Free chapter · Read without an account
11
Kallo mai cike da tsananin sha’awa YARIMA HALADU yake bin KULUWA dashi wacce ta rab’e jikin bango tamkar zata shige ciki gaba d’aya jikinta kyarma yake saboda tashin hankali, YARIMA HALADU ba inda idonsa suka fi karkata sai kan dukiyar fulaninta da suke cike duk da hijabin dake jikinta hakan bai hana masa nuna zalamar sa, Bakinsa na k’asa ya lasa kad’an yana matsowa kusa da ita tamkar zai had’e jikinsa da nata yace “Haba Kulu babe ya kike abu kamar ba wayayya ba kin wani manne da bango”. Ya ware hannayensa yace “Zo ki rungumeni muji d’umin jikin juna na gamsar dake zuma mai dad’i da gardi”. Hannu tasa tai saurin toshe kunnenta saboda girman kalaman da suka shiga kunne da k’wak’wawalarta, Yarima murmushi yayi irin na mazan bariki da suka saba mu’amala da mata, Ya matso gaf da ita, yasa hannu ya zare hijabin jikinta ya cillar dashi gefe, take jikinta ya shiga kyarma sosai, tayi saurin sa hannayenta biyu kan k’irjinta, Kallo cikin k’wayar idonta yayi da suke cike da tsoro yace “Ba da amincewarki kika zo nan ba”. Kai ta d’aga masa tana jin wani irin tsoron sa na shigar ta, “To meyasa kike haka, ki saki jikin ki, muji dad’in mu na miki alk’awarin shayar dake zumar dad’i, ki sauke hannayenki na fara sarrafa albarkatun k’irjin ki”. KULUWA sake k’ank’amewa tayi gu d’aya tana jin nauyin yadda zata sake ma na mijin da bai biya sadakinta jikinta yayi yadda yake so, anya batayi kuskure ba kuwa na zuwa dan ta bada kanta a arha, “Mahaifinki zaki kub’utar”. Wani sashe na zuciyarta ke ayyana mata, Tunanin halin da mahaifinta ke ciki na sake kai kawo a zuciyarta, a hankali ta fara sauke hannunta d’aya a hankali, wanda ganin haka yasa YARIMA sakin wani murmushi yana k’ok’arin kai hannunsa kan k’irjinta, “WALA TAQARABUZ ZINA KADA KU KUSANCI ZINA” itace ayar da ta fad’o mata a kai tayi saurin matsawa gefe hannunsa ya kai kan bango, “Kina tunanin idan kika bada kanki mahaifinki yaji hanyar da kika bi kenan zaiyi alfahari dake, wacce hujja gareki ta kare kanki ranar gobe k’iyama, abunda Allah ya haramta shi kin aikatashi idan Allah ya d’auki ranki kina cikin aikatawa fah”. zuciyarta ke dasa mata haka take wani irin tsoron Allah ya shigeta, tayi saurin duk’awa zata kai hannunta ta d’auki hijabinta, YARIMA HALADU ya take hijabin cikin fusata yace “Me kike k’ok’arin yi?”. “Bazan iya baka kaina ba, Allah yana sane damu shi zai kub’utar da mahaifina”. Dariyar kin zo da rainin hankali yayi yana dubanta yace “Baki isa ba wallahi KULUWA, tunda na d’aura idona kanki ban sake samun natsuwa ba, da k’yar nake samun bacci dalilin ki, wallahi yau bazaki bar d’akin nan ba sai na samu abunda nake so daga gareki ko da kuwa ta hanyar fyad’e ne”. KULUWA hankalinta yayi mummunan tashi cikin murya mai tsananin rauni had’i da firgici ta had’a hannayenta gu d’aya alamar rok’o tace “Dan Allah ka barni na tsira da mutuncina kada kamun komai, Dan Allah ka barni na tafi”. YARIMA HALADU ko kad’an bai ji tausayinta ya ratsa zuciyarsa ba, hannu yasa ya fisgota da k’arfi yana k’ok’arin jefata kan gado ta kai masa cizo, kafin tayi yunk’urin d’agowa ya sauke mata lafiyayyen mari kan kuncinta wanda tsawon rayuwarta tafin hannu bai tab’a kai kan fuskarta da sunan mari ba, kanta taji ya masifar juyawa zafin mari ya shigeta sosai, amma bata fasa yunk’urin sake tashi ba, YARIMA HALADU hannu yasa ya maida ita da k’arfi ya rank’wafo kansa yana k’ok’arin had’a bakinsa da nata, k’afa ta saka ta kai masa duka a abarsa, yayi saurin kai hannu ya rik’e yana sauka daga jikinta saboda azaba ba k’aramin duka ta kai masa ba, hijabinta dake gefe tai saurin d’auka ta nufi k’ofa cikin ikon Allah tai saurin bud’ewa ta fice a guje ba tare da YARIMA HALADU ya iya dogon motsi ba balle ya hanata, gudu take sosai wanda bata tab’a tunanin ta iya irinsa ba saboda baiwar natsuwar tafiya da Allah ya bata, sai dai tai nisa da gidansu YARIMA, ta tsaya tana kuka sosai ta saka hijabinta, Tana tafiya tana jan numfashi tare da godiya ga ubangiji da ya kub’utar da ita daga wurin YARIMA HALADU,
Mafi akasari mutane sun shige gidajensu saboda hadarin da ya gauraye sararin samaniya har ana yayyafi, KULUWA bata ci karo da kowa a hanya ba, a matuk’ar tsorace kuma a kid’ime ta shigo gidansu, UMMA HABIBA na d’aki zaune jigum kewar mijinta na cikata a irin lokacin nan da suna tare suna hira, sai take jin d’akin ya mata fad’i duk da kasancewar rashin wadattacen fili na d’akin amma rashin MALAM GARBATI ciki ya zamar mata tamkar k’aton fili na sukuwar dawakai,
KULUWA sai a yanzu da ta shiga d’akinta tunanin me zata cewa UMMA HABIBA ke kawo zuciyarta, ko zata sanar da ita gaskiyar komai tana ganin b’oyewar bashi da amfani hasalima sai da ya jawo k’ara shigowar YARIMA HALADU rayuwarta ta hanyar mahaifiyartata, Ganin ruwan bai yalwata ba har lokacin yayyafi ake KULUWA ta fito ta tsaya k’ofa tayi wa UMMA HABIBA sallama, wacce ta amsa muryarta na nuna farin ciki tace “Kin dawo?”. KULUWA murya raunane tace “Eh Umma”. Ta d’aga asabarin da ya ba d’akin kariya ta shiga ciki, zaune gefe d’aya ta samu UMMA HABIBA wacce ganin KULUWA ya sake fad’ad’a murmushinta tace “Yau za’a fiddo Malam d’in ko sai gobe”. KULUWA hawaye taji sun cika mata ido murya sanyaye tace “Umma cewa yayi sai na bashi kaina ko zai bani kud’in da za’a fito da Malam”. Umma Habiba zabura tai tana kama baki tace “Innalillahi shi Yariman”. KULUWA ta d’aga kai tana matsar hawaye “Na yarda da tarbiyarki KULUWA nasan bazaki tab’a amince masa ba, ba sai na tsaya tambayarki ba nasan ke kamilallace”. Kuluwa wani sanyi taji ya ratsa ranta na jin dad’in rashin ba YARIMA HALADU da ta tabbatar UMMA ba zata tab’a farin ciki da hanyar da ta samu kud’in ba, Cikin jimami da takaici UMMA HABIBA ta cigaba da cewa “A duniya yanzu ba’a taimako Dan Allah, kud’in da yafi k’arfinsa sune zaice sai ya lalata yarinyar wasu kafin ya bada, na tabbatar da wata ce tuni zata basa kanta shiyasa da yawa yan’ matan yanzu suke lalacewa, Allah Ubangiji ya shiga lamarinmu ya cigaba da kare mun ke”. KULUWA a cikin zuciyarta ta amsa da Amin, tana sake addu’ar Allah ya kawo musu mafita ta alkhairi.
Ta b’angaren YARIMA HALADU bayan fitar KULUWA ya jima kafin ya daina jin zafin abarsa, yayi ta tsine mata yafi sau cikin kwando yaci alwashin d’aukar mataki kanta ba zai barta ta tafi haka ba, ko fyad’e sai ya mata na wulak’anci wanda zata tozarta a k’auye, ya d’aukarwa kansa alk’awari,
*********************
Kujeru biyu ne zagaye da k’aramin tebur a keb’antaccen wuri mai cike da tsari da kyau, MAJOR UMAR ne zaune kan d’aya daga cikin kujerun sanye yake da pyjamas designer masu taushi kaf’afunsa sanye da silifas wanda suka zo tare da kayan, Hannunsa rik’e da notepad yana duba wasu bayanai da suka shafi aikin sa, Gefensa coffee mai zafi cikin k’aramin mug akan saucer wanda shi ya had’a coffee da kansa, yana yi yana d’auka yana sipping, Ya d’auki kusan awa d’aya kafin ya kammala ya d’aura pad d’in kan teburin, yana d’an yin baya jikin kujera tare da lumshe idon sa, UMAIMA yake tunani yaji yana son ganinta dan tabbatar da lafiyarta, gaba d’aya zuciyarsa ta gama yarjewa sihiri aka mata, wanda yayi magana da wani babban malamin Sunna mai bada maganin gargajiya kan gobe da safe zaizo ya dubata, Mik’ewa yayi ya zura hannunsa d’aya cikin aljihu ya soma taku yabar wurin zuwa b’angaren UMAIMA, A falo ya tarar dasu AYDA an musu shirin bacci suna kallo tare da mai’ aikin HAFSA wacce yanzu dukkan kulawarsu ta koma kanta, Tana jin muryar su Ayda na fad’in Daddy suka zo da gudu suka rungumeshi, bata iya d’aga kai ta kalle sa ba saboda tsoron sa da kwarjininsa murya na rawa tace “Ina wuni?”. “Lafiya”. Ya amsa a dak’ile ya umarci yaran suje su kwanta ya wuce d’akin UMAIMA,
Yana bud’e d’akin ya shak’i k’amshi mai dad’i, kansa ya kutsa cikin d’akin, UMAIMA na tsaye bakin madubi cikin wata fitinanniyar rigar bacci dake bayyana dukkan surar jikinta, MAJOR UMAR wata ajiyar zuciya ya sauke yana jin sanyi na ratsa sa zuciyarsa na tabbatar masa UMAIMA d’insa ta da ta dawo, shirin da ta saba masa yau ta masa, a hankali ya taka zuwa bakin madubi, yanayinsa na canzawa sha’awarsa na motsawa, hannayensa biyu ya kai kan k’ugunta yana rik’ota ta baya, Yana k’ok’arin kwanto da kansa kan kafad’arta ta fisge jikinta da k’arfi ta juyo tana kallonsa fuskarta tamke sosai tace “Meye haka?”. Kallonta yayi zuciyarsa na sake hasassa masa tabbas aikin asiri ne, gashi ta masa shiri alamar tana buk’atar sa amma yana tab’ata ta canza, A ransa ya ayyana ko waye ya shiga tsakaninsu ya canza masa UMAIMA sa ba zai tab’a gafarta masa ba da kuma zai san waye sai ya d’auki hukunci mafi tsauri kansa, UMAIMA ganin ya kafeta da lulu eyes d’insa ta murgud’a baki tana juyar da kai tace “Please ka tafi d’akin ka, mutum sai jarabar masifa kai dai kullum abu d’aya, ai sai kasa mutum ya tsufe da wuri ma”. MAJOR UMAR bai ce komai ba, zuciyarsa na sake tabbatar masa da zarginsa sanin lokutan baya ko sau nawa zai buk’aceta bata tab’a nuna masa gajiyawarta dukkan had’in kai take basa, Juyawa kawai yayi ya fita d’akin cikin matsananciyar sha’awa,
UMAIMA bayansa tabi da kallo tace “Shawararku ZULAI tayi, sai dai ba haka naso ba, naso ya nace kan sai na bashi kaina nak’i ransa ya b’aci sosai, shaa muje zuwa”. Tai dariya tana hayewa kan gado ta d’auki wayarta ta hau whatsapp, ta shiga group d’insu wanda su uku ne ciki ita, zulai sai saratu, ta fara basu labarin yadda yau d’in ta kasance, suna k’ara tsara mata.
****************
KULUWA da UMMA HABIBA yadda suka ga dare haka suka ga safiya ba wacce ta iya runtsawa cikin su, tunanin Malam Garbati da halin da yake ciki ya hana musu natsuwa, sai addu’a da suka kwana yi na Allah ya kawo musu mafita, duk da ga kayan abinci na gun Yarima a gidan, sam basuyi yunk’urin d’aura tukunya ba, damuwar da suke ciki ta kori yunwa.
*************
“Ni fah ina ganin hanyar da zan mallaki KULUWA yazo mun cikin sauk’i”. IRO ke sanar da abokinsa Tasi’u, wanda suke zaune a gona k’ark’ashin wata bishiya, Tasi’u yace “Ban fahimci zancen ka ba”. Iro ya gyara zama yace “Malam Garbati kasan dai an kamasa kan bashin mutane da yaci, ina ga zan same sa kan cewar matuk’ar ya bani auren KULUWA zan biya masa bashin ya fito”. Tasi’u dariya yai yace “Kai mutumina baka tsufa dai, kace kawai ka kusa angwancewa dan nasan babu abunda zai hana MALAM GARBATI amincewa yana ganin sa cikin wannan uk’ubar”. Iro yai dariya yace “Ai ina komawa gida zan sa a fara gyaran sashen amarya”. Tasi’u yace “Sai dai fah LADIDI kasan hali ya zakayi da ita”. Iro numfashi yaja yace “Barni da ita kawai, amma aurena da KULUWA fah ba fashi, yarinya komai ya zauna mata, ga fatarta luwai luwai kamar ba tashin k’auye ba”. “Mutumina baka tsufa wallahi, bada jimawa zaka aurar da yarinya ta uku fah”. Iro yana dariya yace “Barni nayi k’ara’i”. Tasi’u ya tuntsire da dariya.
Tooo fans ya kuke gani MALAN GARBATI zai amince ya bada auren KULUWA kuwa???