Free chapter · Read without an account

27

by Fareeda Aliyu · Taƙaitaccen Tunani

Sai da nayi kwanaki biyar ina jinya kafin na warke garas. A kuma tsakanin kwanakin jinyar an zo an bayar da bus zuwa duba ni daga makaranta. An kuma faɗa wa Inna amma tunda ta zo sau biyu ba ta ƙara zuwa ba saboda ganin yanda suke matuƙar kula da ni. Haka su Shukura (mun yi musayar lambar waya da su, sun kuma kira don su ji ko lafiya saboda mun daɗe ba mu haɗu a Hangout ba) sun zo dubiya bayan Rufaida ta shaida masu ban ji daɗi ba lokacin da suka kira waya. Rukky kullum sai ta zo ita ma. Kai har ƙawayen Rufaida ma sai da suka zo duba ni. Irin wannan ƙauna da mutanen nan suka nuna mun sai Allah ne kaɗai zai biya su. To shi kan shi Daddy sai da ya baro tafiyar da ya yi ya dawo gida domin ganin ya jikin nawa yake, ya kuma juya washegari ya koma.

********************


Rannan da yamma muna zaune tare da Rufaida a harabar gidan muna ta kallon jaridun kwalliya, karatu-karatu kallo-kallo muke yi, sai kawai na tuna ranar da na dawo ba ni da lafiya kamar na ga baƙi a falo don haka na ce "Rufaida? Ni kam ranar nan ya aka yi da su Hasina kuwa?"


Dariya ta fara yi "Kai! Allah ya yi maki sauƙi to! Wallahi na ɗauka ba ki lura da su ba sam. To ai tunda Ya Buhari ya rikice bana jin ya ƙara yin ta kan su fa. Bayan kin samu bacci ne suka yi mana sallama, shi ma iya harabar gidan ya raka su ya dawo yana gadin ki. Idan ma basu san da abu tsakanin ku ba, a ranar dai sun sani, shi da ko kunyar Mommy bai ji ba bare ta wasu?"


Zuwa yanzu kam Anty Aysha kayi face-face cikin jarabawar ta. Shi kuma Ya Buhari kwata-kwata ba ya zama domin kammala gininsu ake yi, kuma a ɗan tsakanin ne shi da Daddy suka yi tafiya domin siyo injin aikin kamfanin. Mu kuma a gida rashin namu hutun ya ta'allaƙa ne ga shirye-shiryen bikin Anty Aysha domin sati biyu bayan kammala jarabawar ta ne bikin.


Zuwa yanzu kam fin rabin kayan da za mu yi amfani da shi a bikin, Daddy ne suka taho mana da shi a dawowar da suka yi, amma kayan amarya kuwa zan iya cewa an gama domin akwati babba aka kawo mata don fitar biki. Kayan ɗakinta kuwa haɗuwa muka yi da ita duka muka zaɓi wani ta internet muka turawa Ya Buhari, su suka siyo mata shi ma.


Ragowan kayan da zamu yi amfani da shi ni da Rufaida wannan dawowar suka ƙarasa kawo mana, kuma hakan bai hana Mommy siya mana wasu anan ba. Sam ba ma ɗaura zani amma sai da ta ɗinka mana kala uku-uku ban da masu skirt da kuma dogayen riguna, ni sai na ce mu ma lefen aka yi mana. Mommy sam ba ta zama, kullum a tafiye take na siyayya, haka ma rannan ta samu a gaba muka je wani wurin aka cike mana bayani tare da ɗaukar hotunan mu.


Na ɗago kaina da har wuyana ya ƙage, na kalli Abban da ko gajiya da saurare na ba ya yi, nayi ƙaramin murmushi. Na ce " Kasan abinda zai ba ka mamaki da halin mutanen nan? Rannan mun dawo daga makaranta muka iske visa tawa da ta Rufaida za mu raka Mommy dubai siyo ainihin kayan ɗakin Anty Aysha don ta ce wanda su Ya Buhari suka turo bai kamata ya zama shine ainihin kayan ɗakin ba. Wannan tafiyar za'a yi shi babu amarya saboda jarabawa duk kuwa da ba ta taɓa zuwa ba.


Farin cikin da nake ɗauke da shi a lokacin ba zan iya fasalta shi domin ko ɗankwali ban ɗauka ba bare takalmi na tafi kai wa Innarmu albishir ina ihu. Tare muka dawo da ita ta zo tayi wa Mommy godiya.


Mommy kam cikin hanzari ta katse godiyar Inna ta ce "Haba Innar Halima, ai babu godiya tsakanin mu. Haifar ta kawai ki ka yi amma mune ke tare da ita, idan ma morar ta ake yi ai mu ne masu morar, don me ye marabar ta da sauran yaran gidan? Kuma ai naga ta kusa zama ta mu gabaɗaya idan da rai da lafiya?" Dolen Inna ta yi shiru lokacin da ta rufe maganar da cewa "Allah ya ƙara yalwata arzikin ku, Ya kuma ba da ladan kowanne aikin alherin da aka yi domin shi."


Ko da Anty Aysha ta dawo daga makaranta da gudu muka tare ta wurin motar ta da maganar tafiyar mu. Tare muka rankaya zuwa falon Mommy. Tana ganin mu kuwa ta fara dariya, ita kuma Anty Aysha ta fara buga ƙafa tana faɗin "Ni Mommy gaskiya ya ya za'a yi da ni to? Kin san ban taɓa zuwa ba ai."


Cikin murmushi sosai Mommy ta ce "Ke da za ki bar mana gidan? Ai duk inda ki ke so mijin ki sai ya kai ki. Amma na yi maki alƙawari idan Allah ya ba mu aron rai, idan har kun shirya zuwa ke da mijin ki zan biya maku kuɗin jirgi, masauki da ɗan kaɗan na abun kashewa sai ku ƙara da naku. Rabu da waɗannan 'yan zugan, su fa siyayya zasu je yi, ke da za ki yawon buɗe ido ma?"


Rufaida ta ce "Oho dai! Ai dai mun riga ki zuwa."


Ni kuma na ce "Kar yi ki yi mamaki lokacin da zaku tafi ma Daddy ya sake biya mana ya ce mu bi ku mu ma idon mu ya buɗe, Allah ma yasa lokacin muna hutu."


Mommy ce ta katse hanzarin Anty Aysha na magana ta ce "Kar ki kula su don babu wanda zai bi ku idan lokacin tafiyar ku ya zo. Sannan antin ku ce za ta zo ta zauna tare da ke kafin mu dawo (Anty Maryam kenan, ƙanwar Mommy), tare da Jaana ('yar yayan Mommy ce kuma sa'ar Anty Aysha) da kuma Rahma (ita ma sa'ar su Anty Aysha ce amma ɗiyar ƙanin Mommy ce).


A take Anty Aysha ta warware ta hau murna saboda Anty Maryam ɗin kamar ƙawa suka mayar da ita, don zama a ke ana yi hira ana tafawa. Ita Allah bai azurce ta da haihuwa ba kuma tana da ƙaramin jiki, sam ba ta shiga cikin sa'anninta a dangi kullum tana tare da nieces ɗin ta, da an yi magana sai ta ce "Kura a daji ai da yaranta take wasa."


Sai kuma Anty Aysha ta tsaya tana nazari ta ce "Mommy kar su zo mu haɗu na kasa karatu kuma."


"To in dai haka ne gara na ce su yi zaman su, don ba za su zo su hana mun ɗiya karatu ba. Kin ga sai ki yi zaman ki ke kaɗai har mu dawo."


Da sauri ta ce "A'a! Zan san yanda zan dinga ratsa su cikin jadawalin karatuna. Kawai su zo, ai ina kewarsu da yawa."


Ranar da suka iso mun sha hayaniya, wai Allah! Kuma a ranar muka bar Kano da magriba zuwa Lagos domin tashi zuwa dubai ɗin.


Tun isar mu muka fara baccin gajiya don daga ni har Rufaida ba mu runtsa ba a tafiyar sai da muka masauki. Daga muka fita yin abinda ya kawo mu. Kwanaki muka yi muna zagaye kafin muka daina ruwan ido muka zaɓar mata saiti biyu na kayan ɗakin. A irin zagayen shagunan nan ne muka hango wani shago sun yi displaying wata doguwar riga, a tare da Rufaida muka gani, ai kuwa muka damu Mommy akan a siyawa amarya ta saka a event ɗaya na bikin ta. Duk dagiyar ta na faɗin cewa an gama da kayan sawar amarya tuntuni bai hana mu nacin ba, dole ta haƙura ta siya tare da sarƙa, ɗan kunne da abun hannu.


Ba wai zallar kayan ɗakin ba ne kawai muka siya, har kayan ƙyalƙyalin gida, gaskiya mun kashe kuɗin Daddy babu laifi sai dai fatan Allah ya sa gidan Anty Aysha ya zamo babba yanda zai kwashe wannan uban siyayyar.


Yaya Buhari ne ya ɗauko mu a filin jirgi bayan dawowar mu, shi ma kwanan su biyu da dawowa ƙasar kenan. Doguwar rigar da muka siyowa Anty Aysha da yake a wani akwati suka sa mana shi muke ta ɓoyewa ba ma son kowa na gidan ya gani, mun fi son sai amarya ta sa ranar bikinta kowa ya gani, don ɗaki muka kai shi muka kulle. Tsabar ɗokin ta zo mu gwada mu gani da muke yi, ji muke kamar mu je makaranta mu ɗauko ta. An rabawa tsaraba an bawa su Anty Maryam.


Ƙarfe biyar ta gota ta iso gidan, da ihu muka fito domin taro ta daga haraba amma sai ganinta tare da yayanmu ya katse mana hanzari, mun san ƙara ɓata mana lokaci zai yi.


Shi kuma yana ganin mu ya fara murmushi ya ce "Inye? Ka ga ƙanne na, saukar yaushe? Yara sun ji sabon yanayi sun canza." Muka fara dariya muna gaishe shi. Sallama kawai ya yi ya ce zai dawo gobe bari ya bar ta tayi mana sannu da zuwa da kyau. Cikin daɗi muka ja ba mu bari ta raka shi ba muna cewa ta zo mu nuna mata abinda muka siyo mata, da ƙyar muka bari ta fara gaisawa da Mommy. Ita kanta Mommy cewa ta yi "Ku je idan sun gama da ke kya zo, idan ba su gama da ke ba ba barinki za su yi ba." Kuma muka doka sa'a su Jaana basu biyo mu ba.


Sai da muka rufe ƙofar ɗakin sannan muka jawo ɗan akwatin rigar. Kafin mu buɗe sai Rufaida ta dafe akwatin tana cewa "Gaskiya Anty Aysha ki sauri ki yi wanka sai ki gwada abin da muka kawo maki, don Allah kar ki ce komai ke dai ki yi sauri." Ganin irin ɗokin da muke yi ya sa ba tsaya musu ba ta faɗa banɗakin kawai tayi abinda aka buƙata.

*****************


Ƙarshen tika-tika-tik! Bikin kam ya matso sosai don gidanmu har ya fara cika da jama'a. Mun sha rabon kati har mun gaji sai kuma ta dalilin rabon katin Allah ya sa muka ziyarci gidan su Zainab (ƙawayenmu na Hangout) muka kai masu kati.


An yi jere, gidan sama da ƙasa ne don haka gida ya kwashe siyayyar mu har ma da wanda Ya Buhari ya fara siyowa. Maa shaa Allah, gida kam Alhamdulillahi sai dai fatan Allah ya basu zaman lafiya.


Yayanmu a kwanakin nan kam ya mayar da gidanmu kamar nasu shi da abokansa, kusan koyaushe suna gidan.


Ni da Rufaida sarakan son gulma sai da muka sa Anty Aysha a gaba muka je gidansu Rahina kai mata kati, reactions ɗin ta kawai muke son mu gani. Me hali baya bari, don muna zuwa ta tari Anty Aysha da "An ce kina ta rabon katin biki ni kuma ban ga kin kawo mun ba, har na fara tunanin ko laifi nayi maki."


Anty Aysha ta amsa "Ni kuwa me za ki yi mun? Kawai na fara rabon daga na nesa ne, bacin haka ma ai ke ta hannun dama ta ce, ko ba kati nasan muddin na faɗa maki ai za ki halarta har ki gayyato jama'ar ki. Ko ba haka ba ne?"


"Ayyo. Dole na ai. Kwana biyu kuwa kun haɗu da Yusuf? Don naji ma an ce shi ma satin bikin shi kamar ya kama. Wait... Ko lokaci ɗaya ne da naki?"


Anty Aysha ta ƙi amsawa sai ma zaro katina da tayi ta miƙa mata tana cewa "Ga katinan ki da na waɗanda za ki gayyata, ranar laraba za'a fara."


Ta biyo zata raka mu, duk yanda ta so yin zancen Anty Aysha sai bagararwa take yi tana ƙoƙarin tsayar da ita daga rakiyar. Ni kuma na ce ai gara ta ƙarasa wurin motar su gaisa da angon. Shi kuma kamar ya san abin da ke faruwa, yana hango mu ya fito tare da buɗe mata ƙofa. Reaction ɗin Rahina ranar har muka je gida dariya kawai muke yi, tsamo-tsamo tayi.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol