Free chapter · Read without an account

Twenty One

by Hauwau Shafiu · DUNIYA BIYU

_Dutsinma_*



Satin daya wuce suka gama zana jarabawar Waec, yanzu sun dan samu hutune kafin su fara neco. Duk da tasan cewa ita jarabawa irin wannan ba'a yanke hukunci akanta da wuri, tana da yakinin cewa zasu yi abin kirki su duka don kuwa sun dagewa karatu da addu'a sosai.


Ta dauki hijabinta da take ajiye akan gadon Nana ta rufa akan riga da siket na atamfa mai ruwan ganye dake jikinta. Fita tayi daga dakin bayan ta duka ta dauki babbar bakar leda dake kasa ajiye a gefen gadon.


Nana tana cikin madafi tana tuka tuwon dare akan murhu. Ta kalli Ameenah dake kokarin sanya takalmi, tace, "har kin fito ne?".

Tace, "ehh Nana, bari muje".

Nana tace, "ki duba Larai din da kyau don Allah. Muma zamu kara komawa ko zuwa gobene ni da Asabe sai mu kara dubata".

Ta gyada kai, "zata ji in shaa Allahu". Ta kada kai ta fita.


Gidansu Hauwa'u ta wuce kai tsaye, ta sameta a shiryenta tsaf tana jiranta. Suna gaisawa da mutanen gidan ta shiga dakin da Hauwa'u da kanwarta Asiya suke zaune, ta dan harareta cikin wasa lokacin data sameta a shiryenta, tace, "ai nayi zaton yau ma wani jiran zan sake sha".

Itama ta harareta, "dalla can Malama, an ma yi kokari an shirya da wuri din sai an yiwa mutane korafi?!".

Ameenah tayi yar dariya, "ni don Allah taso mu tafi kada dare yayi mana a hanya kinga yamma tayi".

Hauwa'u din ta tashi babu musu ta dauki hijabinta itama ta sanya suka fita.


Inna Larai mahaifiyar Ahmad tayi rashin lafiya sosai har da kwanciya a asibiti, duka-duka jiya aka sallamota. Da yake basu samu sun je asibitin dubota ba sai Nana da makociyarta da suka je, sai yau ne ta nemi Hauwa'u da ta rakata.

Tun da safe taje bakin kasuwa ta sayo kayan marmari masu kyau har da karawa da lemun fanta da teem guda bi-biyu.


Tayi sa'a tun wannan fadan da suka dan yi akan Ahmad ita da kawayenta suka dan sassauta duk da cewa har lokacin basu saki jiki dashi sosai ba amma kuma suna kokarin ganin cewa basu nuna mishi basa maraba dashi ba karara. Shi kuwa da yake mutum ne mai barkwanci da shiga harkar mutane sosai, tuni ya mayar dasu abokanshi suma. Duk inda ya gansu zai dakata ko akan mashin yake ko wani abu su gaisa dasu, don haka babu laifi sun dan fara sabawa dasu.

Da wayar hannun Hauwa'u tayi amfani ta kira Ahmad ta sanar dashi sun fito, don haka a kofar gidansu suka sameshi yana jiransu.


Tunda suka karya kwanar gidan, ya kura mata ido fuskarshi dauke da murmushi. Kusan kwanaki biyar basu ga juna ba sai ta waya kadai suke samun damar gaisawa shima sai idan taje gidansu Hauwa'u ko kuma ita taje wajenta take taboshi su gaisa.

Hauwa'u ta zungureta da hannunta tana mata nuni da Ahmad din da yake ta faman kallonsu, tana daga mata gira cikin tsokana. Ameenah taji kamar kasa ta tsage ta shige ciki, ta dai daure ranta har suka karasa wajen da yake.

Sanye yake da wandon jeans wanda daga gani ya fara jin jiki amma kuma a wanke yake tsaf a goge, ta kula yana da tsafta babu laifi. Sai ya dora yar tee mai guntun hannu. Bata taba ganinshi da kaya native ba, sai kanana, idan ka cire lokacin da zai yaje duba Baba Habu. Idan ma ka ganshi da rigar shadda ko ta yadi, to sai dai shigar nan ta samari yan zamanin yanzu, rigar shadda da wandon jeans. Ya taje sumar kanshi irin ta fulanin usul da yake yawan tarawa akanshi, amma ba kamar ta sauran samari da zaka gani tayi tsaye cirko-cirko a kansu ba, shi tashi a kwance take luf kamar ya sanya wata relaxer ko kuma ya shafa mai.


Magana ta gaskiya Ahmad kyakkyawan mutum ne. Ba kyakkyawa da za'a sa cikin jerin kyawawan mutane ba, amma kuma ba za'a sanya shi cikin jerin munana ba. Daga ganinshi kaga dan fulani, yanayin hancinshi da kuma idanunshi. Ya kallesu fuska dauke da murmushi, yace, "barkanku da zuwa, ya hanya?".


Ameenah tayi kasa da kanta tana dan murmushi, sai Hauwa'u ce tayi yar dariya tace, "wai ya hanya sai kace wadanda suka yi tafiyar zango bayan nan ne baya!".

Yayi dan murmushinshi idanunshi akan Ameenah, "amma dai kunyi tafiyar ko? Gimbiya barka da yamma". Ya maida akalar maganar ga Ameenatu. Da kyar ta iya daga baki tace mishi "ina yini?".

Yace, "lafiya lau Gimbiya Ameenah. Mu karasa daga ciki ko?", ya musu jagora suka shiga gidan.


Gidan babban gidane da tarin fili a tsakar gidan. Dakuna biyu ne a gidan, sai bandaki da wani waje da aka zagaye da langa-langa duk tayi baki da tsatsa daga gani ba ta yau bace, tafi kyautata zaton madafi ne. Duk da fadin tsakar gidan da kuma cewa kasa ce a shimfide babu suminti, amma a share yake tas baka ganin ko kwayar haki.

Ahmad ya musu jagora har zuwa cikin dakin Inna Larai, suka sameta zaune a gefen gadonta na karfe irin na mutanen da, taci kwalliyarta cikin atamfa block wax. Ta taresu da fara'arta sosai, suka zube a tsakiyar dakin da yake malale da ledar tsakar daki wadda ta fara yagewa da cirewa suna gaidata.


Tayi musu nuni da kujera dake daukar mutum biyu, ita kadai ce a dakin bayan kayan kallo, sif da kuma gado. Tace musu, "haba don Allah, ku tashi ku zauna akan kujera mana!". Hausarta bata fita sosai, daga ji kasan cewa fulani ce tsantsa.

Kamar hadin baki, ita da Hauwa'u suka girgiza kai, suka ce "ina wuni Inna?".


Tace "sannunku-sannunku yanmata, ya gajiyar gari?".

Suka ce, "Alhamdulillahi Inna, ya saukin jiki kuma?".

Tace "jiki yayi sauki ai, madallah, sannunku nagode-nagode!!".

Hauwa'u ce tace, "Allah Yasa kaffarane inna".


Su duka suka ce ameen. Ta kalli Ameenah tace, "ya tsofi kuma? Naji ance ke jikar Nanar Malam Habu ce ko? Ranar nan ai sun je suka dubani ita da Asabe, mutane masu kirki da mutunci! A kara min godiya a wajensu don Allah, nagode Allah Ya bar zumunci da kauna".


Ameenah ta dan sadda kai kasa, "itama tace a dubaki sosai Inna, tace zasu sake lekowa su dubaki".

Tace, "madallah madallah! A gaya mata nagode, ai nama ji sauki wallahi!".

Ahmad ya fita ya dawo musu da ruwan pure water da lemun mirinda mai sanyi, daga gani bai jima da sayosu ba a shago. Ya tsiyaya musu a kofi ya mika musu, dan kurba kawai suka yi. Inna Larai tana jansu da yan hirarraki har zuwa lokacin da suka mike zasu tafi, Hauwa'u ta matsa ta ajiye mata ledar a kusa da kafafunta, Inna tace, "abin har da hidima kuma yanmata? Gaisuwar ma ai ta isa wallahi. Sannunku da kokari, nagode, Allah Ya shi muku albarka. A gaida manyan a kuma yi musu godiya kwarai!!".

Suka mata sallama suka tafi cikin rakiyar Ahmad.


Suna fita, Hauwa'u ta danyi gaba ta barsu yadda zasu tattauna sosai. Ahmad ya kalleta da wani irin kallo da yake mata a cikin yan kwanakin. Sai taga yana mata irin kallon nan da kamar rayuwarshi tana revolving a tata rayuwar ne, kamar babu wata halitta abar girmamawa a wajenshi kamar ita. Wannan... Shi yake sa wani lokacin ta kasa hada idanu dashi, ko kuma taji kamar kasa ta tsage ta burma ciki.


Yace, "na gode sosai Ameenatu, wallahi ban san da bakin da zan miki godiya ba ko kadan, nagode kwarai, Allah Ya saka da alkhairi".

Sai ta rasa abinda zata yi ko ta ce mishi, ta rufe fuskarta da hannuwanta biyu tana girgiza kai a hankali, "haba haba! Godiyar me kake yi mun haka? Inna ai tamkar uwace a gareni, don haka ban ga amfanin wannan godiyar da kake yi ba".

Yace, "duk da haka Ameenah! Nagode, ki barshi a hakan kawai! Bayan doguwar tafiya da kuka sha haka kuma har da wata hidima ta daban?".

Ta gyada kai, "to shikenan!".


Ya daga kanshi yana kallon sararin samaniya data fara yin duhu alamun magriba ta kawo kai, yace, "kada Hauwa ta gaji da jira, gashi kuma dare ya fara alamun yi. Idan na samu sarari anjima da dare zan leko in kara muku sannu".

Tayi dan murmushi, "Allah Ya kaimu daren lafiya. Sai anjima".

Ya dan daga mata hannu shima yana murmushi, "sai anjima Ameenah!".


Ta juya da sauri ta tunkari inda Hauwa'u take a tsaye tana jiranta. Suka jera suna tafiya suna hira wadda ta danganci irin tarbar da Inna Larai ta musu. Ba karamin jindadin tarbar suka yi ba, akwai alamun halin dattako da mutuntaka a tare da yar tsohuwar sosai.

Suna zuwa kofar gidan su Hauwa'u suka rabu bayan ta mata godiya sosai, Hauwa'u ta shige gida ita kuma ta karasa nasu gidan.


Ta samu Nana tana fama da gyaran naman kai, ta cire hijabin jikinta tana murmushi, "yau kice dadi zamu ci a gidan!".

Nana tayi yar dariya, "ke dai bari! Malam ne da rigima wai ya amso wajen yan albashi wai a dan motsa baki".


Tace, "to in dai an samu an motsa bakin ai da sauki, Allah Ya hore Ya kuma kawo wadanda za'a biya bashin dasu idan watan ya kama".

Nana tace, "ameen dai, amma ban cika son dauke-dauke bashin nan ba musamman na karshen wata, mutane ba kirki da uzuri ke garesu ba, sai kiga ana neman sabani ya shiga akan abinda bai taka kara ya karya ba".


Ta jinjina kai, ita kanta bata son haka. Taki jinin a biyota bashi koda na kwandala ne. Sa'ar su daya ma da Malam Habu din bai cika wadannan dauke-dauken ba, idan har kaga yayi hakan to dama sai ire-iren wadannan abubuwan, suma kuma ba koda yaushe ba.


Tace, "bari in canza kayan jikina sai inzo in kama miki".

Nana tace, "a'ah, yi zamanki abinki. Kije kiyi sallah tunda yanzu za'a fara kira, in kin gama kuma ki dauki littafi kiyi karatu, ke mai shirin fara zana jarabawa nan da yan kwanaki?".

Ameenah tace, "to shikenan, bari in shiga inyi sallah!". Ta shiga daki tana rage kayan jikinta. Kafin ta fita da niyar yin alwala.


*_Katsina_*


Turaren Saudi Oud ta dauka tana fesawa a jikinta. Duk cikin tarin turarukan dake jere a saman mirror dinta, shi kadai yake mata dadin shaka. Shi yasa ta tarkata duka sauran turarukan ta watsa su can karshen wardrobe dinta. Ta zaro wata siririyar sarka mai kululun adon rose mai fadi baki ta makala a wuyanta tare da makala yan kunnen a kunnenta. Karewa kanta kallo ta dinga yi a cikin babban mirror din dake gabanta. Gabadayanta ta wani kumbure kamar wadda ake hurawa. Idanunta da suka dan yi ja, sun shige cikin fuskarta da tayi suntum!.


Ta ajiye wani nunfashi a hankali, hannu ta kai ta dafe cikin jikinta daya fara fitowa, ya kusa shiga watanninshi na bakwai yanzu. Idanunta suka dira akan kafafunta da suma suka kumbura, likitarta tace hakan is normal musamman ga masu cikin da suke a matakin da take kai, amma ita tasan har ma da damuwar da take cikin ranta. Ko awon da aka yi mata wancan karon ya nuna jininta ya hau fiye da yadda yakamata har likita din ta shawarceta data rage damuwar da take cikin ranta. Amma damuwar dake ranta ba wadda zata ragu kai tsaye bace, ko kuwa itace??!!.


Ta sake ajiye gwauron numfashi kafin ta tashi tsaye, wani irin jiri ta fara gani, black spots suna yawo a idanunta. Ta dafa mirror din ta durkusa har sai da jirin ya saketa kafin ta mike. Wannan jirin shi take fama dashi a cikin yan kwanakin. 

Wayar hannunta da jaka da mayafi ta dauka ta fita falo inda tasan Fahad yana kari. Da so samune ya kaita wajen awo taga likita kafin ya sauketa a wajen aikinta don bata tunanin zata iya yin tuki a halin da take ciki. 


Akan teburin abincin, su biyu ta samesu shi da aminin nashi. Ita yanzu zuwan Sahabi gidan har ya zame mata jiki, ta daina mamakin yadda zata tashi tun da safe ta ganshi a gidan kamar anan ya kwana. Ko yanzu lokacin data lallaba ta tashi ta hada abin kari baya gidan, amma bata yi mamaki data sameshi akan kujera a gefen mijinta yana kwasar garar data hada ba. 


Ta ciza lebenta a hankali ta karasa wajen. Kujerar da take fuskantar Fahad taja ta zauna fuskarta dauke da dan murmushi, tace, "barka da safiya honey!".

Ya dan kalleta, "barka dai, kin tashi lafiya?".

Sahabi ya kalleta yana murmushi smugly, "maman baby! an tashi lafiya?".

Harara ta watsa mishi a kaikaice. Har ga Allah bata so amsa mishi ba, amma tsoron irin tijarar da Fahad zai mata akan haka yasa ta daga baki kasa-kasa tace, "lafiya lau!".


Ta ja kula tana zuba farfesun kayan ciki da tayi. Tunda ta tashi da safe taji abinda take marmarin ci kenan, amma kuma yanzu sai taji bata da appetite din ci ko kadan. Ta fara ci a hankali kamar wadda ake tursasawa cin. 

Tana ji su Fahad din suna yan kananun hirarraki, amma bata yi gigin sanya musu baki ba. Suna gamawa, kowa ya ture farantin gabanshi ya mike. 


Ta kalli Fahad da yake gyara zaman neck tie dinshi a wuyanshi tace, "sweetheart, don Allah ko zaka saukeni a wajen awo ne kafin ku wuce? Bana jin kuzarin jikina yau ko kadan!".

Ya dan hade fuska, "gaskiya muna da muhimmin meeting da zamu yi da wasu manyan baki, I can't afford to be late! Ba motarki tana nan ba wai? Don me aka sai miki motar ne har ake baki kudin mai da na gyara?".


Wani abu yazo mata wuya ya tokare, ta cije, "amma na fada maka bana jin dadin jikina fa!".

"Nima ai na fada miki ina da abinyi ko?", ya fada a dan zafafe. 

Ta gyada kai, wannan abu daya makale mata a wuya yana kara girma da fadi ta yadda yawu ma ya fara yi mata wahalar hadiya, tace, "to shikenan, ka gaida wajen aikinka. Allah kiyaye hanya!".


Ya juya ya tafi Sahabi ya rufa mishi baya. Sai daya kai bakin kofa wai kuma sai ya juya yana kallonta, yace, "ko kuma kizo mu tafi din".

Ta girgiza kai, hawaye suna rufe mata idanu har bata iya ganin abinda yake gabanta, "a'ah, kuje kawai. Zan kai kaina!".

Ya daga kafada hadi da tabe baki ya bude kofar falon ya fita. Suna fita hawayen da take rikewa suka fara mata zarya akan kumatu kamar an bude ruwan famfo. Ta jima a haka kafin ta mike cikin sanyin jiki. Ko kayan da suka bata bata dauke ba ta koma dakinta ta wanke fuskarta ta dan goga hoda a fuskarta yadda zata rage dan ja da alamun kukan da tayi. Makullin motarta ta dauka, a tunaninta haka nan kawai zata daure ta je asibitin a dubata, in yaso daga can sai ta wuce gidansu kawai ta wuni a gefen Mommynta mai sonta. Wajen aikin ma da tayi tunanin daukar hutun haihuwa nan da wata daya da rabi, amma zata rage yadda zata samu ta huta.


Sai dai tana bude kofa zata fita taci karo da direban wajen aikinsu Fahad, ta ganeshi sarai. Yace mata, "madam, oga ne yace inzo in kaiki unguwa".

Da har zata ce mishi ya juya abinshi bata so, sai kuma ta yiwa kanta fada. Tasan a yadda take jin jirin nan da ganin duru-duru, bai kamata tayi tuki ba, don haka taja kofar ta mata key, ta bishi a baya har wajen inda motar take. Ya bude mata ta shiga. 


A asibitin dogayen ka'idoji ne aka shimfida mata, mostly sune rage damuwa da kuma cin abinci akai-akai, sai kuma fita exercise koda yawo ne a cikin gida ko unguwa, aka kara mata da tarin vitamins. Bayan ta gama da asibitin, ta umarci direban da ya kaita gidansu kai tsaye. Acan ta wuni a gefen Mommy da Fauza, ta kuma ji dadin zuwan sosai. Sai taji ranta ya danyi wasai, babu wata damuwa. A irin wadannan lokutan ne take jin haushin dalilan daya hanata yin abokai. Don abokai tana dasu da yawa, sai dai ba na kut-da-kut ba, kawai dai abota ce ake yi wata iri, don a dinga tattauna cigaban da wasunsu suka samu, ba don a zauna ana fadin matsalolin juna ba ko kuma a magance su ba. 

Ta tuna lokacin da za ayi aurenta yadda ta dinga watsawa abokanta maganar auren a fuskarsu, har da yan habaice-habaicenta. A lokacin, kaf cikinsu babu wadda ta kamo kafar irin sa'ar da tayi. Yadda kuma ta dinga babatu da abinne yasa har wasu suka kasa boye bakin cikin da suke ciki, suka fita suka nuna mata shi kiri-kiri. Akwai wadda ta tareta gaba da gaba tace mata tana ta musu wani dagawa akan auren hadin da aka mata, ta jira zata gani da idanuwanta. A lokacin bata dauki hakan a komi ba face kalamai na bakin ciki da hassada, gani take yi tafi karfin duk wani wulakancin da namiji. Gashi yanzu tana gani din kuwa. 


Amma a halin da take ciki yanzu, ta isa ta bintawa daya daga cikinsu irin zaman da take yi da mijinta ba tare da sunyi gunduwa-gunduwa da naman jikinta ba sun kasa a kafatanin kasuwannin dake cikin garin Katsina ba??!. 


Abincin dare ma sai daga cikin nasu Mommy din aka debar mata. Mommy ta sanya direban gidan ya maidata gidanta bayan ta sallaci magriba.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol