Free chapter · Read without an account

Page 11

by khadijah danasabe · ALƘALAMIN SO

ALƘALAMIN SO




DIJAHAM(OUM AMANI)



Page 11




🎤🎤🎤🎺 ALBISHIRINKU


Amarya da💃💃💃💃uwar gida da masu taron biki ko suna ko taron birthday, basai kin wahalar d kanku wajen siyan kayan fitar bikiba kizo UMMU SUDAIS tashare muku hawaye. Zatabaku hayar duk abunda kuke bukata akan farashi me sauki


i€¥^


Muna bada wedding gowns, alkebbar kai amarya, kayan Fulani nayara d manya farare dakuma blue black,, Muna d abun dauri head & shoulders, Muna d kayan kamshi kala kala sai Wanda kikeso,sai angwada akansan na kwarai💃💃



********


Slm jama a Muna d Zumar nono d kibbah da duwawo jadidan inkikasha Bata Mikiba kizo abaki kudinki,

Kiyi kyau kalar Yan gayu,kiba maikyau ba da kwayaba


Haba hajiyata kina zaune 

Oga najin haushinki jiki duk kasusuwa Dan Allah kidaure kisiya ki gwada kigani batada Wani side effects. Sai angwada akansan na kwarai


Muna da Sabulun tsarki (liquid soap) inganttacce yana mgnin kyakayin gaba zafin saduwa yana ciko d mace ga kuma y matseta yana Kara dadi d gardi,yana Kara ni’ima yana dauke warin gaba, dade sauran matsalolin mu na mata 


Munada turaren tsugono 

Dakuma na kaya

Muna bada renting duka a wajen Ummu SUDAIS


Zaku iya tuntubar mu ta wannan numbern

***





BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM





  na kasa dagowa na kalle sa hannaye na kawai nake matse wa da karfi don na hana rawar da jiki na yake min duk kuwa da cewa jikin nawa bai dai na rawar ba.

  Wannan ranar na dade ina dakon ta, rana ce da na dinga mafarkin zuwan ta amma yau tazo min a bazata ban taba kawo zuwan ta kusa kusa ba, hawayen fuska ta kuwa gudu suka kara yi sosai.


Kallona kawai yake yi yana sauke ajiyar zuciya, yau daya fada mata cewa yana kaunar ta ji yake kamar an sauke masa wani nauyi a kirjin sa.


A hankali ya bude bakin sa ya ce “Ina kaunar ki sosai Aisha wanda Ina kyautata zaton mutane da ywa sun san haka, ke na zauna Ina jira tun tuni a shekaru na ynxu ya kama ta ace na dade da aure har kuma na fara tara iyali amma na hakura na jira ki duk sbd kar a ce kin yi min yarinta da yawa, na samu Abba da maganar ya ce min na yi hakuri ki gama school ynxu kin gama, dazu naje wajen Dada na nemi auren ki a wajen sa ya ce na same ki in har kin amince shi a shirye yake a ko wanne lokaci”.


Shiru yayi yana karantar yanayin ta kafin ya cigaba da cewa “nima a shirye nake na dade da gama gini na lefe ma na dade da hada wa yana gurin Kareema kuma duk abinda kike so shi ta saka a lefen, ko anjima aka ce za’a daura mana aure na shirya, amincewar ki kawai nake so little”


Na kasa magana baki na ya rufe ruf abubuwa ne da yawa suka taru suka min yawa a zuciya ta, so nake na bude baki na fada masa wani abu amma na kasa gaba daya jikina rawa yke yi.


Murmushi yayi ya ce “kar ki damu yarinyar Uncle na baki kwana biyu kiyi shawara zan jira İn sha Allah, tun da na iya jiran shekaru sama da 20 kwana biyu ba wani abu bane İn sha Allah”


Sunkuyar da kai na nayi kawai, kafin kamar wacce aka mintsina na mike da sauri na fita daga dakin.


Murmushi kawai Aliyu yake bayan fitar ta, shi fa ji yake kamar ma ta gama zama tasa ne İn sha Allah, zai nuna mata soyayya mai suna soyayya kuwa.


  Fisgo hannu na aka yi da sauri na juya ganin Sultan ne ysa ni sauke ajiyar zuciya, dakin sa ya shiga ya rufe kofar sannan ya zaunar da ni a kan kujera.


Kallona kawai yake yi kamar mai nazari na, ni kuwa kuka na nake yi har lokacin wanda ban ma san dalilin sa ba. 


Cikin damuwa Sultan ya ce “fada Ya Aliyun yayi miki?”


Girgiza masa kai nayi Ina share hawaye na duk kuwa da sun ki tsayawa.


Ajiyar zuciya ya sauke ya ce “to me yayi miki?”


A hankali na ce “cewa yayi yana so na kuma aure na yake so yayi”


Zaro ido yayi yana tsugunna wa a gaba na, cikin farin ciki ya ce “bana son wasan banza don Allah”


Harara na watsa masa kafin nayi tsaki na ce “to abin da ya fada min kenan ni”


Shiru nayi kamar yadda shima yayi shirun yana kallona fuskar sa dauke da murmushi.


Dan lumshe ido na nayi kafin na bude a hankali na ce “Sultan ban San mai zan yi ba, ya ce min shi ya dade dana so ma ynxu a shirye yake muyi aure ashe har ya samu Dada ya masa magana dazu, wai ni kawai yake jira Ina fada masa abinda na yanke shikenan”


Zama Sultan yyi sosai yana kallo na ya ce “ynxu Aisha abin da nake so na fara tambayar ki kina son Ya Aliyu ko bakya son sa?”


Shiru nayi kawai ina Jin yadda zuciya ta take bugawa da karfi, mai zan ce ni Aisha maganar ma bana son sa ai bata taso ba.


Ganin yadda tayi shiru yasa Sultan murmushi ya ce “ba wai irin son da kike masa lokacin da kina yarinya ba, Ina magana akan so na aure kamar yadda ya fada miki shi a shirye yake kuma ya dade yana son ki wanda ko ni zan bada shaida akan son da yake miki wallahi”


Ajiyar zuciya na sauke na ce “Sultan Ina son sa mana, yau ko da a ce bana son Uncle ni din ba butulu bace da zan watsa masa kasa a ido, ni kai na nasan yana so na kuma in har na aure sa zan ji dadi matuka da gaske tun da ya gama shagwaba ni dama a gida”


Murmushi kawai Sultan yyi ya ce “inyeeee su Aisha ynxu a gaba na kike cewa zaki ji dadi in kika aure sa tun da ya gama shagwaba ki dama tun a gida?”


Tsaki nayi Ina hararar sa na ce “bana son iskanci ni ba wannan nake nufi ba”


Dariya Sultan yayi ya ce “meye ba shi kike nufi ba yi min bayani naji sosai”


Kau da kai na nayi Ina murmushi, kafin na juya Ina kallon sa a shagwabe na ce “amma ni kunyar sa nake ji Allah Sultan, ada nayi tunanin baxan ji kunya ba amma ynxu tun da ya furta da bakin sa cewa yana so na kawai naji Ina Jin kunyar sa, ban san ma ta inda zan fara fada masa cewa na amince ba”


Tagumi Sultan yayi yana murmushi, ganin yaki magana sai Murmushi da yake tayi ne yasa ni tsaki na mike kawai zan fita.


Da sauri ya ce “kiyi hakuri mana dawo don Allah, kawai mamaki ne ya kama ni wai yau keçe kike cewa kina jin kunyar Ya Aliyu, Uncle din ki ne fah”


Tsaki nayi na ce “kaji matsalar ka ai, ka tsaya ayi magana da Kai cikin nutsuwa baxa ta tsaya ba”


Dariya yayi sosai ya dawo dani muka zauna, tsara ni y shiga yi da yadda zan fada masa nan da kwana biyun kamar yadda ya bani lokaci.


Mun dade muna tattaunawa da aminin nawa Sultan sannan na tashi zan tafi, har na kai kofa ya kira suna na.


Juyo wa nayi na kalle sa, murmushi ya min ya ce “kar ki fada wa Maryam amma cewa Ya Aliyu yayi confessing feeling din sa kin ji”


Kallon sa nake kamar zan yi magana sai kuma na gyada masa kai kawai ina murmushi na fita.


Ina shiga part din mu direct dakin Mami na nufa, sai da na tsaya nayi knocking ta ce min na shigo sannan n shiga.


A zaune na same ta tana gyara wardrobe din ta, zama nayi Ina taya ta ban ce komai ba don wallahi kunya nake ji matuka da gaske.


Kallona tayi tana murmushi ta ce “wanne abu ne zai sa Shatu na Jin kunya ta haka?”


Hannu nasa na rufe fuska ta cike da jin kunyar da ni kai na ban san zan iya jin ta.


Dariya tayi tana ajiye hijab din data ninke ta ce “fada min Uncle din naki ya fada miki abinda ke zuciyar sa ne?”


Da sauri na cire hannu na daga fuska ta ina zare manyan ido na na ce “ya akai kika sani Mami?”


Murmushi tayi irin nasu na manya ta ce “ga alamu nan a fuskar ki, a yadda na san ki dai tun da Aliyu ya hure miki kunne kin ki kula saurayi, maganar sa ce kadai zata saki wannan blushing din”


Shagwabe fuska nayi na ce “ni kunya ma nake ji wallahi Mami”


Murmushi Mami tayi ta ce “ya kuka yi da shi?”. Duk abinda ya fada min sai da na fada mata, cikin murna ita ma ta ce min hakan yayi dai dai in yaso sai a hada da bikin Ya Haidar da Ya Hamza da za’a yi nan da wata biyu.


Cikin kwanaki biyun daya bani wasan buya muke yi, duk hanyar da nasan zan gan sa bana yadda ta hada mu da wuri nake zuwa aiki kuma in na dawo sai na fara leko wa in na tabbatar ban gan sa ba sai na wuce da gudu cikin part din mu.


Kunyar sa nake ji ba ta wasa ba bama yau da na tura masa message din na amince, shima kuma daya fahimci kunyar nake ji kyale ni yayi sai zafafan messages da yake turo min, ni wasu ma in na bude mamaki yake rufe ni sai kuma na sa hannu na rufe ido ina fadin Uncle ya lalace nima so yke ya lalata ni(na ce uhmmm🤌😂)



Cikin sati daya su Abba suka je wajen Dada aka biya kudin zance da sadaki, kuma aka sa ranar biki tare dasu Ya Haidar ya kasance bikin saura Wata daya da satı uku.


Irin murnar da Maryam tayi abin har sai da ya bani mamaki don sai da na ce mata wai Maryama kin gaji da gani na ne kike ta farin ciki zan yi aure na bar gidan, murmushi kawai ta min tana jan kumatu na ta ce ita farin ciki take taya Ya Aliyu finally zai yi aure.


Maganar ya Aliyu ni ynxu ba abinda zan ce sai da na ce Allah ya shirye shi, ban taba sanin cewa Uncle zai bude baki ya fada min wasu manyan maganganu ba sai ynxu, ni wani lokacin in ya Kira ni a waya yana min wasu maganganun ma shiru kawai nake nayi ta zare idanu, to magana ta domin Allah maganganun sun fi karfin shekaru na.


A gefe daya kuma Hajja da Mami sun dage sai bani magungunan sanyi suke, ban taba kin karba duk abinda Mami ta min, don Hajja da ita hadda kaji da tattabaru ta min farfesu ta kawo da kan ta kuma ta zauna tana kallona sai da na cinye su tas…



   ASAD



Kwanan sa uku da dawo wa daga Canada, kuma a yau ne yake so ya kai wa Alh Bala ziyara wanda ya kwashe wata guda a hannun yaran sa.


Tsaya yake a gaban mirror din sa yana fesa turare wato mutanen yau shigar Mr black ta daban ce, yau bayan p-cap din sa da boot ga kuma face mask baki yau hadda hand gloves bakake, idon sa da kunnen sa ne kawai farare.


Fito wa yayi daga dakin sa hannun sa rike da wasu kananun wuƙaƙe yana juya su cike da ƙwarewa tare da sakin wani sıririn fitoo(yau abin na masu yi ne ni dai nayi ta kai na🏃‍♀️)


Khalil da tun fitowar Ogan nasa yake kallon sa yana murmushi, don da alama yau Ogan yana cikin yanayi mai dadi tun da ya gansa da abubuwan wasan sa(Khalil wuƙaƙen ne abubuwan wasa😳 eh lallai dole nayi ta kai na🤾‍♀️) 

  Cikin girmama wa yayi gaba yana bude masa kofa, shi ne a gaba Ogan nasa a baya da yake tafiya cike da mazantaka, gaban wata shegiyar black Rolls Royce Phantom suka nufa Khalil ya bude masa back seat, bai shiga ba sai da ya soke abubuwan wasan sa a aljihun wandon daga wajen gwiwar sa sannan ya shiga motar.


Mai da kofar Khalil yai ya rufe shima ya shiga yaja ta suka bar gidan…………




DijahAM

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol