sun fiki muhimmanci a gidan" Dariyar shakiyanci Falmata tayi "Kai anayi ina jin dadi ana bari ina jin haushi, kema kin san mafarki kenan, Aiko ban Aure Yaya Goni ba na wuci ya hadani da wa'innan tarkacen bare kuma ina da personality na zama a gidan, ke dai kawai naki idanu".


Wani irin Abu Jidde taji ya tokare mata zuciya, murya A sanyaye ta juyo ta dubi Falmata "Don Allah karki bari shaidan ya sami gurbi a zuciyarki? kiyi wa Allah mu zauna lafiya kamar yanda Mijin mu yake so? Duk wacce zata nemi shiga tsakaninki da Abokiyar zamanki ba kaunarki takeyi ba. Kubra ina so kiji tsoron Allah kisan zaki mutu, ke mata ce Aure za kiyi, kuma kema za kiso kije ki zauna lafiya da Mijin ki, shikenan idan ya gwada miki kauna kin mallakesa? To babu kyau yanke hukunci bisa Abinda baki sani ba, ba kuma zance miki komai Akan gidan Iyayena ba, idan ba kije ba 'Yan-uwan ki sunje, idan zasu fada miki gaskiya mun wuci Maula".


"To bugeni Jidde? Sabida nace Maula akazo gidan Yaya na? Ki fada min karya nayi?"


"Uhumm Allah dai ya isa tsakanina da masu bina da sharri" Tasa kai tabar Palon zuciyarta nayi mata kuna. Dariya Falmata tayi tana nuna Jidde da yatsa harta haura sama "Wallahi Kubra baki da dadi Sam, to tace kiji tsoron Allah! Idan ba haka ba Allah ya isa mata' Ta sake shekewa da dariya' ki duba yanda kika tunzurata Sai tafiya take kamar doki raf-raf sabida takaici?"


"Hahaha Kubra ta sheke da dariya harda kwallah.


Jidde kuwa tana shiga daki ta zauna a bakin gado ta fashe da kuka, 'wannan wace irin rayuwa ce haka? "Matukar su Halima za suna shiga mana Rayuwar gida to babu yanda za'ayi a samu zaman lafiya" Haka ta cigaba da share kwallah. A wannan yanayin Hafsa ta shigo dakin cikin shirinta na tafiya, ganin Jidde tana share kwallah yasa taja tsaki "A haka hawayenki zai Kare Ai, wannan irin mutuwar Rai har ina? babu Abinda zan sake ce miki Akan lamarinki da kishiyar ki ko Kannen Mijinki, kije kiyi ta ruwan ciki kece zaki mutu A tsaye, kuma wallahi saina fada wa Mama, karma ki bani hakuri don ba hakura zanyi ba" Ta karashe Maganar tare da daukar Akwatin da Jidde ta hada mata kaya zata fita "Haba Hafsa ta? haka kike so mu rabu kina jin haushi na? Don Allah kiyi hakuri ki zauna? Tsaki tayi ta zauna a gefenta, Hafsa nasan haushi kike ji sabida nayi magana wa Falmata? nayi hakane sabida na fita hakkin ta, kuma ina so na gwada wa Kubra hada kai za muyi mu zauna lafiya, don Allah Hafsa karki fada wa Mama komai? Nayi miki alkwari zan gyara, kuma da kin tsaya da za kiji amsar dana bawa Kubra" kallonta Hafsa tayi "Kin bata amsa shine kike zubda kwallah? Wani abu ya hadaku ne bayan na shigo nan?"


"Aa Jidde ta Ambata da sauri, kawai na fada Mata taji tsoron Allah, na kuma jawa Falmata kunne akan masu zuwa don su hanamu zaman lafiya"


"Allah ya kyauta Hafsa ta Ambata ta mike, kin san tafiyar Akwai nisa nikan ya kamata Ace na dau hanya yanzu?"


"Hakane da wannan" Suna shirin fitowa Alhaji Goni yana bude kofar, domin yana fitowa daga dakin Falmata dakin ya nufo kai tsaye, ganinsu a tsaye yasa yace "Lafiya Hafsa ina zuwa da Akwati haka?" Dan rusunawa tayi "Antashi lfy Abban Abie?"


"Lafiya kalau Alhmdullah ya baby Nana?"


"Lafiyan ta kalau tana wajen Saddiqa, dama wucewa zanyi jiya Bashir yace na koma"


"Ikon Allah da wuri haka? Nina dauka zaki kwana biyu?" Murmushi Hafsa tayi ba tace komaiba "Yarinya ce ba lafiya shine dalilin komawa ta"


"Subhanallah meye ya sameta?"


"Zazzabi"


"Allah ya bata lafiya"


"Ameen" ta dauki Akwati tayi waje, kallon Jidde yayi "Hajja ta ya Akayi? Kin tashi lafiya? Ina su Sabriya?"


"Lafiya kalau suna Islamiya" Ta amsa A takaice, jawo hanunta yayi suka zauna "Kiyi hakuri nasan haushi na kikeji ban fito sallah ba, nasan shine babban korafinki, kiyi hakuri ni kaina banso hakan ba, dawainiya tamin yawa! kinsan kwana uku kenan bana samun barci sabida hidimar Auren nan, ga mutane na da suka zo daga wasu jihohi, gaba daya jiya suka tafi, shiyasa na samu sukuni harna samu barci haka, Amma kiyi hakuri kinji? Wallahi kina zuciyata Jidde?" Ajiyae zuciya ta sauke "Amma nakira wayarka baka dauka ba?"


"Ikon Allah kuma ya gwada miki ya shiga? Dana farka duk na bi miscalls banga naki ba" Kallon sa tayi kamar ta fada mishi ya sukayi da Falmata, Amma yanda ta lura dashi sam bai san Falmata ta dauki wayar saba, 'Huhmm Lallai Falmata ta iya makirci'.


"To hala network ne"


"Ba mamaki, meye ya kamata muyi wa Hafsa gashi tafiyar ta shammaceni?"


"Ni kaina banso tafiyarta yau ba Amma ya zanyi Mijinta ya fimu iko da ita"


"Hakane ki bani Lipton sai kizo muga meye za'ayi mata"


"Lipton kuma? Baga Hajja ta Aiko muku da breakfast ba?"


"Nace ki kawo min lipton ko? Nida gida na sai An fada min meye zanyi? Ko da Hajja ke kawo min Breakfast? Bana son sakarci"


"Kayi hakuri" ta Ambata ta fice A dakin. Ko data sauka kasa ko kallon inda su Falmata suke ba tayi ba, tana jinsu suna mata Habaici amma ta wuce kitchen abinta hada wa Alhaji Goni Lipton daya Aiketa, nan ta soya mishi kawai da Bread, haka ta jerasu A madai-daicin tire ta fito. Kanta A kasa ta haye sama Abinta "Ke Aunty Anya Matarnan bawa Yaya ta hada wannan breakfast din ba?"


"Ke haba karyane yana dakina fa? Ai yasan Hajja ta Aiko da Breakfast, kuma yasan shi nake jira"


"Uhum to shikenan Amma dai?"


"Ke ba wani yana waya a daki. Akwai Aikana A wajen Mama ina so na kira Babangida ya kawo min, Aida kin fadamin dana tsaya na karba"


"Hakane to ai kinsan ban san da zuwan ki ba"


"Hakane da wannan". Hiransu suka cigaba da yi cike da nishadi.


Jidde tana shiga ta jawo Stoll dake jikin mirror ta dire masa komai Akai "Allah ya miki Albarka Matar so, Amma kamar kema baki karya ba?"


"Na karya mana yanzu karfe goma ta gota fa?"


"Huhmm to zaki sake karyawa yanzu, domin wannan yamin yawa, hanu yasa ya gusturo Bread ya kai bakinta, murmushi tayi ta bude bakin yasa mata. Haka suka kammala cin Abinci cikin farin ciki da nuna wa Juna kulawa " Ina so zan fita zanje company Akwai Abinda zanyi, Amma ina so naga su Amaan"


"Eh to ai sun kusa tashi zuwa 11 zasu shigo gida insha Allah"


"Allah ya dawo dasu lafiya, Barin tura miki kudi sai ki cire kiba Hafsa idan kinje rakata tasha"


"Da wahala haka? To Allah ya biya da Aljanna"


"Ameen ya rabbi ya amsa ya mike, muje idan sun dawo ki tura min su guest Palo"


"Shikenan" Tare suka fito suna raha suka sauko kasa. Falmata tana ganin su ta tamke fuska tamkar anyi mata albishir da shiga wuta, suna saukowa Kubra tace "Yaya Antashi lfy?"


"Lafiya ya Hajja?"


"Lafiyan ta kalau"


"To masha Allah, Falmata ya Akayi dai? Ina so zan fita ne ko Akwai Abinda kike bukata idan zan dawo?"


"Fita kuma Yaya?" ta Anbata A shagwabe "Eh wallahi Akwai abidan zanyi A company"


"To Amma ba kayi breakfast ba? Tun dazu kai nake jira fa?"


"Kiyi hakuri Jidde ta hada min breakfast na riga na karya saina dawo?"


"A dawo lafiya?" Jidde ta Ambata yasa kai ya fita a palon. "Kan Bala'i Falmata ta Ambata gamida kallon Kubra. tabe baki Kubra tayi "Na fada miki Ai washi za'a kai kina min musu ba gashi ba? Aina fada miki sun gama dashi, shiyasa na tsaneta, mata makira haka? idan tana Abu sai kace mumina"


"Bakomai! Idan Jidde tasan wata Ai bata san wata ba" Falmata ta Ambata tare da mikewa "Shikenan nikan zan wuce na fada miki ina da lectures?" 


"Allah ya tsare miki hanya a koma gida lafiya" Ameen ta Ambata ta fice A gidan, Falmata ta dan jima A tsaye tana tunanin mafita kafin ta haura sama zuwa dakinta.


Sabriya da Amaan kuwa suna shigowa gida suka hadu da Daddyn su zai shiga Palon baki, da gudu suka rungumesa "Oyoyo Daddy?" Shafa Kansu yayi "Ku nake jira tun dazu dana fita, rabona da ganin ku tun jiya! Ya kuke ya makaranta?"


"Fine Daddy, kama hanunsu yayi zuwa palon baki suka zauna suka Dan taba hira kafin yace su wuce cikin gida, yana ganin kulewarsu ya kira Bala Driver dinsa ya fito da Motor.


Jidde kuwa tana haurawa sama dakin da Hafsa take ta nufa, tana zaune jiranta kawai take "Yauwa na matsu ki shigo wallahi na tafi, bani so nayi dare a hanya"


"Babu wani dare da za kiyi yanzu zamu tafi, ina zuwa?" Dakin Saddiqa ta nufa ta kirata ta fito da kayan Hafsa zuwa compound, suna fitowa Jidde tace "Kiyi wa Falmata sallama?" Kama baki tayi da mamaki "Dake kanwar Uwata ce ai dole nayi mata sallama"


"Haba Hafsa?"


"Kyaji dashi" Ta Ambata ta sauko ta barta, ganin haka yasa ta biyota da sauri, kafin su fito Saddiqa ta kira Driver ya kwashe Akwatin Hafsa ya zuba a motor, suna fitowa ya daukesu tare dasu Sabriya sai tasha. suna isa Jidde ta ciro kudi masu yawa ta damka mata "Ga wannan Abban abie yace na baki 30k kiyi kudin Motor, ni kuma na kara miki 10k Allah ya tsare miki hanya"


"Ameen ya rabbi nagode" Hafsa tace ta karbi kudin tana mai nuna farin cikin ta, haka suka tsaya sai da Hafsa ta sami Motor kafin sukayi sallama Driver ya dawo dasu gida.


Falmata kuwa tana shiga daki ta kiran wayar Gwaggo Hajara, tana dauka tace "Amarya baki laifi, ya Akayi ne? Yanzu Surajo ya fita a gidan nan, ya kawo Yaran nan, wai ya dauka yaune wuni" Eyya to ai sai akawo su nan gidan?"


"Kai Haba Falmata da wuri haka?"


"Mama Akawo su nace, ita Jidden kannenta kusan shida ne a gidan, Akawo min yarana"


"Laha'ila na shiga uku guda shida? suke me a gidan? Kai wannan Mata Akwai Al muna?"


"Huhmm Mama ba wannan ba, kin san miye?" Nan ta kwashe Abinda ya faru ta sanar da ita "Tabdijam Ai Abin haka yake, toki kwantar da hankalinki, kiyi uzuri zuwa ki karbi girki, idan hakan ta sake faruwa zan fada miki miye za kiyi, ke dai koda wasa kada ki mishi rashin kunya, idan tsakanin ki da Jidde ce ni Mahaifiyarki nace karki raga mata, idan kika daure ta haka zaki samu yanda kike so Falmata, ki kara hakuri"


"Shikenan Mama sai sunzo, karki manta ki basu tsumi na su kawo min"


"Ba matsala 'Yar Albarka" Ta Ambata ta kashe wayar.


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.