Free chapter · Read without an account

Fourteen

by Hauwau Shafiu · DUNIYA BIYU

Tunda suka tashi ranar basu koma barci ba. Suna ta hidimar bakin su Affan da suka kwana a gidan, da kuma wasu daga cikin dattawan danginsu da aka yi musu masauki a dakin Anty Hadiza.


Sun dai saka ankon da aka yi a ranar, wani rantsattsen leshi ruwan silver mai kananun gida-gida. Dinkin riga da siket aka yiwa Ameenatu. Rigar ta dauketa tsaf, ta fitar da ita. Hannun rigar anyi mishi tattara, wadda aka sa wani yadi mai taushi, ash, aka mishi kwalliya da stones a jiki. Tayi daurin dankwalinta mai sauki, amma duk da haka ta fito Masha Allah da ita.

Ameerah kuma doguwar riga aka yi mata ta gown, ta sha kwalliyarta kamar ita ce amaryar.


Ameerah bayan ta gama fente fuska da kwalliya kamar yadda ta saba, ta kalli Ameenah dake sanya takalmi a kafarta tace, "Kinyi kyau sosai Anty Ameenah!".

Ta dan rausayar da kai gefe guda, "kyau har na kamoki Ameerah? Nasan ba'a kawai kike min!".


Duk da cewa suna kama su dukansu ta yadda babu yadda za ayi aga daya ba tare da an dangantata da daya ba, amma kuma Fauza da Ameerah sun kere ta a kyawu da kyawun jiki nesa ba kusa ba. Kana ganin Fauza kasan cewa kaga kyakkyawa, ita da Ameerah, kyawunsu har daukar ido yake yi. Ga kira da dirin jiki duk da cewa dai itama ba daga nan ba. Ko a yanayin haske sun fita hasken jiki har Anty Badi, ita sai ta dauko yanayin mahaifiyarta Saddiqa duk da cewa itama din ma ba baka bace, yanayin fatarta dai babu yabo babu fallasa wajen haske amma Ameenah din ta fita, sai kuma su Fauza suka ce kau ban guri!.


Don haka jin cewa tayi kyau daga bakin wadda ta kereta a kyau, kyawun ma wanda ta kara mishi hoda da janbaki, Ameenah bata dauki maganar da gaske ba sam.

Ameerah ta kada idanu tana girgiza kai, ta kula haka Allah Ya halicci Ameemah din, bata iya daukar compliments ba ko kadan. Hannunta taja suka fita zuwa farfajiyar gida suna daukar hoto. Suna nan su Ameer ma da Affan suka fita aka cigaba da daukar hoton dasu.


Sai wajen karfe daya sannan suka samu kansu, lokacin mazan duk sun tafi wajen daurin aure. Su kuma baki an kai su gidan su amarya.

Ameerah ta sake cancada wata kwalliyar, Affan yaje ya dauketa suka tafi wajen kai amarya. Ita kam, sai ta buge da gyaran gida. Ameer da Baqeer ana daura aure suka koma Abuja.


Zuwa karfe hudu, gidan ya fito tas, kamar ba shine yake kama da gidan masu somin-tabin hauka ba.


Hajja ma ta ci tata kwalliyar cikin atamfarta cote d'evoire da Daddyn Abuja ya dinka mata. Amma fa tana kishingide shame-shame a bakin gado, motsi kadan tace baya ko kugu suna mata ciwo. Wai a hakan ma sai da Ameenah ta fita da kanta ta sayo mata maganin ciwon jiki a daren jiya tunda nata din ya kare.


Ameenatu ta zube akan gadonta cikin tsananin gajiya, har wani ji take yi kamar ana juyi da ita a tsakiyar gadon saboda jiri.


Hajja ta tabe baki, "yanzu saboda Allah, daga gama gyaran gado, kawai sai ki haye kiyi dai-daya akai? Dama ana haka ne?".


Ta kalleta daga kwancen da take, "to ai ladar aiki na ce na ci Hajja. Ko babu komi dai ni nice mai gyaran".

Ta harareta, "to gaya min bakar magana!".

Ta kame bakinta tana dariya, "ni a su wa? Kada ki damu, zan gyara miki shi da na tashi".

Ta maida kanta ta kwantar tare da lumshe idanuwanta. Da yake dama ba wani barci take samu ba na azo a gani tunda taje gidan, nan da nan barci yayi awon gaba da ita.


*


Sai wajen karfe tara na dare sannan su Ameerah suka dawo daga wajen dinner din da aka yi. Bakinta fa yaki yin shiru, tana ta basu labarin irin barin kudi da kalar shagalin da aka yi wajen dinner. Ameenatu na zaune a gefenta tana karanta littafin Hisnul Muslim, tana binta da daga kai idan ta saka ta a cikin hirar tata.


Wayarta da tayi kara ne ta katse mata hanzari, ta daga tare da kara ta a kunne.

Tana kashewa ta juya ta kalli Hajja, "Hajja Yaya Affan yake tambayar abinci idan da akwai".


Hajja ta nuna mata wata babbar kula da aka kai daga gidan Anty Uwani da yamma saboda baki, tace "akwai abinci a cikin can, babu ma wanda yaci. Ameenatu tashi ku kai musu".


Ta rufe littafin ta ajiye a gefen gado. Hijabinta data sauka har kasar gwiwarta ta sanya. Ta fita ta dauki filet da cokula a kicin, suka zuzzuba abincin, shinkafa ce dafa-duka da ta sha naman kaza da na sa, ga soyayyiyar doya da dankalin turawa, aka kuma kawo hadin coleslaw aka dora a sama.

Suka cicciba suka nufi dakin su Affan din dasu.


A falo suka same su shi da tarin abokanan shi kusan su biyar, Ameenatu bata yi mamakin yadda aka yi Ameerah ta san abokan nashi ba, don a yadda ta fahimci yarinyar cikin dan lokacin da suka yi, ita din ta kowa ce.


Suka gaishe dasu kafin su ajiye abubuwan. Ameerah ta zauna tana mikawa kowa, Ameenatu kuma ta koma ta karbi makullin firjin ta dauko musu ruwa da lemuka.


Tun shigarsu ta farko, idanun wani Mus'ab yake kanta kamar wanda zai cinyeta danya. Yanzun ma kallonta yake yi, lokacin data ajiye gorar ruwa da lemu a gabanshi, idanunsu suka hadu bisa kuskure. Ya sakar mata dan murmushi, da sauri ta dauke idanunta ta kaisu kasa.

Tana gamawa dasu, ta mike da sauri ta suri tire da sauran filets da ba'a yi amfani dasu ba. Tana ji Ameerah tana musu sai da safe kafin ta bi bayanta.

Ita kam, sai data fara bi ta kicin ta ajiye kayan, ta bi ko'ina ta rufe, ta kashe wuta, kafin ta koma daki. Kai tsaye alwala taje ta dauro, ta haye kan gado ta kwanta.


A falo kuwa suna bada baya, Mus'ab ya juya yana kallon Affan cikin zakuwa, "_Dude!_, wannan dakwalar fa wacece? Ka santa? Don Allah ka min hanya mana in dan shiga daga ciki!!".


Affan ya watsa mishi harara cikin wasa, "sai me idan na santa? Sanin kanka ne, ko yar aikin gidanmu ba zan hadata da kai ba balle kanwata".

Bai damu da zagin daya mishi a kaikaice ba, yace "ashe ma kanwar kace? Kace ta ma kwana gidan sauki, yaushe zaka raka ni gidansu ne? Ko kuma lambar wayarta zaka bani?".


Affan ya harari wayarshi daya ciro daga aljihun gaban rigar shaddarshi, yayi scoffing, "in your dreams!".


*


Ameerah tayi nasarar janta suka tafi wajen budar kai gidan amarya washegari. Can Yar'adua road gidan yake. Babban gida hawan bene daya, da dakuna wadanda basa kirguwa. Amarya dai an cika mata bedrooms uku, biyu a kasa, daya kuma a sama, sai falon kasa da aka cika mata su da kayan kujeru har kala biyu. Kicin kuwa duk fadinshi, sai da aka cika shi tsil da kaya har babu masaka tsinke.


Suna isa gidan, Ameerah ta tafi daukar hotuna ita da amarya, ta bar Ameenatu ita kadai a tsakar falo tana zare idanu. Kowa ta kan shi yake yi a wajen, ta gaji da zama dai, ta tashi ta fara lellekawa cikin dakuna da wajaje.

Komi na gidan abin kallo ne, hatta da abin famfon tsakar gida abin kallo ne, balle sauran abubuwa. Kicin kuwa data leka, sai da lebenta ya kusa fadowa kasa. Komi na amfani biyu a ka kai mata. Tun daga kan gas cooker, da su washing machine. Su kuloli kuwa ba'a magana. Wani sai yayi tsammanin ko shagon sai da kayan kicin ne ya shiga.


Ta gyada kai sosai, ta girmama lamarin mutanen nan, daga baya ta musu addu'ar Allah ya bada zaman lafiya. Ta juya taci gaba da touring din gidan.


A falo suka ci karo da Eeshey ita da abokanta, tana ganinta ta wuce wajenta da sauri. Ita bata ganta bama sai da taji ta ambaci sunanta, sannan ta juya da sauri.

Cikin mamaki ta saki murmushi, tace "Eeshey!!".


Ga mamakinta sai ta rungumeta kamar wata shakikiyarta da suka jima basu hadu ba dinnan, ta daga baki da mamaki. Kafin ta saki yar dariya, ta sanya hannu itama ta rungumeta awkwardly. Kafin su saki juna.


Eeshey tace, "jiya nayi ta sa ido ina nemanki a wajen dinner, ashe baki je ba".

Ta gyada mata kai, "ehh. Kinsan mun sha ayyuka ne ai jiyan, shi yasa".

Suna tafiya suna yar hira har suka je inda abokanta suke, suka gaisa da Ameenatu din, kafin Eeshey ta kalleta, tace "me zai hana mu dan zauna? Yanzu zasu fara fito da refreshment, na gaji kwarai. Tun safe muke nan muna gyare-gyare".

Babu musu ta bita suka zauna akan daya daga cikin kujerun falon masu taushi kamar wasu cushions ko kuma auduga.


Babu jimawa kuwa aka fara fito da kananun plates masu dauke da samosa spring rolls, da lemu akai.

Zuwa lokacin gidan ya cika tsil da mutane, kowa ka gani taci kwalliya babu ta yar wa, kowa gani take yi ta isa fa ta kai.

Bayan sun gama cin abincin, amarya ta samu fitowa. Tayi shiri cikin wani rantsattsen yadin vowel ruwan jini, ta sha kwalliya kamar ba ita ba. Gabadaya ta canza kamanni, sai dai fa ta sha kyau Masha Allah. Nan aka fara daukar hotuna da sauransu.

A takaice dai sai can yamma aka tashi.


Eeshey ta sake sauke su a gida ita da Ameerah. Wannan karon har cikin gida ta shiga suka gaisa da Hajja kafin ta wuce gida.

Ranar nan dai da wuri suka kwanta su dukansu, saboda gajiyar zirga-zirga da suka sha.


*


Washegari a gidan Anty Maryam, yayar Saddiqa mahaifiyarta dake aure anan kofar Kaura ta wuni.

Ba cika zuwa gidan tayi ba, shi yasa ba wani sabon azo-a gani suka yi ba.

Yanayin tarbiyar gidan gabadaya tayi daban da irin tarbiyar data taso akai. Haka aka saki yaran sakaka, suke rayuwa. Babu kwaba balle gyara a cikin al'amuransu. Babu babba babu yaro, ga rashin tarbiya. Kada kuso ku ga yadda zaka ji babbar yarta na yaba mata magana kamar wata sa'ar wasanta, amma bata taba kwabar mata. Shi kuwa mijin ma da yake an fi karfinshi, bashi data cewa.


Itama da ba don Saddiqar da kanta ba ta dameta akan taje ba, da babu inda zata je.


Tunda tayi sallama gidan, aka yi mata jagora zuwa cikin gidan, bata kara ganin gilmawar kowa ba. Tana jiyo hayaniyar yara masu buga kwallon kafa a tsakar gida da wata dake fitowa daga dakin yaran masu kallo.

Gidan yanayin gininshi na masu rufin asiri ne daidai gwargwado. Dakin Anty Maryam din hade yake da ciki da falo da bandaki, sai na yara maza da mata sai kuma dakin maigidan da kicin da bandaki na tsakar gida.


Sai zuwa can sai ga Anty Maryam din ta fito daga can uwar dakar dakinta, wai gyaran bandaki take yi. Suka gaisa a tsaitsaye, ta kara fita tsakar gida dora girki.

Babbar diyarta mace Hafiza, na tsakar gidan akan kujera a zaune tana buga game a wayarta.

Ganin zaman haka nan ya isheta, yasa ta tashi ta fita tana tayata ayyukan. Su biyu suka hada abincin rana, yayin da sauran yaran kowa yake aikin gabanshi, babu mai ko yi musu sannu.


Suna saukewa, Hafiza ta dira a kicin din da plate a hannu, babu ko magana, haka uwar ta karbi plate din ta zuba mata abinci har da dora mata cokali, ta karba ta fita waje abinta ta zauna tana ci.

Daya bayan daya yaran suka dinga zuwa suna karɓar nasu abincin, sai da ta sallami kowa ma sannan shi mijin aka zuba mishi nashi. Aka zubawa Ameenatu nata itama.

Anan kicin ɗin ta zauna ta ci, tana gama ci, ta haɗa kayan da suka ɓata ta wankesu gabaɗaya ta shirya, ta share kicin ɗin ta goge, sannan ta fita daga kicin ɗin.


Inda yaran suka ci abinci duk anan suka bar kwanukan, wasu ma rabinsu duk abinci ne wanda ba'a gama cinyewa ba. Ta girgiza kai kawai ta shiga ɗakin inda Anty Maryam ɗin take zaune tana cin nata abincin.

Ta yiwa Ameenatu sannu, ta amsa. Hijabinta ta laluba tana ƙoƙarin sanyawa, Anty Maryam ta kalleta da mamaki tace, "har zaki tafi kenan".


Ta gyaɗa mata kai tana murmushi, tace "wallahi kuwa. Nasan Hajja tana can tana jirana, don tace kada in daɗe".

Tace "to madalla, sai yaushe za'a sake kewayo mu kenan?".


Ameenatu dai ta mata sallama ta tafi, a ranta tana furta, 'ƙila sai wata shekarar!'.


☆


Tana komawa gida, ta samu Ameerah na haɗa kayanta cikin wani rantsattsen akwatu. Ta kalleta sototo! cike da mamaki, tace "ba dai tafiya zaki yi ba ko?".


Ta ɗaga kai ta kalleta tana murmushin nan nata, tace "ai Ammy ta damu ne, kinsan bata son rabuwa da ƴar autarta! Amm kada ki damu, anan zamu yi sallah ai in Allah ya yarda".


Ameenatu dai bata ce mata komi ba, ta zauna a gefenta tana tayata gyara kayan har suka gama. Ta rasa abinda zata bata, sai ta ɗaga kayanta ta ɗauko humrar data haɗa, ta fita ta lalubo kwalba cikin shirgin kayan Hajja ta tsiyaya mata. Tayi ta mata godiya kuwa kamar wadda ta ɗauki wani hamshaƙin abu ta mata kyauta dashi, har sai data sanya Ameenatun taji kunya. Sai dai ta riga ta fahimci halin Ameerah ɗin sarai, haka Allah Ya halicceta. Ɗan ƙanƙanin abun alheri idan ka mata, ta dinga maka godiya kenan kamar bakinta zai tsinke. Sam bata da rainuwa. Wannan yana ɗaya daga cikin halayenta da yake burge Ameenatu sosai.


Gabaɗaya sai take jin ba daɗi game da tafiyar Ameerah ɗin. Ta riga ta saba da ita sosai, har mantawa take yi da cewa ba anan Katsina take da zama ba.


Washegari direban gidan Anty Uwani da zai kaita gida yazo tun da safe, Ameenatu da Hajja suka rakata har bakin mota. Ji take yi kamar tayi kuka, sai dai ganin Ameerah ɗin har ta fara share hawaye, yasa ta danne nata tana lallashinta. A haka suka tafi. Suna bada baya ta ɗauke kwallar data taran mata a ido, ta juya da sauri ta shige cikin gida.


Ranar gabaɗaya haka ta wuni, cikin kaɗaici da kewar Ameerah. Sai can bayan Azzahar ta kirasu ta wayar Hajja ta sanar dasu sai lokacin suka ƙarasa. Suka mata sannu da zuwa da Ala-huta gajiya.

Da yamma ta shirya ta shiga maƙotan gidansu Hajja, tana yawan shiga su gaisa lokaci zuwa lokaci.

Suna cikin yin hira, Maman Fatima, wata mata dake yin haya a gidan, da yake babban gida ne. Take tambayar Anty Habiba wadda Aminatun take zuwa wajenta, ko ina zata samu wadda take haɗa humra da turaren ƙamshi mai kyau? Ƙanwar mijinta zata yi aure, ake so a haɗa mata.


Ameenatu tayi caraf, tace aikuwa tana haɗawa. Ta shiga gida ta kawo musu ta wajenta suka ji yanayinta, nan suka zauna suka kuɗance tun daga abubuwan da za'a buƙata da kuɗin sallamarta, ta cewa Ameenatun washegari sai taje ta amshi kwatan kuɗin, idan ta gama zata bata cikon.

Da murnarta ta koma tana faɗawa Hajja. Abin ba ƙaramin daɗi yayi mata ba. Dama zaman haka nan ɗin ya fara takura mata ƙwarai.


Washegari kuwa ta shiga kasuwa ta fara siyayyar duk abubuwan da zata buƙata.


*


Sai ana washegari za'a ɗauki azumi sannan Huwaila, wadda take zaune da Hajja ta dawo Katsina ɗin.


Ko bayan data gama yiwa Maman Fatima humra ɗin, har cikin azumi akwai waɗanda suka dinga zuwa suna kaiwa tana musu, akwai masu yin ta sayarwa, amma yawancinsu matan aurene da suke yin amfani da ita a gidajen mazajensu. Ameenatu ba ƙaramin daɗi taji ba da bata yi ƙwauron baki ba ranar, tunda gashi ko banza ta samu abin riƙewa a hannunta. Da kuɗin da take samu suka ɗan yi sayayyar azumi, tunda ita dai Anty Uwani bata waiwayesu ba.


A wata waya da suka yi da Ameerah, tace a gabanta Daddyn Abuja ya turawa Anty Uwani kuɗin da za ayi musu sayayyar azumi da su, amma bata kai ko ƙwayar gero ba. Duk uba-uban aikin nan da suka sha na tuyar kayan biki, har yau basu ga wata sallama ba. Ameenatu dai bata saka abin a cikin ranta ba.

Abu ɗaya ta sani, shine, kowa yayi da kyau, kansa. Kuma kowa ya ɗebo da zafi, to bakinsa!.


Da yake ma babu laifi, sun samu kayan rabon azumi daga maƙota da abokan arziki babu laifi. Wani abokin marigayi Alhaji ma haka ya aika mata buhun shinkafa, katan ɗin taliya da macaroni da garwar mai, ya kai dubu biyar ya ɗora a sama ta cefane. Balle sauran alherai data samu. Don haka ko Anty Uwani bata kai musu komi ba, suna cikin godiyar Allah.


Sai da aka yi azumi na goma, sannan taje gidan ita da Fauzah. Affan ya riga ya koma bakin karatunshi.

Da dare suka je bayan an sha ruwa a tsaitsaye. Suka kai su garin kunu dana tuwo, da sauran kaya. Hajja nata zuba mata godiya da albarka, ita kuwa kai ya ƙara ɗagewa sama, sai wani amsawa take yi da ƙyar, tana wani shan iska.

Da takaici ya ishi Ameenatu sai kawai ta zari hijabinta, Hajja na tambayarta ina zuwa? Tace "wajen tarawihi".

Da yake bayan gidan suke zuwa ita da Huwaila, inda babban masallacin unguwar yake, tunda haɗe yake da ɓangaren mata.


Tana ji Hajjar na ƙorafin, "lokaci fa bai yi ba!". Ko kulata bata yi ba.

Huwaila ma ta ɗauki hijabinta tabi bayanta.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol