Free chapter · Read without an account

SHA BIYU

by ZAINAB M BAWA · WATA ALAƘA

*WATA ALAKA*

*YAN TAGWAYE BIYAR*


ZAYNAB BAWA

&

STYLISH BCH



Assalamu alaikum


Ina masu son ayi masu Logo ko flyer, E-book cover's ko stickers, invitation card ko kuma invitation vedio domin ƙawata kasuwancinku da janyo hankulan customers ɗinku? 

To ku matso kusa ga S fari graphic design sun shirya tsaf domin yimaku abinda zai zo daidai da ra'ayinku bisa farashi mai sauƙi.



Sai ku tuntuɓemu ta 

CALL OR WATSAPP

***/***.


Mungode.




*SHAFI NA GOMA SHA BIYU*


 Tsawon lokaci mai martaba ya ɗauka a sashen Fulani domin Fulani narkewa tayi kamar maijin ciwo da gaske, babu yanda Mai Martaba baiyi da ita akan ta tashi akaita asibiti ba amma firr taƙi tace zataji sauƙi. Dr Jameela yasa aka kira akan tazo ta duba Fulani saida Dr Jameela ta iso kafin mai martaba yabar sashen Fulani ransa cike da damuwar halin da take ciki. Mai martaba yana komawa ɗaki yayi contacting likitan da Fulani take gani a India ta email ɗinsa domin bazai iya jurar ganin halin da Fulani zata shiga idan akace wani abun yafaru da wannan yaron na cikinta ba. Bayan 2hours likitan ya dawo masa da saƙo a lokacin har Dr Jamila ta kammala dubata ta sanya an sanarwa da mai martaba akan bataga wata matsala ba tafi tunanin juyi yaron yayi. Likitan ya buƙaci akan a maida masa da Fulani ta haihu a can dama a tsarin dubata daya saka a ciki dole ya kasance a can zata haihu domin matsalarta bayan haihuwa ce ba kafinta ba domin duk abubuwan da yayi mata a baya rigakafine akan matsalar da take fuskanta. Da kiran waya ɗaya mai martaba ya sanya aka shiryawa Fulani tafiya india batare da yayi shawara da ita ba. Ya Kilishi kawai yayi contacting ta tabbatar masa zata samu zuwa domin wannan karon ma da ita takeso a tafi tanaso Fulani ta haihu a gabanta. Mai Martaba dama yasan ba lallai tanada uzurin da zai hanata zuwa ba kawai dai ya nemi izinin ne saboda hakan ya kamata. Mijin Kilishi babban ɗan siyasa ne kuma matan shi 4 itace ta biyu sannan shi kansa bai cika zama a ƙasar ba. Da farko lokacin daya auri Yaa kilishi ko'ina da ita yake zuwa da yayi amarya sai ya ajiye Kilishi a gefe ya ɗauki amaryarsa ko'ina zaije da ita. Itama wancan Amaryar haka yayi mata a lokacin da yayi wata sabuwar amaryar saboda shi irin mazan nan ne masu ajiye matansu a gefe da zarar sunyi amarya shi yasa tsoffin matan suke da dama da saken zuwa duk inda sukaga dama a lokacin da sukeso. Sai bayan mai martaba ya gama shirya komai na tafiyar sannan ya sanarwa Kilishi. Wani irin kallo take masa wanda ya bayyana rashin jin daɗin abunda kunnuwanta suka jiye nata daga wajan mai martaba, muryarta har sarƙewa takeyi kamar wacce take shirin fashewa da kuka tace.


"Takawa dan Allah ka duba lamarin nan sam banson tafiyar nan yanzu ne fa cikina yashiga wata na takwas, haka zanje can nayita zama har kimanin nan da watanni biyu? Idan Allah yasa na haihu da zarar nashiga wata tara shine bazan fi 1month da satikai acan ba, bana son zama a can ɗin nan ni kaɗai Allah ya gani." Ta faɗa cike da ƙunar rai da dana sanin ƙaryar ciwon datayi akan kawai ance mata Ummi na sashin Mai martaba wanda hakan ya jawo yanzu zatayi nesa da mai martaba gabaki ɗaya tabarwa Ummi shi na tsawon watanni. Murmushi mai martaba yayi cike da kulawa ya kamo hannunta yana shafawa cikin sigar lallashi yace.


"Toh ai dama a yanayin tsarin aikin ya kamata ace kin haihu kusa da likitan da yake duba ki, tunda kinga matsala sai bayan haihuwa take rising wasu lokutan kuma a irin wannan lokacin ne ake samun matsala. Zanfi samun ƙwarin guiwa idan akace kina tare da mai kula da lafiyarki Fulani." Hawayen da Fulani take haɗiyewa ne suka zubo ta dubi mai martaba tace.


"Takawa bayan alluran daya saka akemin duk bayan 2weeks da maganganu da yake rubutawa mai zaisa yace lallai sai a wannan lokacin zan koma? Dan Allah yabari nashiga koda 9month ne yanda muna zuwa nasan ba daɗewa zan yi ba in sha Allah zan haihu ni sam banason rabuwa dakai har na tsawon wannan lokacin." Murmushi mai martaba ya sake yi sannan yace.


"Ni kaina zanfi samun nutsuwa da kwanciyar hankali idan kika haihu kusa dani, amma hakan ma in sha Allah bazai gagara ba da zarar lokacin yazo ni zanzo can ɗin." Fulani sam ranta baiyi na'am da wannan batun ba amma babu yanda ta iya ta rigada ta jawowa kanta tafiyar da babu shiri. Cikin week ɗin su fulani suka tashi izuwa india, apartment guda dake wani building kusa da hospital mai martaba ya kama musu sabods sauƙin gijila don ba'ason yawan jijjiga ga ita Fulani.


__

 

 Ummi gabaki ɗaya ta cire damuwar Fulani da ƴan uwan mai martaba a ranta tayi focusing rayuwarta akan yaranta guda uku Hydar da ƙannenshi mata guda biyu, Maryam da Bilkisu sai ƙawarta Mami (Maman Hidaya) wacce a halin yanzu ta dawo Aminiyarta wacce kaff ƙasar nan ta Nigeria idan aka cire mijinta da ƴaƴanta toh batada kamar ta. Kamar yanda alaƙar dake tsakanin Hydar da Hidaya a kullum ƙara girma take haka alaƙar dake tsakanin Ummi da Mami take girma, lokaci-lokaci sukan ziyarci junansu idan Mami bata jeba Ummi zataje idan Ummi bata zoba Mami zatazo, mai martaba shi da kansa wasu lokutan yakan cewa Ummi ta shirya tafafi wajan Mami idan yaganta cikin damuwa domin ya lura tana samun nutsuwa sosai idan tana wajan Mami hankalinta ya kwanta da ita sosai ya lura ita take yiwa kallon ƴan uwanta da basa kusa da ita.


_____



 Duk wata kulawar data dace Fulani tana samu daga wajan Likita da Yaa kilishi sai dai gabaki ɗaya hankalinta yana wajan mijinta data bari a hannun Ummi gani takeyi kafin ta dawo Ummi zata gama tsaface shi gabaki ɗaya ya zama nata ita ɗaya. A lokacin data shiga month na haihuwarta ta matsawa mai martaba akan ya cika alƙawarin daya ɗauka na zuwa gareta da zarar ta shiga watan haihuwarta. Mai martaba shima kansa hankalinsa na wajanta saboda yanayin da take ciki don haka yabari saida Edd ɗinta ya rage saura 1week kamar yanda scanning ya nuna sannan ya nufi India bayan yabawa Ummi damar fita a duk lokacin da takeso don yasan duk inda zataje bazai wuce wajan Mami ba kuma hakan zai ɗauke mata kaɗaici sosai da yasan dole ne ta shige shi idan baya kusa da ita kasancewar har a wannan lokacin da Ummi take da kimanin Shekara 9 a ƙasar bata saba da mutane da yawa ba, tafi yarda dashi akan kowa sannan tafi sabo dashi akan kowa. A koda yaushe idan baya a tare da ita toh a takure take, shi yasa yake jin daɗin mu'amalalarta da Mami, yana ganinta cikin farin ciki a duk sa'ilin da taje ko Mami tazo mata for the very few times bayan zuwanta ƙasar.


_____



 Tunda mai martaba ya isa India baya samun lokacin da zasuyi magana da Ummi sosai saboda kusan koda yaushe yana tare dasu Fulanin sarki da Kilishi, yakan kira kawai yaji lafiyarsu sai suyi sallama. Ita kanta Ummi duk yanda takeson suyi hira mai tsayi dashi daga tajiyo muryar Yaa kilishi ko Fulani shikenan saita miƙawa Hydar wayar suyi hira da mahaifinsa. Sau dayawa da Hydar sukan ɓata lokaci suna magana shima ba koda yaushe ba, Mai martaba yayi kewar yaron sosai saboda Hydar yasa yanzu idan ba Hajji ko Umra ba sam bai son yin tafiya mai tsayi, dan baya son abunda zai nisantashi da yaronsa na tsawon lokaci yanzu haka makarantar Hydar kawai ta hanashi tahowa dashi, gashi akoda yaushe yanzu ƙaunar yaron ke ƙaruwa a cikin ransa, yana girma yana ƙara nutsuwa sannan yana sake shiga ran mahaifinsa.


 Kwanan mai martaba 3 acan aka yiwa Fulani C.S aka cire mata yaronta kamar yanda likitan ya buƙata domin bincikensa ya nuna masa a wajan haihu ma akan iya samun matsala gwara ayi c.s. Mai martaba, kilishi, Fulani, gabaki ɗayansu sun kasance cikin zullumi da taraddadi sannan kuma ga farin ciki da murna marar mislatuwa. Hajiya da zamanta kusan gabaki ɗaya yanzu ya koma egypt labarin haihuwar yana zuwar mata ita da autar su mai martaba wanda yanzu gabaki ɗaya suka koma can suka nufo India tare. A gabaki ɗaya wannan daren Fulani da Mai martaba babu wanda ya rintsa a cikinsu Fulani gani takeyi kamar idan ta kwanta bacci shima yaron zai koma, sai da safe likita yayi mata allurar bacci kafin ta samu ta rintsa.


Airport mai Martaba ya aika driver aka ɗakko Hajiyarsa kai tsaye asibitin aka wuce da ita. Hajiya dattijuwa ce da zata iya kaiwa 60yrs sai dai girmanta bai ɓoye kyawunta ba, Kyakkyawa ce sosai Fara sol gabaki ɗaya yaranta kusan tafisu kyau ta wani ɓarin Hydar yana ɗan kama da ita dan akwai ɗibar kamanninsa sosai a jikinta. Fuskarta cike take da kamala kallo ɗaya za'ayi mata a fahimci mecece ita mai kirki da sanin ya kamata tana cike da mutuntaka. Mai martaba yana ganinta ya miƙe tsaye, ƙarasawa tayi gaban gadon da yaron take kwance dake har lokacin likita bai bada umarnin afara ɗaukansa ba ya sanya tayi masa addu'a daga inda take sannan ta nufi kujera ta zauna idonta yana kan Fulani da har a lokacin bacci takeyi. Cike da girmamawa mai martaba ya gaisheta yana mai jin daɗin ganinta duk kuwa da bai daɗe da zuwa wajanta ba. Amsawa tayi tana masa sam barka da fatan Allah ya raya yaron. A ciki ya amsa sannan ya ɗaura da faɗin.


"Hajiya da gida aka wuce dake kika huta kafin kika taho nan ɗin saboda gajiya." Murmushi tayi sannan tace.


"Yanzu ai sai naje koh? Tunda nazo na gansu hankalina ya kwanta." Hatta da yanayin da take magana cike yake da kamala sannan yanayin yanda take furta zantukan cike da hikima. Bayan Yaaa Kilishi ta iso sannan su kuma suka nufi gida. 


Bayan 2days Mai martaba ya haɗa Ummi da Fulani a waya tayi mata barka. A ɗaddare Ummi ta gaisheta babu yabo ba fallasa Fulani ta amsa. Gabaki ɗayansu hankalinsu bai kwanta ba har sai da yaron yakai 5days lokacin suka ɗan samu nutsuwa amma bawai hankalinsu ya kwanta ɗari bisa ɗari bane. 


______



 Gabaki ɗayansu ne zaune a Palour jaririn na hannun Aisha autarsu mai martaba Hajiya ta dubeshi cike da kulawa tace.


"Abba har yau baka yiwa yaron huɗu ba ba? Yakamata ace anyi ai koh? Kaga dai cikin Iko da hikima irinta ubangiji yau yaron nan kwanasa biyar a duniya kuma muna fata Allah ya rayashi yayi rayuwa mai tsawo cike da albarka." Gabaki ɗayan palourn suka amsa da amin sannan Mai martaba yace.


"Hajiya tun yana ƙwana uku a duniya nayi masa khuduba da suna Umar Faruq." Kabbara Hajiya tayi tace.


"Madallah ka kyauta sosai Abba nima hakan naso ince amma nabar maka zaɓi a hannunka sai gashi kayi halin girma." Da mamaki haɗe da sanyin jiki Fulani take kallon Mai martaba me yake nufi da sakawa yaronsa sunan Mahaifinta Umar Faruq instead of Aliyu Hydar da yazama shine Line na sarautar garin? Kallon Yaa Kilishi tayi idonta ya cicciko da hawaye Yaa kilishi ta girgiza mata kai zaman Hajiya a wajan yasa basu iya cewa komai ba. Fulani ta miƙe ta shiga ɗaki Yaa kilishi ta bita a baya. Duk yanda taso riƙe kukan saida ya ƙwace mata Yaa kilishi ta zauna kusa da ita tafara bubbuga bayanta.


"Haba mana Fulani meyasa haka kin manta bakida lafiya?"


"Yaa kilishi dole ne nayi kuka dama na faɗa miki Mai martaba bazai taɓa ɗaukan matsayin daya kamata ya bawa yaron nan ba kinaji sunan Baba ya saka masa tunda masarautar nan ta kafu ko a Tarihi kin taɓa jin sarauta tabar hannun Aliyu?" Cikin ƙarfafa mata guiwa Yaa kilishi tace.


"Za'a fara a wannan karon Fulani ga dukkan alamu anzo lokacin da sarauta zata dawo hannun Umar Faruq, karkiji komai don haka ki share hawayenki kar Hajiya ta fahimci wani abin kinji bazataji daɗi ba." Kai Fulani ta gyaɗa duk da maganganun Kilishi sun ɗan saka mata ƙwarin guiwa amma takasa tashi ta koma palourn.


____



  Saida su Fulani sukayi sati biyu a can kafin suka dawo bayan likita yagama bata duk wani taimakon da zai iya bata. Mai martaba tunda ta cika sati guda da haihuwa ya dawo gida Nijeriya. Sai bayan sun dawo ne sannan akayi bikin suna. Biki na gaske wanda gabaki ɗaya ahlin mai martaba suna cikin kulawa kowannesu yana cikin farin cikin wannan lamari. Ummi tana shiga cikinsu ne kawai a lokacin da Hajiya take wajan domin Hajiya sam bata nuna wani bambamci tsakaninta da Fulani, sannan Aisha ma tana ƙaunarta sosai. 1month kaɗai Hajiya sukayi suka koma daga nan rayuwa ta komawa Ummi yanda take a baya koma ace fiye da yanda take abaya, domin tsanar da sukayi mata a yanzu har tafi ta baya muni. Bambanci da suke nunawa tsakanin Hydar da Faruq abun ba'a cewa komai, ko zuwa Hydar yayi wajan mai martaba a lokacin za'a kai Faruq wani lokacin Faruq ana kaishi yake fara kuka sai amaidashi, Mai martaba yana ƙaunar yaransa gabaki ɗaya amma irin soyayyar da yake yiwa Hydar tafita daban yanda yake jinshi a cikin ransa gabaki ɗaya cikin yaransa babu wanda ya shiga ransa kamar haka, duk wani wanda yake mu'amala da mai martaba yasan yanda yake jin Hydar a ransa. Fulani tana iya ƙoƙarinta wajan ganin Faruq ya shiga ran mai martaba fiye da Hydar tare da bin shawarar ƴan uwan mai martabar.





#Wata Alaka 

#Zee Bawa 

#Stylish bch 

#YAN TAGWAYE.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol