Free chapter · Read without an account

Five

by Hauwau Shafiu · DUNIYA BIYU

*_Tarihi_*



Alhaji Badamasi da Alhaji Hamisu yan uwa ne uwa daya uba daya. Su biyu ne kacal wajen iyayensu, sun kuma taso cike da hadin kai, son juna da taimakon juna. Sun samu kulawar iyayensu dai-dai misali, sun kuma samu ilimi na zamani da na Muhammadiyya. Sun rabu da iyayensu tun a zamanin samartakarsu, sun rabu dasu cikin sanya albarkarsu da fatan alkhairinsu. 

Mahaifinsu Alhaji Sama'ila ya kasance ruwa biyu, mahaifinshi ya auri wata baturiya Janet da taje karatu a jami'ar Ikko, shi kuwa lokacin yana yan sana'o'inshi a can. Bayan sunyi auren, auren ya ki ya yiwu. Sunyi auren akan sharadin zata musulunta, sai bayan auren sannan ya fahimci dalilin da yasa ta aure shi, ashe da manufa biyu ta aureshi. Tana so ta samu takardar zama a Najeriya ce ta din-din-din. A cikin halin zaman doya da manja suka haifi dansu na farko Sama'ila. Yana da watanni takwas Janet ta sake samun wani ciki, nan rigimar da basu taba yin makamanciyarta ba ta tashi. Tace zata zubar da ciki, shi kuma yace bata isa ba. Rigima fa ta safe daban, ta yamma daban. Kwana uku suna kaiwa suna kawowa akan haka, ana hudu dai sai ganinta yayi a gabanshi. Ta fada mishi taje ta zubar da cikin da yake ta tayar mata da jijiyar wuya akai, don haka ya sama mata lafiya. A take ya dauki takarda da biro, ya dankara mata saki dai-daya har uku. Washegari sai sammacin kotu ya buga mishi kofa tun da safe. Taje kotu ta fadi karya da gaskiya, wai ya rabata da iyayenta akan zai kula da ita, kuma baya kulawa da ita din. 


Nan aka shiga kotu aka hau fafatawa, zamansu uku a kotun, da yake yana da shaidunshi, makotansu, akan duk irin dibar albarkar da take masa da batun zubar da ciki, alkali ya yanke hukunci. Dama bisarta ta kare, suka kadata kasar Landan. Shi kuwa ya tattara kayanshi gabadaya da dansu da tun a kotu ta fita tace ba zata rike shi ba, ya koma Katsina inda nan ne mahaifarshi. Ya samu wata bazawara ya aura. Allah bai kara basu wata haihuwar ba har ya rasu. 


Gabadaya Badamasi da Hamisu haka suka dauko jinin mahaifinsu Sama'ila. Haka zaka gansu jawur dasu, ko bayan sunyi aure sun hayayyafa, yawancin ya'yansu sun dauko jininsu, hakan yasa mutane suka fara kiransu da Turawa. Ko kwatancen gida ne, ka ji an ce gidan Turawa. Har lakanin ya bi su. 


Bayan rasuwar iyayensu, kowannensu ya kama sana'arshi yana yi. Shi Badamasi ya fara sana'ar sayar da kayan masarufi, Allah Ya daukaka mishi Ya sanya mishi albarka, nan da nan yayi arzikin shi yayi fice. Shi kuwa Hamisu ya kama sana'ar sayar da kayan sanyawa. Shago guda ya bude, ya zuba yadika, atamfofi, kayan sanyawa na maza da mata, shima nan da nan likkafa ta bude, ya fara zuwa kwatano yana saro kaya. 


Karayar arziki ta sameshi kai tsaye, lokacin daya auri Hajara (Hajja) da shekara daya. An saro kaya himili guda daga Kwatano, suka nutse a cikin ruwa. Ba ayi hakan da cikakkun watanni biyar ba, shagonshi na kaya ya kama da wuta, ba'a fitar da komi ba. Nan fa 'yan uwa da dangi suka mishi caa, akan ya auro musu mai farar kafa, yayi kunnen uwar shegu dasu, kasancewar shi mutumin da bai cika daukar gutsuri tsoma ta mutane ba. To da yake ma dan uwanshi mai yawan taimakawa ne, yana iyaka bakin kokarinshi wajen ganin cewa ya taimaka mishi. Sai dai da yake shi din mai zuciya ne da son neman na kai, baya karba daga gareshi haka siddan. 


Kusan a lokaci daya suka yi aure. Badamasi ya auri Fatima, wadda aka fi sani da Uwale, wata yar unguwar Kan Giwa. Watanni bakwai tsakani shima Hamisu din ya auri Hajara. Bayan karayar arziki ta samu Hamisu, haka Badamasi ya hada su su duka da matansu ya kaisu makka suka sauke farali. 


Hajara, da tun da suka dawo daga Makkah, sunanta ya koma Hajja Hajara. Babu wanda ya isa, hatta da yan gidansu ya kirata da Hajara gatsar, bata yanka mishi magana da gorin da suka fi karfin jin shi ba, nan da nan Hajja Hajarar ma ta bata, sai Hajja kawai. 

Haka take a zaune ita kadai, bata sayar da ko kullin gishiri sai Hamisu ya nemo ya bata. Idan aka yi rashin sa'a kuwa ta nemi abu a wajenshi bashi da halin yi mata, sai dai kawai ya rufe kunnuwanshi ya kuma kai zuciyarshi nesa. 


Gidansu Hajara gidan malamai ne, mahaifinta da manyan yayyenta maza, dukansu malamai ne. Mutane, kodayake hatta da shi kanshi Hamisu din, su kan yi zaton kasancewarta yar malam zata yi halin malam, amma ina! Hajara bata dauki komi daya dace ace yar gidan malamai tana dashi ba, halinta na daban ne. Son abin duniya ya rufe mata idanu, duniya ta rude ta, tsiwa da rainuwa sune manyan halayenta, bata ganin kan kowa da gashi har shi mijin nata, gwanda ma shi Badamasin tana raga mishi don kuwa yana da matukar cika ido. Amma matar shi? Yadda kasan kishiyoyi haka suke. Sam basa gani ido da ido. 

Gidansu ba wani mai nisa bane dana juna, amma fa su kan jima basu ziyarci dayansu ba. Duk kuwa ranar da Hajara ta je gidan Uwale ta dawo, to in Allah ya yarda sai sun sha rigima da Hamisu. Duk abinda ta gano a gidan, kalar kayan sanyawa ne, kayan kyale-kyale ko na ado, sai taje ta turke Hamisu tace lallai sai ya sai mata irinshi. Bai taba samun rintsawa mai dadi har sai ya bata kudin ta saya ko ya sayo mata irinshi sannan ne zai samu kwanciyar hankali. 


Ita kuwa Uwale sana'arta take yi hankalinta kwance, ba ruwanta da tsayawa jiran miji ya mata abu. Ga ta mace ce mai dattako, kyauta da son mutane, gabadaya ta kama dangin mijin ta rike kam a hannunta. 


A shekarunsu na biyu da aure, Uwale ta haifi Hadiza. Zuwa lokacin tuni dangin su Hamisu sun sanya idanunsu akan Hajara din. Sai ma da Uwale ta sake haihuwar wani da namijin, Jamilu bayan ta haifi Hadiza da shekara daya da rabi, nan suka musu caa, akan lallai sai Hamisu ya sake yin aure. To yaron ma data haifa bai dade ba ya koma. Bayan shekara daya ta sake haihuwar wani dan aka sanya mishi AbdulKareem. Lokacin Hajara tayi barin ciki har sau biyu. 

Dole sai da suka sanya Hamisu yayi wani auren dai, ya auri wata bazawara Sa'ada (Nana), bata taba haihuwa ba. Ya hada su da Hajara aka yi ta fafatawa. Duk son Nana da zaman lafiya, Hajara bata bata hadin kai ba, kullum masifar safe daban, ta rana daban, wai ma don bata taba kula ta ba. 


Kusan a lokaci guda aka haifi Lawal da Shamsiya, wadda suka yiwa lakabi da Uwani. Hajara fa abin nema sai ya samu, yan uwan Hamisu masu zuwa barka, duk wanda yazo sai ta danna mishi bakar magana. Wai ana kiranta da juya, marar haihuwa mai farar kafa, har ana sanyawa ayi mata kishiya, to ta Allah ba ta mutane ba, gashi nan itama tayi abin kanta, ta haifi magajin gida, daga yanzu sai su san kuma wadda zasu kira da marar haihuwa. Su kam dai sai wasa kawai suka dinga maida abin. 


To da yake ma abin na Allah ne, daga Uwale din har Hajara babu wadda ta kara haihuwa a cikinsu, haka itama Nana, ko batan wata bata taba yi ba. 


A haka yaransu suna tasawa cikin tarbiya da hasken ilimi, rayuwa ma na kara tafiya. A hankali cuta ta fara cin Alhaji Hamisu. Itama Hajja ta fara kwantar da hankalinta, suna zaman lafiya da Nana da sauran mutane. Lawal na dan shekaru sha biyar, Allah ya karbi ran Alhaji Hamisu. Ba karamin kuka dangi da iyalanshi suka yi ba, mutum ne wanda dole ayi kewarshi. 

Bayan rasuwarshi, Badamasi yaci gaba da kula da duka iyalanshi, basu nemi komi sun rasa ba. 


Rayuwa na ta tafiya, Hadiza na gama karatun jami'a aka daura mata aure da Hilaluddeen, wani dan gidan Yayar Uwale da yake aikin soja a kasar Amurka. Ana daura auren suka tafi can.

To haka rayuwar taci gaba da tafiya. 


A rana daya aka hada aka yi auren AbdulKareem da matarshi Maimuna, yar garin jihar Adamawa ce da suka hadu a makaranta, dukansu mechanical engineering suka karanta, suka kuma samu aikinsu a garin Abuja da taimakon mahaifin Maimunar, don haka suka yi kaura can. 

Shi kuwa Lawal ya auri Saddiqa, yar nan cikin unguwarsu ce. Lokacin ya gama karatunshi na degree akan Islamic studies. 

Ita kuma Uwani ta auri Yakubu. Duk suka tare a gidajensu. 


Duk cikin Yayan Alhaji Badamasi, AbdulKareem, wanda yaran suke kira da Daddyn Abuja, shi kadai za'a iya cewa ya dauko halin dattako, son zumunci da kyauta irin na Alhaji Badamasi. Anty Hadiza ma duk da cewa bata a kusa dasu, tana kwatanta yin zumunci bakin iyaka kokarinta. Anty Uwani kam ba'a maganarta, abu ne da su kansu iyayenta kan koka da ita tun yarintarta, don kuwa bata dauko komi a cikin halayensu ba. Bata son shiga cikin mutane yan uwa, bata kuma yin hulda da mutum sai shi ko iyayenshi sun tara abin duniya. Sunyi nasihar, sunyi fadan, amma tayi kunnen uwar shegu dasu. Da tayi aure kuwa ta samu miji mai irin halinta, sai wulakanci ya ci gaba. Sam ita da Lawal basu yi sabon da suka yi da AbdulKareem ko Hadiza ba. Gani take yi tunda mahaifinta yake daukar nauyin komi nashi, to shi din ba komi bane a wajenta face wani mabaraci, wanda mahaifinta yake ciyar dashi. Ita kuma bata harka da mabarata. 


Matar AbdulKareem ta fara haihuwa a cikinsu, ta haifi diyarta Muneerah. Bayan shekaru uku, ta haifi Baqeer wanda suke yiwa lakabi da Lamido saboda sunan mahaifinta ne aka sanya mishi. Ganin cewa tunda Hadiza tayi aure bata taba ko batan wata ba, ya dauki Muneerah sukutum ya bata ita kyauta har aurenta. Ba karamin dadin hakan suka ji ba kuwa ita da mai gidanta, takanas suka zo Najeriya suka yi godiya, suka kuma dauki diyarsu suka koma. 


Sai da Baqeer ya shekara biyu sannan Uwani ta haifi Badi'ah, don ita tsarin iyali ma tayi, sai data gama cin amarcinta, a cewarta, sannan tayi ciki. Ita kuwa Saddiqa Allah ne bai kawo ba, suna ta sanya idanu. 

Cikin Ikon Allah ba'a jima da haihuwar Badi'ah ba, ta samu ciki, ta haifi diyarta Murjanatu. Ita da Malam Lawal ba karamin farin ciki suka yi ba da wannan haihuwa, suka fara rainonta cikin kulawa da tattali. Lokacin Malam Lawal ya bude shagonshi inda yake sayar da kayan gwanjo. 


Uwani ta sake haihuwar dan ta namiji aka sanya mishi suna Affan. 

Bayan shekaru biyu Saddiqa ta haifi Ameenatu. Bata yi cikakken wata uku ba Uwani ta haifi Fauziyyah. 

Duk a kusan lokaci dayan ne dai itama Maimunah a can Abuja ta haifi 'ya'yanta tagwaye mace da namiji, Ameer da Ameerah. 


*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.