Free chapter · Read without an account
Twenty
by Hauwau Shafiu · DUNIYA BIYU
Anty Momy ta biyo matakalar jirgin daya daukota daga Jos, a hankali, kuma cike da gajiya. Wani meeting ne da aka yi da manyan matan gwamnoni dana yan siyasa ta halarta. Kasancewar zabe yana ta matsowa, gashi duk da sakin kudin da suke yi ita da mijinta amma babu alamun nasara a bangarensu, gashi duk wadanda suke bukatar su sanya musu hannu sunyi biris dasu, shi yasa ta kara kaimi. Wanda zai zama matakalar da zata sadata da shugaban kasa take nema ruwa a jallo, domin tasan da maganarshi daya akansu, zasu iya lashe zaben primary election dake tunkarosu a satika masu zuwa.
Kamar da wasa taji ana kiran sunanta daga bayanta, ta juya da sauri tana kallon wata hadaddiyar mata. Tun daga kan takalmin kafarta har zuwa yan kunnayen dake kunnenta, kasan cewa kaga babbar mace. Mommy taji kishin matar ya caketa a kahon zuciya a take. Ta tsani taga wani wanda zai yi shigar data dara tata. Amma daga ganin yanayin matar tasan cewa wannan tafi karfin tayi mata wulakancin data saba yiwa mutane, don haka ta kalleta da yar fara'arta a fuska, tace, "na'am?!".
Matar tayi dariya data fitar da jerin fararen hakoranta tas-tas, tace, "haba! Ni fa ince kamar Uwani Badamasi, ashe ke din ce da gaske!!".
Mommy ta kalli matar da mamaki zane akan fuskarta, tace, "naji kin fadi sunana, sai dai ni ban gane ko wacece ba!".
Zuwa lokacin sun gama sauka daga kan jirgin, suka jera suna fita. Tace, "dama ba lallai ki gane ni ba, Aisha Sade ce, tare muka yi ABU dake?".
Ta kare mata kallo zuciyarta cike da tantama, mawuyaci ne kuwa hakan ya wuceta. Don kuwa lokacin da suka yi makaranta, duk wani dan mai kudi da shuni ta san shi, don kuwa shine abokinta. Bata harka da wasu tagajan-tagajan, don haka da kyar ne ta kasa ganeta. Duk da haka sai ta sake yin murmushi tana kallonta, tace, "ai da yake kinsan shekarun da dama gaskiya".
Aisha ta gyada kai, "hakane gaskiya. Ya bayan rabuwa?".
Mommy tace, "Alhamdulillah! Kina zaunene anan Katsina?".
Ta girgiza kai tana dan murmushi, "a'ah, a Europe nake zaune. Surukata da tayi rashin lafiya muka zo dubawa".
Mommy tace, "Allah sarki! Allah Ya kara mata lafiya".
Tace, "ameen!".
Sun fita daga waje inda yan acaba da motoci suke jiran mutane, Mommy ta hau raba idanu tana neman ganin direban gidansu. Tun kafin ta taso ta kira Fauza da a ranar suka fara rubuta jarabawar waec akan ta tura mata direba, tace to. Babu mamaki barci ta hau yi abinta don dama tana ta mata korafin a gajiye take. Wayarta ta ciro daga cikin jaka ta fara kiranta, amma kuma wayar nata ringing amma ba'a daga ba. Tasan a silent ta sanyata. Tayi tsaki a ranta tana tunanin idan ta kuskura ta koma gidan sai ta bata mata rai sosai.
Tana shirin juyawa ta tsallaka wajen masu napep taji Aisha tana yi mata magana, ita har ga Allah tama manta da ita. Aishar tace mata, "har zaki wuce ne?".
Ta juya tana dan murmushi, "wallahi kuwa. Direban da zai daukeni bai karaso ba, da alama sakon dana bari a gida bai karasa gareshi ba".
Itama sai tayi yar dariya, tace, "yara kika barwa sakon ko? Kinsan su fa sai a hankali. Me zai hana kizo sai mu saukeki? Ga d'ana can yazo daukata".
Ta nuna mata can tsallaken titi. Tana shirin cewa ta gode, ta hango motar da Aisha din take mata nuni da ita. Wata bakar Jaguar tana ta daukar ido a cikin hasken rana, daga ganinta ko dai sabuwa ce ko kuma wadda ba'a cika hawa ba. Mommy ta daga baki, lebuna suka kusa faduwa kasa saboda tsabar mamaki, wacece Aishar nan exactly da har za'a dinga zuwa daukarta a Jaguar? Jaguar dinma daga gani ba irin kananan bane.
Aisha tace mata, "muje ko?".
Mommy actually stutters, abinda bai cika faruwa da ita ba, tace, "to!!... Ehh.. muje!!". Suka jera zuwa wajen motar. Tun kafin su karasa, wani hadadden matashi daya sha jamfa ya fita daga gefen direba da sauri ya bude musu gidan baya. Aisha din tana zuwa zata shiga motar ya duka yana bata sumba a kumatunta, yace, "sannu da zuwa Ammina!".
Tayi murmushi cike da nuna kauna, "yauwa my Anwar! Ya Katsina din?".
Ya kada idanu yana tabe baki cike da wani irin malle, "good, I guess!".
Aisha tayi dariya tana shigewa cikin motar. Sai daya bari Mommy itama ta shiga sannan ya maida murfin motar ya rufe tare da zagayawa daya gefen. Aisha ta kalli Mommy dake raba idanu a cikin motar, interior din motar ya matukar dauke mata tunani, wasu zallan leather masu dan banzan taushi da sheki. Tace mata, "Anwar kenan babban dana! Wannan ne karo na farko da yazo Nigeria in like 5 years, a kasar Landan yake karatunshi akan kasuwanci hade da siyasa".
Mommy tayi wani dan murmushin yake, jikinta ya gama yin sanyi da wannan mata gabadaya. Tace, "Allah sarki!", don kalmominta sun gama karewa.
Sai da Anwar ya dauki titin shiga cikin Katsina sannan Aisha ta kalli Mommy tace mata, "a ina zamu ajiyeki?".
Mommy tace, "A unguwar Kangiwa nake". Aisha ta fara ba Anwar direction na inda zai shiga. Basu kara cewa juna komi ba sai da suka shiga unguwar su Mommy. Anwar yayi parking din motar a kofar gidansu Mommy, tace musu "ba zaku karasa daga ciki ko ruwa ku sha ba?".
Aisha ta girgiza kai da sauri, "a'ah wallahi mun gode, sauri muke yi kinga yamma ta fara yi".
Mommy tace, "to shikenan. A wace unguwa kuke zama? Yakamata muzo mu kara yin godiya mu kuma duba surukarki da jiki".
A'isha tace, "a gidan Alhaji Abubakar Turaki muke!".
Sai da Mommy taji kamar zata fadi kasa saboda jirin daya daukota a zaune! Ta daure tun karfinta bata yi ihu ko ta zube kasa ba, suka yi musayar lamba ita da Aisha din, ta fita daga motar Anwar yaja su suka tafi da alkawarin zata je mata ziyara kafin su koma. Tana tsaye a bakin gate har suka bace mata, kafin ta juya ta shige gida jikinta na masifar rawa saboda doki da murna. Iyalan Turaki? Turaki dai da danshi yake shugabantar Nigeria a wannan marra? Ita kuwa yau wace irin sa'a ce taje mata kamar daga sama? Tayi dan murmushi, tsohuwar abokiya kuma surukar gidan Abubakar Turaki? Wannan fa shi ake kira tsuntsu daga sama gasasshe!.
Sai data watsa ruwa ta kuma ci abinci, sannan ta dauki waya ta turawa Hajiya Aisha sakon gaisuwa da godiya akan mutuncin da suka mata. Ta kuma sanar da ita a gobe-gobe zata je gida ta sameta.
Dakin Fauza ta wuce, ta sameta a kwance akan gado tayi dai-daya tana barci ko uniform dinta bata cire ba. Mommy ta girgiza kai kawai in adoration, ta kara saita mata gudun split tare da maida mata kofar dakin ta rufe.
Kai tsaye bangaren Alhaji Yaqub ta nufa. Idan ba wata magana bace mai muhimmanci ta tashi ba, sai tayi fiye da wata ma ba tare data taka kafa taje bangarenshi ba. Tuni mu'amalar ma'auratan ta koma pure business. Babu wata mu'amala a tsakaninsu a yanzu data wuce ta siyasa da kasuwanci, bayan haka babu komi. Kwanaki can baya abin ya dameta kwarai, har ta sanya kanta harkar bin malamai da yan tsibbu wajen ganin ta karkato da hankalinshi kanta. Taga dai abin bai yiwuwa, ita kuwa girman kanta ba zai barta ta bi kan miji ta laluma ba don haka ta watsar da komi a gefe ta rungumi duniya da kyale-kyali. Gani take yi tafi karfin ta zauna tana bin kan namiji akan ya so ta ko ya kula da ita.
Akan daya daga cikin kujerun falon ta sameshi yana kurbar lemu daga cikin kofi, ya saka babbar TV din dake a cikin falon yana kallo, ga kuma waya a hannunshi yana dannawa.
Ta samu kujerar dake kusa da tashi ta zauna fuska dauke da dan murmushi, tace, "Alhaji har kun dawo daga gun meeting din?".
Ya kurbi lemu tare da dora kofin akan karamin teburi dake gabanshi, "wallahi kuwa, babu wata nasara da muka samu. Mun dai samu Alhaji Munzali Harka ya koma bayanmu, amma duk da haka muna bukatar wasu mutanen... Ya naku meeting din ya kasance?".
Ta tabe baki, "kusan dai babu nasarar duk da mun kara samun magoya... Ai baka san wa na hadu dashi a filin jirgi ba yanzu Alhaji!!".
Ya kalleta a kaikaice, "wa?".
Tayi dan murmushin jindadi, "Daya daga cikin surukan Alhaji Abubakar Turaki!".
Sai lokacin ya dauki duka hankalinshi ya mika mata. Ya karkata sosai yana fuskantarta, yace, "da gaske? Ta yaya?".
Mommy ta gyara zama ta bashi labarin yadda suka hadu da ita tun daga farko har karshe, har ma da alkawarin ziyartarta da tayi, duka ta fada mishi, Daddy ya rasa abinda zai ce saboda tsabar mamaki, sai "wow!!" kawai daya iya furtawa. Mommy ta dinga gyada kai tana murmushi.
Yace, "Hajiya! Wannan ai lokacin zama bai samemu ba, zuwa zaki yi ba tare da bata lokaci ba ki tuntubeta akan maganar, ta samu ta hadamu da Mr. President".
Mommy ta mishi kallon kasa-kasa da idanunta, "amma kasan wannan harkar ai bana sanya ko? Tuni na sanar da ita zamu je gobe, ta kuma dawo min da amsa akan tana zuba idon ganinmu!".
Ya gyada kai cike da gamsuwa yana murmushi sosai, "gaskiya kinyi kokari sosai. Shi yasa nake matukar alfahari dake wallahi! Idan bake ai har ban san yadda zanyi ba!". Mommy kanta yayi fum! ya kara girma. Sai a irin wadannan lokuta da samu ya samu take ganin murmushi da kalmomin yabo daga bakin mijinta. Amma hakan bai taba damunta ba ko kadan.
Daddy ya tashi zuwa wajen wani shelve da aka jera kofuna na gilashi iri-iri, ya dauko daya tare da bude dan karamin firjin ya tsiyaya lemu a ciki. Ya koma wajen da take zaune ya mika mata, ta amsa. Bata cika shan lemu mai inabi a ciki ba, amma ai one time thing ne ko? Kuma ba sani bata son inabi yayi ba, don haka babu damuwa. Ya dauki nashi lemun ya mika mata alamun cheers, tayi murmushi tare da daukar nata suka yi clinking bakunan kofunan, yace, "to a bright future!".
Tayi murmushi tana maimaita abinda ya fada, suka kai kofunan baki suka kurba a lokaci guda.
Sunyi shiru suna kallon labarai da ake nunawa, ta gyara zama tana kallonshi, "kasan tana da babban da kamar Affan dinmu wanda ya gama karatu a London? Kuma akan kasuwanci da siyasa yayi karatun?!".
Ya kalleta, "so?!...", kafin wani tunani ya darsu a cikin ranshi, ya dubeta sosai, "kar dai?!...", murmushin da yaga tana yi shi ya tabbatar mishi da zargin da yake yi. Ya girgiza kai cikin jinjinawa tunani irin nata, yana yar dariya yace, "Hajiya! Hajiya!! Allah dai Ya bar min ke!!".
Mommy tayi murmushi idanunta akan TV, kanta yana kara huruwa!.