Free chapter · Read without an account

Six

by Hauwau Shafiu · DUNIYA BIYU

Gabadaya yaran sun taso cikin mabanbanciyar tarbiya, rayuwa da kuma kulawa. Iyayensu maza da mata, kowanne ya kasance mai mabanbancin hali. Yadda kowannensu yake nuna kulawa ga ya'yansu, ta banbanta da yadda dayan zai nuna. 


Yayin da Alhaji AbdulKareem ya kasance mutum mai tsauri da kausasawa, hakan bai hana shi tsayawa tsayin daka wajen ganin cewa gidanshi da iyalinshi basu karkace ba. Don kudi da budi yana dasu daidai gwargwado, sai dai hakan bai sanya mishi girman kai da dagawa ba. Bai kuma yarda wani daga cikin yayanshi yayi wannan hali ba. Maimunah, matarshi, mace mai kawaici da rashin hayaniya, sai dai fa akwai dan banzan girman kai da dagawa. Mace ce irin fulanin usul dinnan. Kakanta shine magajin garin Bade dake garin Yobe, kafin sarautar ta bar dakinsu. Wannan kawaici na ta, kunya da girman kai da suka hadu, yasa hatta da mijin nata ba ya'yanta ba kawai, suna ganin rashin kula daga gareta. Musamman ma Baqeer da ya kasance dan fari kuma mai sunan mahaifinta. Don haka AbdulKareem ya ja yayanshi a jikinshi sosai. Sun saba dash fiye da yadda suka saba da mahaifiyar tasu.


Gidan Alhaji Yakub da matarshi Uwani kuwa rayuwa ce kamar wadda aka ciro daga cikin wani hamshakin shirin fim na nasara. Mijinta ya fito daga gida na tsohon siyasa, Iyaye da kakanni na wannan gida babu wanda bai taba wani bangare na siyasa ba. Abin sai ya zame musu kamar wata gasa, ko kuwa al'ada. Idan kai ba dan siyasa bane, to lallai ka zama babban dan kasuwa da babu wanda zai ja da kai. Idan baka kasance daga cikin biyun nan ba, to fa kai da babu a cikin wannan iyali duk daya ne. Ba zaka kasance wani mutum mai tasiri ba, daga kai har iyalinka. 


Soyayarsu da Uwani ta samo asali ne daga wata ziyara da suka kai makarantarsu lokacin da yake taya mahaifinshi kamfen din neman kujerar sanata ta nan Funtua zone. Lokacin anyi wata zazzafar muhawara a tsakanin yan ajin su Uwanin da wasu yan ajin. Yadda Uwanin ta hakikance tana zubar da bayanai, dama gata tsohuwar manipulator ce, tun yarinyarta. Nan da nan ta karkato da hankalin gabadaya alkalai har ma da yan kallo kanta gabadaya, da zakin baki da misalai na karya da gaskiya ta ciyo musu na daya. Dama abinda aka fi bukata kenan a muhawara irin wannan, iya kalamai da kuma kawo hujjoji, ba wai gaskiya da rashin gaskiyar abu ba. 

Aikuwa bai bari an gama abin bama ya nemi ganinta. 


Kowa yasan Uwani daga yan gidansu, zuwa yan ajinsu, da yan makarantarsu. Bata tsayawa da kowa. Lakcarori da dama sun nuna sha'awar suna son ta, amma bata bawa kowa fuska. Saboda a ganinta duk cikinsu babu wanda ya kai matsayin ta tsaya dashi. A yadda take dinnan, wani babban sanata ko gwamna take hangowa kanta. 

To kuma sai Yakub Alkali ya bayyana kwatsam. Duk wanda yake cikin birni da kewaye na garin Katsina, kai har ma da makotansu, babu wanda bai san zaman wadannan Ahali ba. Manyan yan kasuwanni, manyan yan siyasa, manyan alkalai, babu wanda basu tara ba. Ita a ganinta, dami ne ta tsinta a akala. Musamman tunda a halin da ake ciki mahaifinshi na shirin zama sanata, ta san cewa shima babu dadewa zai dauki hanya. Don haka babu wani tunani ko wani bincike, ta amince mishi. 

Ba wata soyayya suka yi ba, babu zancen fahimtar juna a tsakaninsu. Kowannensu kawai yasan zai amfanu da dan uwansa, to abinda suke bukata kenan. Shi yasan ya ga wadda zata tsaya mishi tsayin daka wajen harkokinshi na kamfen da siyasa, mace ce mai tsananin dakewa akan duk abinda ta sanya a gaba, kuma duk tsanani sai taga bayanshi. Ga kuma kudi da nasaba irin ta danginta, dangi masu mutunci da ake tsananin ganin girma, mutunci da kimarsu a garin Katsina. Don haka shi a ganinshi ita ce daidai a wajenshi. 


Ita kuwa dama burinta a duniya tayi rayuwa ta watayawa da facaka, rayuwa ta manyan motoci da manyan mutane. Yakub kuwa shine wani tsani wanda zata taka ta kai matsayin da take so. Don haka itama a ganinta shine daidai ita. Don haka babu bata lokaci manya suka shiga ciki aka fara maganar aure. 


Ana yin auren, ba'a rufe wata biyu ba suka fara yawon neman kujerar takarar dan majalisa da yake yi, Allah bai nufa ya samu ba. Don haka ya fada harkar kasuwanci da karfinshi, mahaifanshi hamshakan wadanda suka ci, kuma suka tada kai da naira ne. Ita kuma Uwani ta nemi aiki a wani babban asibitin kudi a nan cikin Katsina. Zuwa lokacin da ta fahimci zaman da take yi da mijinta ba irin zaman daya dace ma'aurata su yi bane, lokacin ya lallasheta tana shan pills na hana daukar ciki, a cewarshi bai shiryawa rainon 'ya'ya a lokacin ba. 


Sai a lokacin ne taso ta gyara rayuwar aurenta, sai dai tuni lokaci ya kure mata. Duk hanyar da ta bi, boka, Malam, kissa, babu wanda yayi aiki. Sai ta watsar da komai a gefe daya, dama ba wata damuwa tayi ba. Ta daina shan magungunan, har ta samu cikin Badi'atu. Sun so su samu rikici dashi akan cikin, yana zarginta da cewa ta yaudare shi ta daina shan maganin daya bata. Ita kuma tayi amfani da yaudara ta gamsar dashi kan cewa maganin ne ya daina aiki kawai. 


Shikuwa Malam Lawal rayuwa suka yi shi da matarshi ta kadaran kadahan. Sana'arshi babu laifi ta rufin asiri ce, bata hana su cin yau da na gobe ba. Ga matarshi Saddiqa mace ce mai fahimta da hakuri, idan an samu zata karba hannu bibbiyu ta gode. Idan ma ba'a samu ba dai zata yi godiyar, da yan sana'o'in hannu da take yi zata samar musu abinda zasu kai baka a kuma biya bukatun rayuwa na yau da gobe. 


Ko bayan sun fara hayayyafa, hakan bata canza zani ba. Tayi iyaka bakin kokarinta wajen ganin cewa ta raini yaranta cikin tarbiya. Shi yasa suka taso kansu a hade, cikin tsananin kaunar juna. Daya bata son ganin bacin ran dayar ko da wasa. Tsakaninsu da Iyayensu ma so ne mai tsafta da kulawa. 


AbdulKareem yayi iyaka kokarinshi wajen ganin cewa ya hada kansu gabaki dayansu. Sai dai gabadaya kokarinshi sai ya kasance na banza. Saboda na farko shi dai ba a gari yake zaune ba, sai lokaci zuwa lokaci ne yake ziyartar su. Yanayin aiki da nisan waje kuma bai hana shi ziyartar su. Wasu lokutan idan aka yi hutun makaranta haka yake dauko Baqeer yaje ya musu hutu, wani lokaci kuma ya dauki su Murjanatu ko su Affan, watarana ma su duka ya kaisu can gidansu Abuja suyi nasu hutun. 


Sai dai daga wani lokaci da Badi ta kone da man suya, hakan har ya so ya sanya wata tangarda a tsakaninshi da Uwani, sai ya daina daukarsu. Yana tunanin daga lokacin ne ma suka daina mutunci da matarshi da Uwanin. Dama dai can basa ga maciji a tsakaninsu. 

Maimunah mace ce mai sakaci. Su kansu yaranta ba kasafai ta cika samun lokacin kula dasu ba, shi da yan aiki ne ke wannan hidimar. Ita fa bata ki komi yan aiki su mata ba. Ba karamin dabi da masifa suka sha a farko-farkon aurensu ba, saboda nunawar da tayi ita fa ba zata aikatu ba, sai dai kowace hidima tata yan aiki su yi. Sai da yayi mata jan ido sosai kafin suka zauna lafiya. A hakan ma wasu ayyukan ne kawai take yi, ba duka ba. 

To sai ya zamana idan ma ya kai yaran suyi hutu, sai yan aiki ne ke kula dasu. Ga masifar fada, kullum cikin dambe ake tsakanin Badi da Murjanatu. Musamman idan daya daga cikin Badi ko Affan suka taba Ameenatu. Ita Murjanatu bata damu su sauke mata kwandon tsokanarsu a kanta ba, amma daga lokacin da suka taba Ameena, to fa anan ne zasu ga tsaurin ido. Lokacin Ameenatun tana yarinyarta karama, zuwanta gidan ma bai fi sau biyu ko uku ba. 


Wani lokaci ne da safe ana hada abin kari, Badi ta yiwa kicin din tsinke suna cikin soya dankalin turawa. Maimunah na can dakinta ko tashi daga barci bata yi ba lokacin. Badi taje tana yiwa masu aikin dibar rashin albarka, akan me yasa zasu soya dankali a maimakon agada. Yarinya ce yar kankanuwa a lokacin, amma rashin ta idon da zata yi wani lokacin ko babba wanda ya haifeta ba zai iya yi ba. Cikin tsautsayi ta kamo hannun kaskon suyar, gabadaya kayan ciki suka zube a tsakiyar kicin din. Mai ya dan zubar mata a kafa.


AbdulKareem yana gefen matarshi akan gado a kwance yana barci, sai jin karar ihun kuka yayi. Ya zabura ya tashi, suka nufi kicin din hankali a tashe.

Kunar ma da tayi ba wata mai muni bace, suna dawowa daga asibiti inda aka yi mata wankin wajen, ta lalubi waya ta kira mahaifiyarta. Babu lokaci ta kira AbdulKareem din, a cewarta rashin kulawarsu ne yasa diyarta ta kone. 

A takaice dai basu kara kwana a Abuja ba, a ranar ya maida su Katsina. 


Daga wannan rana ya hakura da zancen kai yaran gidanshi. Amma fa duk lokacin da yazo gaida mahaifanshi, ya kan leka ya ga yaran da Iyayensu. Watarana shi da Baqeer suke zuwa, watarana shi kadai yake zuwa. Shi yasa yaran suka saba dashi sosai. 


Babu yadda bai yi da Lawal akan ya bude mishi shagon sayar da kayan masarufi ba, ko kuma ya bishi can Abuja ya sama mishi aiki, amma Lawal din yace ya gode. Sana'arshi ta bashi rufin asirin da yake bukata. Don haka ya kyaleshi. Amma fa alkhairai iri-iri yana mishi shi da iyalanshi, wanda shima da kyar Lawal din yake karba. 

Haka rayuwar kowane gida take tafiya. 


Ana cikin haka ne, Lawal ya raka Hajiya babba asibiti check up da aka saba yi mata saboda ciwon sugar da hawan jini da take fama dashi. Dama shi ya saba kai ta a duk lokacin da zata je, musamman idan Uwani bata gari. Mota guda AbdulKareem ya ajiye mata saboda irin haka. 

Akan hanyarsu ta komawa gida suka karawa wata daf data dauko shanu. Ajali ya tar da su anan. Babu wanda aka fitar da rai. 


Rasuwar wadannan mutane biyu tayi matukar girgiza ilahirin iyalan gidan Alhaji Samaila Turawa. Sun san cewa sunyi babban rashi, wanda mawuyaci ne su iya mayar da kwatankwacinsa. 

Ana isarwa da Alhaji Badamasi wannan mummunan labari, ya yanke jiki ya fadi. Cutar barin ciki da mummunan hawan jini. Yana gadon asibiti a kwance aka suturta mamatan aka kaisu gidansu na gaskiya. Bayan farfadowarshi yayi kukan rashin kamilar mata da kuma da mafi soyuwa a gareshi. Lawal bai kai sauran yan uwanshi kudi ba, sai dai zai iya cewa ya fisu biyayya, sanin ciwon kai da sanin darajar dan Adam. 


Sai da aka yi kwana bakwai cur, kafin aka sallameshi ya koma gida. Ko bayan ya koma din, jikin nashi sai ya zama yau da lafiya, gobe babu. A hankali sai abin ya fara munana. Kusan mawuyaci ne ayi cikakken wata daya ba'a kai shi asibiti ba. Cikin shekara daya kacal gabadayanshi ya fige, ya zama kamar ba shi ba. 


Lokacin wani bazawari a Dutsinma, Malam Habu ya fito yana son auren Nana. AbdulKareem da Anty Hadiza suka yi shawarar mai zai hana su hada auren Hajja da na Alhaji? Tunda ita dai Nana Dutsinma zata koma, ga Saddiqa tana shirin komawa Sudan wajen iyayenta. Su kuma basu son ta tafi da yaran can. Don haka suka ga jifar tsuntsaye biyu ne zasu yi da dutse daya. Zasu samu wadda zata kula da Alhaji, duk da cewa ba'a san gawar fari ba, kuma wadda zata mishi takaba, sannan Hajja ba zata zauna ita kadai da yara a wajenta ba. Don haka suka shawarci manya, suka yi na'am, aka hada auren Nana da Hajjar aka daura a lokaci daya. 


Da Nana zata tafi ne ta roki alfarmar a ba ta rikon Murjanatu, dama sun fi sabawa da ita, aka bata. Ita kuma Hajja aka yi za a bar mata Ameena idan Saddiqa ta tashi tafiya. Hajja ta koma gidan Alhaji inda aka ajiye mata dakinta daban, aka zuba duk abubuwan bukata, tsohon na Hajiya Uwale kuma aka rufe shi. 


Bayan wata daya, Saddiqa ta gama duk shirye-shiryenta, da kanta ta dauki Ameenatu ta kai ta wajen Hajja. Lokacin shekarunta shida. Ta sha kuka da rokon ta tafi da ita, kafin suka yi sallama da ita da kyar, tayi kaura Sudan. 


Daga wannan lokaci ne zata ce rayuwarta ta shiga cikin matsatsi da takura. Kusan kowane lokaci su Affan suna gidan, babu kuma wanda yake nuna mata koda dan guntun so ne. Kullum cikin kyara da hantararta suke. Mai tare mata kuma bata nan. Bata cika ma zuwa Katsinar ba. Tun suna mata tana kai karar su wajen Hajja ko Alhaji, har ta gaji ta daina. Don idan ma ta kai karar tasu an yi musu fada, babu abinda hakan yake haifarwa sai ma kara tunzura su da yake yi. Gani take kamar ma kara musu tsanarta ake yi. Don haka ta kame bakinta tayi shiru. Sau tari sai dai ta shige daki ta sha kukanta ta koshi. Ko kuma idan Alhaji ya ga abinda suke yi ya tsawatar musu, amma Hajja kam koda wasa. Har ta riga ta saba da hakan. 


Don haka ba karamin jin dadi tayi ba data bar wannan gida da wannan rayuwa.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol