Free chapter · Read without an account
BABI NA SHIDA
*BISHIYAR TSIYA*
*DAGA ALKALAMIN YAN TAGWAYE*
*Umm Asghar*
*Sadiya Nasir Dan*
Arewa book
@ummasghar
Page 6
Tunda Sulaiman ya iso gida ya samu Batulu bata nan ya ƙudirta a ranshi sai ya koya mata hankali, zuciyarshi cunkushe da baƙin ciki ya shiga wanka, a cikin toilet tunanin irin yadda zai ci Uban Batulu yake yi, da irin tsattsauran matakin da zai ɗauka akanta, haka dai ya samu ya kammala ya fito. Yana tsaye jikin mirror yana tsane ruwan jikinshi yaji knocking ɗin gate, tsaki yaja ya cigaba da shirinshi sanin wacece mai bugawa, Jallabiya ya saka ya ɗauki wayarshi da keys ya fito.
Batulu waje ta nema ta zauna, gaba ɗaya kafafunta sun yi mata tsami saboda gajiyar data kwaso, tasan Sulaiman zai iya wulaƙanta ta yaƙi buɗe ƙofar akan lokaci duk don ya hukunta ta. Kama hannun Fahad tayi ta zaunar dashi a cinyarta, ta cigaba da sauke ajiyar zuciya saboda fargabar da take ciki.
Sulaiman kai tsaye jikin gate ya nufa yasa key ya bude, Batulu data tsunduma duniyar tunani ba taji fitowarshi ba sai saukar hannu da taji kan kuncinta. "Don Kutumar ubanki me kika dawo yi nan gidan?" Wani yawu Batulu ta haɗiye mai ɗaci, a take jikinta ya soma rawa. Rai a ɓace Sulaiman ya ƙara matsowa gaf da ita ya kama hannunta ya murɗe ta baya, wani irin ƙara Batulu ta saki saboda tsananin azabar daya ratsa har ƙwaƙwalwarta, "wato kin mayar dani ɗan iska wanda bai san abinda yake yi ba ko? Ina matsayin Mijinki ban isa ince kiyi ko kar kiyi ba? To rashin tarbiyarki ta isheni, ki koma gidan Ubanki ki zauna ki cigaba da rashin kunyar." Ya sake hannun tare da wurgata ta faɗi ƙasa ta buge kanta. Ihu Fahad ya saka ya nufi wajen mahaifiyarshi yana ƙwala kiran sunanta, da ƙarfi Sulaiman ya fisgeshi a jikinta. Duk da tsananin zafin da goshinta yake yi mata bai hanata aro jarumta ta miƙe ta nufo inda yake ta durƙusa tace, "Daddyn Fahad don Allah kayi hakuri, wallahi matsala aka samu ta abjn hawa, ka tambayi..."
"Yi mini shiru yar bura uba munafuka, da anyi magana kin iya rantsuwa ki nemi kare kanki, to wallahi bari kiji, in dai ba tsohonki ya gina gidan nan ba billahillazi gidan ku zaki wuce, ina dalili, ni duk Hajiya ta cuceni da tuni na yasar da kwallon mangwaro na huta da ƙuda, haba da Allah." Yaja hannun Fahad da sauri suka wuce ciki. Sosai kalmar gidan Ubanki ya tsaya mata a rai, amma a halin yanzu duk abinda Sulaiman zai faɗa mata ko zai yi mata dole tayi haƙuri ta shanye ta samu ya barta ta zauna, a halin da Baba yake ciki nutsuwa da kwanciyar hankali yake buƙata ba wai tashin hankali ba. Hawayen fuskarta ta share ta shige gidan da sauri, ganin Sulaiman na ƙoƙarin shiga motor yasa ta nufeshi da sauri ta kama kafarshi, "Habibi don darajar Allah ka barni na zauna a ɗakina, In Sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba." Fusge kafarshi yayi ya turata gefe, "Kalma daya tak idan kika sake faɗa a bakin aurenki." Tamkar dirar mikiya haka Batulu taji maganar Sulaiman, Fahad na kuka haka ya turashi cikin motor, "Ki wuce ki fita mun a gida zan rufe." Kuka Batulu ta fashe dashi ta fita a gidan zuciyarta nayi mata ciwo, tana kallon fitowar Sulaiman ya rufe gidan shi suka wuce, durƙushewa tayi a ƙofar gidan ta saki wani marayan kuka abun tausayi, ita a yanzu ina ta nufa. Bata son zuwa gida ta tayar musu da hankali bayan ga halin da Baba yake ciki, to amma kuma idan bata je gidan ba ina zata daya wuce gidan nasu. To ko dai gidan Hajiya zata je ta sanar mata da abinda ya faru ko ta samu ta saka baki Suleiman yayi haƙuri ya barta ta cigaba da zama a ɗakinta sanin baya taɓa tsallake maganar Hajiya.
Da yin wannan tunanin taji wani ƙwarin gwiwa ya shigeta ta tashi daga wurin cike da karsashi ta nufi gidan Hajiya duk da cewa akwai ƴar tazarar tafiya a tsakaninsu duk da suke a unguwa ɗaya. Tana tafe tana share hawayen daya ƙi tsayawa daga idonta, tana jin baƙin ciki da takaicin wulaƙancin da Suleiman yake yi mata, sam babu tausayi bare tausasawa a zamansu kamar ba waɗanda suka yi auren soyayya ba, ita ta rasa daga ina wannan rashin jituwar ta shigo cikin zamansu.
*****
Duk da yadda ranshi yake a ɓace yana ganin ɗan uwanshi sai yaji dukkanin wata damuwar shi ta yaye. Akwai shaƙuwa da kyakkyawar mu'amala a tsakaninsu tun tasowarsu sam ba'a jin tsakaninsu tamkar ba sako da sako ba. Zama yayi akan kujerar two sitter a kusa da yayanshi. Hannu ya miƙa mishi suka gaisa yace "Yaya me kake ci ne a Abujan ka ajiye kumatu haka?" Yace yana kai hannu zai taɓa kumatun Yayan nashi yayi maza ya kauce yana cewa "meye haka Suleiman? Kai me yasa baka girma ne." Dariya Hajiya tayi tana girgiza kai tace "ato kada dai ku manta ga ɗanku nan a zaune yana kallon ku." Zuciyarta fal farin cikin kasancewa tare da ƴaƴan nata, har kullum tana alfahari da haɗin kansu da yadda suke ƙaunar junansu.
Hannu Abdulhamid ya miƙawa Fahad yace "Mallam Fahad zo ka faɗa mini waya taɓa ka tunda kuka shigo kake kumburi," tasowa Fahad yayi yana share hawaye sai dai tsoron Babanshi ya hanashi buɗe baki yayi kukan sosai don tun a hanya yaja mishi kunne akan kukan da yake yi mishi. Zama yayi a jikin Abdulhamid sai dai yin duniya yaƙi buɗe baki yayi magana sai sharar hawaye da yake yi shi kuwa Suleiman ya ɗauke kai tamkar bai san meke faruwa ba.
Har ta ƙarasa gidan Hajiya tana saƙe-saƙe hakan yasa sam bata ji wahalar tafiyar da tayi ba. Sallama tayi daga bakin ƙofa, Hajiya ce ta amsa haɗe da cewa "wa nake ji kamar Batulu, dama tare kuke ne?" Ta tambayi Suleiman tana kallon shi ganin yadda ya haɗe fuska tamkar bai taɓa dariya ba. Shigowa Batulu tayi jiki a sanyaye ta zauna akan carpet tana gaishe da Hajiya. Fuska a sake Hajiyar ta amsa mata sannan ta juya ta gaishe da Yaya Abdulhamid, shima cikin sakin fuskar ya amsa mata. A kaikaice ta kalli ɓarin da Suleiman yake babu shiri ta mayar da kanta ƙasa ta ajiye don wani irin mummunan kallo da yake jifanta dashi, cikin ranshi dai yana ƙara tabbatar da rainin da Batulu tayi mishi don gashi nan yace ta tafi gidansu ta biyo shi nasu gidan don ta nuna mishi bai isa ya sakata ko ya hanata ba. Shiru ne ya ratsa palon ƴar hirar dasu keyi ma suka daina, gaba ɗaya Batulu sai taji ta takura a tsarge take tana ganin kamar tuni Suleiman ya sanar dasu abinda ke wakana. Ɗan muskutawa tayi ta gyara zamanta ta buɗe baki kenan zata yi magana taji muryar Suleiman cikin tsawa yace "uban me kika zo yi anan gidan? Ba gidan ubanki nace ki tafi ba shine don raini kika kwaso jiki kika taho wurin Hajiya, uwar ubanki zata yi miki da kika zo nan ɗin?" Baki buɗe Hajiya da Abdulhamid suke kallon shi jin yadda yake danna mata ashar. Murya a sanyaye tace "Hajiya wurinki nazo don Allah kisa baki Daddyn Fahad yayi haƙuri ya ƙyaleni a ɗakina, wallahi bada gangan na saɓawa umurninshi ba abun hawa na rasa."
Tasowa yayi kamar zai kai mata duka yace "abun hawan ubanki? Munafuka algunguma wacce sai anyi magana ki wani dinga sunkuyar da kai kamar wata mutuniyar kirki." Abdulhamid ne ya janyo shi ya zaunar dashi akan kujerar daya tashi yace "haba Suleiman meye haka? Matarka ce fa kake yiwa irin wannan zagin tsamar naman, kowanne irin laifi tayi maka bai dace kayi mata irin wannan zagin ba kuma don abun kunya a gaban ɗanku, baka gudun gurɓata mishi tarbiyya." Komawa yayi ya zauna yana huci, ita dai Batulu ta sunkuyar da kai tana kuka sai dai komai zai ce idan har zai yi haƙuri ya barta ta koma ɗakinta zata shanye don kuwa zaman gidanta shine marufar asirinta. Sai sannan Hajiya tace "a gabana Suleiman kake irin wannan ɗiban albarkar, ashe ba zata ci arziƙin zuwa gabana da tayi ba komai tayi maka kayi haƙuri."
Ƙwafa yayi yana hararar Batulu ƙasa-ƙasa yace "wallahi Hajiya haƙuri na ya ƙare, Batulu sam bata da mutunci. Kin san dai ke kike tausata kina bani haƙuri amma ko kaɗan bata gani in har bata yi abinda zai ɓata mini rai ba hankalinta baya kwanciya shi yasa naso ki ƙyaleni na rabu da ita ta tafi can tayi rashin mutuncinta a gaba ba a gidana ba." Girgiza kai kawai Hajiya tayi ta saki wani murmushi mai ciwo tace "har wani laifi Batulun take yi maka da baza ka iya haƙuri ba Suleiman, anya Suleiman ba zaka daina wannan baƙar zuciyar ba sai ta kai ka ta baro ko."
Kama hannunshi Abdulhamid yayi suka fita waje ganin yadda yake huci alamun ranshi a ɓace yake matuƙa. Zama suka yi akan fararen kujeru da aka ajiye a harabar gidan don zama a sha iska, bai ce mishi komai ba sai kallon shi da yake tayi yana kallon yadda yake kokowa da numfashin shi har sai da zuciyarshi ta huce sannan yace mishi "ka dinga yin haƙuri Suleiman kana sassautawa zuciyarka kada kaje ka janyowa kanka wani ciwon, sannan kuma bai dace kana yiwa matarka irin wannan zagin ba ba mutuncinka bane gaskiya ban kuma ji daɗi ba. Kowanne irin laifi tayi maka tunda har tazo gaban mahaifiyarmu ya kamata ka sassauta tunda ai sanin Hajiyar ta isa da kai yasa tazo gabanta ."
"Yaya wallahi baka san irin haƙurin da nake yi da yarinyar nan ba shi yasa kake cewa haka, sam ta raina ni bata ganin mutuncina to ni kuwa ana miye zan dinga raga mata bayan nima ba daɗinta nake ji ba, wallahi in banda Hajiya tana hana ni da tuni na yarda ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda."
"Kada kace haka Suleiman, matarka ƴar gidan mutunci ce idan ka rabu da ita baka san wacce iri zaka je ka kwaso ba."
"Wallahi Yaya ko wacce iri ce nasan ta fiye mini Batulu sau dubu." Shi dai Abdulhamid sai lallaɓa shi yake yi yana bashi haƙuri.
A cikin gida kuwa Hajiya ta tasa Batulu a gaba tana yi mata faɗa akan yawan saɓa mishi da take yi don ba yau ne karo na farko daya kawo mata ƙararta ba ita take tausar shi don a zauna lafiya, nasiha sosai tayi mata sai dai Batulu bata iya buɗe baki ta faɗawa Hajiyar irin abinda yake yi mata ba ta dai bar wa cikinta tana fatan wata rana komai ya daidaita ya zama tarihi....
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce
*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jidda Aliyu
*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch
*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.
*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso
*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000
*BANK ACCOUNT*
***
Opay digital services
Shaidar biya ***
*KATIN MTN*
***
Shaidar biya ta lambar.
_*ƳAN TAGWAYE BIYAR*_
#SADIYANASIRDAN
#UMMASGHAR
#ƳANTAGWAYEBIYAR