Free chapter · Read without an account
20
Ruƙayya, Rufaida, Anty Aysha sai Nusaiba da Hafsa (ƙawayen Rufaida) ne zaune a falon suna ta surutu. Da ihuna na ƙaraso falon don murnar ganin su, barin ma Rukky, watau gorin da nayi mata jiya yayi aiki. Suna ta tsokanata ma wai na daɗe ina wanka kamar mai canza fata. Abun ka da zallar 'yan mata sai shagali ya tashi.
Mun baje kayan ciye-ciye a gaban mu banda kulolin abincin da suke wurin. Daga saka kiɗa sai abun ya zama gasar rawa, kowa ya fito ya taka irin nashi, mu kuma muna ta hailing ɗin me yi. Rukky ce ma ta dage wai ita ba ta rawa, amma kowa ya ƙi yarda dolenta sai da tayi. Ni da Rufaida kam babu mazari irinmu. Mun sha nishaɗinmu sosai gaskiya, don Anty Aysha ma zamanta tayi a cikinmu ba kamar yanda ta kan tashi ta bar mu ba idan mun yi baƙi 'yan makarantar mu.
Daga baya muka saka wata tsohuwar waƙar Lionel Richie ta 'when a man loves a woman.' sannan muka zauna muna ta shan lemo da kuma kala-kalan biscuits da aka zuba a babban faranti, sai kowa ya zaɓi abinda yake so kawai. Hirar mu muke a haka.
A hakan kuma Ya Buhari ya shigo sassan mu, tsabar sakewa ma daidai da ɗankwali babu mai shi a cikinmu. Shigowar shi tasa Ruƙayya da Nusaiba jan ɗan kwali suna ƙoƙarin rufe gashi banda ni, Rufaida da Anty Aysha don mun saba zama a haka a gabansa. Hafsa da take kishingiɗe riƙe da gwangwanin biscuit ko gyara zama ba tayi ba bare a yi tunanin za ta ɗaura ɗankwalin ta ma (ko don ta san tana da gashi ne ? Oho). Ni da na kalleta ma sai kamar kallon ƙurilla take yi masa. Sun gaisa kuma ya gane Ruƙayya, har kuma lokacin ƙala ban ce masa ba.
Hafsa ta bi shi da kallo lokacin da yake fita daga falon tana ajiyar zuciya, don kowa na cikin falon ya jiyo ta. Ta kalli Rufaida ta ce "Waye wannan don Allah Rufaida? Wow!"
Rufaida na murmushin tsokana ta kallo gefena kafin ta ce "Yaya Buhari ne kamar yanda na faɗa maku ɗazun a lokacin da na gabatar da ku. Ai shine babba a gidan nan ko da bayani ne?" Ta kannewa ƙawarta ido.
Hafsa ta amsa "Da za ki taimaka da kin sani cikin sahun surukan gidan nan, don ba ƙarya yayanku yayi. Kayyasa! Duk da nasan ciwon zuciya zai iya kamani don da gani ba sai an faɗa ba da wuya ya rasa 'yan mata Wallahi."
Rufaida dariyar da take yi har da ƙyalƙyalawa ta ce "Ai kam dai akwai su, amma ta ƙarfen ta shi a JS take a makaranta ma. Amma dai kaman tana gamawa za'a yi masu biki na, bai sauran shekaru ƙalilan ba."
"Kuma tana sane yana da su? Kodayake 'yar ƙaramar sakandare ce ba lalle ma wayo ya isheta ba."
"Ni da Rufaida idan kin hango hanya ko yaya ki soka ni a wajen, ba ruwana da ƙwailarsa."
Rufaida ta zaro ido "Ke Hafsa ki rufa mun asiri da rigimar Yaya. Bar ganin ya zo nan yana fara'a kun gaisa, yanda kika makunni fitila, idan ya juya ɗaya side ɗin sai na gwammace ban taba sanin ki ba ma. Rufa ni ki saya ni."
Da naga Hafsa ba ta da niyyar barin maganar sai na tattara ledojin biscuits ɗin da aka ci na fito waje akan zan zubar. Lokacin da nake dawowa zan shga sai na ji Rufaida na cewa "Tunda kin ƙi sakin maganar nan, kin san hanya mafi sauƙi? Ki bi ta hannun Halimatu don tafi kowa shiri da shi a gidan nan."
Da ƙarfina na ce "Inji uban wa?..." Na kuma datse bakina da hannuna saboda ba'a zagi a gidan nan, kuma duk wanda ya girme ka sai ka girmama shi. Yanda na zaro ido da reaction ɗina ya sa suka fara dariya, da kuma haka maganar ta tsaya. Biyar ma nayi duk suka ɗau haramar tafiya gidajensu.
Rufaida ce ta roƙi Anty Aysha ta taimaka mu mayar da su gida, don haka Daddy muka yi wa waya akan ya bamu aron ɗaya daga motarshi daga gida ganin motar Anty Aysha ƙarama ce. Ya ce mu karɓa makulli a wurin Momy amma a tabbatar an yi tuƙi da nutsuwa. Biyar da rabi daidai muka tafi kai su.
Muna dosar gate ɗin gidanmu domin fita sai ga shi an buɗewa Ya Buhari zai shigo, don haka muka ɗan dakata ya fara sai mu fita. Kusa da motar mu ya tsaya saboda a zaton shi Daddy ne zai fita. Anty Aysha ta sauke glass ɗin ɓangarenta na mai tuƙu, ni ina kusa da ita sai sauran a baya. Ta ce "Za mu je mayar da baƙinmu gida ne."
Bai amsa wannan ba sai cewa da ya yi "Dad yana ciki ne?"
"A'a, amma ai mun tambaye shi." Ta amsa masa tunda ta lura yana tambayar ne saboda ganin mun ɗauki motar Daddy.
Ya sake cewa "Drive with care Hajiya. Sai kun dawo."
Ya fara juya sitirayin shi don wucewa ciki wurin parking, Hafsa ta zuro kai tana kallon shi ta ce "Mun gode Ya Buhari, sai an jima."
Ya ɗago kan shi tare da dafe shi ya ce "So sorry pls, hankali na yayi gaba, don Allah ku yi haƙuri. Mu ma mun gode ƙwarai, ku gaida gida."
Rukky ce kusa da mu, ita ya kamata mu fara saukewa amma tace a'a, mu je mu gama sauke su tunda ita akan hanya take idan muka dawo sai ta sauka.
Gudu Anty Aysha take abinta mu kuma sai surutu muke abin mu har da ita ɗin ma, har muka je muka sauke Hafsa da Nusaiba. Akan hanyar mu ta dawowa Rufaida da ni muka damu Anty Aysha ta tsaya a Hangout Zoo Road mu yi ko da minti talatin ne. Kamar za ta ƙi, amma magiyar mu ta isheta da kuma ƙarin tana son ta ga me muke jin daɗi a zuwan da muke yi ya sa ta yarda muka wuce can kai tsaye.
Yanayin tuƙin da Anty Aysha ta shiga wurin da shi ya ja mana kallo. Ga shi dama jeep ɗin Daddy ce, ga shi mu kuma yaran 'yan mata ne. Sai da muka samu wajen zama kafin na tafi siyo mana abun taɓawa, kuɗin ma a aljihun motar muka gansu muka ɗiba amma za mu faɗa masa mun ɗiba idan mun koma gida. Kowa na siya masa abinda nasan yana so, Rukky da ban san me take buƙata ba sai na siya mata irin nawa kawai. Sai na zo biyan kuɗin shine na tuna ashe mu huɗu ne, ni na manta shaf. Don haka nace kar ya cire komai a ledar bari na koma wurin motarmu na ɗauko masa cikon kuɗin tare da miƙa masa kuɗin hannuna da na zo da su.
Da sauri na fice sai da na tsaya wurin Anty Aysha na yi mata bayani tare da karɓar mukullin motar, na ƙaro kuɗin har ma ya wuce cikon, in case wani zai ga wani abun yana buƙata.
Da na koma wurin biyan kuɗi sai na iske ledar a gefe da kuma kuɗin da na bari a samanta. Sai kawai na lissafa cikon kuɗin na kuma ɗauki na saman ledar na haɗa duka na miƙa masa (mun saba sosai saboda yawan zuwanmu wurin amma ba wai mun san sunan juna ba ne ko muna zaman hira ba).
Ya kalle ni yana murmushi ya ce "Ai yallaɓai ya biya maki, ya kuma gargaɗe ni da kar na karɓi kuɗin komin dagewar ki."
Tsayawa nayi ina kallon shi galala da alamar mamaki zane bisa fuskata, sannan na ce "Kar mu yi haka da kai, domin ina kyautata zaton kuskure aka samu, don ni ban san wani yallaɓai ba."
"Ki yi tafiyar ki kawai, shi ya sanki sosai ai. Ba sunan ki Halima ba? Don da sunan nan naji ya kira ki."
Ganin zan ɓata lokacina a banza sai kawai na ja kayan siyayyar tamu na koma wurin zaman mu. Na zuɓe kuɗin tare da kayan saman teburin.
Ganin kuɗin sai Anty Aysha ta ce "Discount aka samu ne? Ko kuɗin ne suka yi yawa? Na labarta masu abinda ya wakana.
Rufaida ta ce "Koma waye ya biya meye na damuwa? Ba shi ya ga zai iya ba? Mu kar ki dame mu, sai tsoron bala'i."
A haka muka fara cin abinda na kawo bayan na bawa kowa na shi. Iskar yamma na kaɗawa muna kalle-kalle da magana sama-sama. Garin hange-hange na hango Ya Yusuf (saurayin Anty Aysha da yayi mana hoto ranar haɗuwarsu ta farko), tare yake da abokansa guda uku.
Ina murmushi ina ɗaga mashi hannu, shi bai lura da mu ba har wannan lokacin haka ma Anty Aysha bata ganshi ba. Sai kawai na tashi nace masu ina zuwa, shi kuma a lokacin ya tsaya teburin wasu yana gaisawa da su. Ina ƙarasawa na salƙafo hannunshi ina dariya, cike da mamaki ya juyo don ganin waye wannan sai kuma ya fara dariya ya ce "Ƙanwata ya ki ke? Ina ɗayar ƙanwar tawa?"
"Yayanmu (muna mayar masa da haka ni da Rufaida idan ya kira mu ƙannensa) ina wuni? Ga mu can a zaune amma da albishir domin tare muke har da Anty Aysha amma ba wanda ya ganka a cikinsu sai ni."
Ya ƙara washe baki ya ce "Ai kuwa dole a baki albishir domin kin kawo labari mai daɗi, kin ga ya kamata na sake sawa a tsorata mun ke sai na sake yi maki wani sabon hoton."
Na zumɓura baki na ce "Ai kuwa ba zan ƙara kawo maka albishir ba daga yau" Na fara tafiya da baya-baya na ce"Na tafi na zuga ta mu koma gida yanzun nan yanda sai dai ku gaisa a tsaye. Abokan yayanmu ina wunin ku? Sai an jimanku."
Ko jiran amsawar su ban yi ba na wuce, ina jin shi yana cewa "Zo mana ƙanwata, haba mana, wasa ne fa." Ganin na ƙi juyowa sai ya biyo ni.
Ina dariya na juyo saboda na ji shi ya biyo ni na ce "Ni ma na rama ai, 1-1"
Kafin ya amsa har mun iso wurin su Anty Aysha don haka sai bai ce komai ba ya koma ta bayan ta a sanɗa ya rufe mata ido. Mu kuma gulma ta sanya muka zuba masu ido duk mun yi tsit. Ta hau laluɓen hannun amman kamar ta kasa ganewa sai ta ce "Hannun nan dai kam tabbas ban san ko na waye ba, amma ƙamshin turaren kamar...ummm...ummmm... Ni kawai buɗe mun idona, idan ba Yusuf ba ne ban san ko ma waye ba." Muka dinga yi masu dariya.
Rufaida ta ce "Lallai Anty Ayshan nan tamu sai a hankali, watau har kin san yayanmu ne. Kai soyayya!"
Ita kuma ta harare ta ta ce "Kin ci gidanku Rufaida." Yanda ta yi lokacin da ta faɗi haka yasa muka ƙara kwashewa da dariya.