Free chapter · Read without an account

005

by Halimatou Khabir · MAI DAKI

*MAI ƊAKI...!*

        Fitattubiyar


     ©️ *Nana Haleema.*



*Book 1*

*Page 5*


     Sassanyan dad'i yaji yana shiga ilahirin jikin sa, farin ciki yana mamaye ko wanne gurbi na zuciyar sa kamar ana soka masa allurar farin ciki haka yake ji dan tunda yaji ta amsa yasan shikenan kuma amma bai nuna mata ba ya rausayar da kai ya kalli idanun ta yace, "My choice kar fa na takura ki kiyi abinda ba shi kike so ba, na fad'a miki zan iya hak'ura."


Hawayen da suka sakko mata ta goge tace, "babu takura my Choice ayi hakan kawai, in ta mutu ta dalilin ka kamar ta dalilina ta rasa ranta, ga alk'awarin da ka d'auka gwara kawai ayi a wuce wajan." Tsam tsam ya rungume ta yana jera mata kisses a fuska da bayan ta son da take masa bai tab’a yi masa rana ba sai lokacin yace, "Na gode My Choice, na gode Allah ya biya ki da gidan Aljanna. Ke din mai qaunar cigaban rayuwata ce Allah a barmu tare dani dake har abada.”


Ya d'ago ta daga jikin sa yana kallon ta yaga tana murmushi tace, "yaushe zamu samu Ammah da maganar?." Fuskar sa baza ka fassara yanayin sa ba yace, "Sai muje da safe kafin na wuce office. Amma dan Allah my choice ban cutar dake ba?."


"Duk abinda kake so shi nake so koda zai cutar dani" ta fad'a a sanyaye tana kallon sa ya sauke numfashi yana binta da kallo yace, "Duk yadda akayi Allah ya k'addara ita d'in matata ce, kin san k'addara tun tana ciki Allah ya rubuta sunana a matsayin mijinta tun bamu zo duniya ba. In badan haka ba banga dalilin da zai saka na auro wata bayan ke ba, ke kawqi nake so dake kawai naso rayuwa amma k'addarar aure ta kan iya d'aukar rai."


Numfashin itama ta sauke bata ce komai ba yace, "Allah zai baki ladan taimakona da kika yi itama kuma kin taimake ta. Har abada bazan manta da wannan taimakon naki ba My choice, Allah yayi miki albarka ya baki duk abinda kike so." Ta amsa da amin a ciki ya bita da kallo yasan akwai abinda take ji a zuciyar ta amam shi dai tunda ta amsa shine burin sa duk abinda zata ji wannan daga baya ne.


Yace, "Me kike so ki fad'a min ko meye." Sai ta fashe da kuka tace, "Kar ka sake nisa dani, ka cigaba da zama a my choice din dana sani tun a baya. Kar ka koma min Yusuf dan Allah,sam bana jin dad'in hakan ina cutawa sosai. Kar kuma ka aure ta ka wulaƙanta....." Bata k'arasa ba ya toshe mata baki da hannun sa yana girgiza kai yace, "Har abada hakan bazata faru ba My choice, kece farko kece k'arshe babu wata bayan ki. Ina sonki" ya fad'a yana kallon idanin ta itama haka.


Kwanciya sukayi zuciyar sa tamkar audiga sabida haske farin ciki yake ji sosai yana kuma gode Allah da ya bashi mata mai k'aramin wayo kamar Ameena wacce soyayyar sa tayi mata yawa zata ita komai sabida shi, Burin sa kawai gari ya waye dan yasan da anje an samu Amma zancen ya k'are sai dai tayi fad'an ta gama amma zata amince tunda Ameena din ce zata fad’a da kanta.


Bata iya komawa bacci ba shima haka ta b'angaren ta zallar damuwa ce da dana sanin amincewa shi kuma farin ciki yayi masa yawa har taso ta fahimci hakan duk da yana b'oyewa amma taso ganewa dan labarin zuciya a tambayi fuska, yanayin fuskar ta saki sosai sai sun had’a ido sai ta d’an yi murmushi.


Yana fita sallar asuba itama ta d'auki Zaitun ta bar d'akin nasa gabad'aya bata jin dad'in zuciyar ta haka ta koma nata d'akin ta kwanta bayan ta idar da sallah ba tare da tasan abinda yake damun ta, jin zuciyar ta take kamar an d’ora mata dutse sabida nauyin da tayi mata ga zafi da take ji a duk jikin ta. Da ya dawo yaga bata nan d'akin nata ya nufo ya same ta a kwance.


"My choice" ya fad'a yana shigowa ta d'ago ta kalle shi ya k'araso yace, "ya naga kin sakko?." Tace, "Babu komai."

"Akwai my choice, kalli fuskar ki fa duk ta canja alamun Kinyi kuka. Ko maganar jiya ce dai?."


Ta girgiza kai tace, "A'a, kawai bana jin dad'i ne shiyasa." Ya sake kallon ta yace, "To me ya same ki haka?."

"Nima ban sani ba."

"My Choice na fad'a miki in akwai damuwa a bar maganar nan farin cikin ki yafi min komai a duniyar nan."


Ta girgiza kai tace, "ba wannan ne a raina ba kawai ina tunanin Mamana da Abbana ne." 

"To ai addu'a zaki musu ba tunani ba ko?." Ta d'aga kai alamun eh yace, "Jiya an fara karatu a islamiyyar da aka Gina domin su, yanzu zancen da nake miki sun fara samun ladan karatun alkur'anin da ake a ciki domin makarantar gabad'aya sadaukarwar su ce."


Sai taji sanyi a zuciyar ta tayi murmushi tace, "Allah yasa hakan, Allah yasa suna aljanna." Yayi murmushi yace, "Amin ya rabbil alamin. Yanzu dai taso mu koma sama ina son a sake bani irin farin cikin jiya." Ta langwabar da kai tace, "Allah kaina ciwo yake min bana son tashi.”


Ya mik'e tsaye ya zaga gefen ta ya d'auke Zaitun ya kwantar ya dawo ya kwanta a kusa da ita yace, "to mu kwanta a nan" ya fad'a yana jawota jikin sa. Murmushi kawai tayi bata ce komai ba gabad'aya sai take ji a jikinta kamar canjawar nan tasa akwai dalilin yinta zuciyar ta sai take fad’a mata duk abinda ya fad’a ba gaskiya bane kawai yayi dan cikkon burin sa, tunda yayi mata waccan maganar ta kasa sukuni a haka bacci ya d'auke su ita dashi.


Ya rigata tashi ya bar d'akin bai jima da fita ba itama ta tashi ta yiwa Zaitun wanka itama tayi ta bata abincin ta ta gyara d'akin kamar kullum ta hau saman da niyar gyara nasa d'akin. Abin mamaki ya gyara d'akin tass tamkar itace ta gyara tabi d'akin da kallo tana kallon sa tace, "Morning my Choice." Bai amsa ba ya matso ya mata kiss a goshi yace, "Morning my beautiful wifey" ya fad'a yana karb'ar Zaitun.


"Da kanka kayi aikin nan?." Ya kalle ta yace, "naji kince baki da lafiya shiyasa nayi dan kar ki wahala." Tayi murmushi tace, "amma ni nasan bana son yin shara, ya akayi kayi haka yayi kyau?.” Ya kalle ta yace, “ai dakin yana samun kula a wajan ki wata ran sai kiga kamar ba’a kwanta ba.” Tayi murmushi tace, “kayi k'ok'ari." Shima murmushin yayi tace, "Bara na d'ora breakfast" ta fad'a tana fita taja tsaki shifa duk ba wannan yake so ba kawai ya gansu a gidan Amma shine burin sa shiyasa yayi mata aikin dan kar ma a jima basu tafi ba.


In badan kar ta fahimci wani abun ba ai bazai barta ma tayi wani abinci ba to baya so tayi sauri d'agowa shiyasa ya share ya k'yale ta. Nan da nan kuwa ta had'a musu breakfast ya sakko suka ci tare ya kalle ta yace, "zan tafi office ni." Ta kalle shi tace, "da wuri haka?."


"Eh, ai zan biya na gaida Ammah” ya fad'a dan ya tuno mata maganar jiya ya lura tana sharewa kamar ta manta kuma yasan tana sane. 

"Bara na d'auko mayafi muje." Yayi murmushin jin dad'i yace, "okay." Ta hau sama ta sakko da mayafi ya d'auki Zaitun suka fita bayan sun kulle falon suka hau mota kai tsaye suka wuce gidan Amma gaban ta yana fad'uwa.


Lokacin da suka faka a babbar harabar gidan su Yusuf ya kalle ta yaga tana kallon wani wajan daban ya kamo hannun ta yace, "My choice!." Ta kalle shi yace, "Ni naga fa duk kin canja." Tayi murmushi tace, "Babu komai, muje" ta fad'a tana fita daga motar ta shiga ciki shima ya biyo bayan ta. 


Amma ce kad'ai a zaune sai k'anwar su Humaira suka yi sallama suka shigo ta amsa da murmushi tana fad’in, "Ga daughter, ga Takwara ta" ta fad'a tana karb’ar Zaitun a hannun Ameena.

A kan carpet suka zauna gabad'ayan su Yusuf yace, "Barka da safiya Amma." A ciki ta amsa Ameena tace, "Barka da Safiya Amma."

"Barka dai Ameena, ya gidan?."

"Alhamdulillah" ta amsa da murmushi kamar yadda Ammah take murmushi.


Tashi yayi ya shiga cikin wajan Abbah Ammah ta kalle ta tace, "Lafiya dai ko na ganku da safiya?." Tayi y'ar dariya tace, "Lafiya lau Ammah. Humaira ina school?." Tayi dariya tana karb'ar Zaitun daga hannun Mama tace, "Munyi hutu, yanzu ma zancen zuwa gidan ki nake yiwa Ammah dan na gaji da zaman nan."


Amina tace, "Ai kuwa da naji dad'i." A lokacin Yusuf ya fito ya kalle ta yace, "My choice har na dawo kina nan ko zaki wuce?." Ta kalle shi tace, "Har ka dawo d'in." Ya girgiza kai ya kalli Ammah yace, "Ammah sai anjima" ya fad'a yana fita ta bishi da kallo ta kalli Ameena tace, "Ni dai ban amince da yanayin ki ba, inda matsala ki fad’a min."


 Ameena tace, "Wajan ki nazo daman Ammah." Ammah tace, "Taahi muje d'aki." Ta tashi suka shiga d'aki aka bar Zaitun a hannun Humira Ammah ta zauna a kan gado ita kuma ta zauna a kan carpet Ammah tace, "me yake damun ki?."


Ameena tace, "Ammah alfarma nazo nema a wajan ki nasan kuma zaki min." Ammah da mamaki tace, "Wacce irin alfarma kuma?."

"Ammah dan Allah ki amincewa Daddyn Zaitun ya k'ara aure kamar yadda yake so. Wallahi Ammah in baiyi auren ba hankalina da naki bazai tab'a kwanciya ba tunda yana so gwada kawai yayi a wuce wajan, hankalin sa zai fi kwanciya nima nawa zai fi kwanciya.”


Ammah tayi shiru tana jin abinda take cewa cike da mamaki tana girgiza kai da jinjina tsananin wayo irin na Yusuf tace, "Ameena taso ki dawo kusa dani ki zauna." Ba musu ta tashi ta zauna kusa da ita Ammah ta rik'e hannunta tace, "Ke da kanki kike cewa na amincewa mijin ki ya k'aro miki kishiya? Kin san wacece kishiya kuwa?." Ameena tayi shiru Ammah tace, "Fad'a min shine ya saka ki kizo ki same ni?. Ni tunda naji ana kiran my choice a gabana nasan akwai wata tsiyar daya shirya, fad’a min shine ya turo ki?.”


Ta girgiza kai alamun a'a tace, "Ammah baiyi min ma wannan maganar ba na lura in baiyi auren ba komai sake lalacewa zaiyi. Yana son yi Ammah kuma Allah ya wore masa gwara kawai yayi tunda shi ya saka a gaba koda yanzu ya hak'ura nan gaba sai yayi gwara kawai ayi na huta shima ya huta kema ki huta Ammah. Dan Allah ki amince, amincewar ki kawai yake jira shiyasa nazo na nema masa alfarma da kaina a wajan ki. Ki amince yayi auren sai hankalina yafi kwanciya nima kinga in yayi na huta da tunanin auren” ta fad'a tana zamewa daga kan gadon tana kallon Ammah tana hawaye.


Ammah ta sauke numfashi ta d'ago Ameena itama ta mik'e tsaye tana kallon ta tace, "Amina y’arki ko yaye ta baki yi ba amma ki dinga zancen na amince mijin ki ya k'aro aure? Har yanzu kika gama sanin sa da zaki so ya kawo miki wata?. Kin san meye kishiya kuwa? Kin san yarinyar da yake niyar kawo miki?.”


Amina tace, "Ammah yana so wallahi in baiyi ba bazai tab'a komawa yadda na sanshi a baya ba. Dan Allah ki amince badan shi ba danni zaki amince Ammah." 

Ammah ta sauke ajiyar zuciya tace, "Soyayyar sa har tayi miki yawan da zaki Zab’i farin cikin sa akan naki? Namiji ne fa nan gaba kar kizo kina dana sani akan abinda kika aikata Ameena. Ni ke nake ji in badan ke ba ya auro d'ari bai dame ni ba. Yusuf d’ana ne amma sabida ni na haife shi bazan fasa fad’ar gaskiya a akansa ba, wallahi in ma shi ya saka ki dad’in baki yayi miki cutar ki kuma zaiyi yana yin auren ya gama dake, ke kin san namiji kuwa…..?.”


Ameena tace, "Babu komai Ammah, in sha Allah babu abinda zai faru ni nace na amince taki amincewar kawai nake so." Ammah tayi shiru kafin ta kuma kallon ta tace, "Baki san meye kishiya bane shiyasa kike fad'ar haka."

"Naji na gani Ammah."

"Ameena da k’uruciya a lamarin ki.” 

“A’a Ammah, kawai ayi a wuce wajan yafi sauki.”

“Shikenan zanyi shawara." Ameena tace, "To Ammah na gode Allah ya k'ara girma. Dan Allah Ammah ki amince kar ki yanke akasin haka."


Kai ta girgiza tana kallon ta Ameena ta fita daga d'akin jikinta a sanyaye Ammah ta bita da kallo tana jinjina yawo irin na namiji in yana son abu yasan yadda zaiyi ya samu koda ran wani zai b’aci.


Waya Ammah ta d'auka ta kira babar yarta mace da take Abuja ta d'auka suka gaisa Ammah tace, "Kin san dalilin da ya saka na kira ki?." Daga can b'angaren tace, "A'a Ammah."

"Ya kike gani akan maganar auren Yusuf, na amince masa ko kuwa?."

"Ammah amince masan shine yafi, namiji ne fa tunda ya saka auren a ransa in baiyi ba Ameena bazata tab'a jin dad'i ba, in kuwa yayi shikenan an wuce wajan hankalin kowa zai kwanta. A ganina barin sa d'in shine yafi Ammah sabida gani yake yi Ameena ita take hana ki amincewa.”


Ammah ta girgiza kai cikin gamsuwa tace, "Amma an cutar da Amina."

"To ya za'ayi? Barin sa baiyi auren ma cutarwa ne dan bazata tab’a jin dad’in sa ba kuma ita ba fad’a miki take yi ba, gata marainiya babu wanda zata kaiwa kukan ta kinga zata dinga cutuwa ne, in kuwa akayi shikenan an wuce wajan."

Ammah tace, "Shikenan" ta fad'a tana kashe wayar tana ji a ranta barin nasa shine ya dace amma sai tayi shawara.



#Vote

#Share

#comments


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol