Free chapter · Read without an account

SHAFI NA 6

by Fatima Zara Alhassan · JOƊA

Su kashi da fitsari ba a maganar su, kowa a wajen zaiyi abun sa.

Wasu ma kazantar wajen ke kashe su.

Shiya sa ko an saki mutum da wuya yayi sati biyu a duniya, sabo da shi kadai ya san irin azabobin da ya sha.




Ci gaba...


Haka rayuwa ke tafiya ana dauki ba dadi tsakanin Sojoji da barayi, sai dai kuma abun takaici baya karewa, ganin yadda makaman soji ba su kamo kafar na miyagun ba!

A ko wace rana sai ankashe kaki, bila' adadin, sabo da irin girman makaman da yan ta'adda suke rike da su.


Cikin kwanakin nan, babu irin kalolin zabobin da ba su sha ba.


Ta saba da shi sosai,  sabo da kusa da shi aka daure ta tun zuwan ta.



Yau manyan barayin za su fita operation, hankalin su joɗa tashe, ba sason manyan su fita, sabo da kananan da ake bari su tsare su zalunci sai wanda su ka manta.



Bayan su Duna sun fita, suka bar yaran su da matayen su, su tsare su joɗa.



Haka za su samu Sanduna suyi ta dukan su, babu ji babu gani.


Duk wanda aka kama har ya dawo babu maganar Sallah.


Dan Allah dan uwa zanyi fitsari a can wajen, joɗa ta fada cikin harshen fulatanci.



Kallon uku saura kwata barayin su ka dinga yi mata.


San nan daya daga cikin su ya kwancenta.

Bayan tayi fitsari ta dawo, san nan su ka sake daureta.



Can zuwa tsakar dare ta banye hannuwanta tare da kafafuwanta, san nan ta koma wajen mutumin dake kusa da ita ta fara yanke mishi igiyar da aka daure shi.


A firgice Lukman ya tashi yana kallon wannan yarinya.


Tana kwance mi Shi ya yi sauri ya karbi askan dake hannunta cikin sauri ya je yana banye wa sauran yan uwansu, yana tunanin inda yarinyar ta samu Aska yake yi?

Ya kwance mutane da yawa, wasu kuma ganin ko ya banye su ba za su iya gudu ba duba da raunukan dake jikinsu, shiya sa su ka ce ya bar su anan kawai, sun yanke kauna daga rayuwa, haka ya tsallake su ya koma kan wasu.


Duk wannan bidirin da su Joɗa suke yi, barayin na can suna sharholiyarsu, sun sha kayan maye sun bugu.



Ga dai shi sun kwance kansu, amma hanyar kubuta ta gagare su ganewa.

Gabas zasu bi, ko arewa, yamma ce zata kubutar da su ko kuma kudu ce hanyar tsirar su?


Tunani Lukman ya tsaya yi, shi kansa da yake Soja wanda ya sha gwagwar maya a fagen fama a cikin dajuka, bazai ce ga hanyar da zata fitar da su ba.


Kafin ya gama tunanin sa, har Joɗa ta ce kafa me naci ban baki ba, ta yanki hanyar Arewa ta fara falfala gudu ita da sauran jama'a.


Bayan su yabi , ganin irin jarumtaka ta wannan yariya.

Mamaki yake yi har yanzu ganin cewa shekaransa kusan daya a wannan wuri, amma be taba tunanin guduwa ba, ko yayi wata dabara wadda zai bar wajen a matsayin sa na soja wanda ya sha tirenin.

Duk da ko a yanzu ya san ba lallai su kubuta ba, amma dai ya jinjina ma yariyar.


Haka suke ta nausan daji, ga kayoyi ta ko ina, zura kafar su suke yi ta ko ina tun da duhun dare ne, ba sa ganin me ke kasa balle gabansu.


Hankalin joda ne ya tashi, ganin tamkar zagaye ne su ke yi, wanda har yanzu ba su bar wajen wadan nan azzaluman ba.


Wai ga wa tayi ta ga irin jama'ar dake biye da ita suna son ceton ransu, sun yi amanna da ita.

Hawaye masu zafi su ka shiga zubo mata, taya za ta kalle su ta ce musu zagaye su ka yi? Hango lukman tayi shi ma yana tsaye ita yake kallo.


Wajen ta ya nufaa, san nan ya ce mata, "Har yanzu bamu bar wannan yankin ba, tun dazu zagaye muke yi"




Cikin kuka tace mishi "Na sani kado,  bana son na koma hannun wadancan azzalumai, babu wanda zai zo ya taimake mu,  ba wanda ya san irin kuncin da muke ciki, tare da fashewa da kuka mai tsanani...


kwallace ta cika mishi ido, a matsayinsa na Soja me hidimta wa kasarsa, tun ranar da aka kama shi baiyi zaton zai yi kwana daya a hannun bandit ba, ba tare da kasar shi ta kwato shi ba.


Ashe bai canka daidai ba, babu wanda ya sake bi ta kansa har kawo zuwa yanzu,  



To shima fa kenan, ina ga su kuma wadannan jama'a wadanda ba suji ba su gani ba, idan shi ya fito domin yaken su, to su wadannan bayin Allah me su ka yi musu? Ya kamata shi ma yayi wani abu, tun da har yarinyar ta bude musu kofa. Ya fada a cikin zuciyansa.



"Ku biyo Ni"


ya fada yana me nufar wani yanki na daban.


Bayan sunyi nisa sosai san nan ya waiga yaga yadda jama'a suke yi mishi hannu, cewa dan Allah ya tsaya su huta.



Haka ya sa su ka ya d 'a zango a karkashin darbejiya katuwa domin shinfida hakarkarin su sabo da gajiya.


Hasken farin wata, ya sa su farkawa, sai dai kuma me za su gani?


A razane su ka mike tsaye sabo da firgici, ganin azzalumai zagaye a gabansu dauke da bindigu.




KARKU MANTA KU YI MIN...👇

**SHARE

**COMMENT

**LIKE

**VOTE

** FOLLOW

San nan ku garzaya #Arewabooks domin samu sauran littafai na.

ko kuma ku je #wattpad acan ma zaku samu.

ko kuma a YouTube channel di na

#YARMUTANARGUNGU.

NAGODE 🙏

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol