Free chapter 路 Read without an account
Page 3
馃拵ZAREN 茦ADDARA........
.....Ba ya tsinkewa馃拵
馃摑 Mohammed Munirah Abeejo (Mh卯z 脗b锚j么么h )
Free Page 3
Haka dai ta cigaba da tafiya, ba ta ko kallon inda ta ke sanya 茩afar ta, 茩wa茩walwar ta ta gama cushewa, tunanin ta yana gaf da tsayawa, bacci kawai ta ke da bu茩ata a daidai wannan lokaci.
Tafiyar minti biyar ce ta kai ta hanyar da ta zagaya zuwa gaban gidan na su, don haka ta bi ta, sai dai kamar wacce ke jin tsoron a ganta, a hankali take tafiya tare da 蓳uya da zarar ta gano mutum har sai y wuce, a haka ta isa ga gida, ta ma yi Sa'a mutanen ba wucewa su ke da yawa ba, kuma duhu ya 蓷an fara yi, a haka ta samu damar shigewa cikin gidan.
Tana shiga su ka yi kicibis da Baba wato mahaifin su Malam Auwal, saura ka蓷an su yi karo da juna ta yi saurin ja da baya tare da du茩ar da kai 茩asa tana mai gaisar da shi.
"A'a, mamana me ya ke faruwa ne, sai yanzu ki ke dawowa"
Murmushin ya茩e ta yi don kawar da hankalin sa daga hasashen yanayin da ta ke ciki, haka zalika jin cewa har yanzu abinda ta ke tunani 蓷in bai faru ba, da alamu har yanzu labari bai zo nan ba, ko kuma fa tsakanin unguwar su MK da ta su da akwai 拼ar tazara, bai zama lallai labarin ace ya iso ba, da ga nan ta ce " Baba, ba komai, mun tarar da mutane ne da yawa a wurin"
"Tom shikenan, sai ki yi sauri ki je ki yi sallah, na san dai ba ki yi ba" ya fa蓷i yana ma ficewa daga gidan, wata kila masallacin zai koma, don ta yi mamakin ganin sa ma a gida yanzu, don kuwa shi idan aka yi sallah a masallaci ya ke cigaba da zama har sai an yi sallar Isha'i.
Itama "to" kawai tace tare da wucewa cikin gidan, babu kowa a tsakar gidan, ba ta son ha蓷uwa da maman su a halin yanzu, don kuwa ita ba kamar Baba ba, da akwai ta da tambayar 茩wa茩waf, sannan kuma a iya maganar ta za ta iya hasaso yanayin ta, don haka a hankali ta shiga gidan, tunani ta fara yi game da yin Sallah kamar yadda Baba ya bu茩ata, bayan haka kuma Ubangiji ma蓷aukakin sarki ya wajaba ta garesu, a halin da ta ke ciki, ji ta ke yi ba za ta iya sallar ba, kasala da bacci, damuwa da yanayin da ta ke ciki, ji ta ke yi kamar ba za ta iya ba.
Wata zuciyar da shai蓷an ya rinjaya abinda kawai ta ke fa蓷i mata shine ta je kawai ta kwanta ta manta da sallar nan, sai dai kuma da akwai farar zuciyar da ta kawo mata akasin hakan, wai shin ta yi imani da Allah kuwa?, eh idan har ta bar sallah bayan wajaba ta da Allah ya yi sai ta ke ganin wata rashin nutsuwar ce za ta 茩ara 茩ir茩irarwa kanta, bayan kuma nutsuwa ta ke bukata a halin da ake ciki, haka zalika wai shin ba kamata ya yi a wannan halin da ta ke ciki ba, ta koma ga Allah maimakon 茩o茩arin bijire masa, ta ro茩i allah sau茩i game da lamarin da ya ke tunkaro ta.
Ta 蓷auki tsawon minti guda a 茩ofar 蓷akin na ta tana nazari akan abinda ya dace, kafin ta 茩irga biyar da mantawa da zuciyar da ta ke cewa ka da ta yi sallar, ta je ta kwanta kawai, don haka ta dawo baya ta nemi buta ta shiga bayi, tare da yin alwalar ta a ciki, daga nan ta fito a hankali ta shiga 蓷akinta, ta yi iya bakin 茩o茩arin ta don tabbatar da cewa ba'a ji motsin ta ba, don ba za ta iya amsa tambayoyin maman na ta ba.
Tana shiga ta jawo darduma ta gabatar da sallar magariba, tare da yin iya bakin 茩o茩arin ta wajen ganin ta yi addu'a tare da mi茩awa Allah kukan ta iya iyawarta, daga nan ko dardumar ba ta iya na蓷ewa ba, haka ma hijabin ta ba ta iya tsayawa cire shi ba, ta fa蓷a saman katifar ta, tare da fara 茩o茩arin yin bacci.
Tunanin rayuwa ta fara yi maimakon baccin da ta taho da zimmar yi, ita 蓷in yarinya ce da ta ke gaf da cika shekaru 19 nan da wani kankanin lokaci, mahaifinta shine malam Saleh, haifaffen garin Sakwaya ne da ke jihar Jigawa, mutum ne shi mai neman na kai ainun, shi ka蓷ai ne 蓷a namiji a wurin mahaifinsa, haka zalika na farko, sai kuma 茩annensa uku ne wato Maryam, suwaiba da kuma kubrah, Maryam da itace babba da kuma suwaiba sun yi aure kafin ya yi, sai kuma kubrah 拼ar auta da a ko da yaushe a shirye ta ke.
Malam Saleh ya je makarantar allo kamar yadda aka saba, sai dai shi ya dawo gida da wuri sakamakon halin cuta da ya addabi mahaifinsa don haka duka nauyin gidan sai ya dawo kansa.
Yayi sana'o'in hannu da dama kafin ya samu nasarar bu蓷e shagon sayar da hatsi, bayan ya yi noma wata shekara daga nan ya samu jarin da zai fara kasuwanci.
A haka, ya dinga kula da gidan nasu, da maganin mahaifin na shi har zuwa lokacin da Allah ya yi masa rasuwa, 蓷awainiyar gidan gaba 蓷aya ta dawo karkashin sa, a haka aka yi wa Maryam da suwaiba aure duka a cikin garin na Sakwaya, ya rage saura kubrah kadai.
Bayan shekaru biyu itama kubrah ta samu mijin aure, don haka shi ma ya ga cewa ya dace yayi auren, bai kuwa bata lokaci ba wajen za蓳en rayhana wacce ta kasance 茩awa ga kubrah a matsayin wacce ya ke so, yarinya ce mai nutsuwa da sanin ya kamata, da ilimin addini, da kuma 蓷an ilimin zamanin da ba'a rasa ba, ta kuwa amince masa cikin 茩an茩anin lokaci aka sanya rana guda a matsayin ranar auren biyu na kubrah da wanda za ta aura, da kuma na shi, don haka ya gyara gidan na su iya iyawarsa, ya zamana cewa ranar 蓷aurin aure kawai ake jira.
Komai nisan jifa 茩asa zai fa蓷o, duk lokacin da aka riga aka yanke da sannu-sannu za ka ji an ce ga shi ya zo, ranar aure ta zo aka sha shagalin biki aka watse, Amare duk a ka kai su gidajen mijin su, sai dai ita kubrah mijin na ta a birnin Kano ya ke.
Rayuwar auren Rayhana da Malam Saleh abar sha'awa ce, kowa yana mutunta kowa, ita tana yi masa biyayya da ganin ta faranta masa a matsayin mijinta, haka shi ma yana 茩o茩arin sauke duka ha茩kin ta da ke akan su.
Allah ya azurta su da samun 拼a拼a har bakwai, shida gaba 蓷aya maza ne sai kuma 拼ar auta Munirah, biyu daga ciki Allah ya musu rasuwa don haka yanzu Usman, Ayuba, Yakubu da Abdullahi ne ka蓷ai sukayi saura.
Usman da Ayuba tuni sun yi aure, Yakubu da Abdullahi ne ka蓷ai ya rage, duka sun 蓷an yi ilimin addini daidai gwargwado tare da ilimin boko da babu wanda ya ke wuce diploma a cikinsu, sai Munirah da ta gama karatun Computer shekarar da ta gabata a polytechnic ta jihar Jigawa da ke dutse.
Mama jajirtaciyyar uwa ce da ta tsaya tsayin daka wajen kula da tarbiyyar yaran ta, har ta kan fi mahaifin su zafi wajen yin hukunci idan yaro ya yi laifi, bin 茩wa茩wafi don tabbatar da cewa yaranta ba su afka wata gur蓳atacciyar hanyar ba, haka zalika da yi musu nasiha a ko da yaushe wajen ha蓷in kai don cimma gaci a rayuwa, ta kan yawan fa蓷a musu su zama tsintsiya ma蓷aurin ki 蓷aya, hatta a sana'a, su kan ha蓷u wajen gina sana'ar su tare, idan 蓷aya daga cikin su yana da abu, to 蓷ayan bai da fargabar cewa ya rasa, don kuwa kamar na shi ne.
Game da Munnirah kuwa, ba ta kasance kyakkyawa ba, amma ba za ka sanya ta ko kusa da layin munana ba, sakakkiyar fuska mai 蓷auke da murmushi ga kowa matukar bai kasace mace ba, haka kawai ita jinin ta bai ha蓷u da mata ba, idan har ba yan uwan ta ba, ko a makaranta ta fi sakewa da mata, sau da yawa ta kan za蓳i fita ta ha蓷u da abokan ta maza su je su yi ta fira da abokan ta maza, amma fa hakan bai hana ta samun 茩awaye ba, sai dai ba ta cika ba su muhimmanci ba kamar yadda ta bawa maza.
Duk da wannan halayyar ta Munirah ba ta yin soyayya, ba ta ta蓳a soyayya ba, duk da alaqar su da maza, amma sau da yawa ta kan dakata da yi wa duk wanda ya yi mata maganar soyayya magana, wani zubin ma ta yi masa wulakanci tare da gaggaya masa magana, ta kan yawan cewa har Yanzu ba ta ga wanda za ta iya soyayya da shi ba.
A haka Allah ya ha蓷a su da Mukhtar Kabir, wanda aka fi sani da MK, kyakkyawa ajin farko, wanda ya la茩anci soyayya da kuma yadda ake jawo hankalin 拼an mata, ta da蓷e tana mamaki farkon lokacin da ta afka a duniyar son MK.
Anya kuwa ba asiri ya yi min ba?, ta maimaitawa kanta wannan tambayar ba adadi, amma sai ta ba wa kan ta amsa da cewa "kawai dai ya karance ni ne tun kafin tunkara ta, haka zalika ya cancanci soyayya ta, bisa ga haka zan kuwa so shi har karshen rayuwa ta"
A ko da yaushe ta kan maimaitawa kanta cewa "ba ta ta蓳a jin cewa tana son MK saboda kyawunsa ba, sai don kyawawan halayen sa, sanin ya kamata da kuma kyakkyawar manufa a rayuwa, a ko da yaushe, ya kan bata labarin yadda ya ke tsare-tsaren rayuwarsa, abin yana 茩ayatar da ita"
Da akwai wani abu da munirah ta 蓷auka a rayuwa, wanda kuma ta koya daga wurin mahaifiyarta cewa ba laifi ba ne auren talaka, amma laifin shine auren wanda ba shi da wata manufa rayuwarsa, wanda bai ma san ina ya tunkara ba a rayuwa, ta ya kuma zai tunkari rayuwar, har ma ta kan ji a ranta cewa da ace wani matashin 蓷an gata kuma 蓷an gidan masu ku蓷i, da kuma matashi mai rufin asiri da kyakkyawar manufa a rayuwa za su zo gare ta da tayin soyayya da tabbas da wuri za ta karbi na wannan matashin mai rufin asiri, saboda tana da tabbacin da taimakon Allah zai iya cimma wani matsayi nan gaba a rayuwa, haka ne ma ya sa wannan itace tambaya ta farko da ta ke fara yi wa duk wanda ya yi mata tayin soyayya "shin menene burin ka a rayuwa?, wanne kalar zama ka ke son yi da matarsa? Ta ya za ka iya cimma manufofi da burikan ka " da sauran kalar wa蓷annan tambayoyi.
Fara soyayyar su da MK ya kawo canje-canje masu yawa a rayuwar ta, shi ya dakatar da ita daga kule-kulen maza idan ya wuce gaisawa, ko da yaushe ya kan nusar da ita kura-kuran da ta ke yi, ya kuma nuna mata fushinsa a kai, ita kuma wanan ne ka蓷ai ya ke 茩ara zurfafa soyayyar sa a cikin zuciyarta, don ta na jin cewa ba zai bar ta ta蓳e ba, haka zalika zai zama tsayayyen mijin da ta ke fatan su yi rayuwar farin ciki batare da kuntatawa juna ba har abada."
A wata na biyar da fara soyayyar su, manya suka shiga maganar ka'in da na'in, har a kai ga sanya rana, a kowacce rana kuwa 茩ara tsunduma ta ke yi a cikin kogin son masoyin na ta, wanda shi ta fara so kuma ta ke zaton shi za ta so har 茩arshen rayuwarta, don kuwa ba ta 蓷auki soyayya da wasa ba, don haka ba za ta ta蓳a 蓳ata lokacinta wajen yaudarar wani ba, wanda tana da tabbacin ba abinda za ta samu a cikin hakan."
Sai dai kash! Ga abinda ya wakana,da alamu mafarkin ta na sonsa shi ka蓷ai ba zai cika ba, tunda dai ya yi alwashin cewa ba zai iya auren ta ba.
Zuwa wannan lokaci Munnirah ta yi nisa a tunanin ta, har aka idar da sallar Isha,. mahaifin su ya dawo daga masallaci, sai a wannan lokaci ne mama ta ke fa蓷a masa cewa har Yanzu fah Munirah ba ta dawo ba.
Tun farkon shigowar mahaifin na su ta dawo daga dogon tunanin da ta shiga, don haka ta ji duka maganar maman na su.
"Kai, ai ina ga ta dawo tun fita ta, na ha蓷u da ita tana fitowa, amma kin duba 蓷akin ta" Baba ya fadi yana mamakin jin cewa har yanzu ba ta dawo ba.
" Sai dai na duba yanzu" maman ta fa蓷i tana nufowa dakin na ta.
A daidai nan Munirah 蓷in ta fita, don haka sai ta tsiya tana fa蓷in "Ashe ma ka ganta tana 蓷akin ma, amma ta shigo gidan ko zuwa ta sanar da ni ma ba ta yi ba"
"Ni fa nace na san dai na ga dawowar ta" Baba ya Fadi yana mai wucewa dakin sa.
"Wallahi mama, wani bacci na ke ji lokacin da na shigo, shi ya sa ba ki gani ba"
"Tom Allah ya sa ma dai, kin yi sallar magariba da Isha "
"Eh na yi magariba, isha ce yanzu zan yi sai na kwanta" munirah 蓷in ta fadi.
"Tom, sai ki gaggauta ai, ki zo ki ci abinci kafin ki kwanta 蓷in, amma dai lafiyar ki 茩alau koh, da zaki kwanta da wuri haka" mama ta fadi tana juyawa zuwa dakin ta.
" 茦alau Mam " dag nan itama ta wuce ta yi alwala, ta koma dakin ta ta yi sallar Isha, ta na son yin sallar shafa'i da witri amma kasala ba za ta bar ta ba, don haka ta 茩ara komawa kan gado, abinci ma ba ta waiwaya ba, ta cigaba da tunani har zuwa lokacin da bacci 蓳arawo ya yi awon gaba da ita.
To fah, yanzu labarin anzo ga蓳ar da zai fara 蓷aukar hankalin masu karatu, ku biyo mu a group 蓷in mu na WhatsApp wato Zaren 茩addara don biyar yadda labarin zai gudana.
***
Mun gode
#ZarenKaddara