Free chapter · Read without an account

Chapter 2

by Rashida Adamu gwaram · HAKURINMU

HAKURINMU 2


    fatima, amina da sumayya duka kirar kalangune sede na wani yafi na wani, sumayya duk ta fisu gashi anma bata kaisu haske ba duk fatima tafisu haske, sede amina akwai idanuwaa masha Allah ga hanci, fatima akwai hanci da lashes se hamdala sumayya kuma akwai full lips babu wacce za'a cewa mummuna acikinsu. Sun shiga motar fatima ne me kirar picanto domin zuwa ziyara, a nan suka tarar da aunty mariya wacce take qanwar babansu tazo gida dan a gombe take da zama da ita da danta qwalli daya tallin tal wanda ta dorawa son duniya me suna Usman muhammad abdullahi wanan da bade rashin ji ba shekarunsa 17 a duniya ya gama secondary school yana jiran admission shine ya biyo babarsa domin sada zumunchi.

suka sha hirar su suka gama, kakannin su sunji dadin zuwansu sosai a yayinda aka tambayesu ko akwai wacce take da wani domin ta fito dashi, haka duk sukaja bakinsu sukai shiru, dayake uncle sulaiman yana nan abin ya bashi haushi anma bece komai ba se cewa yai dama gidansu zeje yayi kwana biyu beje ba, hakanan de akaita raha sannan suka tashi suka tafi domin zuwa gidan uncle ma'aruf da umma maryama, fitowarsu harabar gidan suka tarar da uncle sulaiman na magana da wani bawan Allah, fatima setaga kaman ta taba ganinsa anma bataa ce komai ba tashiga suka wuce, basu suka dawo gida ba se bayan isha, don sun biya departmental store domin yin siyayya dan sumayya taqi tai musu shiru wai ita ice cream takeso..

Isowarsu gida wande yake cikin farawa housing estate gida ne babba me four bedrooms suka tarar an aje musu abinchi anma mummy bataa kusa suka tarar dakinta akulle basuyi tinanin komai ba dan wani lokachin in batason adameta haka takeyi, suka tafi daki domin huta gajiya fatima ta kulle gidan dan shikenan kuma se gobe sede in anyi baqi dan megadi ma ansallamesa an bada abinchinsa, suna kallo a falo bayan sunchi abinchi se ji sukai fatima na magana ita daya, ya Allah na tina inda nasan sa a AKTH  nake ganinsa he must work there definately, amina da sumayya suka kalla junansu, sumayya ta tambayi amina, wai me take cewa ne? Amina ta daga kafadunta alamar bata sani ba, seta juya gun da fatima take tace ya faty whats going on?

Fatimaa ta kalleta tace da muka fito daga babban gida bakiga wani mutum tareda uncle sulaiman suna magana ba? Sumayya tai shiruuuu tanata kifta idanuwa tace ah ah banga kowa ba, fatima ta juya gun amina kema bakigansa ba?

Ah ah ya fati ni de banga kowa ba, well ai shikenan, i thought he looks familiar ne time danagansa so se yanxu na tina a hospital nake ganinsa, to me yakeyi a babban gida? Am sure ba dangin mu bane. Whatever ya fati you wan carry person matter put for head, tell her ooo sumayya, well ni bacci nakeji kuma har yanxu mummy bata fito ba i hope lafiya de, she is fine in sha Allah inji fati, she is probably having one of her bad days, toh Allah ya sa, amin sumy. Kai anma fa yau munsha roasting, fati ta dago kai daga kallin TV din datakeyi ta dannaa gilashinta da yatsanta ta kalli amina tace fadi ki qara fada, at this rate wallahi we better be serious because yadda mukasha grilling yau kawai ko ma mr wrong ne lets just drag him to the right, sumayya ta juya kai tareda cewa i agree to disagree ya fati, why not wait for someone you love, someone who gives you the jitters and butterfly in your stomach, who cares about you, who loves you no matter what who....hy hy hy ya isa madam romantic fairytale amina ta katse ta, i agree we should marry someone we can live with but na sumayya is too much please ki dinga dawowa reality, pshhhh sumayya taiwaa amina gwalooo whatever kawai you guys will not understand.

Amina and sumayya what am trying to say is we should be serious and very careful i feel su uncle sulaiman are planning something dayafi karfinmu, you think so? Amina ta tambaya, yes and am 80% sure and you know am never wrong, toh toh toh make your head no swell madam serious observer, amina ta daka mata duka acinya tareda cewa sumayya this is serious fa, yea i know me xamuyi sede addua kawai, Allah zaba mana mafi alkhairi, Allah sa kar akawo mana abinda yafi karfinmu.

Amin duk suka fada atare yayinda suka tashi duka domin tafiya bacci.


Washe gari bayan sun tashi anci abinci mommy ta tarasu a falo suna kasa tana zaune asama, na taraku nan ne domin muyi wata magana da ku, daam gaban fatima ya fadii, jiya kawunku ya zoo kuma munyi magana me tsahon gaske kuma yanada gaskiya, sede har yanxu bansan taya zan fara gaya muku ba, banason abinda ze quntata muku rayuwarku banason kuje inda bazakuji dadin zama ba, anma me anfi karfina a wannan magana sede inaso kusani duk abinda kukagaa zaku cutu ni babarku ce kugaya min kuma zan yi iya karfinna naga na tsaya muku kusani cewa dan Adam yana nasa Allah kuma yana nasa shima, kusani hakuri shine makamin mumini aduk inda akafi karfinsa, mummy mene kin fara tsorata ni, karkidamu sumayya zakiji koma menene, jiya kawunku sulaiman yazo min da wata magana, magana ne akan zancen aurenku, yasaka ranar aurenku nanda wata 4, yace mufara shiri.

WHAT?? 

Duka suka fada atare, ni mummy bantaba jin inda akai irin haka ba, mummy su waye xamu aura to? Mummy anma kin masa bayani ko? Zasu bamu dama mu zaba koma waye anma ko? Anma sunce mufito da wanda mukeso ko? Haka sukaitai mata tambayoyi, anma inaa mommy takasa ansa su,tausayin yaranta yakamata harda hawaye, ganin tafara hawaye yasa yaran yin shiru, jin sunyi shiru yasa tacigaba tareda cewa ke fatima kawunku yace akwai wani dayazo neman izini domin yafara zua ganinki yan kwankin baya dasuka wuce sede kawunku yace becemishi komai ba se bayan dasuka kammala bincike akanshi sannan ya bashi izini, anma mummy basu tambayeni ba ko ina sonsa? Fatima hakuri zakiyi   dan Allah kiyi hakuri kinjini, i know this is not easy but bear with me please, kiyi hakuri ki ganshi for just a month then sekiyi judging, but mummy anyi fixing date fa? Wanan bakomai bane kinji, sunan sa Doctor Al-amin, jin sunan fatima ta koma gefe tasa kuka, mummy najinta bata ce komai ba ta dage taci gaba da magana, kekuma amina dan gidan kawunku sulaiman zaki aura yace zemasa magana shima, halifa? Amina ta tambaya, ni tinda nake ba abinda ya taba hadani dashi ,infact am not interested in auren zumunci, mummy tacigaba, kekuma sumayya dan gidan kawunku farouq zaki aura. Bade ashraf ba, amina ta fada, shikuwa, mummy bafa musan halinsa ba yaran uncle farouq gabadaya ba'a kasannnan suke ba, rayuwansu kwata kwata ta turawa ce, taya xa ai adauka sumayya abawa yaronnan, bamusan halinsa ba uncle farouq ma yanachan abuja ba ganinsa ake ba ballantana. kawunku yace nigeria ashraf din ze dawo, gaskiya this is wrong inji fatima yaronda tin yana karami acan yake bawai ma ace karatu yaje yi chan ba ah ah mamansa ce achan sabida haka shima acan yatashi bamusan halinsa ba bamusan tarbiyar da akai masa ba, mummy am against this, wanan ai gwara ma ya halifa da wani ashraf. Sumayya de tai shiru batace komai ba hakama mummy ta tashi ta tafi ta barsu a nan, amina tabi mummy da ido yayin da ta bar falon tareda cewa, it seems this is harder for her than us..ranar haka suka wuni kamar anyi rasuwa agidan.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol