Free chapter · Read without an account
Two
by Hauwau Shafiu · DUNIYA BIYU
Bayan an fita zuwa tara, tana aji ita kaɗai a zaune. Ta sauke ajiyar zuciya tare da maida littafin lissafi da aka musu cikin jakarta. Sai lokacin ta kula da doyar da Hajja ta zuba mata. Abin ka da ba sabon ba, ta ma manta da ita.
Ta cirota ta buɗe ta fara ci a hankali tana karewa yara sa'anninta da suke wasa a ƙofar ajinsu kallo.
Bata da aboki ko ɗaya a makarantar, ta fara wasu abokan lokacin da aka kawota. Sai da Fauzah tayi yadda tayi ta janye duka abokan nata suka koma nata, daga nan duk wanda ya tunkareta da sunan abota, ba'a jimawa za ta ga suna zamewa.
Daga baya take jin labarin abinda su Fauzah suke faɗa a kanta, cewa ita ɗin ƴar aikin gidansu ce, mahaifinta talaka ne mai sayar da kayan gwanjo. Hakan bai dameta ba, sana'ar mahaifinta da suka raina ce ta dameta. Ita sayar da gwanjo ba sana'a bace? Ko babu komi, halalinshi yake nema, a kan wannan sana'ar kuma ya mutu. Duk da hakan, mutum ne mai tsananin wadatar zuci, wanda abinshi bai tsone mishi idanu ba bai kuma damu dana wasu ba. Bai kuma ɗauki kyautar da abinshi da bada sadaka a bakin komi ba. Har ya mutu, gidansu basu taɓa neman abu suka rasa ba. Suna da rufin asirinsu dai-dai misali, ga cima mai kyau da sutura mai kyau. Don haka ita kam, bata ga aibun sana'ar da yake yi ba. Ko babu komi, tayi musu rana.
Ko bayan data gama cin abincin, zama taci gaba dayi tana saƙe-saƙe har aka dawo. Yara suka fara tururuwar shiga ajin.
Fauzah da take zaune a gefenta kaɗan, ta shigo ajin da zugar yara abokanta suna binta a baya kamar wata sarauniya, su kuma fadawa. Tana kallo suna mata shune da baki suna dariya, bata ko ɗaga kai ta kallesu ba, har malami ya shiga ajin.
Yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa ta takura Alhaji akan ya yiwa Daddyn Abuja magana akan ya canza mata makaranta. Abu ne dasu Fauzah suka sha faɗa mata, suke kuma kan faɗa mata, makarantarsu ba makaranta bace irin ta su ya-ku-bayi irinta. Makaranta ce irin ta su ta ɗiyan masu hannu da shuni.
Ita a karan kanta ta sani, wannan makaranta tafi ƙarfinta. Tasan hakan tun ranar farko data saka kafarta a makarantar. Daga farko tayi tunanin zata iya jurewa, ta nuna hakan bai dameta ba. Sai dai hakan yana ƙoƙarin ya zame mata gingimemen aiki.
Yarinya ce mai alfahari (pride) da girmama kai (self-esteem), saboda haka ganin yadda kullum ta Allah suke ƙoƙarin ganin cewa sun muzantata a gaban mutane, da kuma ganin yadda ta kasa yin fitting in (sajewa da mutanen wajen), yana ci mata tuwo a ƙwarya. A ganinta idan ta bar musu makarantar, zasu sakar mata mara tayi fitsari. Ta tabbata zata fi maida hankali kan karatunta ma.
Tayi nisa cikin tunaninta, bata san lokacin da malamar dake koyar dasu yaren Farans ta iso ta tsaya a kanta ba. Sai data ɗan buga saman teburinta sannan tayi firgigit! ta kalleta.
Madam Annabelle, magidanciyar mata ce ƴar kimanin shekaru talatin da biyar, tun daga ƙasar Switzerland aka ɗaukota musamman saboda ta dinga koyar dasu yaren faransanci.
To yawancin malamansu ma hakan suke, kamar Mr. Jeffery, baturen Collarado dake koyar dasu harshen turanci, ko kuma Amtu Salaamah, balarabiyar Al-Dera dake koya musu larabci.
Cikin yaren farans ɗin Madam Annabelle take tambayar Ameenatu abinda yake damunta. Cikin ɗan ilimin data samu na yaren ta mayar mata da amsa kan cewa lafiyarta lau.
A hankali ta sauke ajiyar zuciya lokacin da matar ta matsa daga kusa da ita, ta koma gaban ajin, taci gaba da koyarwa.
Gab da zata fita, ta raba musu sakamakon jarabawar gwaji da ta musu satin daya wuce. Kamar yawancin lokuta, ta samu sakamako mai kyau, fiye da rabi-rabin wanda Fauzah ta samu.
Babu abinda gabanta yake yi sai faɗuwa lokacin data hango kaifafan idanun Fauzah ɗin a kanta. Ta tabbata da kallo yana kisa, da tuni kaifin mashinan da idanunta suke jefo mata sun kar ta. A hankali ta ɗauke kanta, ta mayar kan malamin dake shiga ajin a lokacin.
Karfe biyu dai-dai aka kaɗa musu ƙararrawar tashi. Malam Hassan wanda yake koyar dasu yaren hausa, ya rufe littafin 'Uwar Gulma' da wata ƴar ajin, Zaynab, take karanta musu a matsayinta na speaker ɗin ajin. Ya sallamesu tare da faɗin zasu ɗora daga inda suka tsaya a aji na gaba.
Yana fita daga cikin ajin kowa ya fara tururuwar fita shima. Ba'a bar Ameenatu a baya ba, cikin gaggawa da rawar jiki ta ɗauki jakarta ta goya a baya. Ba tare data ɗaga kai ta kalli kowa ba, ta kama hanyar fita.
A ƙofar ajin taji ta kaiwa mutum karo. Ta ja da baya da sauri, a kuma tsorace, idanu a waje. Ta sauke ajiyar numfashin da bata san ta riƙe ba, lokacin da ta sauke idanunta a kan Fahad, wani ɗan ajinsu wanda yake a J.S.S. 1A, ita kuma tana 1B.
Kaf faɗin makarantar 'Prestige', shi ne kaɗai wanda kashedin dasu Badi da Affan suke mishi bai taɓa shigar shi ba. Ba sau ɗaya, ba sau biyu ba, ta sha ganin Fauzah, ko ɗaya daga cikin tauraran masu wutsiya ya ja shi gefe yana mishi magana a duk lokacin da suka ga ya tunkareta. Sai dai da alamu duk abinda suke faɗa mishi baya kaiwa cikin kunnenshi. Tunda hakan ba shi zai sanya idan ya ganta a washegari ya ƙi yi mata magana ba. Bata sani ba, ko rashin fahimta ne ko wani abu ya kawo hakan?.
Ya saki murmushinshi mai burgewa tare da ambatar sunanta. Ta amsa ciki-ciki kamar wadda take tsoronshi. Kodayake akwai tsoron, sai dai ba nashi bane. Tsoro take wani daga cikinsu ya ganta dashi, tasan cewa cikin matsala hakan zai sanya ta. Duk da cewa ba wai tana mugun tsoron su bane da hakan zai sanya ta hanawa kanta farin ciki ko samun abokai ba, ita ba sakara bace ba, tasan cewa ko babu komi suna da gaskiya da suke cewa ita ɗin, babu dai-dai da ajinta a cikin makarantar nan. Ta sani. Shi yasa take ƙoƙarin gujewa duk wani abu data san zai haɗata da wani ko yasa su saba.
Tana da matuƙar gudun wulaƙanci, zuciya da jajircewa. Abu ne wanda ta riga ta sani lokuta da dama da suka wuce, su masu hannu da shunin nan da iyayensu, ganin wanda yake ƙasa dasu suke yi kamar wani kashi. Gani suke kamar idan na ƙasa dasu ya raɓe su, kwaɗayi ne kawai ya kai shi. Su kuwa hausawa cewa suka yi; 'inda kwaɗayi... Akwai wulaƙanci'. Don haka take ƙoƙarin ganin cewa ta hana wulaƙantar da kanta a wajen ire-iren waɗannan mutanen.
Ƙoƙarin neman hanyar silalewa daga wajenshi take yi. Ya buɗe jakar shi ya ciro fakitin biskit ɗin 'New Yorkers' ya miƙa mata, yana mata murmushi da suka fito da duka haƙoranshi, "ga tsarabata. Kinsan sai jiya da yamma muka dawo daga Kaduna ni da Mommy".
Ta girgiza kai da ɗan sauri, "a'ah, nagode! Amma na ƙoshi".
Ko a jikinshi bai nuna mata ba, sai ma wani murmushin da yayi, yace "dama nasan abinda zaki ce kenan".
Bai bari ta sake cewa komi ba, ya zuge mata zif din jakarta ya tura mata biskit ɗin ciki, daga nan ya juya da gudu babu ko waiwaye. Ta bishi da kallo baki a ɗage.
Lokacin data dawo cikin hankalinta, kowa ya washe y barta. Ta girgiza kanta a hankali tare da fara tafiya.
Tana fita ƙofar makarantar, ta hango Affan yana shiga cikin motar da aka zo ɗaukarsu. Ta ɗauke kanta a hankali kamar bata gansu ba. Jerin gwanon motoci ne iri-iri suke shige da fice a cikin makarantar, duk na ɗaukar ɗalibai. Tayi imanin ita kaɗai ce wadda take zuwa a sayyadarta ko kuma ta bi motar haya, idan ma akwai wasu, to lallai basu da yawa. Don bata taɓa ganinsu ba.
Ta ɗaga kafa da sauri ta tsallaka ɗaya ɓangaren inda anan ne zata hau mota. Allah ya taimaketa babu jimawa mota tazo, ta hau suka tafi.
Φ
Haka kawai taji gabanta yana faɗuwa. Tana sauka daga motar, taji kamar an ƙara mata wata faɗuwar gaban. Ta samu kanta da nanata kalmar 'Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un!'.
Ranar juma'ah ce. Karfe sha biyu ake tashinsu a kowace rana ta juma'a saboda masallaci. A hankali ta gangara tabi hanyar data saba bi zuwa gida. Saboda tashin hankalin data ji ta shiga kai tsaye, bata san lokacin data ɗaga ƙafa tana sauri ba. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci sai gata a ƙofar gidansu.
Daga farko tarin motocin data gani a ƙofar gidan ne bila adadin suka bata mamaki. Sai kuwa tururuwar mutane dake kutsa kai suna shiga cikin gidan. Fuskokin wasu cike da jimami, wasu na hawaye, wasu ma na kuka. Sai jikinta ya ƙara yin sanyi. Tabbas babu lafiya.
Ta ɗaga ƙafafunta da suka fara rawa da sauri ta kutsa jikinta ta shiga gidan. Kowace ƙofa ta gidan a buɗe take, mutane nata tururuwar shiga. Sai kuwa sautin kuka da take ji yana fitowa daga ainihin falon gidan. Nan ta shiga.
Taja tayi turus a tsakiyar falon. Hajja na zaune dirshashan tana rafsar kuka, mata sun zagayeta suna bata haƙuri.
Daga ɗakin Alhaji ta ga Daddyn Abuja ya fito, kyakkyawar farar fuskarshi da idanunshi sunyi jawur, haka ta ga Anty Mommy mahaifiyar su Badi a can gefe a zube a ƙasa wanwar, ana watsa mata ruwa.
Ɗan ƙarfin daya rage mata a ƙafafunta ya ƙare. Ta sulale ƙasa itama, ƙwalla ta cika idanunta a take. Tace 'Innalillahi wa Inna Ilaihi raji'un! Allahumma ajirni fi musibati, wa'aklifni khairan minha!!'. Ƙwallar ta tsiyayo ta sauka akan kumatunta. Sai kuma kuka ya biyo baya.
Babu abinda take tunawa sai fuskarshi a lokacin da zata tafi makaranta ranar da safe. Kwana biyu jikin nashi yayi tsanani, har sai da aka ƙara kaishi asibiti. A kanshi Hajja da Yahya suka kwana, aka wayi gari da niyar a sake mayar dashi asibitin. Ta ƙi shiryawa ta tafi makaranta, saboda bata so ta tafi ta barshi a haka. Sai da Yahya ya danganata da Alhajin, da lallami da ban baki ya shawo kanta ta tafi, akan cewa washegari da ita za'a tafi kaishi asibitin. Ashe bankwana yayi mata!.
Ta rarrafa ta ƙarasa kusa da jikin Hajja ta jingina da ita, a hankali take sauke ajiyar zuciya, hawaye na zarya akan kumatunta babu ƙaƙƙautawa.
Zuwa can bayan an sauko daga masallaci, lokacin an riga an kai mamacin gidanshi na gaskiya. Mutane na kurkusa sun hallara. Lokacin kukan da take tayi ya tsagaita, sai na zuci wanda yafi na filin ƙuna.
Yayarta Murjanatu, su biyu iyayensu suka haifa, tana zaune da kakarsu Nana, ita take shafa bayanta a hankali cike da lallashi. Gabaɗayansu suna zaune a ɗakin Hajja inda anan ake ƙarbar gaisuwa. Ta zubawa wasu baƙi da suke ta kai lomar abinci bakinsu idanu, mamaki ya kamata. Tambaya ɗaya take yiwa kanta a lokacin, ta yaya? Ta yaya har wani abu ya iya shiga cikinsu a lokacin?.
Ta ɗan sauke ajiyar zuciya lokacin data ji an taɓata, ta juya ta kalli Nana. Murya a dakushe tace mata, "je ki store ki samo ruwa mara sanyi a ba Hajja magani".
Babu musu ta tashi ta fita.
Saboda yanayin cunkuson gidan, duk wasu ɗakuna an buɗe su saboda ɓaki. Ɗakin da yake fuskantar na Hajja, nan Anty Mommy take ƙarɓar baƙinta. Ta ɗan jingina da jikin ƙofa tana ba waɗanɗa suke jidar lemuka da kwalayen abincin gwangwani suna kaiwa ɗakin.
Bayan ta ɗauko ruwan, a bakin ƙofa ta kusa kaiwa mutum karo. Da sauri ta ja da baya. Da alama bai ma kula da ita ba, ta bishi da kallo lokacin daya tafi ya kaiwa firjin karo. Taji ƙarar faɗuwar wani abu.
Da sauri ta matsa tana tambayarshi bai ji ciwo ba? Ya ɗaga wasu hargitsattsun idanu, da suka rine da ja, sai dai babu alamun ɗigon hawaye ko ɗis a cikinsu.
Ganin bai ce komi ba, ta durƙusa ƙasa ta ɗauki gilashinshi daya faɗi, ta miƙa mishi. Ya kalleta, hannu ɗaya rike da gorar ruwa mai sanyi, ya kalli gilashin. Tasan cewa yana iya gani ba tare da gilashin ba, amma ba sosai ba. Ba tare da yace komi ba, yasa ɗaya hannunshi ya amsa, kai kawai ya iya gyaɗa mata, ya juya.
Ta bishi da kallo cikin sanyin jiki, mutuwar Alhaji ba ita kaɗai ta girgiza ba. Ta taɓa kowa daya raɓe su. Sai dai gani take yi kamar ita kaɗai aka yiwa rasuwar. Kamar tayi rashin wani babban jigo a cikin rayuwarta.
Sai dai, da ta kalli halittar da ta sake kaiwa bango karo cikin yanayi na ɗaukewar hankali, sai ta samu kanta da canza maganarta. Haƙiƙa ba ita kaɗai aka yiwa rasuwa ba. Ita da Baqeer ne.
Haƙiƙa sunyi rashi!.