Free chapter · Read without an account
GOMA
by ZAINAB M BAWA · WATA ALAƘA
*WATA ALAƘA.....!*
*PAID BOOK*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
NA
STYLISH BTCH
Da
ZAYNAB BAWA
*SHAFI NA GOMA*
"Subhanallahi meyasa haka? Dan Allah karki zubar da hawayenki kawai ki fito ki faɗamin abunda yake ranki ni ne mijinki kuma abokin kukanki da dariyarki." Jan hanci tayi ta goge hawayen fuskarta da har ya fara yin jaa a cikin sanyin murya tace.
"Yanzu ka rigada ka yanke shawaarar badashi ni me zance?"
"Kice komai kece wacce kike da ikon yanke wannan hukuncin idan bakyaso bazan rabaki da ɗanki ba." Samun kanta tayi da faɗin.
"Kayi hakuri ka barmin shi banason rabuwa da Hydar idan takama nabar mata wannan jaririyar ne zan barmata amma banda Hydar." Tafaɗi hakan domin bazata iya imaging rayuwa babu Hydar ba.
"Toh shikenan angama babu wanda zai amsa miki shi idan wannan takai yaye karki manta da cika alƙawari." Gyaɗa kanta tayi tana jin zuciyarta tana sanyi. Mai martaba ya daɗe a sashinta domin saida tafara jin bacci kafin yamata sallama yatafi.
_______
Tunda mai martaba ya sanarwa su Kilishi yanda sukayi da Ummi suka ɗauki wata sabuwar tsanar duniya suka sake ɗaura mata, hatta da kulawar da Mai martaba ya nemi alfarma a wajan Kilishi bata samu ba daga ita sai Hydar da kuma hadimanta dake kula da ita suke harkokin su, sai kuma mai martaba da shima kullum sai ya shiga sashinta ya zauna sun ɗan taɓa hira domin ya ɗauke mata damuwoyin da yasan dole tana cikinsu. Bata da kowa a garin bata da kawa bare aminiya komai shine nata, duk da kulawar da Ummi ke samu wajan mai martaba bai hanata shiga damuwa ba domin a wannan lokaci tanada buƙatar a nuna mata soyayya da kulawa, sai dai kuma bayan mijinta babu wani majiɓanci kusa da zai lura da ita. Ga PPD ( Postpartum depression) da kusan kowacce mace take fama dashi bayan childbirth, wanda kulawa da nuna soyayya da tarairaya a wannan lokacin shine kaɗai ke ɗauke wannan damuwarsu, ita kuma Ummi bata samu hakan ba.
Saida Ummi ta haihu da 5days kafin wasu daga cikin ƴan uwanta suka samu damar zuwa dubata saboda yanayi na bambamcin ƙasa da abubuwa da suka zama wajaibi kafin barin ƙasa zuwa wata wanda koda ace sunso zuwa a dai-dai lokacin data haihu bazasu samu damar yin hakan ba. Ai kuwa zuwansu ya ɗaukewa Ummi 50% na damuwar da take ciki wasu abubuwan ma gabaki ɗaya ta manta su saboda yanzu tana tare da ƴan uwanta masu sanyata farin ciki. Saida ƴan uwanta sukayi kwana ɗaya da zuwa kafin mai martaba ya samu zuwa gaidasu. A ranar da sukazo yaso zuwa dubasu amma hakan bai samu ba saboda shi bawai mutum bane kamar kowanne da yake da lokaci a hannu, sannan tunda Ummi ta haihu ranar ne kawai bai samu yaje ya dubata ba. Bayan sun gama gaisawa da ƴan uwanta suka basu waje somin su ɗan zanta. Dubanta Mai martaba yakeyi yaji daɗin ganinta cikin walwala kwana ɗaya kaɗai da zuwan ƴan uwanta amma har wani kumari ta ɗanyi. Sam baya son ganinta cikin damuwa sau daya idan ya ganta batada walwala shima tasa walwalar takan gushe yakanji kamar duk ta dalilinsa take cikin halin da take saboda shine wanda ya ɗaukota cikin dangi da gatanta ya kawota nan yanda sam ba'a marafa da ita. Mahaifiyarshi kawai da ƴar ƙaramar ƙanwarsu ya lura suke sonta, sukuma ba mazauna bane, domin mahaifiyarshi batada cikakkiyar lafiya, autarsu kuma ita ke kula da ita tunda duk ciki itace kawai maras aure. Sauran sai dai suje su dubata su dawo. Annuri ne ya karaɗe gabaki ɗaya illahirin fuskarsa sakamokon yanayin daya ganta a ciki, cikin tausasshiyar muryar daya saba mata magana yace.
"Ya ya shirye-shiryen? Fatan dai komai da kike buƙata yana isowa akan lokaci?" Ta gyaɗa masa yayi murmushi sannan yace.
"Abbana bai dawo daga makaranta ba koh?" kai ta gyaɗa masa sannan tace.
"Eh bai dawo ba amma sun kusa."
"Uhmmm nace mai zai hana a turawa mahaifan Hidaya katin gayyata? Nasan Abbana idan yaganta a gidan nan zaiyi farin ciki sosai." Murmushi Ummi tayi, itama tayi tunanin hakan amma bata furta ba dai. Murmushi tayi haƙwaranta har suna fitowa tace.
"Hakan za'ayi yanzu barina kira sai akai mata saƙon school kafin a tashi daga school ɗin."
"A'a ba haka za'ayi ba zasufi ganin kamar an mutunta su idan har aka kai musu har gida, idan da hali driver su amso adreshin Hidaya a school ɗin kafin su dawa bayan ya dawo kuma sai a shirya su sukai musu invitation har gida."
"In sha Allah zan sanar musu yanzu." Ta faɗa cike da bin umarni. Murmushi mai martaba yayi akoda yaushe baya gajiyawa da gano kyawawan halaye da kuma nagarta daga gareta, bayan ya tabbatar babu wani abunda suke buƙata kafin nan yayi mata sallama ya wuce izuwa fada.
Mai martaba yana fita Ummi ta sanarwa Sarkin mota saƙon mai martaba, babu ɓata lokaci suka shiga school ɗin bayan sun gama sanar da saƙon mai martaba na neman adreshin Sadiya Muhammad Arabi. Sai da schoool authority suka kira Abban Hidaya suka nemi izininsa kafin suka bada duk kuwa da mai martaba yana da ikon da zai iya cewa abashi kai tsayen a bashi. Amma makarantar suna bin komai a tsari da kuma doka dan karsu ɓatawa wani rai.
______
Ƙarfe biyu 2:30pm bayan Hydar ya gama hutawa Ummi ta sanya aka shiryashi domin zuwa gidansu Hidaya. Bata turashi hannu haka ba saida ta haɗa gift wa Hidaya da Mamanta haɗeda invitation na sunan. Tafiyar 20minutes ce ta kaisu ƙofar gidansu Hidaya daga masarauta, mai gadin bai buɗe musu ƙofa kai tsaye ba domin yaga motoci har guda biyu kuma dukansu mazane baya iya hango Hydar da Tani da suke zaune a bayan ɗaya motar dske tinted ne, sarkin mota ne yafita ya sanar masa akan Magajin gari Hydar Aliyi Turad yazo daga Fada domin kawowa Hidaya aika, ciki yashiga ya snarwa Mamin Hidaya abinda baƙin sukace, kai tsaye tabada dama su shigo, Tani ce ta ɗauki kayayyakin suna tafe har izuwa cikin palourn. Mami tana ganin Hydar ta faɗaɗa Fara'arta taba faɗin.
"Ah lallai ga Hydar" Hydar bai fahinci yanda suka zoba saida yaga Mamin Hidaya sannan ya saki fuska ya ƙaraso ciki da sauri ya a faɗin.
"Mami ina Hidaya?"
"Hidaya tana ɗaki Hydar" Tafaɗa tana nuna masa ƙofar ɗakinta, wucewa yayi da gudu yashiga iabishi da murmushi ita kuma ta ƙaraso ciki tani da ajiye kayan a ƙasa sannan ta zube tana kwasan gaisuwa. Cike da fara'a Mami ta amsa mata babu yanda batayi akan tatashi ta zauna akan kujera ba taƙi. Hydar baifi 2minutes da shiga ba yafito jiki a sanyaye, Mami ta dubeshi taba faɗin.
"Ina Hidayar?"
"Tana bacci" yabawa Ummi amsa a takaice,
"Tasheta kace tazo kaji" Kak Hydar ya girgiza. Mami tayi murmushi tace "Barina tasheta" kamo hannunta yayi da sauri tana kalloeshi ya girgiza mata kai, Mami tayi murmudhi ta shafo kansa tana mamakin yaro mai ƙarancin shekaru da nutsuwa irin haka, a zahiri haka sai ace ya girmi Hidaya a yanayin jiki da kuma nutsuwarsa duk da bawia yafita tsayi bane amma Hydar da Hidaya sa'anni ne rana guda aka haifesu domin sunfara school da 10days Hidaya tacika 3yrs Mami tayi gift na ƴan ƙananun bags ta bada a class ɗin su Hidaya na friends ɗinta da kuma teacher sai gashi a ranar itama Hidaya ta dawo da gift na birthdayn Hydar, shida Hidaya duka birth date ɗinsu ɗaya.
Komawa Mami tayi ta zauna sannan ta jawo Hydar ta zaunar akan cinyarta tana masa tambayoyi dai-dai akan Umminsa da Abie yace duka suna nan lafiya. Basu daɗe a gidanba Tani tabada saƙon Ummin Hydar suka suka tashi zasu tafi domin Ummi face karsu daɗe, dake card ɗin daban suka bayar Mami ta buɗe ta gani taji daɗi sosai cikr da fara'a tace.
"Shikenan zamuzo in sha Allah"
"Allah yayarda" Tani ta amsa suka fice.
_________
Washe gari Hidaya da ɗaukin ganin Hydar ta isa makaranta bayan an shaida mata yaje gida tana bacci. Kamar kullum ana tashinsu aka wuce da Hydar gida itama Hidaya suka wuce gida itada Maminta, ƙarfe uku da rabi 3:30pm na yamma bayan sunyi sallar la'asar suka shirya tafiya walima Itada Hidaya zallah domin Abba yana asibiti jiya bayan tabashi card ɗin yayi mata umarnin zuwa amma shi bazai samu kaisu ba. Ganin anyi parking motoci gabaki ɗaya a titin gaban masarautar yasa Mami gudub saɓa ƙa'idojin masarautar tunda ba taɓa zuwa tayi ba tayi parking motarta a safe waje suka fito ta ɗauki Hidaya da gift data kawowa Ummin Hydar sika shiga ciki. Tafiya ce mai nisa takaisu izuwa sashin Ummi har saida Mami tayi danasanin ajiye motarta a waje domin taga ƴan tsirarrun mutane na shigowa da mota. yanda sukaga mutane suna nufa suma nan sukayi har yakaisu sashin gabaki ɗaya an ƙayata gaban wajan da decation sai kujeru da aka zuba sunyi kyau sosai. Wucewa Mami tayi ciki domin ba'a fara zama a kujerun ba. Iso akayi mata har izuwa palourn da Ƴan uwan Ummi suke, cikin sa'a tana shiga ta haɗu da Tani shiyasa bata barta a palourn da mutane dayawa suke ciki ba, baya tabata wajan zama da ruwa sannan ta shiga domin sanarwa Ummi, a lokacin da tani da sanarwa Ummi ana ƙoƙarin shiryata hakan yasa bata fito da wuri ba, Hydar ne yafara zuwa domin Ummi ta aiki tani shima ta sanar masa, da murna Hydar yashigo palourn Hidaya ma tana ganinsa ta sauƙo lokaci guda suka cika palourn da ihun murna, Mami murmushi kawai takeyi tana kallonsu da sauran dangin mahaifiyarsa da suke kallonsu cike da soyayya, komai Hydar zaiyi abin sone a wajansu, sunkai 10minute a zaune kafin Ummi tafito cikin shiga ta Lafaya wacce tayi masifar mata kyau, babu makeup a fuskarta bacin eyeliner da lipgloss data sanya sai zinaru da suka cika kowanne gabbai na jikinta da suke da mazauni ba ƙaramin kyau tayi ba kazancewar fatarta a murje take da hutu kuma fata irinta larabawa, Mami tayi mamakin yanda Ummi ta amsheta cike da fara'a da farko tayi tunanin She'll not be welcome kasancewar lamarine daya haɗa da masu ji da kansu masu sarauta. Ummi saida tabi gabaki ɗaya ƴan uwanta tana nuna musu Mami a matsayin ƙawarta, Mami taji daɗin hakan sosai domin sun sake bata muhimmanci, tare suka fita.
wajan walima seats daya kasance na ƴan uwanta Ummi tasa aka bawa Mami ta zauna, kafin su fito saida Ummi tasaka akai Hydar da Hidaya wajan Mai martaba domin shima yana yawan zancen Hidayar yana son ganinta, Hidaya tashiga ran mai martaba sosai domin ya lura da irin son da take yiwa Hydar shikuma duk wani mahaluki da zaiso Hydar toh baida wani abun so kamarsa. Zuba musu ido yayi kawai suna wasanninsu suna kasashi nishaɗi. Ana cewa yara idan sun haɗu waje guda da abokanansu suna rashin ji ta ɓarna amma banda Hidaya da Hydar domin asa suke abunsu cike taka tsan-tsan, ƴan guje-gujensu kawai suke a palourn da yake ƙarawa mai martaba nishaɗi kasancewar yaga Hydar ɗinsa da bai cika hayaniya ba ya sake sosai yana wasa.
Sai 6:20 aka tashi wajan Walima Mami Allah -Allah takeyi a gama su kama hanya kafin gari yayi duhu domin Abba ya hanata tuƙin dare, ana tashi Suka shiga ciki tabawa Ummi saƙon da tazo mata dashi tayu murna sosai sannan Ummi ta aika aka ɗauko su Hidaya bayan Mai martaba yayiwa Hidaya kyautar kuɗi, Firr Mami taƙi amsa saida Ummi tace mata ba'a maida kyautar mai martaba sannan ta amsa tasakawa Hidaya a jaka haɗe dayin godiya, Ummi ma kayan walima sosai ta haɗa musu bayan ta amshi numbern Mami don ta fahimci Mami macece mai sauƙin kai kuma da alamu zatayi daɗin zama duka-duka kuma bazasu wuce sa'anni ba. Ummi ce takira sarkin mota akan yazo ya ajiye su gida Mami tace mata da mota tazo tabarta a waje, har wajan motarta dake waje sarkin mota yakaisu sannan suka zuba mata kayan walimar a motarta suka kamo hanyar gida.
___
Kusan gabaki ɗaya ƴan uwan mai martaba cire hannunsu sukayi daga kan duk wani abunda ya shafi Ummi ko wajan walima ma saboda yazama kamar dole ne kuma abun cecekuce ne idan basujeba yasa sukaje, sunce tunda Ummi bata son ɗanta ya raɓesu ta iya runtse ido face bazata bawa Fulanin sarki ba toh suma babu ruwansu da duk wani abinda ya shafeta. Ummi taga sauyin fuska sosai a wajansu amma abun bai dameta sosai ba saboda ƴan uwanta suna kusa da ita sannan bugu da ƙari suma ƴan uwanta ba ƙusar baya bane, koda wasa bazasu fara kawo mata wargi wajan ƴan uwanta ba. Mami da Hidaya sunzo suna, tunda suka gabatar da kansu Hydar da Ummi suka kasa sukuni saboda su, komai Ummi zata gani naci kona sha sai tace a kawo mu, sunga tarba ta mutunci da karamci. 10days ƴan uwa Ummi sukayi wasu daga ciki suka fara tafiya yayin da wasu sai da sukayi 3weeks a lokacin da zasu tafi Ummi taso binsu amma Mai martaba ya hana duk da cewar shima yanaso ta samu nutsuwa wajan ƴan uwanta. Idan tatafi dole Hydar zai koma wajan Fulani kuma koda ta dawo bazai iya amsarsa daga wajanta ba. Jin haka yasa itama Ummi duk yanda takeson tafiyar ta cirewa ranta sai aka bar ƙanwarta budurwa wacce take bi mata akan ta zauna a wajanta na wani lokaci.
___
Wasa gaske wata irin shaƙuwace mai ƙarfi tashiga tsakanin Ummi da Mami Sun dawo ƙawayen gaske close to zama aminan juna. Su da kansu sau dayawa sukanyi mamakin yanda ƙawancen su yayi ƙarfi a gajartaccen lokaci.
#ZEEYY BAWA
#STYLISHBCH
#ƳAN TAGWAYE
#WATA ALAƘA.