Free chapter · Read without an account
Ten
by Hauwau Shafiu · DUNIYA BIYU
Cigaba tayi da aikin, Hajja taci gaba da mata hirar gidan. Kafin Isiya ya dawo har ta gama gyaran dakin.
Ya mika mata kayan a cikin bakar leda hade da canjin, tayi godiya tare da fito da kayan.
Hajja tace mishi "ga fa abincinka da aka ajiye maka, kada ka manta ka tafi ka barni dashi irin na jiya".
Yayi yar dariya, yadda ya mayar da Hajja din kamar wata kakarshi, yace "ai nasan da kyar idan yau ma ba tuwon kika tuka ba. Ni kuwa yau ma shi aka yi a gidana nace musu na koshi. Kinsan fa ni ba mutumin da bane irinku".
Tace "kaji maganar banza! Kenan itama matar taka mutuniyar da ce kenan? Tunda dai itama tana da son cin tuwo! Kuma yanzu haka zancen da nake maka Isiya, masara kadai da cous-cous suka rage mana a gidannan. Wata ya riga yayi nisa, amma shiru kake ji. Nasan babu mamaki hidimar biki ce ta sha kanta shi yasa. Yanzu ma da ba don Allah Ya dube ni da idon rahama ba, aka kawo aikin masa daga nan gidan Alhaji Aminu aka kuma biya ni akan lokaci, ai da ban san yadda zata kasance ba, da ko na itace ba zamu samu ba. Da kudin aka yi mana cefane muka yi miya".
Ameenatu ta girgiza kanta a hankali, gefen bakinta dauke da dan murmushin karon battarsu, gefe daya kuma wani abu ne ya taba mata rai mai zafi. Ba kadan rashin kulawar da suke nunawa Hajja yake taba ranta ba.
Tasan cewa duk karshen wata Anty Hadiza da Daddyn Abuja suke aikawa Anty Mommy kudin abinci da hidimar Hajja. Ita zata hada da nata, sai ta saya mata abubuwan bukata, ta aika mata hade da kudin cefane.
Abin takaicin shine yadda ba'a ma tashi kai kayan abincin sai wata ya cinye wani ya kama, sai kuma a dauki sati ma ba'a hattama kayan abincin waje daya ba. Yau a kai mai, gobe manja, jibi taliya, gata itace. A haka dai. Da ba don Allah Ya sanya tana taba sana'o'in hannu ba ma, ai da abin sai yafi haka muni. To sana'ar na taimakawa kwarai, da ita suke maneji idan ba'a kai abinci ba ko kuma ya kare.
Abin karin takaicin shine, ta dade tana bin kanta akan ta tashi ta koma cikin dangi, koda Batsari ne wajen Baba Rakiya. Tunda bazawara ce, ita kadai take zaune a gidanta ita da 'ya'yanta. Amma Hajjar ta ki. Ita fa duk abinda suke mata, kullum cikin basu uzuri take. Saboda ita a idanunta har lokacin, Anty Mommy da ya'yanta basa yin laifi a wajenta.
Ita kuwa Ameenatu a ganinta, taimakon wanda bai son a taimaka mishi, aiki ne gingimeme wanda yafi girman dutsen dala. Amma duk da hakan, tayi iyaka bakin kokarinta, da taga abin yaki yiwuwa, sai kawai ta kai na mujiya ta zuba mata. Ta dai san cewa akwai ranar kin dillanci.
Ta hada fitilar ta kunna, nan da nan ta kawo dal. Ta bare cazar da aka sayo daga cikin kwalinta ta jona a jikin caji. Nan da nan fara'ar Hajja ta karu, tace "har caja aka sayo min? Oh ni yar gatan Ameenatu, Allah dai ya raya min ke, Ubangiji Allah ya kawo min siriki na gari, wanda zai tallafi rayuwar wannan yar marainiyar jika tawa".
Isiya yace 'ameen', Ameenatu kam dan murmushi ta saki a kunyace.
Gefensu ta koma ta zauna tana sauraren hirar Hajja da Isiya din, wadda yawancinta duk tsokana ce, sai jifa-jifa da suke sako ta al'amuran yau da gobe na rayuwa. Zuwa can da dare dai yayi musu sallama ya tafi. Bayan ya tafi ta tashi ta kunna musu kallo.
Zuwa can wajen karfe goma ta tashi ta shiga bandaki, shiri tayi ta dauro alwala. Hajja na ta shirin kwanciya barci lokacin data koma dakin, ta canza kayan jikinta, ta kwanta a gefen gado. Hajja itama ta fada bandakin ta fito. Ta kunna musu maganin sauro tare da kashe wuta.
Itama gefen gadon ta daya barin taje ta kwanta. Ameenatu tace mata, "sai da safe Hajja!".
"Allah Ya tashe mu da rai da lafiya Ameenatu". Hajja ta amsa mata.
Ta lumshe idanunta, a hankali gajiyar ranar ta fara ratsata, barci ya fara kwasarta.
Ta fara lulawa cikin duniyar barci taji muryar Hajja kamar daga sama tana tambayarta, "Ameenatu har kinyi barci?".
Murya cike da barci da gajiya tace "a'ah Hajja, me kike bukata ne?".
Tace "babu komi. Mantawa nayi in miki albishir, Babanku na Abuja ya miki ankon Badi'atu, har da jaka da gyale ya hado miki, kayan suna wajen Indo na bata ta kai dinki, gobe ma zata kawo su gabadaya. Har kudin dinki ya bada dubu bakwai, yace ayi dinki a kuma sai miki takalmi dai-dai kafarki".
Taji wani irin abu ya tsirga mata a jiki, kaunar da mutumin yake nuna mata a duniya bata taba ganin irinta ba. Hidima iri-iri, har ma da wadda ba dolensa bace, tun daga kan hidimar makaranta, hidimar kayan sanyawa zuwa na amfanin yau da gobe, bai taba gajiyawa ba. Abu ne wanda wani daban ba zai iya daukar wannan dawainiyar ba ta shekara da shekaru face mahaifi wanda ya haifeka ya kuma san zafinka, amma shi ya dauki hakan, yana kuma yin fiye da hakan.
Ta daga baki da kyar, zuciya a cushe, kuma a cunkushe, idanu cike da ruwa suna son zuba, kauna ce mai sanya kuka ta lullube mata zuciya a lokacin. A kullum ta Allah, Girma da mutuncin mutumin karuwa yake yi a cikin ranta.
Tace "Nagode, Allah ya kara Girmah".
Hajja tace, "ameen. Ai tsakaninmu da AbdulKareem sai addu'a kawai da fatan gamawa da duniya lafiya, daga shi har zuriyar shi. Allah ya kara kare su".
Daga can kasan zuciyarta ta amsa, zuciyarta na nuna yarda da hakan dari bisa dari.
*
Tunda tayi sallah bata koma ba, ta fita can bayan gida inda Hajja din take yin girki. Da akwai gas wanda yake amfani, ruwan zafi kawai ake dafawa akai da sauran kananan abubuwa kamar su taliyar indomie dasu macaroni, amma yanzu ya ma lalace. Abin sai yazo da sauki daya kasance Hajja bata son aiki da gas, sai murhu. Ta hada wuta, ta dora ruwa. Ta dauko sauran gasara data gani, ta gyarata ta dama koko. Cikin bokiti mai murfi ta dama, ta sake dora wani ruwan wanda zata yi wanka dashi.
Hajja na kishingide tana sauraron labarai a tashar companion FM tayi sallama ta shiga. Ta tashi zaune sosai, tace "kar dai har kin gama dama kokon?".
Ta ajiye bokitin a gabanta tace, "ai da yake Allah ya taimaka itacen mai kyau ne, ba'a wani dade ba ruwan ya tafasa".
Tace "madallah, Allah yayi albarka, sannu".
Tace "yauwa".
Hijabi ta fara kokarin sanyawa, Hajja ta kalleta tace "ina zuwa kuma? Sarkin yawo kamar wadda taci kafar kare?".
Ameenatu bata san sanda tayi dariya ba, tace "nan ne fa gidan Marka zan je in sayo kosai".
Tace "to ai da sai ki bari Isiya yazo ya sayo, ko kuma danta da yake mata talla ya kawo. Kullum sai kin ganshi ya leko nan".
Tace "bari dai inje, gwanda a sayo mu ci yanzu da zafin kosan da na kokon gabadaya".
Hajja ta gyada kai, "to ai shikenan, ki gaishe ta. Ki ce mata dai ta kara hakuri akan kudinta, sai an biya ni kudin aiki sannan".
Ta daga baki zata yi magana, kullum fadan da suke yi da ita kenan, cin bashi. Duk da dai tasan cewa wasu lokutan halin rayuwa ne kan janyo hakan, amma idan da hakuri da kawaici ita sai taga bashi da amfani sam. Sai kuma ta kame bakinta kawai bata ce komi ba don tasan idan ta furta fada ne zasu fara tun kafin ta yi cikakkun awanni ashirin da hudu a gidan.
Layi ta tarar a gidan Marka, ta samu waje ta zauna har yaje kanta. A gaggauce suka gaisa da Marka din, ta fada mata sakon Hajja a tsaitsaye saboda mutane da suka zagayeta, tace babu komi, har da bada sakon gaisuwa da alkawarin zuwa anjima idan ta samu ta fita zata leka gidan, ta sallami Ameenatun ta koma gida.
Suna gama karyawa suka fara aikin dubulan. Hajj tana karbar aikin dubulan, cin-cin da alkaki na shagulgulan biki ko suna, tana kuma yin masa har ma da nakiya. Da wadannan sana'o'i ta samu tana rike kanta a lokacin da babu komi a hannunta. Saboda magana ta gaskiya Anty Mommy bata kyauta mata, wasu lokuta tasan da gangan take kin kai mata abincin, ko kuma ta dinga kai mata da cire-cire ta yadda duk lokacin da zata yi abinci sai ta nemi wani abu ko kuma kafin akai wani abun wani ya kare.
Buhun fulawa daya da rabi aka kai musu na dubulan ga kuma kwanon alkama goma sha biyar na yin alkaki.
Can wajen karfe sha daya na rana sannan Indo ta karasa gidan da dinkunan Ameenatu da gyaleluwan data sayo mata. Babu ma wanda yabi ta kansu a lokacin saboda aiki, ta kama musu suka fara.
Sai can da dare bayan sun gama aikin, sun ci dafa-dukan cous-cous, sannan suka daga dinkunan. Sunyi gabadayansu babu na yarwa. Atamfofi manya guda biyu, lesuka ma biyu sai wani tsararren material ruwan zuma wanda aka yi masa dinkin gown mai kyau. Tayi godiya sosai da sosai kamar yana wajen.
Sai a daren ranar ta samu ta kira su Nana suka gaisa. Bayan sun gama ta kira mahaifiyarta itama suka gaisa. Ta hadata da yan kannenta, Al-Mustafa da Musa suka jima akan waya suna hira dasu kafin suka yi sallama. Tana kewarsu sosai. Kusan shekaru uku kenan rabon data gansu, tun wani hatsari da Yayar Saddiqa din, Anty Maryam dake aure anan Katsina tayi, ita Saddiqa din taje mata dubiya rabon data ga mahaifiyar tata da kannenta.
Washegari suna tashi suka dora aikinsu daga inda suka tsaya.
Sai da suka share sati suna aikin kayan bikin nan. Saboda bayan sun gama aikin zuwa ranar juma'a, aka kara kai wata fulawar suka yi cin-cin na rabin buhu, ranar Lahdi kuma aka kai musu kaji hamsin suka yi aikin soya su. Duk wannan aikin da suke yi, bata ga giccin kowa ba sai yan aikin gidan Anty Mommy din. Su suke kawo abinda ake bukata, su kuma dauki wanda aka gama. Sai sune aka ba sakon abincin gidan ya kare, suka fada mata. Saboda ko an kirata a waya bata dagawa, a cewarta hidimar mutane ce tayi mata yawa.
Ta bada shinkafa da taliya aka kai, sai mai dasu kayan miya, wai tayi maneji zuwa bayan biki.
Ranar litinin dai suka gama aikin gabadaya. Allah Yasa Hajja tayi dabarar sallamar su Indo da Khadija da Shamsiyya, wasu makotan Hajja din da suke shiga suna taya su aiki, da sai dai taji a salansa don ko na rabawa baki ba'a basu ba. Tasan kuma da kyar ne idan za'a basu kudin sallama
Duk da tsananin zafin da ake zugawa, hakan bai hana Ameena dora ruwan zafi ba tayi wanka, don kuwa a matukar buge take, jin jikinta take yi kamar wadda aka lakadawa dukan tsiya.
Tana gama yin shafa'i da wutiri, ta haye kan gado. Hajja ma tana gama yin abubuwan da zata yi, ta bi bayanta.
Tana kwanciya aka kira wayar Hajja din, ta daga. Tana jin ta ambaci sunan Uwani, ta kashe kunne tana sauraron abinda suke cewa, amma bata jin komi sai amsar da take bata wadda bata wuce, 'ehh, to, da in Allah ya yarda', har suka kashe wayar.
Suna yin sallama ta juya ta kalli Ameenatu, "Uwani tace a tura mata Indo gobe tun da safe zata taya su aiki. Sai ki bita ku je ko?".
Ta cikin duhun dakin ta kalli inda Hajja din take a kwance, tace "sai kace Indon bata da miji, zata kwashi jiki tun da safe ta tafi musu bauta? Ni kuma a suwa da zan dauki kafa in bita?".
Hajja tace "wai Ameenatu me yasa kike haka ne? Kina yin abu sai kace su din ba danginki bane! Kada fa ki manta, Uwani ubansu daya da mahaifinki, hakan ya sanya kika zama diyarta, 'ya'yanta kuma suka zama yayyenki. Amma kullum ke nunawa kike yi kamar su din wasu bare ne. To sai me don kinje kin musu aiki? Shi fa hannunka baya rubewa ka yanke ka yar, kuma duk abinda na waje zasu miki ko su musu, ba zai taba kai wanda na gida zai yi miki ba!".
Tana so ta tambayeta, 'su kina musu irin wannan nasihar? Ko kuma kina nuna musu bacin ranki a duk lokacin da suma suka nuna ni din ba wata aba bace a idanunsu? Shin kina jin haushi idan suka nuna ni bare ce a wajensu, kuma basu damu da ni ba, kamar yadda kike jin zafi idan ban shiga cikin lamarinsu ba?!'.
Amma tayi shiru ta hadiye maganar. Har yau Hajja Kakarta ce, wadda har yanzu take ganin girma da kimarta a cikin idanunta. Ita kanta ba kasafai ta cika son tana yi mata musu ba, musamman akan al'amuran Anty Mommy da iyalanta. Sai dai bata da wata mafita da tafi wannan.
~☆~☆~
Bata da zabi wanda yafi ta dauki kafafu ta bi bayan Indo su tafi washegari. Kai tsaye sashin yan aiki suka wuce, ko Anty Mommy din basu samu gani ba saboda aiki da kuma mutane. Aikin samosa ne suka yi da spring rolls wadanda za'a raba wajen walima da za ayi a ranar da dare.
Aiki ne suka sha ja, Allah ma yasa abincin da za'a ci anyo odarshi da sai aikin yafi haka.
Sai can da rana suka gama aikin. Lokacin anyi sallar la'asar, suka yi.
Suna kicin na cikin gida ita da Indo da wasu daga cikin yan aikin gidan. Su suna ta zuba kayan da za'a raba a ledoji ana lodawa a kuloli, ita kuma tana cin abinci a cikin plate.
Fauza ta fado kicin din cikin wata shiga ta doguwar rigar atamfa cote d'evoire, an yi mata dinkinnan irin off-shoulder, gabadayan kafafunta a waje suke. Wani jan takalmi mai tsinannen tsini data saka sai daya kusa sa kan Ameena juyawa saboda tunanin ta yadda take iya tafiya a kanshi. Gashin kan nan nata ya sha gyara sai sheki yake, ta sauke gashin ya sauko har kafadunta da yake ba laifi, daga ita har Badi suna da mayalwacin gashi.
Ta tsaya tana magana da Jenny, kamar ita ce shugabar masu aikin gidan, akan wani daki da take so a je a share saboda baki wadanda zasu kwana a ciki. Jenny din tace zata tura aje a share. Ta bude fridge inda lemuka suke zube kala-kala kamar anan ake hada su, ta ciro kwalin exotic guda, ta dauki samosa da spring rolls a cikin karamin farantin tangaram, ta juya zata bar kicin din.
"Ameenah?".
Ta ambaci sunan cike da wani irin distate, kamar wadda taga wani disgusting abu.
Ita kam, bata bari yanayin yadda tayi magana ya kai mata cikin ranta ba, ta amsa da "na'am, Fauza. Ya hidimar biki?".
Bata ce mata komi ba, ta tsaya tana kallonta kawai. Kafin daga baya ta juya da sauri ta bar kicin din, kamar wata kububuwa.
Indo ta juya ta kalli Ameena, fuska yamutse da alamun tausayi. Kafada kawai ta daga mata taci gaba da cin abincinta. It hurts! Sosai. Idan da sabo yaci ace ta saba da halayyar su, amma ta kasa sabawa ko kadan!.