Free chapter 路 Read without an account
Chapter 28
HAKURINMU 馃憣馃徎馃尲
Ugh, banganki agun aiki jiya da yau ba, Al-amin ya tambayi ya faty.
Ya faty da take shirin bacci se cewa tai, oo' so sorry na manta bangaya maka ba, i decided to take a leave na kwana biyu.
Al-amin ya danyi shiru sannan yace, na kwana nawa kika dauka?
Sati biyu ne ba yawa ya faty ta fada tareda tura gilashinta da ya dan sauko.
Mesa kika dau leave? Al-amin ya tambayeta.
No reason, kawai i need the rest,
Rest? Kwanan nan fa kika dauka leave kika tafi abuja, then kin kara daukan wani?
Hutun naki seya kare gabadaya ahaka?
It's nothing to worry about, ya faty ta fada.
Is it because mama tayi magana akan zuwa aikin da kikeyi? Al-amin ya tambaya innocently.
Ya faty ta dan yi shaking kadan tareda hadiye yawu, sannan tace ah ah.
It is! Al-amin ya ansamata.
Ya faty jin haka ya sa ta kwashi kayanta tareda cewa "you are impossible" ta shige bandaki.
Washe gari wurin karfe 12 na rana, ya faty ta dora girki tana zaune a dining, mama kuma tana kwance a sitting room akan sofa, se juyi take, wai ita tana ciwo, muhasin ta fito se miqa take tana hamma, da gajeran wandonta na bacci da wata singlet, ga gashinta babu direction din da beje ba.
Mama lafiyanki kiketa murqushe murqushe?
Lafiya muhasin, ciwo ne kawai.
Toh ni ina abinchi na?
Babu, mama ta amsa, dama kadan akai ba yawa, ingaya miki, yaro yakawo abinchi adafa anma wacchan mayyar se tsugulgulashi take, sekije ki gayamata me kikeson chi ta dafa miki, mama de haka ta ware tana zuba, ya faty ko mamaki ya kamata, kaman ba itace taketa kukan ciwo ba, dama de stage din da take bekamata ace tana jin pain haka ba.
Ya faty de tana ganin ikon Allah, muhasin ta zage se shagwaba takewa mama, yadda takeda wanan girman, ko kyau ma bemata ba, she feels disgusted.
Tana wannan tinanin ne se ganin mutum tai akanta.
Tsohuwa tace ki dafa min abinchi.
Ya faty ta gama kallonta sannan tace, an kusan a sauke na rana, ki dan jira inkuma sauri kike akwai sauran na safe a cooler, kije ki diba. Ya faty nagama fadan haka ta miqe tai kitchen domin ta duba girkin ta.
Shigarta kitchen kawai setaga mutum a tsaye.
Ina aikin? Ta tambayi Al-amin.
Gudowa nai, ward rounds ne, kuma nadanyi na gudo, banason wannan dogon rounds dinnan, seka sa house officers dinnan agaba, kadinga bayani ba kakkautawa.
Jin haka ya faty kawai ta sa dariya tareda cewa, kaima fa kayi.
Kuma yunwa nakeji, Al-amin ya fada kaman yai kuka.
Ya faty najin haka, hankalinta ya tashi tareda cewa kaima seda nagaya maka ka zauna kachi abinchi, kace zaka makara, ga irinta nan ai, ya faty ta fada duk idonta ya chichiko.
Nakusan gama abinchi. Na hada maka tea?
Kafin Al-amin ya amsa, muhasin tashigo, kana ganinta kasan da masifarta ta karaso anma ganin al-amin a tsaye yasa ta fasa.
Yayana!!
muhasin ta fada tareda wasu botsare botsare, taje gefensa ta tsaya.
Ina wuni yayana.
Al-amin ya hade rai kafin ya amsa.
Lafiya ya fada.
Kai yayana ko fara'a baka yi? kwana biyu bana ganinka, tin safe se dare, daren ma adakinka kake chin abinchi.
Haba yayana, mesa kakemin haka?
Muhasin tafada tareda lanqwasa murya tana wani shishige masa, itako ya faty yitai kaman ma bata wurin, tachigaba da aikinta.
Ina nan mana al-amin ya amsa ta, kece de bakyazama da shegen yawonki kamar kinchi kafar kare.
Kai yayana, muhasin tafada tareda kallon ya faty wacce ta nuna kaman ma batasan me ake ba, sannan tace, waennan strong words haka yayana.
Fatima, mama tace ki zuba mini abinchi sannan ki hada min tea, muhasin tafada tareda wani kikkifta idanuwa.
ya faty batace komai ba kawai ta juya ta dauko cup din tea.
Ke katuwa dake se an zuba miki abinchi? Al-amin ya fada, muhasin jin yadda ya fada dakuma ganin sa datai duk idanuwansa sunyi ja alamun yaji haushi yasa duk ta tsorata.
Dallachan malama ki samu plate ki zuba kayanki, duk sanda naji kinsa wani aiki agidan nan, kodako masu aiki ne, ni da ke ne ingaya miki, ahaka zakije gidan mijin naki kinayi?
Ko darajar mutane baki sani ba, kar na kara gani al-amin ya fada tareda jan dogon tsaki, nama denajin yunwar ya fada tareda ficewa daga kitchen din.
Muhasin kuwa jikin ta ba karamin rawa ya dauka ba, duk tayi gumi.
Ya faty kuwa da dauka mug din tea tabi bayan al-amin.
Ga tea, ya faty ta fada tareda ajjewa a side drawer, sannan ta nemi gu gefen gado kusa da al-amin ta zauna.
Ba wanda yai wa wani magana, se chan al-amin yace, yanxu ke dan Allah seki bari karamar yarinya tana gaya miki magana haka? Eh? Ai ba haka akeyi ba.
Ba haka bane, ya faty ta fada tareda yin kalar tausayi.
Meye ba bahaka ba? Al-amin ya tambaya.
Baka gane bane, mama ce fa ta aiko ta, ba dakanta tazo ba.
Al-amin kawai ya kalleta tareda cewa, kefa matsalarki kenan.
Toh ki shirya da yamma zanje asibiti, semuje ki duba sumayya, kafin ta amsa, sejitai amai ya taso mata, dagudu ta miqe tai hanyar bandaki, al-amin na biye da ita.
Anya bazamuje asibiti ba kuwa? Al-amin ya tambaya, you seem unusually weak kwana biyu.
Bakomai Dr. Worry, am fine, i just ate something that didn't settle well with me.
Allah sa, Al-amin ya fada.
Kasha tea kar yai sanyi, ya faty tafada domin tai changing subject of discussion.
Ina kika shiga? Mama ta sa ya faty agaba tana tambayarta.
Rana tayi ba'a bamu abinchi ba, wato dan ke kika dafa sekinga damazaki bamu ko?
Ah ah mama, na dan shiga alola ne, anma ai na jera a dining.
Toh al muslimatu, mu ai bamusan alola da sallah ba.
Dan kin jera a dining se me? Waye ze zuba mana?
Yarinyar nan wuyan ki yayi kauri, ni bazanchi wannan jagwalgwalallen dambun shinkafar naki ba, a dafa min wani abun.
Toh mama me kikeso?
Wani abun daban mama ta amsa.
Mama ki fada se a dafa miki.
Nace wani abun, mama ta zabura da fada, ki dafa ko ma meye.
Toh ya faty ta fada, zata wuce mama ta kara tsaida ita tareda cewa, daga yau karki kara bani magani, banason maganin ki.
Hala ma ba dede kike bani ba, muhasin zata dinga bani.
Toh mama, ya faty ta wuce kitchen.
Da lokachin bawa mama magani yai, ya faty da kyar ta samu muhasin ta biyota domin abawa mama magani, sannan tai mata bayani, tareda nuna mata wasu magunguna guda biyu tace under no circumstances, koma meye karta hada su, kar abadasu tare, se bayan awa biyu abada dayan.
Muhasin bata wani maida hankali ba, ita de tace to.
Rayuwa haka tachigaba da wakana, ahaka de akayi kwanaki, jikin ya faty se dada rikicewa yake anma haka take karfin hali tayi abubuwa, takuma qi taje asibiti, ya amina ma datazo ba yadda batai da ita taje asibiti ba, anma taqi, tace in takoma gida taje.
A yau alhamis, Al-amin ya dawo daga aiki da wuri.
Gidan shiru kamar bakowa, ya zauna yachi abinchinsa, har ze tafi daki se yace bara ya dubo mama, yana zuwa kuwa ya tarar da mama se amai take, jikinta duk yayi rudu rudu tsabar susa, duk rashes (kuraje) ya fito mata ajiki, se me aikinta dake gefenta se sannu take ce mata.
Bashiri al-amin yai sauri ya karasa gun datake,
Mama!
Mama!!
Lafiya, subahanallahi, ke kamata mu tafi asibiti.
Suna fitowa daga dakin, yaita kwalawa fatima kira anma bata sauko ba, yakira muhasin nan ma shiru, ahaka de suka tafi asibiti, se bayan awanni sannan yadawo gida ze daukarwa mama kaya.
Agigiche ya shigo kamar ana binsa, ya banko kofa ya shiga, da fada yashigo anma yadda yaga ya faty a bargo se shivering take yasa ya tsaya.
Fatima! Yakira sunanta,
Oo kadawo? Sorry kaman fever nakeji shisa nazo na kwanta.
Sannu al-amin ya fada, tareda neman gu ya zauna akan side drawer, kinsha magani?
Eh ta amsa, baranaje na duba mama ya faty ta fada tareda yunkurin miqewa.
Mama na asibiti Al-amin ya fada.
Subahanallahi!!
Me kace?
Asibitu fa?
Hope lafiya?
Is she stable?
She is, al-amin ya amsa
But i thought ta samu sauqi sosai, ko de check up ne?
Ba check up bane, al-amin ya amsa.
Mama tasamu drug poisoning,
Drug poisoning kuma? Ya fati ta tambaya.
Eh kinjini ai..
Duk ya bata tausayi.
So i was thinking ko tension ne yamiki yawa, shisa kika dinga hada mata medication din.
Nii? ah ah, ai kwana biyu mama tace bataso nadinga bata medication.
Muhasin tace takeso tadinga bata, shine na nunawa muhasin magungunan.
Yanxu muhasin ce take bata.
Al-amin abin ya mugun bata masa rai.
Muhasin fa kikace?
Ita meta sani?
Bashisa aka kawo ki ba.
Daba seki gayamin ba?
Al-amin ya saki dogon tsaki tareda hararar ta.
Muhasin ya maimaita sunan.
Muhasin din banza da hofi, kema kuma harda laifinki.
Yi hakuri dan Allah.
Baza a sake ba In Sha Allah.
Shirya mutafi, kiyi sauri inajiranki.
Ni banga tazama ba, yayinda ya faty ta miqe domin shirin zuwa asibiti.