Free chapter · Read without an account
021
by Halimatou Khabir · MAI DAKI
*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 21*
A mota suna tafiya Fiddausi a gaba kusa da Zakiyya tana tuk’awa Rukayya tana baya tana danna wayar ta abinda yake damun ta daban da abinda yake damun su, Zakiyya tace, “Wato ke Rukky wai d’auka kike mijin da bashi da ko sisi yana da wata daraja ne?.” Rukayya ta d’ago ta kalle ta tace, “da Allah ya tashi bayani akan miji ai bai ware mai kudi yace yafi daraja ba ko?.”
Fiddausi tayi dariya tace, “Kiyya wannan fa bazata fahimci komai ba sai Allah ya had’a ta aure da irin su İbrahim sannan zata gane me nake nufi.” Rukayya bata ce komai ba tayi shiru suka cigaba da tattaunawa ita da Zakiyya kafin Zakiyya ta kuma cewa, “Rukky an ina zan sauke ki ba gida Fiddausi tayi ba.” Rukayya tace, “Sauke ni a nan ma kawai na k’arasa.”
“A’a mu k’arasa gaba sai ki sauka.”
“A’a sauke ni kawai daman Ina so na biya gidan Sajida.”
“Okay to, ki gaishe ta” ta fad’a tana samun wajan parking sukayi sallama Ruky ta sauka su kuma suka yi gaba.
Fiddausi tace, “Ni wallahi tausayin Rukayya nake ji, Gashi ta jima babu aure sannan ga zuciyar son talaka.” Zakiyya tace, “Nima haka wallahi, Ina mata addu’ar samun mijin da zai rik’e ta haka ni kaina bana jin dadi wallahi musamman in Muna tare haka.”
“Dukkan mu da aure da yara ita kadai ce babu, ko saurayin ma bata dashi abin sam babu dadi.”
“Allah ya kawo mata da gaggawa. Ke muyi abinda yake gaban mu, mu k’arasa gıdana ku had’u a can?.”
“Mijin ki baya nan?.”
“Yana lagos sai gobe zai dawo.”
“Muje to.” Hanyar gidan Zakiyya suka nufa kai tsaye dan Alhaji yayi mata waya zai shigo bayan magriba.
Suna zuwa ba jimawa akayi sallah Fiddausi ta sake wanka tayi sallah Zakiyya ta bata kaya ta saka tayi kyau sai khamshi take a wannan lokacin Alhaji yazo yana jiran ta. A hankali take fitowa yana zaune a kujerar da take kallon inda take fitowa ganin ta fito tana tafiya da rausaya ga khamshin da take yi bai San ya mik’e tsaye ba sai da ta ‘karaso yayi murmushi tace, “Barka da zuwa Alhajina, ka zauna mana” ta fad’a tana zama kamar wacce ta bashi Umarni ya zauna yana sake bin t da kallo.
Fiddausi ta had’a dukkan abinda yake so a jikin mace, gata fara, gata mai murjajjen jiki, gata da sura mai kyau. Hakan yana daga cikin abinda ya saka hankalin sa yake tashi, in yana tare da ita dakyar yake iya daidaita kansa a gaban ta dan in badan hakan ba komai zai iya faruwa. Ya kasa daina kallon ta har sai da ta sake yin murmushi tace, “Barka da dare.” Lumshe idanun sa yayi ya sauke Ajiyar zuciya Maimakon ya amsa mata sai yace, “Fiddausi ki tausayawa bawan Allah ki san yadda zakayi dani, wallahil azim bana so na rasa ki” ya fad’a kamar zai mata kuka yana kallon ta.
Fiddausi tayi dariya tace, “Waye yace zaka rasa ni?.”
“Gashi kina neman saka min hawan jini, kin kasa kashe auren ki nace miki zan biya mijin naki ya sake ki kince A’a, kaina ya kulle ban san ya zan miki ba Fiddausiiiiiii!” Ya ‘karasa fada da wani irin salon da ya saka ta jingina da kujera tana kallon sa.
Tace, “Bawai nak’i bane kawai dai….” Ya katse ta ta hanyar fad’in, “Kawai me? Dan girman Allah kar ki min haka in ba so kike na rasa raina tun lokacina baiyi ba.” Fiddausi tayi shiru bata ce komai ba tana kallon sa hakan ya saka ya sake cewa, “Soyayyar ki tayi min mugun kamu Fiddausi, wallahi waya ake min tafiya zuwa America ta kama ni amma na kasa tafiya sabida bana son tafiya ba tare da magana mai k’arfi tsakanin mu ba.”
Fiddausi tace, “Ina bin komai a sannu ne bana son nayi abinda za’a gano nice na kashe auren da kaina, kodan sabida iyayena bana son yin abinda zai jawo musu magana.” Ya girgiza kai yace, “Kina da gaskiya, amma ni kuma takura min hakan yake yi wallahi bana iya yin komai gashi ko waya ban cika samun ki ba, inda ina jin muryar ki da sauk’i to sai lokaci zuwa lokaci. hankalina yana neman bari jikina ko aiki bana yi yi gabadaya.”
Fiddausi tace, “Lokaci ya kusa kar ka damu ni kaina Ina son kasancewa dakai.” Ya sauke numfashi yayi shiru kafin yace, “Kina da international passport?.” Ta girgiza kai alamun A’a yace, “gobe Monday in kina da lokaci zan aiko a d’auke ki a kaiki passport office za’a yi miki emergency passport, ki d’auki national I.d card din ki da hotuna guda biyu. Ana d’aurin auren mu zu wuce America bana son wani tsaiko gwara ayi komai a kan lokaci, kinga sai Kiyi zaman ki a can kiyi karatu.”
Wani irin dad’i ya mamaye zuciyar Fiddausi nan take ta sake jin in bata kashe auren ta ba ai zata iya mutuwa tayi farrr da idanu tace, “shikenan in akwai lokacin zan kira ka sai ka turo nan sai ya d’suke ni mu tafi.”
“Dan Allah kiyi kokari kar wani abun ya hana ki zuwa goben sabida lokaci baya jira.”
“Kar ka damu Baby.”
Murmushi yayi yana kallon ta kafin ya mik’e tsaye yace, “Zan wuce sauri nake yi ki gaida Zakiyya a mik’a min gaisuwa, zaki ji alert.” Itama tashi tayi ta raka shi har bakin mota ya shiga suka yi sallama ya tafi.
A guje Fiddausi ta shiga falon Zakiyya ta tarar da ita a tsaye ta rungume ta tana ihu tace, “Na kusa zama babbar yarinya.” Zakiyya ta cika ta tace, “Ba ke kin tsaya hauka da shirme ba, cikin jikin ki sai k’ara girma yake in baki zubar dashi ba ke a ganin ki zai tsaya har ki haihu ki yaye ne?.”
“Ai wallahi yau d’in nan za’a zubar da cikin nan, zancen yi min passport yake yi gobe fa ana auren mu sai America!” Ta fada da wani irin salo tana juyawa da falon. Zakiyya tayi dariya tace, “kiyi da gaske wallahi in ba haka ba alkhairi kina gani zai wuce ki.”
Fiddausi ta zauna tace, “Bari kedai y’ar uwa, abinda zan yiwa Ibrahim ya sake ni cikin satin nan nake so nayi masa.”
Zakiyya tace, “Ki dai yi tunanin abinda zai yi saurin tunzura shi.” Fiddausi tayi shiru tace, “ na farko akwai cikin nan, na biyu kuma sai dai ko iyayen sa….” Sai tayi shiru alamun tunani ta sake cewa, “zan dai san abinda zanyi.”
“Shikenan, kije ki same su kice ke kina so ya sake ki in ba haka ba zaki kashe shi.” Fiddausi ta kalle ta tace, “Anya hakan yayi? Hajiyar sa tana so na sosai ke kin sani.”
“Shikenan to zauna kallon ruwa kwad’o yayi miki k’afa.”
Fiddausi ta tashi zuwa d’aki tana fad’in, “Bari kedai kawai zan san abin yi.” Nan da nan ta canja kayan ta zuwa na d’azu ta fito Zakiyya ta saka driver ya kai ta gida zuciyar Fiddausi cike da tunanin mafita dan dole tasan abin yi kafin lokaci ya k’ure mata.
Tana sauka a motar Ibrahim yana kallon ta yana tsaye a k’ofar gida ta kalle shi itama ta wuce shi ta shiga gidan ta same shi da duhu ta dafe kai sam ta manta za’a yi mata gyaran solar wallahi, kafin ta kai ga shiga d’akki taji muryar sa yana cewa, “Ina kika je?.” Banza tayi masa kamar bata ji ba ya sake cewa, “Fiddausi daga gidan ubanwa kike!?.” Juyowa tayi ta kalle shi tace, “Daga Unguwa nake, Ina ruwan ka da inda naje?.”
Bai San lokacin da tsinke ta da mari ba abinda bai tab’a yi ba cikin fusata yace, “Uban waye ya ajjiye ki a mota? Waye ya d’auke ki d’azu? Wa kika tambaya da zaki fita?.” Hannun ta yana kan fuskar ta cikin mamaki tace, “Ni ka Mara?.”
“Na mare ki, Fiddausi zaki rama ne?.”
“Baka wuce na rama d’in ba ai, amma bazan rama a yanzu ba sai lokacin yayi zaka tuna da kanka, amma ka sani wallahi bazan fad’a maka ba” tana fad’a ta wuce ciki shi kuma yayi kwafa ya fita daga gidan dan yin sallar i’sha duk da baya nutsuwar sa.
Tana shiga d’aki kiran Zakiyya ya shigo ta d’auka a fusace tace, “Wai ni Ibrahim zai saka hannu ya mara Zakiyya?.” Zakiyya tace, “Mari? Akan me?.” Fiddausi ta girgiza kai tace, “Yana ganin gangar jikina a banza ne shiyasa yake ganin ni ba komai bace, amma wallahi zan koya masa hankali.”
“Daman na Kira ki ne akan na turo a kawo miki maganin abortion din yanzu, zai zo zai kira ki sai ki karb’a .” Da to akwai ta amsa ta kashe wayar tana wuci.
Dakyar ta iya yin sallah i’sha tana idarwa aka Kira ta a waya har lokacin bai dawo ba ta fita taje ta karb’o tana shirin dawowa suka kuma had’uwa lokacin motar ta tafi. Ko kallon sa batayi ba ta wuce d’aki ta kunna fitilar wayar ta ta ajjiye maganin akan mudubi a lokacin ya shigo d’akin ya kalle ta yace, “me kike ji dashi ne?.”
“Abinda kake ji dashi Ibrahim, wallahi sai kayi dana sanin marina da kayi, sai na tabbatar maka ni ba wacce zaka saka hannu ka daka bace.”
“Waye wannan d ya kuma zuwa wajan ki?.”
“Saurayina ne akwai wani abun kuma!?” Ta fad’a cikin ihu tana kallon sa.
Kan madubin ya kalla yaga maganin da yake ajjiye duk da shi ba likita bane amma yayi zaman chemist yasan magani kala-kala, ya kalle ta yace, “Me zakiyi da wannan maganin?.” Sai da gaban ta ya fad’i dan ta manta dashi a wajan da zata d’auke da ya shigo amma sai ta jure ta kalle shi kamar zatayi magana sai kuma ta bud’e jakar ta da take ajjiye ta d’auko result din cikin ta nuna masa tace, “Ciki ne dani kuma zubar dashi zanyi wallahi bazan kuma haihuwa dakai ba, na gaji da tara iyali tare da talaka.”
Kafin ya d’auki maganin ta d’auke jikin sa ya soma yin rawa b’acin ransa ya ninka na baya yana takowa tana yin baya jikin ta yana rawa yace, “Zaki zubar da ciki kika ce?.” Kafin tayi magana ya cafko ta ya murd’e mata hannu ta saki ihu ya kwace maganin hannun nata yana nuna ta da yatsa yace, “Na gaji da d’aukar iskancin ki Fiddausi, na gaji da jure duk abinda kike yi kina ganin kamar tsoron ki nake ji.”
“Daman so nake ka gaji ai, daman haka nake so ka gaji d’in ka sake ni kowa ya kama gaban sa. Na gaji da zama dakai wallahi ka sake ni ko kuma nayi maka abinda baka tab’a tunani ba.” Juyawa yayi ya fita ta biyo shi a guje zuwa tsakar gida cikin murya mai sauti tace, “in ka cika d’an halak ka sake ni Ibrahim, indai akwai zuciya a kirjin ka ka sake ni yanzu ba anjima ba. Kuma wallahi sai na zubar da cikin nan dan ka kwace magani a banza a wofi ai ba na duka duniya ka kwace ba, wallahi bazan sake haihuwa da talaka ba.”
Bai San lokacin da ya saka k’afa ya fyalli ‘kafar ta ta ba ta fad’i k’asa ta saki kuka sabida yadda bayan ta ya bugu sabida bata shirya hakan ba, Tunawa da cikin jikin ta ya saka shi sauke numfashi da dana sanin hakan yace, “Ki kiyaye ni Fiddausi kar ki kaini bango.” Sai kuwa ta mik’e tsaye duk da yadda take ji ta chakume shi tace, “So nake na kaika bangon daman ai, ka sake ni nace in ka isa kai dan halak ne, indai da gaske kake wannan maganar kawai ka sake ni domin bazan tab’a kiyayar ka ba. Aikin banza talaka shashasha mara mammora!.”
Sau uku ya wanke ta da maruka zafafa har ya fasa mata baki ta sake yin ihu tana kuka yace, “Na fiki iya rashin mutunci, duk abinda kike ji dashi na fiki Fiddausi.”
“To ka nuna min iskancin naka mana, indai da gaske mai shi din ne ka sake ni mana. Wallahi ciki kuma sai na zubar dashi.”
Sake zuwa tayi ta chakume shi ta yaga masa rigar da take jikin sa duk da kuka take amma haka take yin abu hauka-hauka tace, “ka sake ni nace!.” Ya kalle ta yace, “Bazan sake ki ba, kuma wallahi kika sake kika zubar da cikin nan a bakin auren ki!.”
“Subahanallahi! Ibrahim Lafiya?” Maman Zainab mak’ociyar su ta fad’a Jin ihun Fiddausi yayi yawa ya saka ta shigo. Fiddausi bata ji shigowar ta bama tace, “daman ai sakin nake nema kuma sai na zubar kaga kenan daga lokacin babu auren ka a kaina, kuma wallahi sai kayi dana sanin dukana dan wallahi sai na d’auki mataki a kanka, sai ka gwammace baka San wata Fiddausi a duniya ba.” Tana gama fad’a ta shige d’aki a guje. Ibrahim ya kalli Maman Zainab tace, “Babu komai Maman Zainab ki koma Mun gode.” Maman zainab tace, “A cigaba da hakuri, sai da safe” ta fita shi kuma ya shiga daki ransa yafi na baya b’aci ganin abinda bai tab’a faruwa ba ya faru shine maqota su shigo gidan sa sabida ihu ko wani abun Mara dad’i.
Bai sake sauraron fa ba dan in ya biye mata zai iya b’allata, ga ciki a jikin ta ko ya ya aka tab’a ta wani abun zai iya faruwa. Bai tab’a kawo zai iya dukan ta ba Tunda suke amma sai gashi shine harda mari sabida halayyar da take nuna masa. Ranar dukkan su kwanan b’acin rai sukayi hakan ya saka koda safe bai waiwaye ta ba ya fice daga gidan kai tsaye gidan su ya nufa san yana son had’uwa da mahaifin sa akan lamarin Fiddausi ya gaji gwara manya su shiga, ya gaji da ajjiye maganar matsayin sirri gwara a Kira ta aji meye yake damun ta.
Mahaifin nasa kuwa yana nan da yayyen sa maza guda biyu harda yayar Hadiza Mariya ce babu a wajan da Fadima ya shiga da sallama duk suka juyo suka kalle shi suka amsa ya k’arasa ya zauna suka gaisa gabadayan su, Hajiya ce ta shigo tana fadin, “A’a, Ibrahim yau ma da safe ka fito?.” Fuskar sa babu walwala ko kad’an kamar yadda ya saba yace, “Eh hajiya, barka da safiya.” Ta amsa tana zama kafin Mahaifin sa yace, “Ibrahim me yake damun ka haka ka rame?, ga fuskar ka ta nuna alamun damuwa sosai, lafiya kake?.”
Ibrahim ya gyara zama yace, “Alhaji daman abinda ya kawo ni kenan wajan ka.”
Alhaji yace, “to ina Jin ka, Allah yasa lafiya.”
“Akan matsalar Fiddausi ne, Ina so na kai ‘karar ta wajan iyayen ta, bana so nayi hakan babu sanin ka shiyasa na fara sanar da kai.” Hajiya ta kalli Alhajin su shima ya kalle ta dan abin ya bawa kowa mamaki karo na farko kenan da yazo gida ya fad’i damuwar sa akan Fiddausi.
Alhaji yace, “Wacce matsala ce har ka kasa jurewa kazo ka sanar damu Ibrahim?. A sanina babu wata damuwar da ka tab’a zuwa ka fad’a mana a kanta balle muce a sake maimaitawa, me yake faruwa?.”
Ibrahim ya kulle ido ya bud’e Allah ya sani baya daga cikin masu son fad’ar damuwar iyalan sa, sabida shi zai iya mantawa ya cigaba da zama da matar sa iyayen sa kuma baza su manta ba har abada, shiyasa ya zab’i yin shiru Akan duk wata magana ta iyali.
Zaiyi magana kenan aka ji sallamar Fiddausi a k’ofar d’akin aka amsa kowa ya bita da kallo ganin fuskar ta ta tasa ga bakin ta ya kunbura ta zauna ta gaishe dasu tace, “Alhaji na kawo k’arar Ibrahim ne, jiya da daddare yayi min duka bayan yasan Ina da ‘karamin ciki, ya dake ni akan gaskiyata dan kawai na fad’a masa laifin sa shikenan ya rufe ni da duka. Bazan zauna ya dinga dukana kamar wata jaka ba gaskiya, ba jiya aka fara ba ko yaushe da nay laifi zai ce zai dake ni. Maganar gaskiya na gaji da halayyar Ibrahim ni kawai ya sake ni, bana son sa, bana qaunar sa, bana qaunar zama dashi ko kusa, in aka tilastamin zama dashi komai zai iya faruwa gaskiya, dan zan iya kashe shi!” ta fad’a kai a sunkuye kamar munafuka kafin ta mik’e tsaye ta kalli kowa na d’akin bata sake magana ba ta juya ta fita.
Baki sake kowa yake kallon ta aka rasa wanda zai fara cewa komai, Ibrahim kamar ya zubar da hawaye haka yake ji a wannan lokacin Hajiya tace, “Ibrahim ka saki yarinyar nan indai nice na haife ka! Babu amfanin zama da ita ka sake a yanzun nan!.”
_Daga page din gobe mun kammala book1, akwai book 2&3 yana nan tafe da zarar Mun kammala wannan akan nair 500 kacal Akwai ajin vip Akan naira 1000 kawai. Direct to me *** via WhatsApp._
#Nana Haleema ce.