Free chapter 路 Read without an account

.

by Khadeejarth Sabi'u Yahyah 路 SARAUNIYAR KYAU (Book 1)

___*馃拫 SARAUNIYAR KYAU 馃拫*




*WASH拢 GARI*


Tana tsaye a kitchen sanye cikin kayan shan iska ta 蓷aura apron saman kayan tana ha蓷a musu Breakfast cikin nutsuwa take komai abinta.


Alamar taku da ta jine yasa ta tsaya da abin da take yi sannan ta juyo. 


Da tsananin mamaki take kallon mijinta dake tsaye gabanta sanye cikin doguwar jallabiya Brown tunani take shin ko ya yi makuwa ne ko me, amma in banda haka mai zai kawo shi kitchen bayan tunda suka yi Aure shekaru wajen nawa ko tunanin shiga baya yi, ko irin yace zai taya ta girki, a'a sai dai wani ba Abubakar sai dai ta girka yaci ba godiya balle 馃グ....


A je tunanin tayi a gefe sannan cikin murmushi ta ce 


"Barka da safiya My Lawful Fatan dai ba neman wani abu bane ya kawo Babban mutum kamar ka kitchen, kai da kanka baka nema wannan servant naka ba a domin ka bata umarni ba."


Murmushi Abubakar Mai Kyau Ya yi sarai ya fahimci abin da take nufi wato dai gatse tayi masa ko ba damuwa, gyara tsayuwar sa ya yi kana Yace


"Ko 蓷aya dama nazo ne na fa蓷a miki ki girka abinci daban saboda..."


Da sauri ta katse shi da fa蓷in 


"Ba茩i zamuyi hala, ai karka damu Yanzu zan kammala sai na saka a kuloli, kaje kayi shirin office kawai oga."


Tayi maganar tana juyowa ta ci-gaba da aikin da take yi, bai kuma cewa komai ba ya fice shima daga madafar.


__*


Wuraren 茩arfe Takwas da Rabi a Ranar tana zaune saman mattress bayan sun kammala breakfast ne tayi wanka tayi shirin zuwa asibiti, shi ne ta zauna a gefan mattress tana jiran shigowar mijinta Abubakar 蓷akin.


Jin shiru bashi ba labarin sa yasa ta mi茩e sannan 蓷auki lab-coat 蓷inta da kuma jakar ta dama tuni ta yafa mayafin ta.


Fitowa tayi kai tsaye ta wuce bedroom 蓷in sa tura 茩ofar tayi bakinta 蓷auke da sallama daga can ta hango sa tsaye sanye cikin shigar alfarma na manyan kaya.


茒an dafe kanta tayi ita ta manta Yau Laraba wacca ta kasance first October babu aiki sam.


Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta 茩arisa shiga ciki tana fa蓷in 


"Oh amma a gaisheni, gaba 蓷aya na manta da cewa Yau 蓷in a Free muke Ranar zagayowar 瞥an cin 茩asarmu abin alfaharin mu."


Tayi maganar tana dariya.

"Karki damu kinji kin kusa samun Abokiyar zama kinga saita dinga tayaki wasu ayyukan inaga idan kika sama Abokiyar zaman zaki rage samun tention da yawa ko kuwa?.."


Tunda Abubakar ya fara maganar Rafi'at take faman antaya masa harara.


Lura da hakan da ya yi ne ya shi canza topic 蓷in ba shiri.馃ぃ


Murmushi Abubakar Mai Kyau Ya yi sannan Yace 


"Okay to ai babu damuwa a haka ma Yadda kike zaki iya Rakani izuwa unguwa tare da Yara."


"Unguwa kuma to wurin wa."


Rafi'at ta tambaya cikin su蓳utar baki.


"Kedai kawai ki shirya zaki gani ai."


Abubakar ya bata amsa, bata kuma cewa komai ba ta mi茩e tana kallon sa sannan ta ce 


"Ka bani mintuna biyar Yanzunnan zan shirya shaf-shaf."


Tayi maganar tana nufar 茩ofa ta bu蓷e sannan fita.


Tana fita bedroom 蓷in ta ta wuce tana shirya wa tana tauna maganganun Abubakar wato Abokiyar zama, kuma ita hmmm, murmushin Takaici tayi a fili ta ce 


"Rafi'at Rafiq Rayyan tafi 茩arfin ayi ma ta kishiya har duniya ta na蓷e forever Wallahi."


Tsaf ta gama shirinta sannan ta 蓷auki jakar ta da mayafinta ta fito waje har lokacin bata gama dawowa dai-dai ba domin kuwa har wani zazza蓳ine taji Yana shirin kamata jin maganar kishiya, wai danma da wasa ya yi ma ta maganar, imagine take yi to da'ace da gaske Abubakar Yake wannan maganar ya zatayi ke nan."


A fili ta ce "Sai dai idan bani a duniyar."


Downstairs ta sauko daga can saman kujeru ta hango mijinta Abubakar ga Yaranta suma a shirye cikin shigar alfarma suna fira da mahaifinsu Abin gunin ban sha'awa.


Murmushi kawai take yi tuni ta manta da maganar wata banza kishiya, hango mijinta da tayi da Yaranta cikin farin ciki.


Sai ita ma ta tsinci kanta a cikin matsanancin Farin ciki taji gaba 蓷aya ba茩in cikin da Abubakar ya 茩unsa ma ta na maganar kishiya ya gudu.


Qarisowa wurin tayi fuska 蓷auke da 茩ayataccen murmushi tana fa蓷in


"Oh My Lawful ayi ha茩uri dani na 蓳ata muku lokaci daya wa ko?."


Tayi maganar cike da 茩issa, murmushi Yayi Yace


"Oh no Yaranki sun qwace ki saboda sun zagaye mahaifin su suna masa tatsuniya."


Tana dariya ta ce "Ai haka ake so."


Abdulmaleek Yaron da bazai wuce shekaru hu蓷u da watanni ba a lokacin ya kalla mahaifiyar sa kana ya mayar da kallon sa akan mahaifin nasa dariya ya yi cikin qwaranci irin na sa Yace 


"Daddy! Mommy!!."


Gaba 蓷aya suka juyo suna kallon shi Yace 

"Momy Daddy Yafi ki kyau cocai cocai."馃ぃ


Dariya suka yi baki 蓷aya kana Rafi'at ta ce 


"Aha ai kowa ma haka ake cewa harni ma na sani saboda shi蓷in kyakyawane a cikin kyawawa."


Tayi maganar cike da nisha蓷i, mi茩ewa suka yi ita ta ri茩e Nailah Yayin da Abubakar Ya 蓷auki Nainarh sannan Ya ri茩e hannun Abdulmaleek suka fita waje, motar sa suka shiga baki 蓷aya sannan ya tayar da Motar, gate man ya wangale masa gate ya fita sai unguwa馃殫..../This is the happiness family/....馃殫


***


Cak murmushin dake akan kyakyawar fuskar ta ya gushe fuskarta ta koma Tamkar bata ta蓳a murmushi ba, saboda tsaban mamakin wurin da taka mijinta Abubakar ya dawo dasu "this is unbelievable."


Wato shiyasa taka jiya da dare ya fita bai dawo ba sai wuraren sha 蓷aya Abin da bai ta蓳a ma ta ba.


Kallon sa tayi dai dai lokacin da shima ya juyo da kallon shi akanta, cike da tsaban takaici ta ce 


"Haba My lawful yana ga ka dawo damu wannan emergency kodai wani ne aka kwantar ban sani ba?."


Tayi maganar cike da sa ran ya bata amsa ba kalar wanda take tunani ba.


Gimtse kyakyawar fuskar sa ya yi alamar ba wasa kana ya ce


"Wurin 瞥ar uwanki muka zo domin tafiya da ita gida."


Ya mutsa fuska tayi cike da alamar tambaya take kallon sa sannan ta ce 


"Wacca 瞥ar uwata kuma Sailuba ba ko wa?."


Girgiza ma ta kai ya yi alamar a'a kana Yace 


"Fito mu shiga zakiga ko wacece ai."


Babu musu ta bu蓷e motar ta fito shima bayan ya fito suka ri茩e Yaran sannan suka nufa ciki Yayin da wasu Nurses ma ta ke bin bayan su da kulolin abincin da suka zo dasu.


Ita dai Rafi'at tafiya take kawai amma gaba 蓷aya hankalin ta baya a jikin ta tunani take shin ko wurin waye haka Abubakar ya kawo su, ita ko ka蓷an bata kawo wannan budurwa da suka taimakawa jiya a tunanin ta.


To akan me ma zatayi tunanin ko ita ce bayan cewa taimakon ta kawai suka yi bawai zasu kasance da ita bane.


Har suka 茩ariso Ward 蓷in bata ankara ba, har sai da taga wa蓷anan Nurses dake gabansu sun shiga wani Room kana ta fahimci nanne Room 蓷in da wacca suka zo wurinta take.


Tura 茩ofar Room 蓷in Abubakar ya yi ya shiga Bakin sa 蓷auke da sallama yayin da ita ma Rafi'at ta take masa baya.


Zaune take a saman gadon marasa lafiya jikinta sanye da kayan asibiti gaban ta kuma tufa ne take ci a hankali, kanta a du茩e tana kallon 茩asa, sai da ta cinye Wanda yake a bakinta sannan ta amsa sallamar da taji anayi a daidai lokacin da ta 蓷ago da kanta tana kallon mutanen dake shigowa 蓷aya bayan 蓷aya take binsu da kallon Rashin sani.


Wani irin bugawa 茩irjin Rafi'at Ya yi ganin kyakyawar fuskar budurwar dake a 蓷akin zaune saman bed.


It's unbelievable menene kuma haka me yasa Abubakar ya dawo dasu wurin wannan to su mata Mene?.


Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sama wuri ta zauna a saman wata farar kujera kusa da mijinta Abubakar da shima ya zauna.


"Sannun ku fa please Mister and Mrs kune kuka taimake ni. In Yesterday?."


Budurwar ta musu tambayar fararen ha茩oran ta duka a waje saboda murmushin dake akan kyakyawar fuskar ta.


Har Rafi'at ta bu蓷e baki zata bata amsa ke nan, likita ya turo 茩ofar room 蓷in ya shigo yana mai musu sallama.


Shiru Rafi'at tayi kamar mai tunani tana ji lokacin da su Abubakar da wannan budurwa suka amsa masa sallamar amma ita tafasar da zuciyarta take bai bari ta amsa ba.


Bayan wannan likita da Abubakar sun gaisa ne, budurwar ta kuma antayo musu tambayar 蓷azu.


Murmushi likita ya yi sannan yace 


"Kedai Wannan patient nawa kinaso ki gano mutanen da suka taimake ki ko to ai sune wa蓷annan a gaban ki."


Dariya tayi cike Farin ciki ta kalla su Rafi'at da kyawawan Yaran dake a gaban su ta ce


"Barkanku dai."


Amsa ma ta suka yi da fa蓷in


"Yauwa kema barka."


Nan kuma suka shiga gaisawa da ita tana musu godiyar taimakon ta da suka yi.


Rafi'at murmushin ya茩e kawai take bin wannan kyakyawar budurwa dashi amma na ciki na ciki.


Kallon kyawawan Yaran tayi cikin shau茩i ta mi茩awa Nainarh hannu alamar tazo, aikuwa Yarinyar ta 蓳angale baki kana ta 蓳an蓳are hannunta daga cikin na Rafi'at ta rarrafa da saurinta irin na Yara, ta 茩arisa bakin gadon da budurwar take zaune sannan ta kama gadon tana kici kicin hawa.


Dariya kawai gaba 蓷aya suke ma Nainarh wato shi dai Yaro ba Ruwan shi 茩aunar kowa Yake ba abin da ya dame shi.


Da sauri budurwar ta kamo hannun Nainarh tahau da ita saman gadon tana ma ta wasa, aikuwa ganin haka suma Nailah da Abdulmaleek suka 茩arisa wurin da saurin su aikuwa duka ta ha蓷a tana musu wasa da alama tana 茩aunar Yara sosai obaaaaa.


Kallon Abdulmaleek tayi da yake Babban cikin su sannan ta ce 


"My friend please Tell me, what is your name?."


Dariya Yaron ya yi sannan cikin qwarancin sa na yara Yace


"Body."


/Buddy/


Dariya tayi cike da nisha蓷i ta ce "Okay wato dai 'Buddy' kake so kace ko?."


Girgiza ma ta kai Yaron ya yi alamar "E," yana dariya.


Ta kuma cewa "To ai na gaskiyar nakeso ka fa蓷amin."


茒an shiru ya yi kamar mai tunani sai kuma can Yayi dariya yace "Abdulmaleek naji Aya Aleem iya kiyana."


"Oh suna mai da蓷i."馃檪


Ta fa蓷a tana dariya.


'Kema Menene sunan ki, ko baki da suna ne?."


Yaron ya antayo ma ta tambayar wacca tasa ta yin murmushi sannan ta bashi amsa da 


"Maleek ke nan ai kowa yana da suna a duniya kamar nima dai suna na, suna na...."


Shiru tayi kamar tana tunani sai da kyar ta iya fa蓷i cikin in'ina


"Suna na Ha-Ja-ah..."


Tayi maganar tana dafe qwoqwon kanta da taji kamar zai rabe gida biyu saboda ra蓷a蓷in da yake ma ta.


"HAJARAH."


Rafi'at ta maimaita sunan cikin ranta tayi murmushi a fili ta ce 


"Sunan ki mai da蓷i kuwa?."


Murmushin 茩arfin hali budurwar mai suna Hajarah tayi tana kuma dafe kanta ta ce da kyar


"Nagode."


"Ah ah kodai kan yana miki ciwo ne, naga kina ri茩ewa?."


Rafi'at tayi ma Hajarah tambayar a yayin da take 茩arisawa wurin da take zaune saman bed.


"Eh Auntie sosai yake mugun rasamin jina nake kamar bani ba."


Hajarah ta bata amsa tana rumtse idanun ta.


Jin haka yasa likita ya yi ma Abubakar alama da su fita.


Ba musu Abubakar ya mi茩e suka fita daga room 蓷in, suka bar Rafi'at tana ma ta sannu ha蓷e karanto ma ta addu'o'i dan ta fahimci kamar hadda jinnu a zancen.


Kai tsaye office na likita suka wuce bayan sun zauna ne, Abubakar da ya gaza jurewa ya kalla likita cikin son jin 茩arin bayani yace 


"Please Dr Khasim ko zan iya samun bayanan Rahoton lafiyar Hajarah kuwa?, danna fahimci akwai abin da yake damunta sosai."


Ajiyar zuciya Dr Khasim ya sauke sannan Ya fara magana


"A gaskiya Mister Mai Kyau akwai abin da yake damun wannan patient Hajarah abubuwa da yawa ma ba abu 蓷aya ba."


"Okay Inajin ka kamar mai da mai ke nan?."


Abubakar ya tambaya yana kuma gyara zaman sa sannan ya mayar da gaba 蓷aya hankalin sa akan Dr Khasim yana jira yaji abin da zaice.


"To kamar dai Yadda kaji na fa蓷a Malama Hajarah tana fama da matsaloli daban daban na Farko dai shi ne....


A binkciken da muka gunadanar akan kwakwalwarta shi ne na farko ta manta da gaba 蓷aya Ahalin ta da kuma ainihin State da take, sai dai abu 蓷aya da ya ba kowa mamaki shi ne....."


Katse sa Abubakar ya yi yana goge zufar da ta karyo masa kana cikin wata kalar murya yake fa蓷in


"Bangane ba Dr Khasim ban fahimci abin da kake nufi ba kwata kwata wai kana so kace min mutum zai iya mantawa da Ahalin sa ne a dalilin wani hatsari ko kuma ta蓳in kwakwalwa?."


Murmushi Dr Khasim ya yi sannan ya amsa da


"Of course wannan mai sau茩i ne, amma ka fara dakatawa kaji sauran abubuwan da suke damunta kafin kayi wasu tambayoyin."


Jin haka yasa Abubakar nutsuwa amma zuciyar sa bata bar bugu ba.


Dr khasim ya ci gaba da cewa


"Kamar yadda kaji ne, tabbas ta mance gaba 蓷aya memory nata da ya ta蓳a faruwa a tsakaninta da Ahalinta, sannan kuma ta manta da sunan State da take gaba 蓷aya a Brain nata...

Sai dai abu 蓷aya shi ne bata manta ko wacece ita ba, ma'ana dai shi ne bata manta sunan ta ba, ko kuma karatun ta ko kuma wani burin ta bata manta dasu ba, sai dai kuma 蓳angaren Ahalin ta dai...

A bisa binkciken da muka gabatar shi ne zata iya tunawa da Ahalinta da kuma sunan State nata kamar nanda shekara 蓷aya ko fi ye da haka a bisa hasashen wasu manyan likitocin duniya...

Amma idan shekara 蓷aya tazo ta wuce wata shekarar ta zagayo bata tuna komai ba, tofah sai dai ayi ha茩uri domin kuwa har abada ba zata ta蓳a tuna komai ba...."


Ido waje wannan karon Abubakar yake kallon Dr Khasim saboda tsananin mamaki ma kasa cewa komai ya yi kawai yana tauna maganganun Dr Khasim ne.


Sun 蓷auki tsawon lokaci a haka ba Wanda ya iya cewa komai, sai can bayan kamar mintuna biyar.

Abubakar ya nisa sannan yace 


"Dr Khasim ina da wata tambaya 蓷aya fa."


Murmushi Dr Khasim ya yi kana Yace


"Okay Go ahead Inajin ka."


Abubakar Yace "To wai dama can an ta蓳a samun kalar wannan matsalar ne, mutum ya manta memory nasa da ya ta蓳a faruwa a tsakanin sa da Ahalin sa a dalilin hatsari ko wani Abun?."


"Eh an ta蓳a samu a 茩asar China Babban Birnin 茩asar wani mutum ya yi hatsarin mota sai gaba 蓷aya ya manta da Ahalin sa da sunan garin sa abin da bai manta ba kawai shi ne shi蓷in 蓷an kasuwa ne, sannan kuma 茩arin abin mamakin bai manta da harkokin kasuwancin sa ba."

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol