Free chapter · Read without an account

Chapter 06.

by JamilaUmarJanafty · IDAN AN CIZA..!

*IDAN AN CIZA..!*


*Wattpad:Jamilaumar315*

*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*Mallakar:Janafty*


*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*


*Page 6*


Mu'azzam bai shigo gidan nan ba sai bayan la'asar Hibba har ta gaji da jiransa, sanda ya shigo har lokacin Jummai tana bangaren Inna Meri ba ta tafi ba daman Mu'azzam ɗin take jira ko za ta samu kuɗi a hannunsa.

Tsaraba kuma sauran wanda ya rage na bangaren Inna Meri ta raba gida biyu ta ba ta rabi, daman dankali ne sai wake da garin rogo, sai siga da ya kan zo da shi a raba ma yan gida da makota.


Turamen zani guda biyun da ya zo da shi yace ɗaya Inna Meri ɗaya kuma Magajiya kuma an kai mata nata amman a inda Mariya ta sauke kayan kallon banza ta yi musu ta kauda kanta nan suka kwana kuma ba ta kauda su ba, ballantana ta ga abin da ke ciki. Ita babban bakincikin ta ita ce mace ta farko da ta auri Danjuma a matsayin saurayi da budurwa tun ya na matashin sa, amman yau daga karshe ita ce koma baya a cikin gidansa. A ce har wata banzan bassakwata ta zo ta fita matsayi aciki gidanta da tun tana da kuruciya take cikin shi. Sannan karin takaicinta gabaɗaya inna Meri ta siye kowa na gidan da kirkinta, sannan ƴaƴan gidan masu kuɗin duk ta tattare su a ɗakinta ita sai abin da ta raba ta aiko mata da shi.


 Ai in da gaskiya acikin lamarinta Mu'azzam ɗan Danjuma ne, ba ita ta haife shi ba in ta rike kayan da AGOLAN ɗanta ya kawo mata tana kan daidanta, amman na wajen Mu'azzam ko na wajen Amina ko Halima ba ta da hakki a kansu tunda ba ita ce uwar su ba, Magajiya duk ta manta lokacin da uwarsu ta rasu da Ɗanjuma ya ce ta rike su tsalle ta da ka ta ce ba za ta iya rike ƴaƴan wata ba. Itama nata sun isheta duk ba ta duba wannan ba sai yau da suka zama wasu take tunanin ba a yi mata adalci ba.

 Tana tsakar gida tana jajjagen kayan miyan abincin dare da za ta ɗora Mu'azzam ya shigo gidan cikin shigan kananun kaya gefe ɗaya key ɗin motarsa wata bakar Jeep katuwa ne a hannunsa yana tafe yana kaɗawa shi fari ne sai dai bai kai Mansoor tsawo ba da ka ganshi ka ga Baba Danjuma saboda suna bala'in ɗibar kama da shi sosai.


 Cikin ladabinsa ya gaisheta kamar yadda ya saba shi dai ta na amsa masa cikin sakewa ba kamar ɗan uwansa da ta ce gaisuwan reni yake yi mata. Har ya gota ta zuwa bangaren Inna Meri tana kallonsa ji be sa yadda ya zama kato ya yi kiba saboda ya samu duniya. Kwallah suka cika mata ido, kaf ƴaƴanta ba mai jin daɗi a gidan auran sa, har gwara ma Zuwaira akan Jummai ita Jummai ai kullum a gida a ke ba ta, ba ta kawo ma uwa ba. Sai dai ta bi ta karɓe Auwalu ne Namiji babba shi kuma ya ƙi karatu sai yanzu take jin haushin yadda ta zura masa ido ya ƙi makaranta in da yau ya yi karatu da Meri ba ta isa ta rika mata famkama da kudin su Mu'azzam ba, su ma ai da karatun su ke takama, ba za ta manta yadda Danjuma ya rika fama da shi akan karatu ba ya ki yi, Ita kuma ta ɗaure masa kugun yin abin da ya ga dama ga shi nan daga karshe sai buga bugan gini ga shi ya yi aure ya tara Iyalai shima fama yake yi da kansa. Saddiqu ne bai yi aure ba har yanzu ya na can garin Ikko ya na neman kuɗi amman sai ya shekara bai zo ganin gida ba sai dai a waya sai sako da ya ke yi musu wani lokacin, shima ba sosai ba tunda Auwalu ya fi shi tausayin iyaye shi kawai domin ba shi da shi ne.


 Mariya ce ta rage a gabanta ita kuma ai ba ta ɗawainiyarta daga karatu har bangaren Surutu ƴaƴan Meri sun ɗauke mata wannan bangaren kuma duk abin da take so suna yi mata ko jiyan ta ganta da hijabi sabo da takalmi ta zo ta na nuna mata da cewa matar Mu'azzam ta kawo mu su ita da Walida, ta san suna kokari amman bakin cikinta ace ƴaƴan Meri ke taimaka mata to na yaushe kuma in taci ta sha su ne, tunda yanzu Ɗanjuma ba kasafai ya ke wanzanci nashi ba, ba kuma kamar a shekarun baya da ya yi suna tunda abun na su na gada ne ba haya ba.

 Duk da tuntuni bala'in magajiya ya sa aka raba girkin bangaren har yau har gobe kayan abinci biyu a ke rabawa, ita rabi Meri rabi ciki har ta san ma sauran ƴaƴanta

Kuma har gobe komai in Inna Meri ta dafa sai ta aika mata da shi sai dai in taki ci, ta bar shi nan Mariya ta ɗauka ta cinye. Har ta gama jajjagen ta tunanin yadda rayuwa ta zo mata ba yadda ta yi tsammani ba da gawayi yanzu suke amfani ta fito da murhun gawayin tana kakkabewa dagacan shashen ta jiyo muryan Inna Meri na faɗin.


 "Ɗan Inna ba za ka tsaya ka ci abinci ba?

Ɗanwake Walida ta yi saboda kai."


Ta na jinsa ya ce"Sai na dawo Inna, in na tsaya yamma za ta yi."


 Ƙaramin tsaki taja. Tana jin wani irin takaici a kasan ranta, Mariya ta ke jira sai ta mata bugun tsiya Jummai ma tunda ta shige har yanzu bata kara lekowa ba kyafci ta yi ita kaɗai ta na girgiza jikinta daga gani za ka san Magajiya ta iya bala'i sannan cutar hassadan dake damunta ne ya sa har gobe ta kasa ganin alherin ƴaƴan Meri ne suka lulluɓe rayuwarta. Ta koma ɗaki kenan taji fitowarsu da mganarsu zuwa shashenta ta ji muryan Jummai na faɗin " Mu'azzam ka taimaka min yara nan duk ba sa zuwa makaranta daga bokon har islamiyan an kore su." Ba ta ji dai me ya ce ba ta dai ji Jummai na ta godiya kamar zata kwanta masa, baƙinciki ya kara cikata ita da ya kamata ya'yanta su ba da, su ne yau za su koma yan maula suna roko a na ba suna godiya.


 Muryan Hibba taji kamar za ta shigo ɗakinta yasa zaraf ta ɗaga labule ta fito sai suka ci karo da juna cikin shirinta ga Walida rike da ƙaramar akwatinta sai Mariya dake dauke da Junoir, gabaɗayan sune har da Bintu da su Amina suma cikin shirin fita kila duk tare za su tafi ko kafin ta samu damar mgana Hibba ta rankwafa cikin ladabi tana Faɗin " Sai anjuma Magajiya yau a Tudun wada zan kwana sai jibi in sha Allahu."

Kadahan kadahan ta ce"Allah ya kaimu, ku gaida gida."


 Mariya ta kallah cikin jin haushinta Mu'azzam kuma ya fice lokaci ɗaya yana fadin"Ku fito mu tafi in na kai ku daga can zan biya wani waje ne."

Amina ce ta bi shi tana faɗin" Kai Mu'azzam ka ce mu zauna kenan ba za ka dawo da mu ba?. Sun fita can waje suna magana su ma su Binta sai suka rufama musu baya, Mariya ta kallah da ke shirin bin su a fusace ta ce"Ke ina za ki je?

Cikin tura baki ta ce"Za mu raka Anty Hibba can ne, Yaya Mu'azzam zai dawo damu a motar sa."


 Wani irin harara magajiya ta sakar mata kafin ta ce"To ki fita ki gani,wlh sai na yi kasa kasa dake acikin gidan nan"

Daga haka ta duka tana zuba gawayi acikin murhun dake gabanta lokaci ɗaya tana kara sakin tsaki, Mariya ba ta da yadda za ta yi dole ta fita waje ta mika ma Bintu Junior ta ce Magajiya ta hana ta zuwa, ba wanda ya damu sanin halin Magajiya duk wanda ke rayuwa a gidan wanzamai ba ma acikin gidan ba har makota su san wacece ita a haka ma ta rage a shekarun baya in ta fara bala'i da masifa sai makota sun ji acikin gida kuma sai su Gaje sun cika tsakar gida suna bata hakuri, abin da ba a taɓa ji ba shine nuryan Inna Meri tana tanka mata daga ita har Baba Danjuma masu hakuri ne da kau da kai daga sha'aninta.


 Da Mariya ta dawo haka ta rika jaraba tana zaginta, Inna Mari na cikin bangarenta ita da Jikokinta ƴaƴansu Amina tunda za su dawo ta nan kafin su wuce gida sai suka bar mata yara a wajen ta, sai ta yi kamar ta leka ta yi mgana sai kuma ta fasa sanin Halin Magajiya yanzu nan sai cibi ya za ma kari, ta kuma san ta na zagin mariyan ne saboda ta zo bangaranta to ta isa ta raba ta da yan'uwanta ne? har ƴaƴan Jummai ta jii an zagi ubansu an ce su da uwarsu marasa zuciya, daga nan Jummai ta tarkata ya'yanta zuwa gida. Sai ta koma kan Mariya har su Mu'azzam suka dawo tana jarabarta.


 Inna Meri na bangarenta t na ba ma yan biyun Bintu da suka saka rigiman koko da za su sha, sai da ta mike ta dama musu sannan ta zauna ta a zaman ba su, sauran ma suna gani suka ce suma sai sun sha, gabaɗaya yaran sun zagayeta Sanda suka shigo Bintu da mgana a bakinta faɗi take yi.

"Innarmu wai me aka yi ma magajiya take ta bala'i haka?

Inna Meri ta ce" Ina zan sani? Tun fitan ku ta ke ta yi ta gama zagin Jummai da Jummai ta tafi gida ta koma kan Mariya ina ga bai wuce dai yinin da ta yi a bangarena tare da ku." Mu'azzam ya samu waje ya zauna yana Faɗin"Har yau dai Magajiya ba ta sauya ba? Wai bakin ta baya ciwo ne?

Walida tace"Inna mariyan ma ta so bin mu Magajiyar ta hana ta zuwa."

Inna Meri ta ce"Bakomai wata rana sai labari, zata daina." Yaya Halima ta zauna a kasa kusa da Inna Mari ta bangaren dama Amina ta zauna a bangaren hagu, Bintu kuma ta zauna kusa da Mu'azzam Walida kuma na kofar daki ta yi tsaye ba ta zauna ba. Yaya Amina ce ke faɗin"Inna ai ban tunanin akwai ranar da Magajiya zata sauya. Har Baba dai ya gaji da halinta ya saka mata ido."


 Bintu ta taɓe baki kafin ta ce"Dan dai ta samu daga Baban har Innan salausalau ne da irin mu ne da tuni ta raina kanta"

Inna Mari ta aika mata da dakuwa tana Faɗin"Mungode ja'ira, ai Annabi cewa ya yi duk wawaye ya gani a Aljannah ba masu wayau ba, kum rayuwar nan duka nawa ta ke? hakuri ribar zaman duniya da na biye mata ai ba ta taɓa biyo ni bangarena ta yi min wani abu ba, ai hausawa suka ce kulawa yabawa ni dai Allahu shi ne shaida na tunda aure ya kawo ni gidanan nake zaune da kowa lafiya, Alheri ne tsakanina da kowa acikin zuciya ta ba ni da niyar cutar da kowa, kuma ina so ku saka ranku a duk in da kuke ku rike gaskiya da amana sannan ku nufi wanda ma ya nufe ku da sharri ku saka masa da Alheri, ku ma sai ku cigaba da ganin Alheri a rayuwar ku har bayan ran ku."

A yadda suka zagayeta za ka fahimci akwai kauna ta uwa da abin da ta haifa a tsakaninsu, Mu'azzam ya yi mirmishi kafin ya ce" Shi ya sa har gobe ba ni da kamar ki Inna ta, Allah ya kara miki lafiya da tsawon kwana."


 Suka amsa da Amin gabaɗayan su, Itama ta amsa da Amin tana faɗin" Nima ai bani da kamar ka ɗan Inna Allah ya cigaba da tsare min kai a duk inda ka sanya kafa Allah ya yi maka jagoranci.' Cikin bayyana farinciki ya amsa da Amin lokaci ɗaya yana kara faɗin " Inna in na samu kuɗi zan kai ki Makka kafin ki mutu ke da Baba za ku je ziyara dakin Allah in sha Allahu."

Gabaɗayansu suka amsa da In sha Allahu Allahu ya sha.


 Inna Meri kamar ta yi kuka ta ce"Amin Amin Allah yasa muna da rabon zuwa, Baban Inna shima kullum zencen sa kenan Allah ya cika muku burin ku na Alheri"

Mu'azzam ya ce"Mun fara magana da shi, Inna suprice za mu ba ku in sha Allahu."

Yan'uwan suka taya Inna da amsawa da cewa Allah ya nuna mana lokacin.

Hira suka cigaba da yi suna hirar su Walida ta je ta zubo ma Mu'azzam ɗanwake ya zauna yana ci lokaci bayan lokaci yana tsoma bakinsa cikin mganar ƴan'uwansa mata. Inna ya kallah sai faman wahala take yi da yara iyayensu na gefe suna hiran su ko ajikinsu.


 Cikin faɗa ya kalle su yana faɗin " Wai don Allah Nanny mai reno kuka mai da inna? tunda kuka zo gida nan ina lura da ku kowacce ta sauke ƴa'yanta sai Inna ke ta faman wahala da su."

Bintu ta ce"Ai sun fi son renin Innan ne ni fa ba domin Bashir ya ce a'a ba da tuni na dawo da su Hassan wajen Innanmu na gaji wlh." Hararanta ya yi kafin ya ce"Dole ki kwaso ki kawo mata mana tunda kin samu jaka ko ita ta ce ki je ki haihu."

rufe baki Bintu ta yi tana dariya Yaya Amina na gefe ta ce" Inna fa ke son kiriniyan yara nan, ko zuwa mu ka yi ba mu zo da su ba sai ka ji ta ce kuka bar ɗiyan ga a gida ba ku zo min da su ba"

Inna na yar dariya ta ce"Kyale su Ɗan Inna rai ne ya kaini, yau in da ba na raye wajen za su je? Wata rana ba za su ganni ba gwara su mori kakar ta su tun yanzu."

Har suna haɗaa bakin wajen faɗin"Ba yanzu zaki mutu ba Inna."

Yaya Halima ta karɓe da faɗin"Ita Inna daman akwai kiran mutuwa ana zaune lafiya."


 Mu'azzam kuma ya ce"Inna sai kin ɗauki ɗan Yaya Mansoor ko ƴarsain sha Allahu."

Inna ta ce"Allah yasa, amman na cire rai da ganin Auran Baban Inna, ganin auransa da ya'yansa ai sai mai yawan rai tunda na ga ba shi da niyyan auran kwata kwata."

Mu'azzam ya ce"In sha Allahu zai yi Inna mu ta ya sa da addu'a don Allah."

Inna ta sauke numfashi kafin ta ce"Addua'armu kullum ba ta yankewa a gare ku, Allah ya sausasauta masa wannan zuciyar ya sanya masa salama acikinta."

Suka amsa da Amin gabaɗayan su Yaya Amina tace"Nifa ina tunanin yarinyar nan ce har yau ya kasa cire ta acikin ransa."

Yaya Halima ta ce" kike gani? Yarinyar da ya zo ya tsani jin sunanta. Ranar Babansu Khairi na kallon labarai nake gaya masa Mansoor ya sota tun tana matashiyarta a zamanta hannun kakarta sai dai sun rabu da jimawa, itama fa ba ta yi aure ba har yanzu"


 Bintu ta ce"Ba ta yi aure ba mana, amman fa tana da kyau ga iya kwalliya ni dai wlh Saboda ita nake kallon tashar su har ga Allah tana burgeni kuma sun bala'in dacewa da Baban Inna."

Inna na jin su duk ba ta yi mgana ba sai da ta nisa kafin ta ce"Ba wanda yasan abin da ke zuciyarsa, ba na tunanin ita ya ke jira saboda ai shi ya fara yanke alaqa da ita ko bayan dawowarmu Mu'azzam kai ka faɗamin tana ta kiransa a waya ya ƙi ɗauka sannan shi ya yanke sauran alaqan da ta rage tsakanina da kakar yarinyar nan. Tun daga lokacin ban kara taka kafata gidan ba itama Hajiya ba ta kara nema na ba, abu ne ya riga ya faru sai a manta baya a fuskanci gaba kullum ya zo nan babanku zai zaunar da shi yana masa nasihan hakuri da rayuwa sai ya nuna kamar ya ji ammh sam Baban Inna ba'a gane in da ya dosa shi dai ƙwallon nan da ya saka gaba ita ya rike bansan kuma me yake tunanin ya mai da rayuwarsa ba."


 Inna Meri ta ƙarishe faɗa cikin bayyana damuwarta Yaya Amina ta dafa kafaɗarta lokaci ɗaya tana faɗin"Bakomai Inna, zai wuce in sha Allahu Baban inna zai yi aure har ki ga ƴaƴansa" Bintu ta yi karaf ta ce"To ai abun haushin ma ko budurwa ba shi da ita." Mu'azzam ya yi jim kafin ya ce"Ai ina jin tun bayan rabuwarsa da Fatima Baban Inna bai kara son wata mace ba, ban jin ma mata yanzu suna burgeshi ta sauya shi fa fiye da tunanin ku, yanzu haka abokan mu sun gaji da min korafi sun hakura ana gari ɗaaya sai su yi wattani ba su gan shi ba ya koma rayuwar kaɗaici abin da na fahimta har gobe abun na ranshi ya kasa mantawa ne."

Yaya Halima ta ce"Nima abin da nake tunani kenan, cire abun a ranshi zai taimaka masa wajen fuskantar wata rayuwar a gaba." Mu'azzam ya ce"Yau ai wajen sa zan kwana zamu tattauna Allah yasa ya bani damar haka."

Inna Meri ta amsa da Amin a samam labbanta har aka kira mangariba suna tattauna abubuwan da suka faru a shekarun baya ne.


 Kiran sallar Mangariba ya tada su Mu'azzam ya yi alwala zuwa masallaci su kuma matan suka yi na su agidan.

Yaya Amina ta fara tafiya tunda ta fi su nisa, Yaya Halima kuma daga baya Bintu dai har sai bayan Sallar isha'i da Baba Ɗanjuma suka dawo tare da Mu'azzam da Auwalu.

Har ɗakinsa ta bi shi suka gaisa Magajiya ke da miji sai kuma abin da Baba Danjuma ya gani ruwa ma Inna Meri ce ta kawo masa mai sanyi tunda tana da ƙaramin firiza a ɗakinta na Yaya Halima ne da mijinta ya siya mata Babba sai ta kawo mata wannan.

Sai da ya sha ruwan ya ji ka maƙoshi acikin ransa ya yi saka ma matar kirki irin Meri albarka yana tuna karamcinta a garesa tun na tsawon shekarun da suke tare.

ƴan Biyun Bintu suka hau jikinsa suna wasa yana dariya yake faɗin"Ku yi min a hankali kar ku ƙarisa ni domin na ga kuna ji da karfi." aka saka dariya gabaɗaya, Auwalu yace"In na kalle su sai na tuna yarinyar nan Bintu ai itama ta yi rashin jin mgana, ba domin Mansoor na tsawarta mata ba da sai Allah."

Bintu ta tura baki kafin ta ce"Haba Yaya Auwalu yaushe na kai yaran nan rashin ji."

Mu'azzam ya ce"Kin fa yi Bintu ai har gobe baki daina ba sai dai in yan abun naki ba su motsa miki ba."


 Tura baki ta yi tana faɗin"Baba ka gansu ko? Ka yi mu su mgana."

Baba Damjuma yace"Ku bari mana Fatima Bintu sunanta mai daraja ne babu ruwanta da rashin arziki."

Nan fa suka yi ta wasa da barkwanci har Bashir ya zo tafiya da Bintu gida Inna Meri tun ɗazu ta yi mata mgana ta tafi gida ta ce ita fa a kusa ta ke daga zuwa gida Inna ta fara cewa ta zo ta tafi, Ahalin tun safe ta zo ta riga kowa ma zuwa shi ne take cewa ba ta daɗe da zuwa ba Inna na koranta gida tunda ta ji haka sai ta kyaleta ta sanya mata ido da kila Baban Inna ya zo ne shi ne dodonta yana cewa me take yi har dare ba ta tafi gida ba? Jikinta na rawa zata haɗa Ƴaƴanta ta wuce tana tura baki iyaka dai ta kwana biyu ba ta zo ba in Inna Meri ta aika walida a duba ta sai ta ce tana nan lafiya ai Baban Inna ne ya koreta kuma a gaban inna ba ta yi mgana ba. Sha'anin Bintu ai sai ita ɓauɗɗiyar mace ce irin Mansoor wasu Lokacin suna da kamceceniya ta bangaren hallaya. Ko domin suna matsayin uwa ɗaya ne?


 Mu'azzam sai wajen tara da rabi ya bar gidan nan zuwa Tunfere gidan Mansoor daman ya tura masa sakon in bazai zo ba shi zai je Camp ya kwana gobe suna da morning trainig shi ya sa ya yi ma su Inna sallama da Baba ya wuce tare suka fito da Auwalu ya rage masa hanya ya sauke shi a gidan shi sannan ya wuce.

Lokacin da ya isa wayar Mansoor ya kira ya ce masa ga shi a waje, sai da ya ɗan ɓata lokaci sannan ya fito ya zo ya buɗe masa get ya shiga da motar Ciki ya yi parking ɗin ta kusa da ta mai gidan.

Yana tsaye a bakin falonsa daga shi sai gajerun wando, ba nepa akwai kuma zafi a garin shi ya sa ya zauna haka, bai koma ciki ba har sai da Mu'azzan ya buɗe bayan motarsa ya ɗauko karamar jakarsa ya shiga falon sannan ya maida kofar ya rufe ya bi bayan sa.


*******


Dukkansu sun sake wanka, Mansoor daman baya shiri da zafi sai ya yi wanka sama da sau huɗu a dare ɗaya.

A ƙaramar katifan Mansoor suka kwanta dukkansu, shi Mansoor filo bai dame shi ba sai ya ba ma Mu'azzam ya dora kanshi a saman matashin, daman ya saba kwana in dai ya shigo garin tuni ɗakinsu na samartaka na gida su ka bar ma Saddiqu yanzu shima yana ƙokarin siyan fili ne ya fara ginin muhallin da za su rika sauka shi da Hibba in sun zo garin.


 Suna kwance Mu'azzam na ta Juye juye Mansoor ya ce"Kana jin zafi ne? duba bayanka akwai mafita sai ka yi amfani da shi."

Mu'azzam ya ce"Gaskiya ya kamata ka saka solar tunda wutar nageria ta zama sai Allah ya kyauta." Kamar bazai yi magana ba sai can ya ce"Zan sa ka in sha Allahu"

Shuru ya kara biyo baya bayan Mu'azzam ya amsa masa da Allah ya sa.

Mansoor ya katse shurun da cewa" Ina Junoir? Mu'azzam ya ce" Suna Tudun wada can za su kwana sai jibi in zamu koma."

Kai Tsaye yace"Gobe da la'asar zan zo gida ka kawo min shi na gan shi."

Sai Mu'azzam ya amsa mi shi da toh kawai wayar Mansor din dake gefensa ya laluɓa ya ɗauka yasan password ɗin watan haihuwan Mu'azzam ɗin ne mabuɗin buɗe wayar Mansoor.


Yana buɗewa a fuskar wayar hoton Junior ne ya fara masa maraba wanda aka yi masa ne na cika 2yrs shi ya tura masa ya yi kyau yaron yana ta bangala dariya.

Mu'azzam ya juya ya kalli ɗan uwan da jini bai haɗa su ba amman ya zame masa wani irin ɗan uwan da babu kamarsa.

Cikin yar driya ya ce"Sai aka cire hotona aka sanya na Junoir har an gama ya yi na kenan Baban Inna?

Ya juya masa baya shi ya sa ba zai fahimci yanayin fuskarsa ba.

Kamar baya son mgana ya ce"E, kai ka girma yanzu."

Mu'azzam ya ce"Ni fa ban yarda ba, dole gobe Inna ta yi alƙalanci."

Har sai da yaji karan sautin dariyansa Lokaci ɗaaya ya juyo ya yi matashi da duka hannayensa idanuwansa na kallon rufin POP ɗin dakin cikin shakewar muryar da gajiya ta saukar masa ya ce" Hausawa suka ce abun cikin ƙwan ai yafi ƙwan daɗi Mu'azzam"


 Mu'azzam ya yi mirmishi bai yi mgana ba ma'adanan hotuna ya shiga yana ta kallo gabaɗaya hotunan shi ne na kwallo sai na yan Club dinsu sai kuma na Mu'azzam da suka cika wayar da Junoir sai hoton Inna Meri da Baba Danjuma da kuma nasu gabadayansu shekara biyu kenan da wata salla shi Mu'azzam ya matsa aka yi saboda tarihi kuma shi ya tura ma Mansoor din hotunan. Ba magajiya domin ta ce ba za ta yi ba, kowa dariya ya ke yi a hoton ban da Mansoor da Mu'azzam ya dafa kafaɗansa ya sunkunya da kansa ta wajen fuskarsa tunda Mansoor din ya fi sa tsawo.

Ya daɗe ya na kallon hotunan yana Mirmishi kafin ya wuce kaf ya bincike hotunan wayar har ya kai kan wani tsohon hoto. Su biyar ne acikin hoton kuma zai kai kimanin shekaru goma sha ɗaaya da ɗaukan hoton.

Mu'azzam bai manta wannan hoton domin hoto ne ma na kati aka yi snaping ɗin sa a waya ina zai manta Shagon Aci kwalba mai hoton yan gayu a anguwansu ta Arawa ya ke. Shi ne a tsakiya sai Ahmad a gefensa na dama hegensa na hagu sannan Nasir.

Makama da Mansoor suna da Tsawo sai suka tsaya agefe da gefe.


 Da ka gansu kasan an baya an sha gayu da ji da kai, Mu'azzam ya fashe da dariya shi kaɗai Mansoor ya kallesa kafin ya ce"Daman ka na da wannan hoton?

Ya faɗa ya na nuna masa hoton kansa ya gyaɗa kafin ya ce"Kai ka taɓa turamin shi."

Mu'azzam ya ce"Bari ko na tura ai na manta na tura maka ina ta neman sa ko wajen su Nasir ban samu ba suma ba su da shi, ina tunanin har na hoton duk sun ɓace mana."

Mansoor ya ce"Ni ina da su acikin tsoffin takarduna na makaranta"

Mu'azzan ya ce zai kai a wanke masa na Tarihi nan da nan ya ɗauko wayarsa ya tura lokaci ɗaya ya na faɗin" kalli wuyan makama kamar lagwani kyan shi a tura ma yarinyar da zai aura ta gan shi a haka."

Mansoor na jin sa bai yi mgana ba sai shi Mu'azzam ɗin ya cigaba da faɗin"Bayan sallah da Sati huɗu ne bikin Makama, in na zo sallah na koma sai bikin zan kara dawowa in sha Allahu."

A shake Mansoor ya ce" Allah ya kai mu."

Shi kuma Mu'azzam ya cigaba da bashi labarin shirye shiyen biki ya na faɗin su abokai sun ce za su shirya dinner

Mansoor ya ce"Makama ya bar Ustazan cin ne da zai yi bidi'a bikin sa.?

Mu'azzam ya ce"Gidan su yarinyar ke son haka ina ganin."

Gyaɗa kai kawai ya yi ba tare da ya yi mgana ba, Mu'azzam ke gaya masa za su yanke ko nawa ya kamata kowa ya ba da.


 Kai Tsaye Mansoor ya ce"Kar ku fara sani cikin yarintar ku, in na tashi zan turama Makama guddumuwata ba ruwana da wani sha'anin sakarcin banza shima dai kamar wani yaro."

Mu'azzam ya yi dariya kafin ya ce"To yaro ne mana, tunda yanzu zai yi aure kai ma ka bari ka ga yadda zamu raya bidi'a a naka bikin."

Wani kallo ya watsa ma Mu:azzam kafin ya kira sunan shi "Mu'azzam..!

Ya amsa da "Na'am'" yana dariya.

Sai kawai ya juya masa baya bai kara magana ba.

Ya bar Mu'azzam na mirmishi ya na tuna shekarun baya akwai wani abu da ya faru da ya kasa mantawa yasa sai da ya kara saka dariya. Da karfi Mansoor yace"Mu'azzam za ka fita falo ka kwana, junior ne kai da za ka rika motsin kwanciya?


 Mu'azzam ya tashi zaune yana faɗin"Wani abu na tuna ka tuna muna a yara in su Jummai su ka ganmu tare sai su ƙwace hannuna daga hannunka suna cewa kai mu ne fa yayyenka wannan ba babanmu ya haife shi ba.

Kai kuma sai ka ƙwace hannuna daga wajensu kana faɗin"Eh din ba Babanku ya haife ni ba, amman ai ɗakin Innata yake kwana take kuma bashi abinci saboda haka ya zama ƙanina ka tuna lokacin?

Mansoor ya Juyo ya na mirmishi shima lokacin yana dawo masa girgiza kai kawai ya yi, Allah sarki Kuruci dangin hauka.


 Mu'azzam ya koma ya kwanta yana cigaba da duba wayar Mansoor ya na yar dariya.

Sai dai ya bata fuska lokaci ɗaaya da ya gama bincike wayar bai ga hotonsa da uniform ba, kuma tare ya tura masa da hoton Junior cikin kufuluwa ya ce" Baban Inna ina hotuna na a office da na tura maka? Kai tsaye ya ce" Na share su."

Baki buɗe ya mike zaune yana faɗin "Ka share su kuma? To saboda mene?

Kai tsayen ya kara cewa"Kai ma kasan dalili."


 Mu'azzam ya yi tagumi kafin ya ce"A masu kakin ma har da ƙaninka ka tsana?

Mansoor ya yi masa banza kamar bai ji sa ba sai da Mu'azzan ya kara faɗin" kuma ai tun a wancan Lokacin kai kace na je na zama duk abin da nake son zama."

Mansoor ya yi shuru kamar ba zai yi mgana ba sai can ya mukusta ya gyara kwanciyarsa Lokaci ɗaya yana faɗin" A lokacin saboda ka matsa ne, amman ni har abada bazan so duk wani aiki mai sanya kaki ba, na tsane su har acikin raina saboda ƙakin su na basu damar cin zarafin mutane yadda suka ga dama." Mansoor ya faɗa ya na jin wannan abun da ya tokare masa kirji ya taso masa sama duk lokacin da ya tuna sai ya ji kamar ya fama damuwar da ya danne shekara da shekaru ne.


 Mu'azzam kuma ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"A ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, a ko'ina akwai na kirki akwai na banza" A tsawace ya ce"Kana gaya amin haka ko Mu'azzam? Ni ban ga na kirkin ba na banzan na gani, kuma da shi zan yi misali."

Kamar Mu'azzam zai yi kuka ya ce"Ni yanzu na banza ne Yaya Mansoor?

Sai ya kasa bashi amsa sai ma koƙarin mikewa zaune da ya yi ya sauka daga kan katifar ya mike da kafafunsa.

Shi kuma Mu'azzam ya b shi da kallo kafin ya ce"Saboda ita ne ko?

Saboda ita ce ka kasa mantawa da abin da ya faru da daɗewa Baban Inna."

Har ya kai bakin ƙofar tiolet sai ya Juyo ya na kallonsa cikin kaushin murya Ya ce.


 "Saboda ita wa???


 Kai Tsaye Mu'azzam ya ce" Saboda FATIMA! Itace silar da ya saka ka tsani masu ƙaki, itace silar rugujewar tuninaninka na zamo wa sojan kasar ka."

Ƙurama Mu'azzam ido ya yi yana jin wani abu a kirjinsa na wani dif dif, me ya sa zai ce saboda ita ne? Ba saboda ita ba ne.

Cikin ɗaga sauti ya ce"Ba Saboda ita ba ne Mu'azzam."

Yana direwa ya taso mai da cewa"To in ba saboda ita ba ne, saboda waye da zai saka har ni ba ka iya kallona da ƙakin yan sanda a jikina?

A tsawace ya ce"Saboda mahaifinta ne Saboda shi ne wannan MAJOR KABIR ɗin ne. Saboda shi ne komai ya ruguje."

Ya faɗa lokaci ɗaya yana tura kofar tiolet ɗin da ke ɗakin ya shiga da sauri ya kuma maida kofar ya rufe ta da karfi har sai ta yi ƙara bam!!.






*Janafty*


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.