Free chapter · Read without an account
SHA HUƊU
by ZAINAB M BAWA · WATA ALAƘA
*WATA ALAƘA.....!*
*PAID BOOK*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
NA
STYLISH BTCH
Da
ZAYNAB BAWA
*SHAFI NA GOMA SHA HUƊU*
*BAYAN SHEKARA UKU*
Cike da zumuɗi Hidaya take shirin zuwa school cikin sabbin Uniform ɗinta, gabaki ɗaya yanayi na ƴan matanci ya nuna a jikinta ta ƙara cika da tsayi sannan ta ƙara kyau sosai masassaƙin budurci gabaki ɗaya ya sassƙeta. Mami ce ta buɗo ɗakin ta shigo itama kuma fuskarta babu yabo ba fallasa. Zama tayi bakin gadon Hidaya kamar wacce take son magana da ita, daurewa tayi tace.
"Hidaya duk zumuɗin shiga SS3 ɗinne haka?" Juyowa Hidaya tayi daga yanayin muryar mahaifiyarta ta fahimci akwai damuwa a tattare da ita domin Hidaya she's very observant duk wani sauyi daga murya ko fuska komai ƙarancinsa tana iya ɗaukarsa. Zama tayi itama gefen gadon cike da kulawa tana tambayar.
"Lafiya Mami? Wani abunne yafaru?" Mami taso shanye damuwarta amma takasa batada abokiyar shawara a yanzu daya wuce Hidaya tunda ba mahaifiya take da ita a raye ba.
"Hidaya Abbanki aure zaiyi, Abbanki ƙaramar yarinya zai auro min da bazata wuce shekara ashirin ba kusan ƴar cikina Hidaya." Wani irin dumm Hidaya taji da sauri ta miƙe zata fita Maminta ta kamo hannunta.
"Ina zakije Hidaya?" Hidaya da idanuwanta suka cicciko tace.
"Abba zan samu Mami, na kwana biyu ina ganinki cikin damuwa ashe dalilin kenan?" Sassuta murya Mami tayi sannan tace.
"Hidaya zoki zauna." Babu musu ta dawo ta zauna.
"Kice masa me Hidaya idan kin sameshi? Abbanki ba haramun zai aikata ba kuma ba fasawa zaiyi ba, kawai dai naso ace da yarinyar da zai aura tafi haka shekeru, amma wannan fa ya haifeta idan ta girmeki da kaɗanne Hidaya. Amma babu komai karki kuskura kice masa komai kinji ko?" Hidaya da take jin ranta yana ƙuna ta runtse ido. Yanzu tun auren yarinta tsakanin Abbanta da Maminta abinda zai saka mata kenan? Wani irin ƙuna takeji a ranta. Wayar dake gefenta ce tafara ruri tana kaiwa fuskarta kai taga Hydar ne. Daurewa Mami tayi tace.
"Jeki Hidaya ga Hydar yazo karki ɓata muku lokaci sannan karki saka damuwa a ranki kinji ko?" Kai Hidaya ta gyaɗa tafice tabar Maminta a nan tana jin ranta yana mata wani irin suya.
Kamannin Hydar na yarinta gabaki ɗaya basu sauya ba yana nan da kamanninsa wanda ana ganinsa anga Cikekken labarabe wanda baza'a taɓa zaton Half-cast bane ba. Hydar Aliyu Turad kyakkyawane sosai mai cikar zati da halitta fuskarsa na ɗauke da dara-daran idanuwa da kuma godon hanci, fatarsa ta ƙara haske sosai sai sheƙi takeyi kamar baya shiga rana babu wani kamanni na mahaifiyarsa balarabiyar asali daya baro. Uniform dake jikinsa yayi matuƙar amsar sa, sumar kansa tayi luff ta kwanta sai sheƙi takeyi sanyin AC dake motar ya haɗu da sanyayyan ƙamshin turarensa ya sanyaya kaff illahirin motar hannunsa a jikin steering motar yayinda idanuwansa suke kan gate na gidansu Hidaya yana jiran fitowarta. Kallo yakai kan hannunsa da gashi ya kwanta luff-luff dake ɗaure da Agogo. na brand ɗin Patek Philippe, finger ɗinsa sanye da Zoben azurfa da piece of black diamond stone ajiki. Buɗe ƴar ƙaramar ƙofar dake jikin gate ɗin akayi ajiyar zuciya ya sauƙe a lokacin daya ɗaura idanuwansa akan Hidaya wani ƙayataccen murmushine ya shinfiɗa akan fuskarsa yana jin wani irin sanyi yana ziyartar duk wasu gaɓɓai da illahirin jikinsa. Kallonta yakeyi yana jin sautin bugun zuciyarsa yana canjawa, iska ya furzar yana tambayar zuciyarsa abunda ya sameta yaga yanayinta gabaki ɗaya a canje. Ƙarasowa tayi ta buɗe front seat ta zauna ajiyar zuciya ta sauƙe bayan ta shaƙi daddaɗa kuma sanyayyane ƙamshin turaren Hydar wanda bata taɓa jin kalarsa a wani wajanba sai ajikinsa wanda ya haɗe da sanyin AC dake motar, bai tada motar ba cike da kulawa ya dubeta yace.
"Twinny ya ya ne? Waya taɓaki kuma?" Ajiyar zuciya ta sauƙe bata iya ɓoyewa Hydar komai ba don haka tace.
"Abba ne twin bro wai aure zaiyi kuma yarinyar daya kusa haifar ta, can you imagine za'a yiwa Mami kishiya da little girl?" Murmushi yayi yace.
"Yawanci maza haka suke twinny karki manta Abiena lokacin daya auri Ummina da yanada yara a lokaci yaci ace yakusa haifarta so abunda Abba zaiyi ba haramun bane kawai mu bishi da addu'a." Turo baki Hidaya tayi tace.
"Shiyasa bazan taɓa iya auran yaro ba twin-bro a lokacin da mace ta fara girma a lokacin ne zai auro yarinya ƙarama, na gwammace ni naje a matsayin yarinya ƙarama wallahi." Gaban Hydar ne yayi mummunan faɗuwa ya dubeta yace.
"Ba kowane haka ba twinny wani idan yayi aure tunna yarinta yayi kenan bai sakewa sai mutuwa ta raba nima in sha Allah hakan zanyi." Ɓata fuska tayi tace.
"Duk maza halinsu ɗaya shiyasa gara ma idan zanyi aure na aureshi a lokacin daya manyanta ya mallaki hankalin kansa a lokacin suka fi riƙe mace yanda ya kamata."
"Age fa is just a number twinny zaki samu yaro mai halin manya Babba mai halin da ko babba baida irinsa"
"Koba Number ba? Drive please kafin ka sake ɓatamun raina. Ni dai bazan auri yaro ba. Babba zan samu naje nai ta yi masa shagwaba yana riritani. Amma bazan auri koda wanda ya bani 10years bama bare ya bari sai na girma ya kwaso min yarinya." Shiru Hydar yayi ya tada motar ransa cike da zullumin abinda yaji tana cewa. Kenan ba zata iya auransa ba idan ya bayyana mata cewa shi ita yake so? Yana jinta tana ta discribing na irin mijin da take buri wanda yaji ko digon yanayinsa bata fado ba. Cikin zuciyarsa ya shiga addu'ar Allah ya canza mata tunaninta domin shi ba zai iya auran wata idan ba ita ba. Bai kulata taba duk surutun da takeyi sai da ta gaji gashi har sun kusa zuwa school ya kalleshi da mamaki fal a fuskarta.
"Twin Bro bakaji Ina ta magana bane ba? Ohhh saboda matsalar taku ce ta maza shi yasa kayi min shiru ko? Uhmm na gane da alama kai ma irin su Abba ne masu karo aure idan sun ga ta farkon ta fara tsufa ko twinny?" Juyowa Hydar ya yi suka hada ido, baki yaga tana turowa yai saurin kawar da kai yana sake riko steering wheel, besan me zai ce mata ba dan yaga kamar tana jin zafin abun nan na karo auren da Abbanta zai yi.
"Bazaka ce komai ba ko?" Ta fada tana sake hade rai da alama tana san jin view dinsa.
"Me zance miki Twin sis? Ra'ayin mu ya bambanta shi yasa kikaji nayi shiru." Hidaya ta zaro ido tana masa kallan mamaki wannan ne karo na farko da Hydar ya zaɓi wani ra'ayi daban da nata, duk yanda yakai ga son abu har indai yaga bata ra'ayinsa toh bari yakeyi, cike da mamaki take fadin.
"Dagaske kai ma haka zakayi?" Girgiza kai Hydar ya yi,
"A'a ni ra'ayina ina so na auri age mate dina, ke kuma naji kina maganar auran tsoho wanda ya kusan tafiya kabari." Hidaya bata san lokacin da ta tuntsure da dariya ba harda tafa hannaye, daidai lokacin kuma suka iso gate aka bude musu Hydar ya shiga da motar yana sake jin faduwar gaba akan ra'ayin Hidaya na mijin da takeso. Wajan da ya saba yin parking ya nufa har lokacin Hidaya bata dena dariya ba shi kuma wata irin nutsuwa yaji zuciyarsa nayi yana jin kamar karta dena yin dariyar yana jinsa cikin wani farin ciki. Sai da ya gama parking motar ta denayin dariyar ya kalleta tana kokarin daukar school bag dinta tana cewa.
"Twin Bro gaskiya kana so ka jawa kanka raini."
"Indai zan auri wacce nake so ko ta raina ni ba komai duk cikin so ne." Hydar ya fada shima yana janyo school bag dinsa tare da fitowa daga cikin motar. Da sauri Hidaya ta fito ta dawo gefensa Tana kallonsa fuskarsa cike da mamakin kalaman sa. akwai bambamcin tsayi sosai tsaknin Hydar da Hidaya gabaki ɗaya baza'a taɓa zaton sa'anta bane akwai tazarar girma a yanayin jikinsu sosai, Jerawa sukai zuwa class din su tana cewa.
"Twin Bro Gaskiya karka yi min haka, Allah idan ka auri age mate din mu ni kaina bazata girmana ni ba. Kace min da wasa kakeyi." Ta karasa maganar cike da magiya.
"Me yasa zanyi karya Twin sis? Am serious, very serious." Hidaya ta turo baki har suka shiga class tana masa magiya akan ya canza ra'ayinsa akan auran sa'arsa ya kafe mata yace shi ra'ayinsa kenan. Sai da suka zauna yaga ta matsa masa kan sai ya canza wacce zai aura. Shafa lallausar sumar kansa da take faman kyalli ya yi tare da tsuke fuskarsa yana cewa.
"Kezaki canza raayi Twin sis, you know what? Zaki auri mai mata uku kene ta hudu. Ga 'ya'yansa kila sunkai ashirin ko arba'in wane love zakuyi? Kika auri mai mata tsoho 'ya'yansa ma ba sanki zasu yi ba. Idan ya mutu yaransa ma rashin mutunci zasu yi miki suna jin haushinki Baban su ya auri jikarsa." Yayi maganar cike da san cusa mata kin auran mai shekaru da yawa. Ga mamakin Hydar gani ya yi Hidaya ta dage kafada alamar bata damu ba tana karbar wayar hannunsa take cewa.
"Toh ni ina ruwa na da hakan? Idan yana so na ba komai zan jure, ni kawai bazan iya auran wanda sai na gama yadda dashi cewa ba zai min kishiya ko irin ya auro min karamar yarinya ba. Gwara na auri babban mutum Twin Bro hankalina yafi kwanciya." Hydar ya rintsa ido kawai, kalamanta zafi suke yi masa, har hango irin mijin da take nufi tana so ta aura yakeyi a cikin brain dinsa.
"Kayi shiru Twin Bro, please say something mana." Wani kallo Hydar ya watsa mata wanda yasa Hidaya yin murmushi dan tana hango jin haushinta a cikin idanunsa. Bata zaci zai kuma furta komai ba sai ji tayi yana cewa.
"Sai na gayawa Mami kina soyayya da tsoho." Hidaya ta bude masa ido baki bude tace,
"Yaushe nayi soyayya Twin Bro?" Hydar yace,
"Gashi nan."
"Ban fara soyayya ba fa, kawai nace idan zanyi to da big man zanyi ba samari matasa ba." Ji ya yi kansa ya fara yin nauyi dan haka yasa yatsunsa biyu ya toshe kunnuwansa. Hidaya dariya tayi ta fara danna wayar, shigowar teacher yasa ta janyo bag din Hydar ta saka masa phone din a ciki ta koma wajan zamanta. Teachern yana fita Hidaya ta dawo kan saman bench ɗin Hydar ta zauna cike da zumuɗin shiga sabon aji tace.
"Yessss SS3 akwai dadi wallahi." ta fada da wani farin ciki lullube a fuskarta tana rungume text book din geography da suka gama class din shi yanzu. Kallan ta Hydar ya yi yadda yaga farin ciki a fuskarta. Yana mamakin yadda Hidaya bata jinsa kamar yadda yake jinta. Gashi ba zai iya nuna mata yanayin yadda yake jinta ba saboda yana ganin akwai suran lokaci. Gefe daya yana ganin idan har ya bayyanawa Hidaya yana san auranta zatayi accepting da gudu Saboda yadda suke, yana da yaƙinin zata watsar da kudirinta na yau da take sanar dashi sai babban mutum zata aura har indai taji kalmar soyayya daga bakinsa.
"Twin Bro ya kaji class 6? Banga kana murna ba." Ta tambaye shi tana kallan fuskarsa.
"bana farin ciki." Zaro ido tayi,
"Why?" Ta tambaya.
"Sabida..." Ya yi shiru yaji bazai iya cewa saboda zai dena ganinta sosai. Dan yasan shigowarsu SS3 yana nuna sun kusa kammala school, amma zaiyi iya bakin ƙoƙarinsa yaga sun shiga makaranta ɗaya sun samu admission a course ɗaya, idan da a sonsa ne kamar yanda ya ƙudirta suna gama secondary school zai sanar da Hidaya abunda yake zuciyarsa toh a wannan lokacin yakamata ayi musu aure sai su tafi wata ƙasar can daban sucigaba da karatunsu.
"Uhmm ina jinka saboda mene baka farin ciki?" Hidaya ya katse shirun nasa.
"Kawai banjin dadi ne."
"Twin Bro ko meyasa?, ni wallahi naji dadi." Hydar ya kawar da kai gefe caraf suka hada idanuwa da Na'ima Tafida yarinyar da take mugun crushing akansa. Janye idanunsa ya yi ya maida kan Hidaya take ci gaba da nishadi, ganin yana kallanta yasa ta cewa.
"Yah?"
"Babu gwara na kalleki Yadda kike farin cikin nan." Hidaya ta saki dariya tana juya idanuwa.
"Kadena to karka hango munina."
"Me zai faru idan na gani?" Ta turo baki gaba tana fadin.
"Shikenan zaka dinga gani na kamar biri." Ta karasa magana kamar zatayi kuka.
"Hakan bazai taɓa faruwa ba!" Ya fada yana janyo wayarsa. Turo baki tayi tana tashi ya bita da ido ta koma wajan su Najwa. Waya yake dannawa amma a zahiri duk wani motsi na Hidaya yana kan idanunsa har biology teacher ya shigo ta koma wajan zamanta.
Yau gabaki ɗaya Hydar Baida walwala tun da yaji kalaman Hidaya, itama Hidaya anata wajan saita fara walwala tana tuna auran da Abbanta zai ƙara sai jikinta gabaki ɗaya ya mutu, tanaji da gaske Abban ta baiyiwa Maminta adalci ba a'iya zamanta bata taɓa ganin mace mai biyayyya kamar Maminta ba, ta ɗauki Abba da muhimmanci sosai da bata haɗashi da kowa ba babu ta yanda ta gaza masa, har shaw'ar yanda Maminta ke kulawa da Abbanta takeyi sau dayawa takanga kamar babu wasu ma'aurata da suka kai mahaifanta iya zama da juna. bata taɓa tunanin da abunda Abba zai sakawa Mami ba kenan.
Ƙarfe 6pm dai-daia aka tashesu a makaranta Hidaya yafara kaiwa gida ya ajiyeta babu yanda batayi dashi ya shigo ba ammam firr Hydar yaƙi gabaki ɗaya yau baya yanyin da zai iya shiga ciki kamar yanda ya saba,
Da sallama yashiga palourn duk da ya tabbatar da cewa babu wasu ma'aikata a sashin a dai-dai wannan lokacin gabaki ɗayansu sun koma wajansu, zama yayi akan kujera yana sauƙe ajiyar zuciya, kallaon sashin Umminsa yakeyi wanda a yanzu ya dawo sashinsa fayau yake kallonsa koda yaushe wajan fili yake ƙara yimasa kimanin shekaru kenan amma har yau yakasa sabawa da rayuwa shi ɗaya a cikin wajan, Ji yayi inama da ace ya yarda yashiga wajan Mami da Hidaya ta dameshi? May be daya rage wani abu daga cikin damuwar da kalaman Hidaya suka jefashi domin a halin yanzu Mami itace wacce ta maye masa gurbin Umminsa. Daƙyar ya iya miƙewa ya shiga ɗaki yana Isa ya cire uniform ya ƙarasa toilet ruwa ya sakarwa kansa a gaggauce sannan ya shirya yafito palour. Kai kallonsa yayi ga warmers ɗin dake shirye akan dining wanda aka shirya masa, kawar da kansa gefe yayi domin baijin zai iya cin abincin, yana zaune har aka kira magrib yafita bai dawo ba har saida yayi isha'i, tsakanin magrib da isha'i yana tare da Abiensa akoda yaushe da zarar anyi isha'i yake daowwa ciki, Takawa da kansa yau ya fahimci Hydar baya cikin walwal bai matsa da tambayarsa abunda yake damunsa ba domin ya tabbataba shekarun Hydar a yanzu sai dai dauriya irin tasa amma yana buƙatar Uwa kusa dashi. Bayan Hydar yashigo daƙyar ya tayshi kansa da tunanin Hidaya bazata taɓa ƙinsa ba zuciyarshi tana bashi yaƙinin a lokacin da Hidaya tasan yana sonta zata watsar da wannan tunanin nata da baisan yanda ta kwaso shi ba, tabbas yasan Hidaya bata son raini amma tunanin auren wanda ya manyanta bai san daga ina ya shigo kanta ba.
Addu'a yake a cikin ransa Allah yasa Hidaya tana sonsa itama koda kwatankwacin yanda yake sonta ne, bai san wani irin so yake mata ba don yanada yaƙini yafara sonta tun a ranar daya fara ɗaura idonsa akanta saboda memory na wannan ranar bai taɓa gogewa akansa ba despite ƙarancin shekarunsa a wancan lokacin.
Da farko bai fahimci irin son da yake mata ba sai a lokacin daya taɓa karanta wasu sign na soyayya hakan ya tabbatar masa da irin soyayyar da yake mata tun a karon farko Soyayya ce irin wacce take tsakanin ɗa namiji da mace domin bata taɓa canjawa ba. Wayarshi ce tafara ruri cike da zumuɗi ya jawota tunda yasan da Hidaya kawai yake waya a wannan lokacin har zuwa baccinsa. Yanayin yanda Hidaya take tambayarsa yaci abinci cike da kulawa ya kawar masa da kaso sittin daga cikin damuwarsa. Da ya nuna bai ciba kamar tana wajan haka ta matsa saida ya tashi zuwa cin abincin, yanaci suna hira harya kammala.
________
Numfashi Fulani ta sauke tana kallan Ayna'u da take daga wasu lafaya da akai musu order din su Fulani ta kallo Ayna'u sannan tayi Murmushi tare da cewa.
"Ina so na yiwa Takawa magana akan fitar da Farooq karatu, ni gaskiya bazan yadda ɗana na ya yi karatu daga matakin farko har zuwa secondary anan ƙasar ba, Hydar daban Faruq daban." Sister Aynah ta ajiye ta hannunta ta kalli Fulani tana cewa.
"Toh ai dama laifin kine Fulani, taya zaki bari ma tun farko akai Farooq school din da Hydar yake yi? Ai ni tun farko banso haka ba. Kina ganin dai tunda makirar matar nan ta bar masarautar nan Takawa ya sake janyo Hydar ajikinsa, da anyi magana yace a dinga tausaya masa uwarsa bata nan sai kace wani yace ta bar gidan." Aynah ta fada tana yatsina fuska da alama abinda Takawa keyi akan Hydar yana damun zuciyarta.
"Naji dadin barin Zaynab gidan nan saboda yanzu nasan Takwara baya tare da kowacce mace sai ni kadai duk kuwa da cewar har yanzu bamusan stand ɗin tafiyarta ba, daga ita har takawa babu wanda yabamu cikekken bayani, sai dai ko babu komai rashinta a masarautar yana min daɗi. Sai dai ina bakin cikin yadda yake bambanta Hydar da Farooq, idan nayi magana yace ai Hydar shine babba. Ayna'u ina tsoran kar lokacin karbar sarauta ya yi ace dole sai babba ne zai yi. Ina so sarauta ta dawo hannun mu ba wai ta tafi jinin wata kasar ba, a gani na wannan abun kunya ne." Tayi maganar damuwa na bayyana a saman fuskarta.
"Har a wajan mu abin kunya ne wallahi Fulani, kuma hakan ma bazata faru ba kwata-kwata, sarauta ba zata bar nan ba insha Allahu. Zaynab kuma kina zaton zata dawo ne? Matar nan ta dauka dan babu ita za'a fasa yin wani abun a masarautar nan. Ba tasan barin ta yafi komai dadi ta samun ci gaba ba."
"Sosai Sister Ayna'u. Ni babban abinda yake damuna shine yadda Farooq yake shigewa Hydar, nayi masifar nayi bala'in akan ya dena amma yaki. Kuma idan kinga yadda Hydar din ke masa wulakanci ba zaki ce sun hada wani abun ba. Rai na yana baci sister Ayna'u ina jin kamar na shake Hydar din." Ta gama maganar ta jan wani mugun tsaki.
"Rabu da Farooq harda yarinta ke damunsa. Ina mai tabbatar miki idan har ya fara mallakar hankalinsa yasan cewa shima yana da wani matsayi irin wanda Hydar din ke dashi, da kanshi zai nemawa kansa mafita kina zaune zaki sha kallo." Fulani tayi shiru da alama bata gamsu da zancen Ayna'u ba, tana ganin tunda ance abinda yaro ya tashi dashi har ya girma dashi yake tasowa. Farooq yana san Hydar tana ganin idan har ya tashi a haka to zasu zama bayinsa abinda bata fata kenan.
"Dole na dage da cusa Farooq cikin zuciyar Takawa, haka ne kawai zai sa ya ture soyayyar Hydar."
"Wannan ma abin yi ne Fulani, domin Farooq shine last hope din mu." Daga nan suka ci gaba da tsara yadda zasu bullowa Farooq ya dena kula Hydar..
#Love and destiny
#Zee Bawa
#Stylish bch
#YAN TAGWAYE