Free chapter · Read without an account

13

by Sadiyamuhammadnasir · Kuluwa



MAJOR UMAR wani abu yake ji yana taso masa tsakanin k’irji zuwa zuciyarsa wanda yake cunkushe da b’acin rai, idonsa ya d’an runtse cikin takaici da son daidaita kansa dan gujewa aikata wani abu cikin fushi, 

Kana ya bud’e manyan idanunsa masu cike da kwarjini wanda farin k’wayar idon cikinsu ta soma sauyawa saboda b’acin rai ya kalli MALAM cikin murya mara sauti yace “Maganin ba buk’atar siyowa kenan ko tunda ta shigo”. "Maganin shima ana buk’atar sa amma yanzu zan fara mata tambayoyi idan amsar su tazo dai-dai da abunda muke hasashe sai ayi mata rukiya". D'ago ido UMAIMA tayi ta dubesu ɗaya bayan ɗaya na rashin fahimtar inda maganarsu ta dosa "Ayi min rukiya? Me hakan ke nufi?”. Tayi tambayar fuskarta na nuna rashin fahimta da son jin k’arin bayani, “UMAIMA MALAM zai miki tambayoyi ina so ki basa amsar komai karki boye wani abu dan maslaha ake nema”. Kalaman MAJOR UMAR suka dawo da ita daga hirar da take da zuciyarta "Bangane a mun rukiya in amsa tambayoyi ba?”. Ta tsare sa da ido tana son jin k’arin bayani daga garesa "Duk wanda yasan mu'amalata dake da yanda muke zamantakewarmu ta aure kulawa, soyayya da ganin mutuncin juna idan yazo yaga irin abubuwan da kike yi yanzu dole zai ce akwai matsalar sihiri ko shafar aljanu tattare dake, bare ni Mijinki, shiyasa na ɗauko Malami saboda ya gaskatar mun da hasashena sannan a samu hanyar waraka”. Shewa UMAIMA tayi gami da tafa hannu har sai da MALAM ya tsorata ya dago ya dubeta yana son ganin ko jinnu d’in ne suka taso, A tsiwance ta kalli MAJOR UMAR tace “Tunaninka shafar jinnu ce ke damuna yasa na sauya? to ka sani babu wasu jinnu tare dani sai sanin yan’cin kaina da nayi yanzu, kuma ya kamata ka gane shekaru suna k’ara nisa wayewa na sake bayyana tunani na zurfi, bari kaji UMAR lafiya ta k’alau babu wata lalura dake damuna, kawai na sauka daga duhun jahilcin da ka sanni dashi a baya yanzu nasan 'Yancin kaina bazan taba yarda da duk wani abinda zai nemi shiga rayuwata ba, ka tattara bak'on ka ka sallamesa babu abinda ya had’ani da shafar jinnu da kuke tunani bare ku daurani kan wasu magunguna”. Taja tsaki ta mik’e tayi hanyar fita “UMAIMAAAA”. MAJOR UMAR ya kira sunan ta cikin murya mai nuna tsananin b’acin rai jikinsa har na rawa yana jin tamkar ya fisgota ya sauke mata lafiyayyen mari, ba UMAIMA ba hatta MALAM sai da yaji hanjin cikinsa ya murd’a yadda falon ya d’auki sautin muryar Major Umar, cak ta tsaya kiran ba k’aramin shigarta yayi ba amma ta dake tana k’ok’arin danne tsoronta, ta juyo cike da rashin kunya tace “Karka sake mun irin wannan kiran idan ba haka ba zan nuna maka shafar jinnu d’ince kamar yadda kake tunani.

Ta gyara jakarta ta fice, dafa goshi MAJOR UMAR yayi take idonsa ya canja launi zuwa wani rikitaccen launi ba komai cikin k’wayar idonsa sai tsananin b’acin rai, Ajiyar zuciya MALAM ya sauke ya dubi MAJOR UMAR da al'amarinsa ya basa tausauyi, tabbas Matarsa lafiyarta kalau hudubar shaid’ance ta riga tayi tasiri a zuciyarta, idan ba tsananin ikon Allah ba had’i da rok’on sa dawo da ita hanya zai yi wahala.


*************************


IRO ya kwana ya wuni da tunanin auren KULUWA wacce yake jin sabuwar shauk’inta na shigar sa da son kasancewarsa da ita k’ark’ashin inuwa d’aya, daga gona kai tsaye gidan DANLADI ya nufa bai zarce gida ba, yana so su tattauna kan maganar MALAM GARBATI labari yazo masa shine mai binsa kud’ad’e mafi yawa. Yaro ya samu ya tura sa cikin gidan yayi masa sallama da shi, yaron ba jimawa ya fito ya shaida masa DANLAD bai dawo gida ba ya tafi cin kasuwar k’auyen wacce take ci duk ranar lahadi a kwanakin mako, IRO hannu yasa aljihu ya zaro naira goma ya ba yaron, wanda ya amsa yana godiya, Ya wuce ya kama hanyar kasuwa, da isar sa ya samu DANLADI zaune bakin teburinsa ya kasa kayan sa, bayan sun gaisa IRO ya dubi DANLADI yace “Daga gidanka nake akace min kana kasuwa shine na k’araso inaso muyi magana”. Gyara hula DANLADI yayi yace "Magana kuma IRO ta me kenan?”. “Magana ce akan MALAM GARBATI da kasa aka kamasa wai shin har nawa kake bin sa? ina so mu tattauna”. “Allah mai iko wato Munafurci yabar wajen Mata ya koma wajen Maza? Idan na fad'a maka akwai abinda zaka iya a kaine? Dubu biyu ma idan ta fita a jikinka har ciwo kakeyi meye naka na tambaya IRO?”. “DANLADI ba nazo kaci mutunci na ko kamin rashin mutunci bane don na tambayeka, idan ba zaka fada mun ba shikenan ai ba'a dole ko" "Ba zan fad'a ba idan gulmanka takai gulma ka hau mota kaje KURA ka tambayesa". IRO kai ya jinjina ransa a b’ace “Zaka sha mamakin jin naje na tamabyosa d’in”. Ya bula rigar shaddar sa yaluwa ya bar gun, Tsaki DANLADI yayi ya cigaba da sababi na irin Munafuncin mutanen kauyen da suke fama da shi, a haka har SHAFA dillaliya ta iso yana abu ɗaya "DANLADI lafiya kaketa zage-zage kai dawa? Tun dazu nake magana baka ji ba”.Tsaki yaja yace “Rai na ne a b'ace Dillaliya IRO ne yazo tsaban gulma yake tambayata nawa ne kudin da ake bin MALAM GARBATI, ina ruwansa meye had’in sa da MALAM GARBATI dama ace mutum ne shi mai alkahiri sai nace watak’ila biya masa zaiyi amma ko yayan cikinsa baya iya kashewa kud’i, Har yana ce mun yau zai je KURA ya tambayo MALAM GARBATI”. “Uhmm”. Cewar Dillaliya tana sauke ajiyar zuciya tace “Tabbas akwai wata a ƙasa amma idan tayi wari za muji, bani gero kwano ɗaya".


*************


Iro yana isa gidansa tun a kofar gida ya fara karo da wasu daga cikin Yaran sa suna Dambe sai auna munanan ashar suke wa junansu “Kai Kai kuzo nan dan Ubanku shegu haihuwar asara”. Iro ya fad’a cikin masifa gami da binsu da gudu zuwa cikin gida, “Ha'a lafiya kuka shigo kamar zaku tureni ba cewa nayi ku fita waje idan ma kashe junanku za kuyi kuje can ku kashe kar wani tsinanne ya shigo min gida ba?”. “Kuzo nan nace”. Cewar Iro ya jawo karan dake gefensa "Da wannan karar zaka bugesu yo me zasuji? Ai gara ka ɗauki tabarya ka jibgesu yanda ba zasu sake amfanuwa ba, yara sai kace 'Ya'Yan Allah bani ko yaya”. Cewar Matarsa LADIDI dake zaune tsakar gida tana tsintar wake zaune d’aure da d'aurin k’irji, wanda yai duk’unk’un rabin gashinta da babu gyara bud’e rabi ne ta rufe da wani tsohon kallabi na tsohuwar atamfa, 

“Wai ke LADIDI meyasa baki da imani ne to bazan bugesu ba tunda ba naki cikinsu baki da asara idan na nakasasu”. Shewa Ladidi tai tace “Ai na rantse idan tak’amar ka kwashe-kwashen mata ne kana aura haka zakaita rainon 'yan iska a gida, ni kuwa babu wanda zan raga masa bayan wanda na haifa ehe”.

Kwafa Iro yayi ya wuce ya d'ebi ruwa ya wuce bandaki yin wanka, yana fitowa ya nufi ɗaki ya shafa mai ya sauya wasu kaya ya fito sai kamshin vaseline yake, 


 LADIDI da kallo ta bi sa tace “Ina zuwa kuma daga dawowarka har da yin wanka ko abinci baka ci ba?". Shafa gemu yayi "Uzuri ya taso, ki ajiyemin idan na dawo zanci KURA zan tafi" "Kura? Kayime a KURA a wannan lokacin?”. “Idan na dawo za kiji”. Yasa kai ya fice zuciyarsa wasai Allah ya kawo masa hanyar mallakar zukekiyar Mace kamar KULUWA cikin sauk’i, “Kai raina tayi” Yai zancen zuci yana washe hak’oransa da suka zama yalu saboda rashin wankewa.


Mutuwar zaune LADIDI tayi gaba d’aya tunaninta ya karkata me IRO zaije yayi a KURA? kar dai tsalle tsalle sa ya k’are a matan k’auyen nan har KURA zaije neman aure? Lallai zamuci Uwar sabada da kai Iro matukar aure kace zaka kara wallahi, kuma ma yar’ kura tabdijam Allah sa hasashena kar ya zama gasiya dai".


**********


KULUWA tare da UMMA HABIBA suna zaune a tsakar gida abun duniya ta taru ya ishesu kallo ɗaya za kayi musu ka fahimci tsantsar damuwar dake tattare dasu, babu abinda ke cikin su tun safe amma ko yunwar basuji saboda girman tashin hankalin da suke ciki, d’ago ido KULUWA tayi ta dubi UMMA HABIBA data zabge lokaci guda tamkar wacce tayi ciwon shekara guda 

“UMMA Dan Allah ki daure kisha ko ruwan zafi ne hankalina yana tashi idan na kalleki ina tsoron karna rasaki kamar yanda muke shirin rasa MALAM”. Hawaye masu d'umi ne suka sauƙo kan fuskarta "KULUWA ko yunwar banaji wallahi musamman idan na tuna MALAM hala ko ruwa bai samu ya sha ba bare abinci saboda azabar da suke mishi ga bakin cikin abinda yaron nan dan mai gari ya bijiro miki da shi”. “Kiyi hakuri UMMA mu cigaba da addu’a In shaa Allah Ubangiji yana ji kuma zai kawo mana mafita, amma nima ina tausayin MALAM matuk’a”. Kuka ke neman kubce mata tana k’ok’arinta na tare sa, ganin tashin hankalin da mahaifiyarta take ciki idan kukan tace za tayi kara mata damuwa za tayi.


*************************


Ajiyar zuciya mai karfi MAJOR UMAR ya sauke MALAM ya juyo a hankali sukayi ido biyu take yaga girman tashin hankalin da MAJOR UMAR yake ciki "Kayi hakuri MAJOR ko wani Bawa daka gani a duniya da irin kaddarar da Ubangiji ya rubuta zai samesa mai kyau ko akasin haka, ka sani ba wai baya sonka bane ya jarabceka, aa so yake ka kusancesa ka cigaba da kai kukan ka garesa yana jin muryarka, idan kayi hakuri ka jajirce da addu’a komai zai wuce”.

“Lafiyarta kalau kenan MALAM?”.

Yai maganar murya a sanyaye “Bazan boye maka ba lafiyar Matarka kalau kawai rudin shaidan ke dawainiya da ita, watakila akwai masu daurata a mummunar hanyar da take ganin itace hanya mai bullewa, ka cigaba da addu’a kana yi mata nasiha idan Allah ya taimaka sai kaga ta dawo hanya, dama a rayuwa ta aure ana had’uwa da jarabawowi iri iri”.


Major Umar zancen yaji sa tankar almara duk abunda UMAIMA take masa a cikin hankalinta take kenan, Jim yayi kad’an kafin ya nisa yace “Ba komai MALAM nagode Allah ya saka da khairan ka turamin account number dinka ta WhatsApp za kaji saƙo" "Nagode sosai MAJOR Allah ya rufa asiri”. “Amin”.

 Ya amsa.


*************************


Ta b’angaren MALAM Garbati babu walwala natsuwa ko kwanciyar hankali tattare dashi, a kwanakin ya sake zabgewa dama ba k’ibar gare sa ba, k’azantar wurin da suke kadai ta isa saka bawa tashin hankali, ga wani wari da bashi da misalin fad'a, 


Zaune yake ya had’a kai da guiwa warin da ya cika d’akin yau wanda ya zarta na ranakun ya saka shi kakarin Amai, ɗaya daga cikin rik’akkun wajen yace “Tsoho kada kace zaka mana amai nan gun ka shanye sa yaseen kuwa, ga botiki can da wannan shegen ya mana zawo kayi aman akai”. Jin kalmar da yaro yake faɗi ya tabbatar wa MALAM Garbati warin meye ya daga masa zuciya, jikin garu ya jingina ya fashe da wani irin kuka, tunani ya soma cikin zuciyarsa haka zai cigaba da rayuwa cikin wannan ukuba har karshen rayuwarsa saboda bashi? Sosai yake kuka har jijiyoyin kansa suna bayyana saboda tashin hankali tare da nadamar cin bashi a rayuwarsa “ Tsoho kana damun ma fah, nan da ka ganmu ba mai son zaman sa nan amma hak’uri muke”.

Uffan MALAM Garbati baice dasu ba sai toshe hanci da yake yana mai cigaba da nadamar cin bashi da yayi a rayuwarsa, kusan tsawon mintuna talatin ya ɗauka yana zubar hawaye kafin ya takaita da hawayen, runtse idonsa yayi take fuskokin UMMA HABIBA da KULUWA suka bayyana cikin idonsa, a hankali ya bud'e ido hawaye masu zafi suka sauka "Allah kana gani kai zaka kawo min ɗauki cikin wannan hali dana tsinci kaina, ban ajiye ba bare na dauka bansan ya zanyi na biya wannan bashi dake kaina ba”.

Yai zancen wanda bai san ya fito fili ba, “Yanzu saboda bashi suka kawo ka nan tsoho? Kai mutane basu da imani”. Hankalin MALAM GARBATI bai tashi ba sai da yaji kiran sallah ya dubi Bayin Allah da suke tare ya tambayesu batun sallah sukace sai ranar daya fita zai had'a, wannan abu ya tashi hankalinsa matuka, Babban abinda ya hanasa cin abincin da aka basu wanda ko wadatar maggi bai samu ba sai uban gishiri, shinkafa ce a bushe kuma chabe da alama ko mai ba’- saka mata, sai yan’ wajen ne suka cinye.


******


Iro yana fita daga gida wurin hawa motar Kura ya nufa, Yana zuwa yaci sa’a shine na k’rashe mota ta tashi, tafiyar mintuna suka iso,


Da saukar sa mota ya tambaya aka kaisa har station din da MALAM GARBATI yake, sunsha artabu dasu sosai har sai da ya basu cin hanci kafin suka amince da zasu barsa yaga Malam Garbati, MAMMAN ya basu kudi kan kar a rangwanta masa ko kadan kuma kar abar kowa ya gansa da tabbacin ta haka zai cimma burin sa.


MALAM GARBATI na raku'be jikin garu dan sanda ya iso jikin kofar cike da raini da rashin mutunci yace "Kai tsoho fito anzo wajenka”. Tamkar anyi wa MALAM GARBATI albishir da shiga Aljanna haka yaji daɗin zancen mutumin, ko ba komai zai samu damar da zaiyi sallah ya kai kukansa gabansa mahalicci, MALAM GARBATI yana sa kafarsa a wajen cell d’in yaji wani ni'imtaccen iska har sai da ya lumshe, idonsa na wadatuwa da haske sab’anin d’akin da duhu yai masa yawa, Ya iso jikin kanta inda IRO ke zaune, ido biyu sukayi da IRO, mamaki da al’ajabi ne suka kasa boyuwa kan fuskarsa "IRO” Ya kira sunan a ransa, a iya saninsa babu wata alak’a da ta tab’a had’asu da Iro, har bashi ya tab’a nema wurinsa ya hana sa ya bi sa da rashin mutunci, “To me ya kawo sa gun sa?”.



Tofa masu karatu shin MALAM GARBATI zai amince da buƙatar da DANLADI yazo masa da ita? Muje zuwa dai..

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol