Free chapter 路 Read without an account
Chapter 14
HAKURINMU 馃憣馃徎馃尲
Anyi launching fashion line, brand and building lafiya kalau, ya amina ta zo da ya faty.
At the latest dying minute ta bawa su umaima da Maimuna ticket, shima kuma a chan baya suke, hakanan de suka karba dan sunaso suje, manya manyan mutane kowa neman sumayya yake, ansha hotuna, anci ansha kuma tasamu kudi.
Su umaima da maimuna se sakin baki suke.
Adaren ranar, su ya faty da ya amina sun sauka a dakin sumayya.
umaima tazo ta kwankwasa, sumayya ta bude, umaima ta miqa mata mukulli.
Na meye? Sumayya ta tambaya, mukullin gidan ki ne umaima ta fada, sumayya ta dan yastine fuska sannan tace ya dawo ne ashraf din?
Ah ah umaima ta amsa, daddy yace abaki kiyi settling a gidan.
Sumayya ta sa hannu ta karba sannan tace a ina gidan yake?
Next street ne ba nisa. Laraba tasan gidan, gobe zakuje da ita sabida zata tayaki gyran gidan, duk da de kwana kin baya an gyra gidan but kawai de dan dusting ne za'ayi.
Ok thank you sumayya ta fada sannan ta koma ciki tareda rufe kofa.
What is it? Ya amina ta tambaya.
Sumayya ta jefa mata key, tareda cewa mukullin gidana.
Ya faty ta daga bunch of keys sannan tace, this your husband se ahankali.
Mmmm! sumayya ta tabe baki.
Ya Amina tace ah ah i don't want her staying home da aurenta, since ashraf is coming back, gwara ya dawo se mugani ko?
Ya faty ta gyara kwanciyarta sannan tace i don't like him.
Wayene ze kaimu? Ya amina ta tambaya.
Laraba ce, sumayya ta amsa.
Wace laraba? Ya faty ta tambaya.
Wata me aikinsu me kirki wallahi, zakiganta dattijuwa, itace babba acikinsu, kamar ma itace babbar su, ranar danazo she helped me unpack.
Allah sarki, but zamu samu damar ganin gidan before we leave tomorrow ko? Ya faty asked.
Yes ofcourse sumayya answered tareda kashe light don su kwanta bacci.
Washe gari da wuri sumayya ta cewa laraba zasu je ganin gidan sabida su ya amina jirgin karfe 2 zasu bi, hakanan laraba ta kwashi kayan sumayyan aka saka a mota sukaje gidan, me gadi ya bude musu, sumayya ta danna kan mota cikin gida.
Duk suka fito suka tsaya ganin gidan, katoton gida ne se Godiya, ga filin parking petal agun, ga shukoki, flowers sun zagaye gidan, this house is huge ya amina ta fada tareda jan hannun sumayya dan su shiga.
Gida ne kato, suka shiga wani dan lobby ne da kujeru da paintings a wall din.
Se sukai wani hallway, wanda ya rabu gida biyu, dayan hanyan guest place ne,da parlour dinsu da dakuna biyu da toilet.
Dayan hanyan kuma parlour ne katoto yasha kayan ado.
Wawu Amina ta fada, i am soo in love with your house, tini kowa yai hanyar sa don ya zaga.
Daga parlour akwai stairs, kasan stairs ta gefen sa akwai dan table wanda aka dora a small round rug se kuma chan gefe akwai sofa, se hanyan kitchen.
Before a shiga kitchen akwai dining area, se kitchen daga nan se court yard sekuma.kafita ta garden.
kana karawa gaba zaka hadu da garden din dayasha chairs, se kukan tsuntsaye kake ji.
Ya amina se cewa tai anya bazan cancelling flight dina ba? I want to stay here ta fada tareda muryan kuka,jin haka sumayya tadanyi murmushi sannan tace dakin taimaka wallahi.
Suka dawo ciki suka hau sama, akwai parlour daban wanda ya sha furniture's nagani na fada, akwai gym, two different rooms, se wani kofa guda biyu wanda akwai parlour,da dakuna guda biyu aciki dayan ma haka yake.
This should be the master and the mistress bedroom ya faty ta fada, sumayya ta daka mata duka sannan tace, mistress ko?
Ya faty kawai tai shrugging tareda zaro wayanta daga aljihu don kiran mummy through video call, itama taga gida.
Haka de suka sha hira da daukan pictures, aka chi abinchi, sannan sumayya taje ta ajje su a airport kamar tai kuka sannan tadawo, ita mamaki take taya za'ai ta zauna ita daya a wannan katoton gidan.
Tana zaune a dakinta kawai seta miqe ta sauko parlour din qasa tareda kwalawa laraba kira.
Ganin madam, zaki zauna a nan ne ko?
Sumayya ta tambaya?
Eh sena zauna anma se antambayi su madam dan se sun bari, bakomai zan tambaye su, but ke kinaso?
Ehh naga ai madam nada kirki, chan ance nice babba anma basa jin magana ta.
To shikenan karki damu, da yamma semuje ingaya musu se adauko kayanki.
Toh madam.
Suna gama magana ta kira mummy dan tagaya mata yacce sukayi.
Mummy tace bakomai haka ma yayi.
Haka ko akai, laraba tadawo gidan da zama.
Akwana atashi yau satin sumayya biyu a gidan, kullum sede ta tashi tai abinda zatai, dan ba ma abinda takeyi laraba ke komai har girki, tabawa me gadi.
Sede tafita aiki ta dawo tai daki,wani lokachin kuma seta zauna a qasa dan sudanyi hira da laraba, yawanchi ma laraban tana kallo take zuwa ta tarar da ita.
Haka rayuwarsu takasance a kwana kinnan.
Wata safiya karar motochi ya tashi sumayya, tini ta miqe tai hanyar window taga motochi manya manya danqara danqara masu numfashi se shigowa suke suna parking, ansaki duma.
Ita de se ikon Allah take gani.
Haka nan ta dauka mayafi ta dora akan doguwar rigar baccinta ta fita anan saman bene tana hango hanyar shigowa,se ganin mata tayi, kowacce ta kama layi sun bar tsakiya bakowa.
Mata ne kowacce da shigarta se Allah kawai, su wando ne da mini skirt, gashinan de, kowacce ta kama layi wasu sunyi left wasu sunyi right, se gashi yashigo da wani fashashen wandon sa blue jeans da white T-shirt maballenma duk abude ana hango ta ciki, ya shigo da wasu mata hanayensa biyu akan wiyansu.
Ya shigo ya tsaya tareda cire gilashin idonsa, ya daga kai ya kalleta sannan yace, i thought you will be cuter.
Sumayya bata ce komai ba, itade ta saki baki tana kallo, tana kallonsa ya bude wani akwati da matan suka shigo masa dashi ya dauko kudi, su kuma matan suka kara hawa layi ya dinga tabamusu bundle bundle na kudi.
Seya musu peck a cheeks ya miqa musu kudin sannan yace thank you sweet heart, ill call you.
Ahaka duk yagama dasu sannan ya hawo sama inda sumayya take ya kalleta sama da qasa sannan yace.
"villager" tareda dauko key daga aljihunsa ya bude dakinsa ya shige.
Sumayya taja tsaki, haushi ya isheta kawai tai ciki ta shirya taja mota ta fita aiki.
Ahanya ta dauko wayanta taiwa ya faty da ya amina text tareda cewa.
Guess who is back?
And my husband is a casanova or a womanizer, call him anything.
Ta tura musu.