Free chapter 路 Read without an account
{45..}
馃挍 HAJAR 馃挍
Da sauri Nurain ya lumshe idonsa tsabar yadda hasken ya kashe masa su, Hajar da tsoro ya sandarar da ita ta kasa wani cikakken motsi, sosai ta razana don ba tayi tunanin akwai mutum a wajen ba, Nurain ya ajiye cup din Coffeen ya kaucewa hasken yace "kee mene haka kuma are you mad...?", da sauri ta janye hasken daga kansa, furiously ya tashi ya kunna bulbs haske ya gauraye palourn, wani irin shan kunu Hajar tayi ta shige kitchen da sigar ko in kula, sarai tasan haske masa ido tayi amma she don't care tinda dai ba intentionally ta aikata hakan ba, wani tu茩u茩i ne ma ya mamaye mata zuciya da taga fuskar tasa, plate ta 蓷auka ta zuba dubulan da Alkaki sai chin chin, cup ta 蓷auka ta bu蓷e tap din sink ta cika da ruwa, daga haka ta fita daga kitchen din, direct stairs ta dosa, Nurain ya mi茩e daga hannun kujerar da ya zauna ya zuba both hands dinsa a pocket fuskarsa a murtuke yace "hey you stay there", tamke fuskarta tayi ta cigaba da tafiya a hankali sbd kar cup din da ta ciko da ruwa yayi tambal tambal ya zube, yayi blocking front dinta yana binta da wani kallon tsana yace "wnn shine karo na 茩arshe da zaki sake fitowa palourn nan idan ina zaune, daga 茩arfe shida na yamma bana son ko silhouette naki ya gifta ta palourn nan, ko me za kiyi ki yisa kafin wnn time din that is weekdays knn, a weekend kuma you just have 3 hours daga shida na safe zuwa tara, daga nan kuma sai gobe, am i clear...?", ta juya lulu eyes 蓷inta ta yamutsa fuska sbd yadda tayi perceiving pure men scent dinsa, ta ta蓳e baki tace "sorry you can't tell me what to do...", yace "ko, toh ki jini da kyau as far as you are living in my house you must follow my rules, bad attitudes din da kike ji dashi toh ki tattarasa ki ajiye gefe, ba dai a nan ba saiki bari lokacin da kika gaji da zama kika sallami kanki ki 蓷auki abinki ki 茩ara gaba, this is my last warning...", da haka ya barta tsaye ya 蓷auki Laptop dinsa da cup of coffeen zai haura sama, wata nannayar ajiyar zuciya Hajar ta sauke, har wani huci take masifar ta motsa, idonta ya kawo ruwa, tana ganin yayi rabin stairs din tace "ji mana malam, karka tsaya wahalar da kanka, ka dam茩a min shaida kaga idan ban 茩ara gaban ba", ya juyo ya wurga mata wani mugun kallo yace "save the time that you are free to roam in my house..." da haka ya juya ya haura stairs, har wajen 50seconds tana tsaye inda ya barta, gya蓷a kai tayi ta numfasa tace "lallai wnn mutumin bai sanni ba, sanin da yayi min na ta蓳in gishiri ne, mu zuba ni da kai wanda ya fasa bai haifu ba", 蓷akinta ta wuce abinta, akan mirror ta ajiye plate da cup din da ta shigo dasu, ta zauna akan stool dake gaban mirror din tana kallon kanta, kwafa tayi ta girgiza kai ta ja plate din gabanta ta fara cin tarkacen da ta 蓷eba, tana gama cin iya yadda zai mata ta sha ruwa, tayi kwanciyarta kan carpet kamar yadda tayi jiya, ta lullu蓳e da duvet don wani azabar sanyi 蓷akin yake mata sbd Ac gashi bata san ta inda zata kashe ba. Nurain ya gama abinda zai yi jikin Laptop kafin ya kashe ya mayar da ita bag, ya fita da cup din daya gama shan Coffee zuwa Kitchen yana dawowa kuma ya kwanta, da Asuba bayan ya shiga toilet ya dauro alwala ya fita daga room din nasa, a corridor ya tsaya yana kallon 茩ofar 蓷akinta, after looking at the for few seconds kawai ya sauka downstairs, bayan ya dawo daga masallaci ya zauna yayi recitation of the holy book, sai wajen 8 na safe ya rufe karatun, daman already yau Monday yake son komawa work, bathroom ya shiga bayan yayi wanka ya fito da towel a hannunsa yana goge cikakkiyar sumarsa, 9 ya gama shirinsa tsaf ya 蓷auki briefcase da ya saka Laptop dinsa ya sauko 茩asa bayan ya rufe part din nasa, bai ga dai alamar ta sakko ba har ya shiga kitchen, ya ha蓷a tea ya dawo palour yana sha, tsaki yayi don ya saba yin full breakfast kafin ya fita aiki, daga karshe dai ya gama shanye tean ya kai cup din kitchen, daga haka ya fita compound bayan ya rufe main door ya zuba keys din a pocket, da sauri Inuwa dake zaune kan white plastic chair a bakin gate ya taso, ya russuna da kyau ya gaida Nurain, a takaice ya amsa yace "akwai wanda suka zo jiya ne bayan fita ta..?", Inuwa yace "Eh alhj anyi ba茩i sunxo nan da kayan abinci..", Nurain ya gya蓷a kai bai ce komai ba ya bu蓷e motarsa da Inuwa ya gogeta tass ya wanke wheels 蓷in kuma, bayan ya gama warming ya ja motar ya bar parking space din ya fita daga gidan dan already mai gadi ya bu蓷e gate, after a ride of 20mins ya isa hospital, yayi parking motar, kallon yawarsa dake kan dashboard yayi kafin yasa hannu ya 蓷auka ya zurata a pocket, ya fito walking majestically ya nufi hanyar office dinsa, securities da sauran ma'aikata suka ringa gaishesa da welcoming dinsa, briefly yake amsa gaisuwar yana tafiya, yana 茩arasawa office din ya bu蓷e ya shiga, secretaryn sa Haleema da ya turawa sa茩o ta email cewa zai shigo on Monday, shiyasa tin ranar friday tasa aka kyara office din, Haleema ta tashi with respect tace "good morning sir", da sakakkiyar fuska ya amsa mata yace "morning, ykk..", tace "alhmdllh sir an dawo lfy..?", yace "fine alhmdllh" da haka ya shige cikin office din, 茩arewa office din kallo yayi kafin ya ajiye briefcase din hannunsa kan huge table dake office din, after surveying the huge office ya zauna kan kujera yana sauke ajiyar zuciya, ya kalli glass nameplate dake gaban table din mai 蓷auke da sunansa (Dr Uthman). wayarsa ya ciro ya kunna, saida ta gama booting uban messages da suke pending suka gama shigowa, call log ya shiga yayi dialing numbern Khaleel, tana fara ringing Khaleel yayi picking, Khaleel yace "ba dai ka dawo ba boss..", Nurain yace "gani ma a office", Khaleel ya katse kiran, after like 5minutes ya shigo office din, Khaleel ya zauna kan 蓷aya daga biyun kujeru da suke gaban table din, bayan sunyi exchanging greetings Khaleel yace "An dawo lfy..?", Nurain yace "alhmdllh, Dr Marwan ya shigo..?", Khaleel yace "yeah amma ya shiga surgery not too long ago", Nurain yace "Ohk", Khaleel ya ciro wayarsa da tayi ringing daga pocket din labcoat dinsa, few seconds ya katse kiran ya tashi yace "i have to go now ana kirana a E.R". Khaleel na fita office din Nurain ya kira Haleema ta landline, tayi picking tace "yess sir", yace "Patients zasu iya fara shigowa", tace "Okay sir". Nurain ya fara attending first patient da ya shigo, yana yiwa patient din 拼an tambayoyi aka bu蓷e 茩ofa aka shigo, kallo 蓷aya ya mata ya 蓷auke kansa ya cigaba da attending patient dinsa, jingina Ruqayyah tayi jikin 茩ofar tana mayar da numfashi, ta lumshe idonta tana sauke ajiyar zuciya sai kuma ta bu蓷e idanun, kamar a yanzu ta fara ganinsa haka ta zuba masa na mujiya, kawai kallonsa take babu 茩iftawa ta jingina da jikin 茩ofar, Nurain yayi prescribing patient din with drugs da cewar zai dawo nan da 2weeks follow up, Ruqayyah ta matsa gefe ta bawa patient din hanya ya fita, tamkar wacca kawai ya fashewa acikin haka ta isa gaban table din nasa kanta a 茩asa tana wasa with her fingers, tinda ya mata kallo 蓷ayan nan bai sake ba, kwata kwata bai nuna yasan ma da shigowarta ba, ya cigaba da rubutu jikin record book, muryarta na rawa kanta a 茩asa tace "Dearest...", next patient ce ta shigo 拼ar dattijuwa, ganin haka yasa Ruqayyah ta bata space, sai a lokacin Nurain ya 蓷ago yayi attending patient dinsa, a haka dai saida yayi attending 5 Patients kuma har lokacin Ruqayyah na tsaye bata fita ba, na biyar din patient na fita, da sauri Ruqayyah taje ta rufe 茩ofa, Nurain ya kira landline yace "i need security now", kasa茩e Ruqayyah tayi tana kallonsa sai kuma ta ha蓷a hannayenta waje 蓷aya tace "plxx talk to me, dan Allah kayi ha茩uri ka saurareni Dearest...", rubuce rubucen sa ya cigaba da yi, Security man ya bu蓷e 茩ofa ya shigo with respect yace "sir you call", ba tare da ya 蓷ago kansa ba yace "get her out of my office", security man yace "yess", ya kalli Ruqayyah da Mamaki ya gama daskarar da ita yace "Muje hajiya..", wani kwallo mai uban tauri Ruqayyah ta ha蓷iya lokaci guda ta fita daga office din with speed hawaye na zuba idonta. Nurse station ta wuce, tana zuwa ta zauna kan kujera ta hade kanta da table din station din ta fashe da kuka, Nurse Jidda da ita ka蓷ai ce a station din duk sauran sun shiga ward ta ajiye kidney dish din hannunta tace "Ruqayyah lfy...?", Kuka kawai Ruqayyah take ta茩i tace komai, da damuwa Jiddah tace "subhanallah dan Allah ki gayamin mene ya faru..?", Ruqayyah ta 蓷ago kanta tana kallon Jiddah da jajayen idanunta tace "Jiddah ni yanxu ya zanyi, Dr ya茩i saurarata...", Jiddah ta jinjina kai ba tace komai ba, ita ganin 茩arfin halin Ruqayyah take, yo ko itace Dr ai bazata saurareta ba, Ruqayyah ta goge cheeks dinta tace "wai fa security ya kira yace yayi waje dani sai kace wata 蓳arauniya..", ta sake fashewa da kuka, Jidda tace "bari na duba patient a ward A" da haka ta saka kidney dish din da ta ajiye a cikin tray ta 蓷auka tabar station din.
鈽匰ai goma da rabi Hajar ta farka daga baccin da ta koma bayan ta idar da sallar asuba, bathroom ta shiga tayi brush ta wanke bakinta da mouth wash, tayi wanka, saida ta wanke bathroom din snn ta fito, tsaye tayi bakin mirror tana kallon uban kayan shafe shafen da Hafsah ta jera mata jiya, wani body lotion ta 蓷auka tana duba sunansa sbd da shower gel dinsa tayi wanka, ta zauna kan stool ta fara rubbing lotion din, ta ringa kallon gashin kanta da duk kitson ya fara warwarewa da kansa, bai 蓷auketa wani minti 20 ba ta gama tsefe 茩ananan kitson kanta tass, daga ta kama jelar zugeta kawai take cause gashinta mai laushi da santsi ne na fulani, combing hair din tayi ta shafa masa oil shima da ta gani, tayi parking dinsa a 茩eya ta tufke jelar, daga haka ta tashi daga gaban mirrorn, ta bu蓷e huge wardrobe tana ta蓳e baki, ita dama a box Hafsah ta bar mata kayanta, wata doguwar riga ta atamfa ta saka, ta zumbula hijab ta fita a 蓷akin ta sauka 茩asa da cup da plate din jiya da taci kayan gara, kayan garar ta sake 蓷iba taci a kitchen din tasha ruwanta a famfo kafin ta fito ta koma room dinta, tanata zaune a 蓷akin saidai tayi game a wayarta inta gaji ta ajiye har akay sallar Azahar, tana idar da sallah taji wata yunwa ta bijiro mata, kayan garar dai ta kuma 蓷urawa cikinta, samm ta茩i yin girki sbd gani take knn ma rayuwa mai tsayi zata yi, palour ta fito ta ringa kallon 茩ofa kafin ta matsa kusa da ita ta kama handle ta mur蓷a, a rufe taji 茩ofar, ta koma kitchen ta bu蓷e 茩ofar da zata sadaka da backyard din gidan, luckily ta jita a bu蓷e, ta ringa kallon backyard din tana 蓷an zagawa, ta zauna kan wani dakali da ta gani wanda shine chamber na ruwa, sosai zaman wajen yayi mata da蓷i don ji tayi kamar an cirota daga ma茩abarta, ba tasan iya awannin da ta 蓷auka zaune a wajen ba tana tunani iri iri, motsin zubar ruwa ta jiyo daga front din gidan, tashi tayi ta ringa bin inda motsin yake, mai gadi ne ya kunna famfon compound din yana alwala, 蓷an russunawa yayi ganinta ya kashe famfon yace "ina wuni Hajiya..", Hajar ta mayar masa da gaisuwar don ta ganesa ranar da suka dawo gidan shi suka tarar, Inuwa ya du茩ar da kai yace "wani abin za a amso miki hajiya...?", Hajar ta girgiza kai ta juya ta koma backyard din, ciki ta koma don yin sallah, tana idar da sallah wayarta ta fara ringing, ta ringa kallon screen 蓷in wayar ganin number ke kiranta kuma bata san numbern ba har kiran ya katse wani ya sake shigowa, picking tayi ta kara a kunne ba tace komai ba, wani murmushi tayi bayan ta 蓷au murya tace "Noor...", Noor tayi dariya tace "ta ya akay kika gane...?", Hajar tayi 拼ar dariya tace "your voice mna", Noor tace "toh ykk ya gida...", Hajar tace "lfy lou and you..?", Noor tace "am great wllh..", Hajar tace "good, toh yaushe zaki zo..?", zaro ido Noor tayi tace "not soon..", Hajar ta marairaice murya tace "kefa kika ce zaki zo..", Noor tace "yeah zan zo amma ba yanzu ba..", Hajar tace "toh shknn sai kinxo", sun 蓷an jima suna hira da Noor kafin daga karshe Noor tayi mata sallama, Hajar ta tashi ta na蓷e darduman da tayi sallah, sai kace wata 拼ar kurkuku haka take jin rayuwar gidan, daga 茩arshe dai ta fara gyara 蓷akinta wanda babu wani datti ta masa turaren wuta wai dan duk ta 蓷an ware, taje kitchen ta ciko plate da kayan garar da ta mayar abinci, da kyar ta iya hawa stairs bayan ta fito daga kitchen sbd 茩ullewar da cikinta yayi, ta samu dai ta shiga 蓷akinta ta zaune gefen gado ta danne cikin da yake kan mur蓷a mata, bayan wani lokaci cikin na mur蓷awa sai ta fara yin 茩alas, mai茩on Alkaki yazo ya tsaya mata a wuya har tana jin kamar za tayi amai.
鈽吰檃rfe biyu da 拼an mintina Nurain ya fito daga office dinsa holding his briefcase, saida yayi attending kaf patient da suka zo shiyasa ya kai wnn time din, acikin doctors da suke aiki a hospital din shine me wnn halin, indai kaga kazo ganinsa bai duba ka ba toh akwai babban dalili amma duk yawan patient yana squeezing ya duba su, Ruqayyah dake zaune bakin office din over three hours tana jiran fitowarsa ta tashi da sauri tabi bayansa, tana zuwa gaf dashi tace "Dr..", dakatawa yayi da tafiyar ya jiyo yana kallonta ba tare da yace komai ba, kallon da yayi nata sai taji gaba 蓷aya 蓷an guntun courage dinta ya narke gami da tsiyayewa ta guiwarta, ta kasa cewa komai amma lips dinta sai 蓳ari suke, shi kam da yasan ma itace wllh bazai dakata ba, shi Allah ya masa wani hali na bagarar da lamari indai ya bar abu topa shknn, don yanzu idan nace muku ya manta muryarta ne shiyasa ma har ya juyo data kirasa kar kuyi mamaki, ya ha蓷e thick eyebrows dinsa ya juya ya cigaba da tafiyarsa, Ruqayyah tayi ajiyar zuciya ta lumshe idanunta da suke mata zugi tsabar kukan da ta sha, da sauri ta kuma binsa sai kace mayya tace "dan girman Allah Dearest kayi ha茩uri, make time for us so that we can discuss about it, i will tell you all what happened...", har suka fito harabar hospital din tana biye dashi tana masa magiya, ganin ba sauraronta zaiyi ba ta tsaya a 茩ofar department din gudun kar ta dizga kanta a public, Nurain yana isa parking space ya shiga motarsa, keys ya zura a ignition ya kunna motar, har lokacin girarsa a ha蓷e take don ba 茩aramin fama masa zuciya waccar psycho din tayi ba, he dislike the sight of her, direct gidansu ya dosa don bazai koma gidansa yaga wani abun da zai sake 蓳ata masa rai ba, bayan yayi parking motarsa ya shiga ciki. Mami na zaune a main palourn da wasu close friends dinta guda biyu, ya 茩arasa shiga palourn ya gaishesu duka da ladabi, Mami dai tayi mamakin ganinsa a wnn lokacin it seems like daga wajen aiki yake shine ya zarto nan a maimakon gidansa, shidai yana gama gaidasu ya wuce upstairs, Mami ta bisa da kallo, Haj Sadeeya tace "Aaa aha ashe duk munyi furfura don Allah kalli yadda yaron nan ya koma Nurainin Mami, kinga ma ban tambayesa iyalin ba don ina Canada kika gayamin zancen aurensa...", Mami tayi ya茩e tace "matarsa na nan lfy baifi kwana goma da yin auren ba..", Haj Sadeeya tace "kwana goma kuma nifa mganar almost one year nake miki..", Haj Fati tace "ni dai nasan wancan an fasa yinsa, bayan nan ma Nurain din ya koma India, toh dai wnn na kwana goman ne bansan dashi ba.." ta fadi hakan tana kallon Mami, Mami ta kallesu duka tace "wllh auren ne yazo unexpected, nima kaina saida aka 蓷aurasa na sani, prof ne ya ha蓷asa da 拼ar abokinsa, shima yaron ba sani yayi ba don lokacin ma bai dawo 茩asar ba..", Haj Sadeeya tace "duk ba labari da fasa wancan din da kuma sabon, toh in banda abinki Mami aiko baza mu zo ba ai kya gaya mana", Mami tayi ajiyar zuciya tace "duk kuyi ha茩uri abin ne yazo unexpected shiyasa, ba a nitse nake ba wllh". uku da minti goma Nurain ya sakko har yayi wanka ya sauya kayan jikinsa, yana kallon Mami yace "Noory fa..", Mami tace "bata dawo schl ba..", yace "Okay" yana kallon hanyar kitchen kafin ya wuce can din, kitchen din ya shiga bayan few minutes ya fito da plate din Abinci, dining ya wuce ya zauna ya fara cin abincin, saida ya cinye tass don yunwa yake ji ba ka蓷an ba tin tea da yasha da safe bai sake cin komai ba banda water, Nurain bai baro gidansu ba sai 茩arfe takwas na dare, a hakan ma sbd Mami ne dan ya lura da irin kallon da take masa ga dukkan alamu tana so ta fadi wani abun ne amma bata fada ba, yana zuwa gida daman a palourn 茩asa yayi branching, yayi powering TV kafin ya zauna kan exclusive sofa dake palourn, almost 30mins da zamansa aka bu蓷e 茩ofar kitchen, da sauri ya kalli direction din, a hankali ta fito daga kitchen din da cup ta ciko da ruwa, ta juya ta rufe 茩ofar, 茩ishi ruwa ne yasata fitowa tin 蓷azu, shine da tazo kitchen 蓷iba ciwon cikin ya mur蓷a mata ta dur茩ushe a 茩asan kitchen din tana mur茩ususu har saida taji dama dama snn ta iya tashi ta 蓷ebi ruwan ta samu ta fito, wani irin ha蓷e rai Nurain yayi, wato bata ji warning din da ya mata ba knn, how dare her zata ringa masa taurin kai, who born her with her bad attitudes, dole tayi abinda yace indai tana son cigaba da zama a gidan, furiously ya tashi yace "ke ba kiji warning din da na miki ba knn..", hannunta 蓷aya ri茩e da cup dayan kuma ta dafe cikinta, da kyar ta iya cewa "daman nace maka naji ne.., na riga na gaya maka you can't tell me what to do malam" tana gama fadin haka ta nufi stairs, bata ankara ba taji an fixgota baya ta bige da hannun kujera.....鉁嶏笍