Free chapter · Read without an account

Eighteen

by Hauwau Shafiu · DUNIYA BIYU

Ta kula tunda ta dawo daga Katsina, Malam Hadi ya kara kafa mata kahon zuka. Yanzu kam kusan duk cikin makarantarsu babu wanda bai san cewa yana sonta ba, don wasu ma cewa suke yi soyayya suke yi. Duk da cewa har yanzu bai kai ga furta mata yana son nata ba, tasan cewa nan da dan kankanin lokaci ne hakan zata faru. Ita kuma gujewa hakan take yi tun karfinta. She's in enough trouble as it's now. Idanuwan matarshi gabadaya a kanta suke, duk wani taku da zata yi a cikin makarantarsu, duk wani lungu ko sako da zata shiga, idan ta waiwaya bayanta sai ta ga matar nan. 

Don haka bata kaunar duk wani abu ma da zai sanya su kebance su kadai, idan ka gansu a karkashin rufi daya to ko dai cikin aji, ko kuma cikin yan ajinsu. 


Yau ma kamar kullum, suna tashi daga ajin da suke zuwa na ranar Alhamis, taja hannun Hauwa da itama ta fara zuwa bayan sun dawo daga wannan hutun, suka fita daga ajin da sauri kamar wasu masu tafiya akan iska. 

Sun danyi nisa kadan kafin su kai ga fita daga makarantar, suka jiyo ana kwala musu kira. Wata matashiyar budurwa yar aji biyar ta tari gabansu tana dan nishi alamun sauri ta shaka, tace, "Ameenatu, Malam Hadi yace yana son ganinki yanzu".


Suka kalli juna ita da Hauwa, kafin ta maida kallonta ga yarinyar, tace, "ya za ayi? Sauri nake yi, jirana ake yi a gida saboda ina da ayyukan yi".

Yarinyar ta dan tsaya tana kallonta baki a dage, kafin ta daga kai a hankali, ta juya ta koma cikin makarantar. 


Hauwa ta kalleta tace, "ina ganin fa mutumin nan ya gama harbo jirginki".

Ta tabe baki, tace "to sai me? Ai bai gama fahimtar hakan ba, tunda da ya fahimta, da ya kyaleni zuwa yanzu!".


Hauwa'u tace, "me yasa ma kike mishi kauce-kauce ne? Nasan ba saboda matarshi bace, nasan halin Malama Rahane sarai, kawai tana yin hakan ne on instinct, kinsan mata. Amma bata da matsala ko kadan".

Dai-dai lokacin da suka wuce ta wajen tiredar Bangis, idanunta suka yi wuri-wuri, tana neman ganin idanuwan matashin wannan data gani kwanaki. 


Tun lokacin data ganshi, ta nemi wata nutsuwa tata ta rasa. Haka kawai lokaci zuwa lokaci, zata ji ya fado mata a rai. Ta samu kanta da son sake ganinshi, bata san me zata mishi ba ko zai bata, ita dai kawai so take yi ta sake sanya shi a cikin idanuwanta. Ta rasa ko me yasa. 

Ta sauke idanunta kasa, ranta ba dadi, ganin tiredar a wannan lokaci babu kowa a ciki sai Bangis din shi kadai yana sauraron rediyonshi. 

Hauwa'u ta dan zungurota, ta danyi firgigit tana kallonta, tace, "tunanin me kike yi ne wai? Na fada miki in dai akan Malam Hadi ne, ki daina sanyawa ranki wata matsala. Da gaske mutumin bashi da matsala, ina miki kwadayin kyawawan halayenshi".


Haka kawai taji ranta ya baci, ta samu ta danni zuciyarta da kyar, bata yi magana cikin fushi ba, tace, "wai duka nawa nake ne da zaki dinga min zancen aure, a gidan kishiya ma kuma? Ki bari in gama makaranta ma tukun kafin ki fara yi mun irin wadannan maganganu da kamfen mana!".


Hauwa'u ta kai mata duka a baya cikin wasa, tace, "kin kuwa ganki kuwa? Ni nasan ko gidan mata uku aka kaiki ke ta hudu, zaki tsira ki zauna lafiya. An gaya miki yanzu girma a fuska yake ne?".

Ta daga kafada kawai. 

Suna zuwa kofar gidan su Hauwa din, ta dakata tana kallonta. Hauwa'u tace, "ba zaki shigo bane?".


Ta girgiza kai, "a'ah, Baba Habu ya fara min fadan kin dawowa daga makaranta da wuri da nake yi. Zan dai shigo anjima kallo".

Tace "to ai shikenan. Ki gaida su Nana".

Ta juya ta shige gida, ita kuma Ameenatu taci gaba da tafiya zuwa inda ta nufa. 



•Φ•¤•Φ•



Saura kiris ya rage ta zube a tsakiyar falonta saboda tsabar firgici. Ta dafe kirjinta da yake masifar bugawa, zuciyarta kamar zata tsaga kirjin nata ta fito. 

Wanda yayi sanadiyar haka din, ya daga kai daga wayar hannunshi da yake kallon labarai da ita. Ya sakar mata murmushi. Bata san lokacin data jefa mishi harara mai zafi ba.


Murmushi ya sakar mata na tura haushi, taja tsaki ta fada kicin kawai. Tana jin haushin wannan abu da abokin Fahad, Sahabi yake mata duk da cewa tasan fuska ya gani daga wajen maigidan. Kusan kullum a cikin gidan yake karyawa, watarana ma har abincin dare acan yake ci. Wannan duk ba matsalarta bace ba, sammakon da yake musu a gida shine abinda yake bata mata rai. Ta kuma yiwa Fahad din korafin haka, amma ya bata excuse din cewar saboda shi PA dinshi ne, kuma tare suke gudanar da duk wasu ayyukan office dinsu. 


Zuciya cike da tunanin wannan lamari ta kunna gas ta fara girki. Ba kamar Fauza da ko ruwan zafi bata iya dafawa ba, ita ta iya girki. Watanni shida ta dauka cur tana ziyartar wata makarantar koyon girki tun da maganar aurenta ta tashi. Haka ko a gida ta kan shiga kicin, musamman idan ranar aka girka musu abinda bai kwanta mata a rai ba. 

Yam balls ta soya musu wanda ta sanya dafaffen kifi da nama a ciki, ta hada shayi wanda yasha kayan kamshi ga kuma wainar kwai a gefe. Ta daukesu daya bayan daya tana kaiwa falo, ta gaban Sahabi dake ta fama da danne-dannen iPad din hannunshi tayi ta wannan zaryar. Bayan ta gama shirya komi sai ta koma dakinta don ta shirya. 


Farko-farkon aurensu da Fahad din duk a dakinshi take shiryawa da komi, sai dai duk su fita a tare su duka. Daga baya sai ya koma yace mata ta dinga shirin a dakinta don shiryawarta anan tana takura mishi, taga menene abin takura a cikin haka? Amma bata ce mishi komi ba tabi maganar daya gaya mata. A hankali shima kwanan dakinshi ya hanata, sai dai duk lokacin da shi yake bukatarta yaje nata dakin. Duk wannan bai dameta ba akan tsana da kiyayyar da danginshi kuma surukanta suke nuna mata kiri-kiri. Ita ba wani mugun hali take nuna musu ba, Mommy dai tace ta basu lokaci ta gani, wai idan ta haihu zasu daina. 


Cikin wata atamfar cote d'evoire brown ta shirya. Zanin single ne, rigar kuma fitted ce, ta kashe daurin dankwalin nan kamar zata je wajen wata shahararriyar dinner. Abinka da kyakkyawar farar mace, sai ta fito das da ita kamar ka dauke ka gudu. 

Ta fita daga dakinta ta shiga falon tana takunta daya bayan daya cike da daukar hankali. Ta samesu su duka biyun akan dinning har sun fara cin abincin. 

Kujerar dake fuskantar Fahad din taja ta zauna fuskarta dauke da murmushi, tace, "dear barka da asubah!".

Ya dan kalleta, "barka dai, kin tashi lafiya??".

Ta gyada kai, "lafiya lau baby... Mommy tace a gaisheka, kwana biyu baka leka kun gaisa ba!". Kokari take yi taja hirar tasu ta danyi tsayi, sai taga ya gyada kai curtly, "ina amsawa", kawai yace. 


Ya maida hankalinshi kan Sahabi suna tattaunawa akan wasu ayyuka da suke kan yi. 

Fahad ya fito daga babban gida, gida na kudi da kuma siyasa kamar dai gidansu mahaifinta. Yayi karatunshi akan architecture and designs, kamfani guda gareshi nashi na kanshi. Suna gina manyan makarantu, gidaje, asibitoci, kai almost everything. Haka duk wata kwangila da zata fita daga gwamnati, to kusan su suke daukarta. Sahabi abokinshi ne na yarinta, tare suka yi karatu dashi kuma tare suke kula da kamfaninshi. Shi Bashir shi yake kula da samar musu kwangiloli, yayinda shi kuma yake daga ofis yana kula da harkokin can. 


Suna ta maganganunsu akan ayyukansu yayinda tayi kasa da kanta cikin kunar zuciya. Tasan cewa auren hadi aka musu, amma a ganinta zuwa yanzu ya dace ace sun rungumi junansu. Amma har yanzu, duk kokarin da take yi wajen ganin ta karkato da hankalinshi kanta, abin yaci tura. Kullum kara ja baya yake yi da ita. Bata san yadda zata yi ba. 


Tsakurar abincin kawai ta dinga yi har suka gama ci suka tashi, ta dauki brief case din Fahad din ta bisu a baya. 

A bakin kofa suka dakata shi kuma Sahabi ya danyi gaba. Ta mika mishi jakar fuska dauke da murmushi, tace, "a dawo lafiya Honey, Allah Ya tsare hanya".

Yasa hannu yana karbar jakar fuska babu yabo babu fallasa, yace, "nagode!", ya juya abinshi. Ita kuma ta maida kofar ta rufe. 


Sauran abincin ta dauke ta sanya a microwave, su zata ci anjima da rana. Dakinta ta koma ta kwanta da niyar yin barci, amma sam yaki zuwa, tayi ta juye-juye akan gado. Daga karshe dai taga ba zata iya yin barcin ba ta tashi tare da jan wayarta ta kira Mommynta. 

Bugu uku ta dauka, sun gaisa kamar yadda suka saba, kafin tayi kasa da muryarta ta fara zuba mata shagwaba akan ita aiki take so a samar mata. 


Mommy ta dan dafe kanta, tace, "yanzu Badi'atu ba zaki kyaleni in huta da maganar nan taki ta aiki ba? Yanzu kina diyar mutum kamar Yakub Alkali, kuma matar Fahad Dukku, aikin me kike bukatar kiyi kuma? Kudi da matsayi kin riga kin gama samunsu!".


Tace, "amma Mommy zaman haka nan din da nake yi ya isheni wallahi. Ni don Allah ko yaya aikin yake ki taimaka a sama min wallahi na gaji da zaman banza!".

Mommy tace, "ai duk laifinki ne baby, ance a samar miki yar aiki wadda zata dinga tayaki ayyukan gida kin ki, to ya kike so in miki? Ke gaki ba wani yawace-yawace kike yi ba kamar Fauza!".


Ta dan tabe baki, ba wani abin mamaki bane, duk cikinsu tafi son Fauzah, kuma bata jin kunyar buga musu misali da halayen Fauza din. Kodayake dole tasu tafi zuwa daya saboda halayensu duk kusan daya ne, tana kuma bin maganar Mommy din sau da kafa koda bata son hakan, abinda ita Badi din bata cika yi ba kenan. Ba kasafai ake sanyata tayi abinda bata yi niyyar yi ba. Tace, "daukar yar aiki yanzu ai yayi kusa Mom, duka menene a cikin ayyukan gidan da ba zan iya yi ba? Ni dai don Allah ki taimaka ko Uncle Mahmud, (kanin Daddynsu) ki yiwa magana ko a asibitinshi ne a sama min wani abu!".


Mommy tace, "shikenan ai tunda kin kafe, zan mishi magana din sai muga yadda za ayi!".

Ta danyi tsalle akan gado cike da murna, "yes! Kai Mommy ina sonki wallahi. Nagode!".

Mommy tayi murmushi cike da murna, tana son farantawa yaranta rai kamar me. Tace, "kina dai shan magungunan nan dana aiko miki ko?".


Badi ta danyi shiru kamar ba zata amsa ba kafin tace, "eh!".

Mommy tace, "Allah Yasa da gaske kike, wallahi kada ki min asarar kayan nan, baki san kudin da aka kashe a kansu ba kafin ma su iso nan kina jina?".

Tace, "da gaske nake Mommy... Ki gaida Fauza idan ta dawo daga makaranta, kwana biyu bata leko min ba". Ta canza akalar hirar tasu tun kafin Mommy ta cafkota ta hau fadan data saba. 


Tace, "Fauza kwana biyu anyi hankali, bata fashin makaranta saboda jarabawar waec dinsu da take ta matsowa".

Ta jinjina kai tana dan murmushi, "lallai, ashe shi yasa naji ta shiru kwana biyu. To a gaishe da ita idan ta dawo".

Mommy tace, "zata ji!", suka yi sallama ta kashe wayar. Kan gadon ta koma ta kwanta rigingine tana wasa da dan pendant din jikin sarkar dake wuyanta. Ita da Mommy take ta faman tura mata magungunan mata tana sawa tana dirka, ko don Mommy din bata san halin da suke ciki ita da Fahad din bane? A sati bai fi ya nemeta sau daya ba, shima ba wani haduwar azo a gani bace ake yi, cikin yan mintuna ya sallameta ba tare da damuwar ita ta samu abinda take so ba ko a'ah. Shi dai tashi damuwar kawai kanshi. Ta kula duk duniya babu abinda ya kai aikin da yake yi muhimmanci a wajenshi. To ina ita ina amfani da kayan mata a wannan hali da take ciki? Daga farko data fara amfani dash, taga suna nema su hargitsa mata lissafi ko kuma su jefata hanyar da bata dace ba, don haka ta tarkata su tana tarawa a ma'ajiya don kuwa basu da wani amfani. 


Wayarta ta sake dauka tana danne-danne, aikin kenan indai tana gida. Ko a mafarki, bata taba tunanin rayuwar aurenta zata kasance a matakin da take yanzu ba. Ta kuma yi kudiri, taci burin shirya rayuwar aure ita da mijinta mai kyau da tsari, cike da so da kulawa. Tana da saurayinta da suka shirya wannan rayuwar dashi, but apparently matakinshi bai kai matsayin aurenta ba a cewar iyayenta. Bata da karfin ja dasu ta wannan bangaren, dole ta rabu dashi ta kama wanda suka kai mata a dare daya. Duk da babu soyayya a tsakaninsu, a ganinta wannan karamin aiki ne a wajenta. Ko babu komi tana da kyau, kudi, da sura mai daukar hankalin da namiji, tayi tunanin wadannan sun isheta zama makaman yakin da zata yaki zuciyarshi da ita, amma hakan yana nema ya zame mata kamar da wuya, wai gurguwa da auren nesa. 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol