Free chapter · Read without an account
SHA BIYAR
by ZAINAB M BAWA · WATA ALAƘA
*WATA ALAKA.*
*PAID BOOK*
*YAN TAGWAYE BIYAR*
ZAYNAB BAWA
&
STYLISH BCH
*SHAFI NA GOMA SHA BIYAR*
Duk wani abunda Mami takeyi daya danganci kula da iyalinta bata fasa yinsa ba sai dai sam batada walwala, daga Abba har Hidaya da sauran ƙannen Hidaya abun yana damunsu, sau dayawa idan sun zauna Hidaya ce ke rarrashinta kamar wata Babba dan tana jin ciwon ganin mahaifiyarsu cikin wannan halin. Murmushi kawai Mami keyi domin tunda ta fitar da abunda yake cinta arai ta faɗawa Hidaya taji nauyin da yake ƙirjinta ya ragu. Shi kansa Abba abun yana damunsa sosai baiyi tunanin Mami zata shiga wani yanayi ba don kawai yace mata zai ƙara aure ba, a tunaninsa duk daren daɗewa dama ya kamata ace mace tasan da wannan idan akwai aure a cikin ƙaddarar mijinta toh tabbas babu makawa sai yayi. Sannan ƙara aure bawai yana nufin baya son matarsa bane ko akwai wani abunda ta gaza ba yi masa. A'a ƙara aure sunnah ce kuma kaddara ce da idan akwai acikin rubutace ƙaddararka toh tabbas sai yafaru. A halin yanzu bazaice ga abunda Mami tayi masa na rashin jin daɗi ba tunda yafara maganar sauransa, amma tabbas ba haka tasaba mu'amalantarsa ba. Wani irin mood tasaka kanta wanda baza iya bayyana yanayin ba amma tadawo kamar wata marainiya. abun yana damunsa sosai shima harya fara taɓashi domin duk yanda yaso yin wlwal idan yaganta ahaka sai komai ya daina masa daɗi. Ita kanta Mami bata isa faɗin ga wani abu na rashin dai-dai da Abba yayi mata tun fara zancen auransa ba, duk da dai ba lallai arasa wasu abubuwan ba domin da zarar namiji yatashi aure koda ace wasu abubuwan bada gayya yayisu ba ita wacce yake zaune da ita taganka hakan kamar yanayi ne don ƙarin aurensa. Kawai ita abunda yake damunta shine yarinya ƙarama da zaije ya auro mata suyi zaman kishi da ita.
Gabaki ɗayansu zaune suke a palour suna hira Mami Hidaya da ƙanin Hidaya maibi mata wato Nasir sai ƙannensa guda uku wato, Adam, Abubakar Sadik, sai autarsu Maryam. Yanda suke hira kamar babu wani abunda yake faruwa a cikin gidan gwanin ban sha'awa ahaka Abba yayi sallama ya shigo cikin palourn. Yaji daɗin yanda ya samesu suna hira cikin farin ciki har Mami dan ya kwana biyu baiga farin ciki a fuskarta haka ba. Cike da zumuɗi ya ƙaraso ya zauna yaran sukayi masa sannu da zuwa babu yabo babu fallasa Mami ma tayi masa sannu sannan ta miƙe ta ɗauki jakarsa tashiga ɗaki. Miƙewa Abba yayi yabi bayanta Hidaya ta riƙo hannun Maryam suka shiga ɗakinsu bayan sauran ƙanneta suma duka sun miƙe sun shige ɗakunansu. Zama Abba yayi bakin gado yana jin ƙwarin guiwar rarrashinta a wannan lokacin domin yaga sassauci akan fuskarta sosai. Cikin sanyayyar murya yace.
"Mamin Hidaya zoki zauna mana." Ya faɗa yana buga gefensa. Babu musu taje ta zauna tayi ƙasa da kanta. Kallonta yayi sosai ya ƙare mata kallon tsaf ya fahimci tabbas tana cikin damuwa, dan haka cikin sigar rarrashi yace.
"Haba Mamin Hidaya me yasa zaki dinga daga hankalinki akan wannan auran da zanyi? Yin aure na bafa yana nufin na dena sanki ba ne dan Allah ki kwantar da hankalinki wallahi ina sonki, girmanki da kimarki babu wani abunda ya ragu a cikin zuciyata. Sannan wannan auran fa ƙaddara ce, kuma babu wata macen da zatazo gidannan ta kamoki bare ta wuceki, babu wani abunda wata zata ɗauka wanda ke baki ɗauƙa ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki bana son ganinki cikin damuwa." Murmushin takaici Mami tayi domin maza nada abun mamaki su da kansu zasu jajiɓo aure sai kuma azo ace ƙaddara ce, sannan namiji akwai iya daɗin baki, yanayin yanda Abba ya kwantar dakai yana rarrashinta yanzu kai kace dole akayi masa auran kamar babu wata mace a duniya sai ita. Kamo hannunta yayi ya sake saisaita murya yace.
"Dan Allah Mami kibani goyon baya duk wacce zatazo a bayanki zatazo har abada kuma bazata taɓa kamo kiba musamman idan kika bani hadin kai." Murmushi mai cike da dauriya Mami tayi sannan tace.
"Na hanaka yin aure ne Abba? Tun lokacin daka faɗamin ai ban ɗaga hankalina ba kawai ƴar yarinyar da zaka hadani kishi da ita ne abin yake bakanta min zuciya, kai a wajanka ba komai bane idan ka auro ƴar cikin ka ko?" Abban Hidaya ya kalleta yana mamakin yadda take cewa zai auro ƴar cikinsa.
"Idan kina cewa yar cikina wani sai yayi tunani yarinyar bata fi Hidaya ba. Yarinyar nan fa tana da hankali kuma ba zan taba bari tayi miki wani abu mai kama da raini ba. Ni wallahi tun farko na faɗa mata kuma zan sake jaddada mata irin muhimmancin da kike dashi a wajena bazan taɓa ɗaukan wani abu na rashin dai-dai akanki ba indai tayi miki." Murmushi mai ciwo Mami tayi sannan tace.
"Allah ya ƙara mata hankalin." Bata jira ya sake cewa komai ba ta miƙe tana faɗin.
"Barina haɗa maka abinci kaci." Miyau ya haɗiye yana jin babu daɗi, ji yake kamar dama bai ɗauko maganar auran nan ba, amma tunda ya riga ya ɗauko kamar yazama dole ya ƙarasa domin gidansu ba ƙaramin gida bane bazai iya maida iyayensa dashi kansa ƙananun mutane ba, bazai so yau ace anzo neman auran Hidaya sai magana ta kankama ace anfasa ba. Shiryawa yayi ya fito kamar yanda Mami ta saba shirya masa abinci haka tayi bayan ya zauna tayi serving ɗinsa tafara ƙoƙarin barin wajan, cikin sauri ya kamo hannunta yana faɗin.
"Dawo ki zauna dan Allah karki bari yaran nan su fahimci wani abun tsakanin mu." Cikin ƙaguwa da yanayin yanda Abba yake nuna kamar tana masa wani abin rashin kyautawa tace.
"Akwai wani abunda nake maka na rashin dai-dai ne da zasu fahimci wani abun?"
"Babu ko ɗaya amma ai ba haka kike yi min ba, yanzu ina ganin sauyi." Ajiyar zuciya tayi sannan tace.
"Ai ba zuciyar ƙashi ne dani ba Abba da zakace zakayi aure and then kayi expecting ɗina nazama kamar babu komai ba, kawai kabani lokaci komai zai dawo dai-dai in sha Allah."
"Allah ya yarda." Abba ya fada kamar wani karamin yaro. Mami ta dawo ta zauna badan ranta yaso ba. Abba ya ninka kyautatawar da yake yiwa Mami sakamakon bai son Mami taji wani rashin daɗi ko taga kamar zai canja saboda auransa. Duk wani abunda Abba yakeyi ba wani burgeta yakeyi ba kawai dai tana tausar zuciyarta ne saboda ta fahimci yana iya bakin ƙoƙarinsa wajan ganin yayi adalci a komai yakeyi hatta da kayan aure iri ɗaya sakk yayi musu colourn akwatinan kawai ya banbanta, sannan ganin ta kwantar da hankali yasa komai zaiyi saiya nemi shawararta. Mami takan daure zuciyarta tabashi shawara gwargwadon iyawarta, Hidaya ma daure ranta kawai takeyi saboda Maminta ta gargaɗeta akan karta yiwa Abbanta magana domin wannan ba maganar da zata shiga bane ba dan ba huruminta bane. Hidaya daure zuciyarta tayi amma har itama tana taya Maminta kishi. Bikin Abba sai ƙaratowa yakeyi saura 2weeks aka fara gyaran sashin da Amarya zata zauna wanda yake gefen na Mami dama shi ba'a kammalashi ne tuntuni dake basufi 6month da dawowa sabon gidan gabaki ɗaya ba.
Daga wajansu Abba babu wani abunda akayi amarya ce tayi events amma Abba bai halarta ba duk da cewa taso yazo amma ya nuna hakan bazai yiwu ba domin yana gudun duk wani abunda zai taɓa ran Mami a wannan auren, shi yanzu duk wani abunda zai sakata rashin jin daɗi kaffa-kaffa yakeyi dashi. Anyi biki angama babu wani tashin hankali sai ƴan ƙananun abubuwan da ba'a rasawa a wajan mata. A ranar da aka kawo Amarya Abba ya haɗasu itada Mami bayan baƙi sun watse yayi musu nasifa mai cike da faɗa da gargaɗi ya gwadawa Amaryar bai son ko da wasa ta raina Mami ya gwada mata muhimnancinta sosai sannan sukayiwa Mami sallama suka tafi. Tunda Abba yafara zancen aure Mami bata samu tayi kuka ba sai a wannan daren. Auransu tsawon shekara goma sha takwas bata taɓa tunanin zataga wannan ranar da Abba da wata mace ba sai a wannan rana data ga da gaske Abba yatafi kwana da wata macen ba ita ba. Bayan tayi kukanta ta tashi tafara Qiyamul laili tana kaiwa Allah kukanta ya bata dauriya da haƙuri, juriya da dangana. Cikin ikon Allah kuma tasamu bacci ya ɗauketa akan sallayar. Kiran sallar asubahi ne ya tasheta, bayan tayi sallah ta daure ta fito ta shiryawa yara breakfast domin zasuje hadda sannan ta shirya abincin Abba da amaryarsa. Sai 10am kafin Abba yafito daga sashin Amarya Mami daurewa kawai takeyi domin Abba koda wasa baya kaiwa irin wannan lokacin a gida duk dai yanda akayi da ɗa namiji saiya nuna shi ɗa namiji ne ko kunyar idon yaransa Hidaya da Nasir da suke gida (Dayqke su sungama Haddarsu) baiji ba ya hantse a sashin amarya har 10am haka yafito yana wani murmushi ga dukkan alamu yana cike da annashuwa wacce ta kasa ɓoyuwa. Mami kuwa kauda idonta tayi daga gareshi bayan ta gaidashi sannan tabashi breaskfast ɗinsu, zama Abba yayi a kan kujera alamun yana son fara yiwa Mami hira, miƙewa tayi tabarshi a wajan sakamkon fuskarsa dake cike da annuri bazata iya ganin wannan farin cikin ba wanda tasan duk a dalilin ya kwana da wata macen ne ba ita ba. Zaman palourn ne yayiwa Abba babu daɗi kasancewar shi ɗaya yake zaune abincin ya ɗauka yawuce sashin Amaryarsa.
Wata Huɗun farko na auren Abba ba ƙaramin haƙuri Mami tayi ba domin ɗauki sosai Abba yake nunawa akan amaryarsa, kulawar da yake bata abun har yaso yayi yawa gani takeyi kamar lokacinta bata samu wannan kulawar ba kasancewar yanzu baza'a taɓa haɗa cikar kamalar Abba da lokacin farkon auransa ba. Kuma yanzu ya ƙara sanin darajar iyali yasa yake bawa amaryarsa kulawar da mazauna tare dashi suke gani kamar yana nuni da ya ɗauketa da muhimmanci fiye da abubuwa da yawa a rayuwarsa. Hidaya idan ta kalli Amaryar Abbansu ƴar ƙarama a'ido baza'a taɓa cewa ta girmeta ba kuma Abba ya bi duk yawani rikice a kanta sai ta ƙara jin bazata taɓa iya auran saurayi da budurwa ba, ta gwammaci ta auri koda wanda bai haifeta ba har indai zata samu kulawa da muhimmanci irin wanda Abbansu yake bawa anaryarsa dan ta lura har indai namiji yayi shekaru da yawa yafi riƙe mace da muhimmanci. Sai da Abba yayi 4months da aure kafin abubuwan suka fara saisaita. A tsakanin wannan lokacin ba ƙaramin haƙuri Mami tayi ba ita kaɗai tasan abubuwan datame ƙunsa cikin ranta. Sauƙin ta kawai shine da yawan abubuwan yarinyar taga batada rashin kunya tana girmama Mami sosai sannan kamar yanda Abba yafaɗa tana da hankali sosai, daɗin daɗawa Mami takama girmanta bata bada wata ƙofa da yarinyar zata rainata ba. Ko shi kansa Abba baya samun sakin fuskar daya kamata a wannan lokaci bare Amaryarsa. A hankali ahankali komai yake dawowa dai-dai har aka gama cin amarci Abba yadawo normal da yin rayuwarsa. Mami dake zaune dashi tasan komai ya dawo dai-dai sai abubuwan da ba'a rasawa amma a idon su Hidaya har yanzu Abbansu yana nan da soyayyar amaryarsa....
________
Dawowar Hydar kenan daga school bayan ya ajiye Hidaya a gida yana ƙoƙarin shiga sashinsa yaji an riƙe masa hannu. Juyawa yayi idonsa yakai kan Farouq dake ɓalɓala masa dariya. Ajiyar zuciya ya sauƙe yana kallon Farouq ɗin ga wata irin soyayya da Farouq din yake yiwa Hydar wanda shi kansa Hydar ɗin har mamakinta yakeyi ganin Mahaifiyarsa bata iya ɓoye rashin soyayyarsa idan bawai a gaban Takawa suke ba. Kawar da kai Hydar yayi a lokacin da Farouq yake jijjiga hannunsa cikin harshen fulatanci wanda mahaifiyarsa tafi amfani dashi yace.
"Hamma Barka da dawowa." A hankali Hydar ya zare hannunsa daga cikin na Faruq ya dubi gefen masu kula da Farouq suna tsaye can a gefen su dama ya tabbata tare suke don Farouq bazai taho har wajansa shi ɗaya ba. Cikin bada umarni Hydar yace suzo su ɗaukeshi su tafi dashi, amma ina, ƙanƙameshi Farouq yayi yana girgiza kai kamar zaiyi kuka yake faɗin.
"Hamma dan Allah yau karka koreni kaji ni nace su kawoni wajanka." Ajiyar zuciya Hydar ya sauƙe yaron yabashi tausayi kullum yazo saiya koreshi kuma hakan ba hanashi dawowa, wucewa ciki Hydar yayi wanda hakan ya nuna cewa ya aminta. Farouq ya shigo da gudu Hydar kuma yabishi ciki yashiga yana murna, barinshi Hydar yayi a palourn ciki yayi wanka, harya fito Farouq yana zaune yana kallo yana ganin Hydar yafito ya faɗaɗa fara'arsa. Hydar ya kauda kansa gefe yace.
"Tashi kaje kar a nemeka kaje ai maka faɗa." Girgiza kai Farouq yayi Hydar ya ɓata rai yana faɗin.
"Idan baka tafi ba bazan barka ka sake shigowa ba." Miƙewa Faruq yayi badan ranshi yaso ba yafara ƙoƙarin fita dan bai son Hydar ya hanashi sake shigowa wajansa, wani irin tausayin yaron ya kamashi gabaki ɗaya bai son yana associating kansa da yaron saboda mahaifiyarsa bata son alaƙarsu ba ko kaɗan. Kiran sunansa yayi a hankali yace.
"Farouq." Da sauri Farouq ya juyo domin Hydar bai cika kiransa ba kwata-kwata. Murmushi yayi yana jin daɗi Yayansa yayi masa magana. School bag ɗinsa daya ajiye akan kujera ya janwo, cikin chocolate ɗin da yake sayawa Hidaya wanda a koda yaushe ba'a rasasu a cikin jakarsa ya ciro yabawa Farouq ɗin. Cike da murna Farouq ya dawo ya amsa yana jin dadin kyautar da Yayan nasa ya yi masa. Ba wai dan basu da chocolate din ba, a'a yaji dadi da ta kasance daga hannun Hydar ta fito. Tun daga wajan ya buɗe yafara sha har yafita zuwa wajan masu kula dashi.
Hydar yana zaune akan kujera Tani ta shigo, Tani itace wacce Ummi tabar amanar Hydar a hannunta a cikin masarautar kuma Tani ta riƙe amana sosai domin ita ke kula da komai daya shafi Hydar ta kasance masa kamar Uwa haka ta zame masa. Tani tana iya bakin ƙoƙarinta wajan ganin Hydar bai nemi wani abun yarasa ba ko abincinsa bata bari wata ta taɓa domin tasan masarauta a cike take da ƙalubale iri-iri akwai abubuwan da suke faruwa da ba'ayi zato ba koda yaushe sai an kasnace cikin kulawa da taka tsantsan. Ido yana kan kowa musamman ma Hydar da sam baida masoya a cikin masarautar, ko Familyn mahaifinsa ba sonsa sukeyi ba. Ƙarasowa Tani tayi ciki tana faɗin.
"Magajin gari an dawo? Barka da dawowa."
"Eh Yawwa." Kawai Hydar ya faɗa a takaice.
"Kaci abinci ko akawo maka nan magaji?"
"A'a banciba fita zanyi ma bansan yaushe zan dawo ba idan na dawo zanyi magana idan ina buƙata." Toh Tani ta amsa sannan ta koma shi kuma ya miƙe ya shiga ciki ya shirya ya fice. Wajan Mai martaba yafara zuwa sai la'asar kafin yabar wajan kai tsaye gidansu Hidaya ya wuce.
_________
Makeken gidane wanda ana ganinsa za'a tabbatar gidane na Babban wani ɗan siyasa wanda yakama ƙasa da hannunsa. Motaci ne guda biyu suka tsaya bakin gate ɗin gidan suna danna Horn domin sanar da zuwansu a bakin gidan duk da kuwa da akwai CCTV camera a bakin gate da gefen gidan da suke nunawa securities duk masu zirga-zirga. Bayan wani security yafito sanye da uniform da wata doguwar bindiga a maƙale a gefen kafaɗarsa wanda yake nuni da mai gadin gidanne ya dubasu sannan ya koma da sauri ya buɗe gate din. Gabaki ɗaya motocin suka danna cikin gidan. A parking lot sukayi parking sannan aka buɗe motar dake gaba. Fitowa yayi ya buɗe ƙofar baya a lokaci guda Fulanin Sarki tafito hadimarta ce tafito riƙe da jakarta a hannu suka shige ciki. A Babban Palourn gidan aka sauƙesu. Wata matace tafito wacce alamu ya nuna itace matar gidan daga yanayinta zuwa suturar dake jikinta sune zasu tabbatar maka da hakan. Tana shigowa palourn ta faɗaɗa fara'a tana faɗin.
"A'a fulanin sarki barka da ƙarasawa." Murmushi Fulani tayi sannan tace.
"Yawwa dai barka Giwar Ciroma fatan na sameku lafiya?"
"Lafiya Ina Farouq?"
"Farouq yana makaranta zuwa jimawa zasu dawo." Mai aiki ce ta fara shigowa da ruwa a hannunta ajiyewa tayi ta koma ciki sannan Wacce Fulani takira da Giwar ciroma ta dubi Fulani tace.
"Yanzu yallaɓai yake sanar dani zuwan naki shiyasa ba'a tanadi komai ba ga ruwa nan kufara sha kafin atanada muku abun motsa baki."
"Babu komai na kwana biyu ina saka rana zanzo gashi ina son magana da Yaya shiyasa yau na daure nace bari nazo na jirashi idan yasan ina nan zaune zai juyo da wuri."
"Aiko kinyi dabara don yanzu yallaɓai baicika dawowa da wuri ba amma na tabbata zai dawo har indai yasan kina jiransa" Cewar Giwar Ciroma. Hira suka farayi har aka kira sallar azahar dama lokacin da Fulani ta iso sha ɗaya ta gota. Sallah Fulani tayi sannan suka koma sukaci gaba da hira domin sukan daɗe basu samu lokaci irin haka ba kasancewar kowacce a ciki a halin yanzu matar wani (matan manya) wanda ba kasafai suka cika fita ba saida kwakkwaran dalilin.
________
GOVERNMENT HOUSE
SSG OFFICE
(Secretary to State Government)
Dai-dai lokacin da Agogon office ɗinksa ya buga ƙarfe biyu na rana ya ɗaga kansa ya kalli agogon, ajiyar zuciya ya sauƙe alokacin da aka fara doka kiran sallah a masallacin dake cikin government house ɗin. Yaci gaba da aiki cikin gaggawa domin ya kammala wanda yake gabansa ya fita zuwa masallaci sannan yasan Fulani tana gida tana jiransa. ALIYU UMAR TURAD shine rubuce a jikin allon dake kan teburin ofishinsa. Bayan yayi sallah ya dawo a mintunan da bazasu gaza cikin hour ɗaya ba ya kammala komai ya turasu ofishin governor sannan ya nemi muƙarrabansa domun su shirya fita daga office din. Cikin ƙanƙanin lokaci aka shirya fita kai tsaye suka kama hanyar gida.
Fulani suna zaune da Giwar Ciroma har a lokacin hira sukeyi sukaji shigowar Motocin Ciroma. Faɗaɗa fara'a Giwar Ciroma tayi sannan tace.
"Kinji yallaɓai ya dawo koh? Dama nasan da wuri zai bar ofis har indai ya tabbatar kina jiransa." Murmushin jin daɗi Fulani tayi tana mai farin cikin yanda Yayanta yake ɗaukar komai nata da muhimmanci. Kai tsaye Ciroma sashinsa yawuce Giwarsa tatashi ta nufi sashin tsawon 20minute Fulani ta ɗauka a zaune ita ɗaya sannan Giwar ciroma ta dawo,
"Yallaɓai yana jiranki a palourn sa." Ta sanarwa Fulani. Babu ɓata lokaci Fulani tatashi Giwar Ciroma tayi mata jagora har izuwa ƙofar palourn sannan ta juya ta koma. Babban palour ne sosai daya ƙawatu da kayan alatu sannan jikin wall na palourn gabaki ɗaya a manne yake da hotunan Ciroma dana Takawa. Da Murmushi Fulani ta ƙarasa ciki ta zauna a kujerar da take facing ɗinsa cikin girmamawa ta gaisheshi ya amsa sannan ya ɗaura da faɗin.
"Ina aka baro Abbana?"
"Dake bai dawo daga school ba shine kawai sai na taho abina."
"Ahh lallai Abba zaiyi fitina idan ya dawo bai ganki ba." Murmushi Fulani tayi sannan yacigaba da fadin.
"Fatan komai dai lafiya?" Canja fuska Fulani tayi cikin yanayi da yake nuni da tana a cikin damuwa tace.
"Yaya kaima dai kasan abunda yake tafe dani, akan Takawa ne ga dukkan alamu Hydar yake son daurawa akan karagar mulki dan kuwa ko soyayyar yaron baya iya ɓoyewa a cikin ransa, kowa yasan irin banbanci da yake nunawa kai kanka na tabbata bazaka kasa jin wani maganganu akan hakan ba. Tayaya za'ace yanzu sarauta tabar hannunmu ta koma na waɗan su ba mu ba? Hydar fa ba ɗan cikinmu bane mahaifiyarshi ba ma ƴar nan bace tayaya za'ace yaron daya fito daga wani tsatso shine zai mulkemu a nan gaba?" Murmushi Ciroma yayi sannan yace.
"Yanzu Hajiya Zulaiha shekarun Hydar nawa?"
"Ina tunanin yakai 17 years." Kai ya jijjiga sannan yace.
"Abbana Fa?" Cikin rashin fahimtar abunda yake nufi tace.
"9years, amm..." Hannu ya ɗaga ya dakatar da ita da faɗin.
"Har yanzu da sauran lokaci kafin ace kin fara damuwa akan wannan lamarin, ki koma gida ki kwantar da hankalinki In sha Allah komai zai tafi yanda kikeso." Fulani tasan Yayanta bai taɓa bata shawarar da bata ɓulle mata ba, kowace shawara yabata sai taci ribarta amma tayaya zaice ta koma tayi shiru? Shin wannan zancen yin shiru ne?
"Yaya idan mukayi shiru yanzu gaba fa?" Nisawa yayi sannan yace.
"Hajiya Zulaiha kenan, toh koda wasa kar kiyi wannan zancen a gaban Takawa ko a wajan da zai kai kunnensa, dan kin tabbata cewa dole sai Takawa baya raye ɗaya daga cikinsu zai hau karagar mulki koh?" Kai Fulani ta gyaɗa Ciroma yacigaba da faɗin......
#WATA ALAƘA
#ZEEYY BAWA
#STYLISH BCH
#YAN TAGWAYE...