Free chapter 路 Read without an account
Chapter 31
HAKURINMU 馃憣馃徎馃尲
Sannu! Kinma tashi ashe? Ya amina dake zaune gefenta ta fada.
Sumayya bata iya magana ba se gyada kai datayi alamar" eh! Yayinda take kokarin ta tashi zaune.
Kinsha bacci! Sakinah ta fada, yanxufa karfe sha daya.
Weakly dai sumayya ta kara gyada kanta.
Kinyi baqi. ya amina ta fada mata,
Da har zasu tafi su dawo anjima, anma tinda kin tashi, ai seku gaisa.
Mara lafiya an tashi? Dr mukky ya tambayi sumayya, sumayya ta danyi murmushi kadan tareda yin yar karamar gyaran murya tace eh natashi.
Toh masha Allah, haka akeso ai, dan kin tsorata jama'a, Allah kara sauqi ya kara kiyayewa.
Amin Amin.
Nagode fa da kokari, dan naji labarin duk abinda kukayi, Allah ya saka da alkhair
i.
Ahh, haba hajiya. Dr. Mukky ya fada tareda dakawa nabeel wanda yake atsaye yama kasa magana duka abaya.
Wanan zakiwa babban godiya bani ba.
Halifa da yake bayansu atsaye se cewa yai, kai Dr. Mukky zo muje mu duba Al-amin, tin daxu yace ze kawo takarda, dan musan anyi discharging dinta officially, anma ya makale, haka de halifa ya jasa suka fita.
Nabeel wanda yasha manyan kaya, brown shaddan nan tasa, kana gani kasan da kudi aka siyeta, ga hula ya dora kamar sabon ango yana tsaye ya kasa magana, se dan dariya da yai ta gefen bakinsa.
Ugh..... sakinah!! Natina zamu kira ya faty a waya, kuma ma inaso naga metron dinnan, tashi muje.
Da farko sakinah tai wa ya aminah kallon bangane ba? Chan kuma seta kalli inda nabeel yake atsaye tareda juyawa ta kalli sumayya wacce take kokarin neman abinyi anma ya gagara... Ohh tafada tareda cewa haka fa, ni nama manta.
Fitarsu daga dakin seda sukai shiru na wurin minti biyu babu wanda yace uffan, sannan sumayya ta bude baki tareda cewa, '' ina kwana?"
Lafiya kalau, sumi.
Jin yadda ya kira sunanta yasa tadan yatsine fuska.
Ya jikin naki yanxu?
Alhamdulillah, ai jiki ya warware sosai.
Toh masha Allah.
Ya halifa da ya amina sun gaya min, bajintar da kayi wurin taimakawa anemo ni.
Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya baku aljannah, dan Allah katayani yiwa brother dinka godiya.
Bakomai, nabeel ya fada, ai yiwa kaine.
Ughmmmm.....
Kafison tsayuwan ne? Ga wuri ka zauna mana. Sumayya ta fada, tareda nuna kujerar dake gefanta.
Ai bakice na zauna ba shisa,
To yanxu nace ka zauna.
Haka nabeel ya jawo kujerar ya zauna.
In tambayeka?
Please! Anything
Wai me ya faru da jazz ne?
And please tell me yadda aka sakasu frog jump and the rest again.
Nabeel ya kalleta, irin kallon mamakin nan, shi besan meke damun ahsraf ba, taya za ai ya bar someone like sumayya to go hakanan, and even hurt her in the process.
Gaskiya akwai question mark.
Nabeel yayi gyran murya tareda fara gaya mata, itakuma ta nutsu tana ji.
Su halifa se dawowa sukai, suka tarar da su se tintsiririn dariya suke, sumayya tana dago kanta tagansu, se cewa tai, baku fada min part din da jazz yaita kira sunan mamansa to come and save him ba?
Ooh sumayya, ya amina ta fada, you really can't get enough of this ko?
It's funny ne shisa.
Anyi discharging dinmu, se mu fara hada kaya, sakinah miqo small akwati dinchan please.
Inkun gama, ku min magana ina waje, ko ku kirani a waya.
Ya amina jin abinda halifa ya fada se cewa tai, Ah ba cewa kai zaka raka su Dr. Mukky gida ba su gaida mutanen gida?
Eh! Haka nace, in na sauke ku se mu wuce ai ko?
Da yamma fa sukace zasu tafi,
Why not ka bani motan ka, inyaso se ku tafi a nasu.
Na baki motata?
Ki kashe min ita kenan?
Sauqi wai nake nema maku ne, seku fi yin sauri.
Halifa ya dan harareta sannan yace ina zuwa.
Yan mintuna kadan se dawowa yai, tareda miqa mata mukullin motarsa,
Halifa: Zamuzo chin abinchi anjima, ki mana girki please?
Harda Al- amin.
Ya Amina: Ai kai dan gidan mummy ne, baka laifi.
Halifa: Kinji???
Ya Amina: Eh naji, tohm.
Allah kiyaye hanya.
Amin, halifa ya amsa.
Ba karamin murna sumayya tai ba data ganta agida, se hamdala take tanata zazzagawa, dukda seta huta anma hakanan tadingayi.
Dan Allah ji kaman bata taba zuwa gidan ba, ya amina ta fadawa ya faty dake gefanta azaune.
Ughm bana tashi, nifa inada masu zuwa chin abinchi ma.
Mummy tace tanada zobo a fridge, ya faty take fadawa ya amina.
Eh! Tagaya min.
Sakinah!!
Sakinah qawataaa, zaki tayani girki?
Ai dama nasan cutata kikeso kiyi, kinsan de yakamata yau naje gida.
Zamu saukeki anjima in zamu tafi.
Muje na tayaki.
Nima ku bani abu natayaku dashi, ya faty ta fada.
Da sauri ya amina ta juyo, tareda dora babban yatsanta da index finger dinta a habarta, niiii kaza, kina bedrest din, haka kurum ya Al-amin ya zo ya chi qaniyata, dama kuma hardashi za'azo.
Kekika jiyo de, ki bani abu na tayaku ina daga zaune shine wani abun.
Ga sumayya nan kuyi hira,
Bai bai, ya amina tafada tareda disappearing kitchen.
Cikin lokachin nan sukai mandi rice, salad da chicken danderu as main dish, se dan snacks da ke freezer din mummy, kawai daukowa sukai suka soya, se yanka musu fruits dasukai ga kuma zobo dasuka dauko agidan mummy se suka kara da juice na kwali.
Mummy bata wasa da irin wannan, she is always ever ready.
Se ya faty datace Al-amin yafison tuwo, aka tuqa mishi semo dan kadan, tareda yin small miya itama.
Basu zo da wuri ba, hakan ya basu damar karasa girkin nasu harda yin turaren wuta.
Suna gama jerawa a parlour din baqi ko sega su, suka zauna suka chi suka sha tareda yin hamdala.
Sannan suka wuce suka gaisa da mummy.
Mummy ta qarayiwa nabeel da Dr. Mukky godiya, harda Al-amin da halifa.
Suna zaune ana hira kafin su tafi, nabeel yadan yiwa halifa magana, yanaso yaga sumayya dan Allah, dan nabeel ya lura halifa na da saukin kai ba laifi inyaso.
Halifa ya kallesa sama da kasa tareda cewa, I'll do that, but muna da magana.
Sumayya ta dauka after dress tafita, rigar tadanso tayi yawo ajikinta daj ta rame.
Ta samesa jingine jikin BMW dinsa.
Isowarta se cewa tai, Dan Allah, dan annabi ka buden motar nan na zauna, saurin gajiya nake.
Al-amin ya bude mata wurin driver ta zauna tareda cewa, "it's expected ai"
Anjima zan tafi.
Nasani, Allah kiyaye hanya, thank you soo much for coming.
Amin,You are welcome.
Ughh inada tambaya, i just hope you won't take it personally.
No please ask away.
Soo ugh.. Yanxu zakiyi iddah ne right?
Sumayya ta kallesa ta danyi shiru sannan tace, actually mummy tace basenayi ba, after ta dan min wasu tambayoyi.
Ouuuuu!!! Nabeel ya fada.
Nabeel ya danyi shiru, sannan yace "i have a proposal"
Am not interested whatsoever it is nabeel, sumayya ta fada tareda juyawa ta kalla dayan gun da baya nan.
It's not what you think, sumayya, i just want to be your friend.
Sumayya ta danyi shiru, tareda juyowa ta kallesa sama da kasa.
NO"! Ta fada.
Ou please, is that how to treat someone who helped rescue you?
Jin haka kawai ta sa dariya, haka sukachi gaba da hirar su, in the end kuma ya karba number dinta anma bata sani ba dan wayarta ya karba, da tai complain akan wani application yace bara yaduba yagani.
Haka sukai sallama kowa ya kama gabansa, ita tai chikin gida shikuma yai hanyar guest parlour suyi sallama da mutan gida.
Washe gari da safe, su mummy da ya faty na zaune a sitting room suna hira, itakuma sumayya physiotherapist dinta tazo gida, ana rehabilitation a guest parlour, sega ya amina tayo sallama da akwatinta ahannu.
Lafiya? Mummy ta tambaya.
Wallahi lafiya kalau, ya amina tafada yayinda take zama kan kujera.
Ya halifa ne yai tafiya yau ba shiri suka kirasa gun aiki, kuma sati uku zeyi.
Allah dawo dashi lafiya, ya faty ta fada.
Amin ya amina ta amsa.
Due to the confusion from my last chapter here is a list.
Baban su sumayya ya rasu anma yana da wa guda daya, shine uncle sulaiman se kuma qanne maza da mata guda shida. Sabida haka hardashi su 8 ne.
Ga list din ya'yan su
1. Uncle sulaiman
Halifa
Muhammad
Sakinah
2. Baban su sumayya (sadiq)
3. Uncle farouq
Ashraf
Umaima
Maimuna
Salim
4. Umma sa'adatu
Abdullahi
Abdulrahman
5. Umma maryama
Zainab
Ayman
Hassana and hussaina (twins)
6. Uncle ma'aruf
Muhsin
Aisha
Asma'u
7.Uncle ibrahim
Maijidda
Mariya
8. Aunty mariya
Usman
Wasu suna garin kano wasu basa gari.
Se kuma mummy tanada kanwa guda daya wacce ake kira da aunty safiyya tanna zaune agarin bauchi da ya'yanta yan mata guda uku
Nabila
Ihsan
Ummu hani
Thank you