Free chapter · Read without an account

Chapter 2

by Maryam Bello Lumu · JININ SARAUTA

***

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

(J.W.A) 

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️






👑 *JININ SARAUTA* 👑





 *STORY & WRITING* ✍️




 *BY* 




 *MARYAM BELLO LUMU* ❤️





 *M.Lumu* ✍️





 *ƳAR LELEN JAJIRTATTU* ✨💃🏻🥀






 *PAID BOOK* 📓




 *Wannan littafin na kuɗine kan Naira 200 only 👌idan* *kintashi biya zaki iya biya ta wannan account* *ɗin* 👇

 *Acc no.7040902537* 

 *Acc name. Maryam* *Bello* 

 *Bank name. Opay* 


 *Domin samun ƙarin bayani za'a iya tuntuɓata ta wannan number* 👇

 ***** 

 *Ko wannan* 

 ***** 






 *Talla* 🗣️🗣️🗣️🗣️



Buyyyyyyy Dataaaaa💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼⬇️⬇️⬇️

Maryam Abubakar

⬇️⬇️⬇️

   BUY DATA

 SERVICES

*_MTN_*🔸

🔸1gb  -  *_300_*

🔸2gb  -  *_600_*

🔸3gb  -  *_900_*

🔸5gb  -  *_1,400_*

🔸10gb -  *_2,800_*


*461*4# to check balance


*_Airtel♦️_*

♦️1gb  -   350

♦️2gb  -  *_700_*

♦️5gb  -  *_1,600_*

♦️10gb -  _3,100_


×140# to check balance


Just a click away

***

Phone:***

Account:0881327701

Account name:Maryam Abubakar Mafara



Thank you as you patronize and refer! 

💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼


 *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* 🙏


 *GARGAƊI* 👉🦻


 *Wannan littafin ƙagaggen labarine banyarda wani ko wata ya* *sauyamin shi ba ta kowace sigar.🙏😒* 




 *Page 3✨* 




_______Dadyy"


"Na'am Mamana miyafaru ne?


"Uhum"


"Miyene gayaman"


"Dady yaushe zamuje Kano?


"Mamana keda ke Boko inake ina zuwa Kano to mizakiyi acan?


"Uhum Uhumm nidai Dady Allah inason zuwa"


"To shikenan idan kunsanu hutu zamuje kinji"


Cikin shagwaɓa ta ɗaga mishi kai alamar "Eh" daganan sukayi lunch ɗin su suka cigaba da hira cikin nishaɗi da ƙaunar junansu.






Suna shiga cikin fada part ɗin shi ya nufa yayi wanka ya dawo part ɗin Ammi.


"Son ya hanyar Allah yasa ansamu abunda akaje nema?


"Wallahi Abba lafiya ƙalau komai ya tafi yadda mukeso Alhamdulillah kawai zamu ce"


"To ma sha Allah haka mukeson ji"


Sarki na ida faɗin haka yayi hanyar fada yabarsu nan zaune.


Ammi ce ta ƙara matsowa kusada Yarima ta ce,


"To injin dai ansamomuna suruka ko?


"Haba Ammi wace suruka ana zaune ƙalau kuma?


"To Jawad idan banyi maganar kayi aure ba mizanyi?


"Haba Balkisu ki bar yaronnan ya sarara mana"


Wadda tayi maganar ta ƙara sa shigowa ɗakin tashi tsaye Ammi tayi cikin ladabi ta gaidata sannan ta koma inda take ta zauna,


"Yawwa Hajja gayamata nifa har yanzu fa yaro ne"


ya ida maganar yana murmushi hararar shi Ammi tayi tabace komai ba Hajja ta ce,


"Kaji Muhammadu rabu da ita Ni da kaina zan samoma mata wadda ta dace da kai"


"Yawwa Hajja ta shiyasa nake ƙara sonki, ai dama ke baki tsufa ba ai dake zan aura in huta da faɗan Ammi"


ranƙwashi Hajja ta sake mishi saida ya saki ƴar ƙara ta ce,


"Ni zakace na tsufa to ka kalleni da kyau nafi uwarka zama yarinya"


gaba ɗayansu suka ɗauki dariya harda Ammi da tun lokacin da Hajja ta shigo kanta yake ƙasa


"To afuwan ƴar budurwa ta"


daganan Jawad yabar su a gurin.





"Ai wallahi ya kawo kanshi badai ya sake ya dawo ba"


"Haj Sadiya mikike nufi da yakawo kanshi?


"Nifa dama wallahi ba son yaronnan nakeyi ba"


"Haba Fatima ɗanki ne fa kike cewa bakya sonshi"


"Eh Sa'adatu ta faɗa ko zakiyi wani abune?


"A'a ba abunda zanyi"


daganan ta tashi tabar musu parlourn suna binta da kallon ƙiyayya.


"Shegiya marar kinshin kanta inbanda rashin kishi kina ƙanwar Sarki amma komai za'ayi bazaki sani ba a cikin masarauta"


" Hmmmm Aunty rabu da ita mukam sai mun ɗaukarma kanmu fansa"


"Ai Fatima ki rabu da ita zata gane kurenta dan nagane batasonmu kwata kwata tafison waccan munafukar matar Sarki gamu ƴan uwanta amma batason abunda mukeso"


daga nan suka cigaba da zaginta ita da Balkisu.



"Bro ina tsarabata?

wata kyakkyawar yarinya tayi maganar cike da shagwaɓa kallo ɗaya zaka mata kagane jininshi ce,


"Beautyna aikinsan koda baki tambaya ba zanbaki ko?


"Eh hakane to amiƙomin nan"


ta ida maganar cike da jin daɗi, miƙewa yayi ya ɗakko wani ɗan kit ya miƙamata,da sauri ta tashi ta rungume shi tana mishi godiya tabar ɗakin da gudu, girgiza kai yayi yana kallon ƴar ƙaunarshi da yake matuƙar so da ƙauna.





"Iham bazaki gane bane banason soyayya hasali na natsani masu yin ta"


"Hhhhhh lallai Beenah Ni wallahi mamaki kike bani taya zakice bakyason soyayya duk irin wannan surar da Allah yayi miki ai kema kinsan doli saikin tara masu sonki"


"Uhumm Iham mubar wannan maganar dan ɓatamin rai kikeyi wallahi"


"To ranki ya daɗe angama"





(Beenah yarinya ce wadda bazata wuce shekara 17 zuwa 18 ba amma Allah yayi mata sura mai kyau dan idan ba angayaman shekarunta ba bazaka yarda ba kyakkyawa ce ajin farko kana ganinta kaga asalin Bafulatana ko shuwa Araf, doguwa ce fara ce sol kamar dangin larabawa, ita ba mai ƙiba ba ita ba siririya ba, Ni banmasan ta yadda zan misalta muku kyau irin na Beenah ba)



Sosai take jin daɗin hirar da Iham ke mata sai dariya takeyi kamar wata zautatta nan take asalin kyanta yasake bayyana kamar bazatayi magana cikin dariya ta ce,


"Wallahi Iham Tsohuwa na bani mamaki haka kawai zata kawo miki miji keba dillaliya ba"


"Hhhhhh ai nikam mamaki tabani wai aure zanyi tagaji da ganina cikin gida"


ta ida maganar suna ƙara sheƙewa da wata dariya.


"Ni tashi ma muje in gaidata na kwana biyu banje ba"


tana ida faɗin haka suka tashi gaba ɗayansu suka nufi hanyar gidansu Iham.





"Ranka ya daɗe Ammi ta ce kana nemana?


"Eh Jawad dama so nakeyi nagayama akwai wani Company tun kana Spain akayishi to shine yanzu lokacin da za'a buɗe shi yayi to dama kai nakeso kaje matsayin MD Company"


"To Abba ba matsala yaushe ne lokacin da za'a buɗe shi?


"Next week"


"To Abba Allah ya kaimu"


da "Amin" suka amsa suka cigaba da shirye shiryen su.




"Ya Jawad wai miyasa bakason muhaɗu gaba ɗaya? tun lokacin da kadawo nakeson ganinka amma nakasa"


"Amal ayukka ne sukamin yawa shiyasa"


ya ida maganar cike da rashin kulawa,


"To Ya yaushe zamu fita?


"Kije keda Mukhtar mana ba yadawo ba?


"To kainakeso"


wani kallo ya wurga mata cike da rashin fahimta daganan yayi gaba baisake cewa komai ba. 


"Wallahi Ya Jawad inasonka kuma bana tunanin zan iya rayuwa ba da kaiba kagama zagaye zagayen ka kawai kadawo dan nikaɗai ce matar da zaka aura"


Amal tayi maganar cike da yarda da kanta daganan tayi ɓangaren mahaifiyarta.






👑JININ SARAUTA �




M.Lumu✍️





Page 4

�




"Yarima Jawad ba kamar sauran mutane bane jininshi cike yake da sarauta da mulki da kuma izza.."


"Dakata Wambai ba wannan natambayeka ba"


"Allah ya huci zuciyar ki"


wani kallo Haj Fatima ta wurgama Wambai tare da cewa,


"So nakeyi duk abunda Jawad zaiyi nasani nasan duk wani motsi nashi kanajina?


"Eh Gimbiya In Sha Allah zaki samu abunda kikeso"


"Ta shi kabani guri"


da sauri Wambai yatashi yabar gurin.



"Kaga malam inzaka dawo ka dawo"


cikin wayar naji ana cewa,


"Calm down my friend I will come back next week"


"Kaga Habib nifa banason wannan iskancin bayan nagayama Next week zamuje buɗe company nan amma zaka wani ce next week zaka dawo"


"To shikenan Yarima zan dawo nan da kwana biyu"


baice komai ba ya yanke wayar dan yaga yanason ɓata mishi rai.



Next week!



Wasu mahaukatan motoci na hango suna tafiya cikin isa da ƙasaita motocin sunfi ashirin, wani Company sukayi parking nan take naga wasu maza su huɗu sunsha manyan kaya sunyi kyau sosai.


"Ma sha Allah tare da yardar Allah, Allah ya dawo muna da Yarima lafiya kuma ina farin cikin sanar daku shine MD na wannan Company"


wani Dattijo mutum ke sanarwa yana nuna ɓangaren da Jawad yake tsaye shida Habib sai taɓi ake musu.



"Kai amma wallahi Yarima nan kyakkyawan gaske ne"


"Aini Lubna nama kasa cewa komai wannan kyannashi ai yayi yawa ke jifa yadda wannan sajen nashi yayi mishi kyau sosai"


a haka matan gurin sukayita yaba yarima har saida aka gama walima kowa ya watse.


"Mutumina ka lura da yadda matan gurinnan ke kallonka"


"Mtswwwww wallahi saida naji nafara tsawwala da gurin shiyasa ma namatsu a gama taron"


"Hhhhhhhhh haba kaifa namiji ne"


"To se akayi yaya inni namiji ne"


"To zafafu garka ɗauki maganar da zafi, yawwa dama so nakeyi ka rakani wani guri"


wani kallo Jawad yayima Habib ya ce,


"Shikenan yanzu kadawo yawon kuma yadawo ina zan rakaka kuma yanzu?


"Hhhhhhhh haba Super market zamuje"


"To bazanje ba"


"Haba kaifa matsala gareka wallahi bafa jimawa zanyi ba"


shiru Jawad yayi bai sake cewa komai ba daganan Habib yayi murmushi dan yasan halin kayanshi.


Umurni Jawad yabawa fadawanshi da kuma sauran motocin akan suyi gaba sukuma zasu biyosu daga baya, daganan Jawad yaja mota sukayi hanyar Supaer market.





"Haba Beenah yanzu fitar da zamuyi zakice sai kinje da Bonbo to yayi miki mi?


"Uhum nidai Allah sai naje da ita"


"To Allah yabada sa'a muje garmuyi dare kinji"


Daganan su Ilham suka fito parlour Momy suka tarar zaune daganan suka mata sai sun dawo tayi musu Allah ya tsare hanya daganan suka fita.




"Haba Yarima kayi tuƙi a hankali mana"


"Baza'ayi a hankalin ba"


Kamin Habib yasake cewa wani abu jikake gaffffff.........




 *To be continued* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻





 *M.Lumu* ✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.