Free chapter · Read without an account
6
_________Baba bana gani!bana gani!!" Ta faɗa cikin tsantsan nuna tashin hankali. Baba Rabe da Baba Lawan ne suka riƙeta suna faɗin" yo zaman me kuma ake akaita wajen Na Allah wanzan ya duba idon nata ko Allah zai sa a tsaida ruwan idanun" Delu ta yi saurin tashi tana faɗin" ku ɗauko ta mu je, Uzairu ɗaukota mu je" wanda ake kira da Uzairu ya nufi Lube ya saɓa a kafaɗa cikin tashin hankali.
Zayyad ne ya ce" Baba kar ayi ganganci zuwa asibiti shine best solution akan wannan matsalar" Baba Delu ta ce" ku rabu da shi do Allah mu je mu ga Na Allah" tamkar zata faɗi je fa ƙafa kawai take tana share gumi.
Yara suka bisu ɗuuu, dan sanin yanda zata kaya.
"Kasan Allah da ka barni da tuni ƴan doka sun zo, kai Allah nayi wajen Yan doka ba zai yuwu a nakasa yarinya kamar Lube ba, yarinya mai bala'in kyau, shekaran jiyan nan fa na ke sanarwa da Innarmu idan Kawu Auwali ya zo, ta sanar da shi a nema min iso wajen iyayenta in fara zuwa taɗi, idan na fitar da kayan gonata in ƙara ta biyu da ita, kuma a makantar da ita kaiii ina alkur'an ko ni nan bazan yarda ba" ce war Ɗanliti.Tunda ya fara magana Zayyad yake kallonsa kallon baka da hankali sai da ya gama zuba sannan Zayyad ya ce" yanzu wannan ƴar yarinyar zaka aura?"
Ɗanliti da yake ta Allah-Allah Zayyad ya wuce ya nufi wajen ƴan doka, cikin ƙosawa ya ce" Luben ce yarinya takai hya huɗu fa, Mata ta tana da sha uku na aureta bare Lube wacce ta fita girma ma" Zayyad ya ce"thirteen years old hahh amma Nanny ka samo mata ko, dan nasan as her age bata za iya komai na aure ba" Ɗanliti ya yi dariya ya ce" kabar wannan maganar sai hankali ya kwanta, ba ri na je ofushin ƴandoka(station).
Da sauri'sauri gudu-gudu ya wuce ya bar Zayyad tsaye yana kallon ikon Allah, murmushi ya yi yana faɗin" ni nasan her eyes is normal, ina especting yarinyar nan kawai akwai aljannu akanta ne, Allah sarki rayuwar villagers akwai abin tausayi, Allah ya kyauta.
Ya wuce dan komawa shagonsa ya zauna yana sauraren abinda zai je ya dawo.
Kafin wani lokaci zance ya baza garin Gulu Inna Maimuna ta tsiyayarwa da Lube Bodara idanu,
Duk abinda ke faruwa Inna Maimuna ba ta da masaniya ta koma gida ta ci gaba da aikace-aikacenta, ƴarta Wattini ta yi wanka ta ɗauki tallan gyaɗa da ƙulinta ta fice, ƙauyen kusa da garinsu dan anan take tallanta, zuciya tas an rama mata dukan da Lube da Mara sukayi mata, Wanki take tayi a ƙasa kan wani dutse tana ta buga kayan tana waƙe-waƙenta daga ita sai zani iya ƙugu, nonuwanta sai reto suke, hankali kwance ba tada sauran damuwa. "Assalamu alaikum" ta ji sallama ana buga ƙofar gidanta. "Amin waye ne" kafin ta rufe baki taga ƴansanda sun shigo mace da namiji."lahaula wala'ƙuwata ofisa lafiya?" ta ja zani zuwa sama ta ɗaure,jikinta ya hau rawa.
Sergeant Rabi ta ce"sannu iya lafiya lau, nemanki ake a office ɗin mu ne shine muka zo tafiya da ke" Wa!!! ni ɗin laifin me nayi wayyo na higa uku na lallace" sai ta kama ciki, copur Garba ya ce" wuce mu je kina ɓata mana lokaci" Kuyiwa Allah da ma'aiki ku yi haƙuri banyi komai ba alkur'an shekara ta arba'in ba uku a garin nan bantaɓa tahin hankali da kowa ba" S.Rabi ta ce" iya tashi mu wuce" gudawa ce ta ke shirin zubowa Maimuna ta ce" kashi nake ji, bari in zaga" riƙe ta S.Rabi tayi ta ce" idan munje can kya yi Iya" ƙugi da rugugu cikin Inna Maimuna yake, a haka suka fito da ita daga cikin gidanta, yara sun cika a ƙofar gidan anata kallo, tamkar wacce tayi sata, tana kuka, "ofisohi,ofisohi ku dakata ina da magana" ce war wani ɗan dattijo da ya tawo da gudu ya ce" daga can ofishin naku kar ta dawo min gida, ni ban taɓa zuwa ofihinku da sunan kallo ba ma bare ƙara to ba zai yuwu a danganta iyalina da wannan baƙin wajen ana faɗin matar Mudi mai tsire ba ce" Copur Garba ya ce" ba wani laifi ba ne Baba kawai wasu ƴan tambayoyi ne zata amsa, yanzu zata dawo kayi haƙuri" Mudi ya ce" ka tabbata?" Garba ya ce "in sha Allahu" sannan ya ce" to ku sauka lafiya" Maimuna ta na kuka ta ce" yanzu sa bo da Allah Malam ba za ka zo mu je tare ba" ya ce "waiiii ni Mudi na Mamuda ai alkur'an kinga ma" ya wuce cikin gidansa yana janyo ƙofar langa-langansa ya rufe.
Ɗanliti yana zaune a station ya na jiran a kamo Inna Maimuna dan shi ne ya je yakai ƙarar fasa idanun yarinya da tayi, kafin su ƙarasa Inna Maimuna ta saki zawo a zani dan tik take, babu komai jikinta sai wannan zani ɗaurin ƙirji, S.Rabi tana ta yi mata masifa, hakama Copur Garba, kunyar duniya ta cika Inna Maimuna.
"yauwa ita ce ofisa ita ce ta kama yarinya ta dinga bugu har sai da ta kashe mata idanu" Inna Maimuna ta ce"ni yaushe alkur'an hyerri(sharri)ne irin na munafukai, rabo na da fita ƙofar gida nafi mako uku ma" ta kuma rushewa da kuka.
Warin kashi ya cika ɗan wajen da suke, ruwa aka bata aka nuna mata bayi ta shiga ta wanke jikinta ta jiƙo zanin jagab, tsamo-tsamo ta yi tana rarraba idanu.
Ba tare da anji ta bakinta ba aka garƙameta a cell, sai iyayen yarinyar da aka kashewa idanu sunzo za'a saurareta.
Na Allah wanzami ya fito kenan daga gidansa ɗauke da jakarsa ta wanzanci wacce take cike da magunguna, ya hango zuga ana nufo gidansa, "ka taimaka mana ka tsaida ruwan da ke zuba a idanun yarinyar nan kar ta makance" ce war Baba Sa'idu, jin abinda ke faruwa ya sa Na Allah faɗin "ku shigo ciki da ita, garin ya ya idanu suka tsiyaye?" Wata muguwar mata ce ta caka mata yatsu a ciki, take suka fara tsiyaya" ce war Baba Delu ta na fashewa da wani sabon kukan.
Kanta Wanzami ya ɗaga yana faɗin "buɗe idanun mugani" Lube da take ihu ta ce" a'a bazan buɗeba zafi yake min" akayi akayi ta buɗe taƙi sai da taji ana a kwantar da ita a gwale su, sannan ta ce zata buɗe, a hankali ta fara buɗesu tana yin sama da baƙin ƙwayar idanun babu komai a ciki sai farin idon da ya yi jajir tamkar an zuba barkono.
"Innalillahi.....Gaba ɗaya suka hau faɗa Delu tana ƙarawa da faɗin"shikenan aikin gama ya gama wallahi bazan yarda ba, ta tashi cikin fushi, Manu ne ya riƙeta yana faɗin " ina ne gidan matar Baba, idanba yau ko ni ko ita ba".
Baba Lawan ya ce" ku tsaya mu ji abinda zaa ce mana" Na Allah Wanzami ya shiga jujjuya kai yana faɗin" ash sha,ash sha wannan abu ya yi muni da yawa, amma zan gyara komai, akwai maganin da zan bata yanzu in idanun da sauransu zasu buɗe, amma idan sun mutu tofahh sai haƙuri" Baba Delu da Manu suka sulale suka nufi gidan Maimuna Manu sai hasko yanda zai soke mata idanu yake, kasancewarsa ɗan tauri, mai sana'ar farauta.
Labarin wai ƴandoka sun tafi da ita suka ji, take suka nufi station ɗin, su suka tabbatar da zubewar idanun Lube ga ƴansanda, Ɗanliti ya dinga matse kwallah yana faɗin " ancuce shi, yasan ko sama da ƙasa zata haɗe ba zaa bari ya auri makauniya ba.
Ƙara tsare Maimuna akayi a station ɗin, sai kuka take tana ganin an gama tozarta ta, da nasani tayi yafi cikin ɗakin akan marin da ya zame mata masifa.
Ɗanliti ne yake sanarwa da Zayyad abinda ke wakana, take Zayyad ya ce"ƙarya ne wanzamin bai san aikinsa ba, na ce muku ba ta makance ba makirci ne kawai, mu je gidansu Luben in tabbatar muku da abinda na ke faɗa" Ɗanliti ya ce" ana kai ka kana gudu, amma muje" sai da ya ɗauki kayan kwalam su sweet da biscuits sannan ya tsaya a wajen mai kifi ya siya da yawa suka biya ta gonar Aminu ya ciro musu kankana mai kyau da zaƙi, sannan suka nufi gidansu Lube.
Tana kwance a tsakar gida tayi rashe-rashe tamkar mace mai ciki wata tara tana ta uban nishi, mutane sun cika tsakar gidan ana ta jimami ana tsinewa Inna Maimuna, Zayyad ya yi sallama.Matan suka amsa fuskar kowa cike da jimami, Mara da Amina ma sun ci kuka sun ƙoshi, hannunsu na riƙe da na Lube.
"Zayyanu ka ji abinda ya faru da gaske ne ko, sun kassara min jika sun mai da ta miskiniya" Zayyada ya kalli Lube idanunta ras babu alamar fitar ɗigon jini ko ɗaya, murmushinsa mai ma'ana da yawa ya yi yana faɗin" subhanallahi Allah ya taƙaita Baba.
Ganin yaƙi zama yasa Baba ta ce" to na gode jama'a ku je ɗana ya shigo kwa dawo jajen anjima na gode" take kuwa matan suka tafi, ƴan gidan gandu suka shiga ɗakin Baba kowa yana ta jimamin yanzu shikenan Lube ta makance.
Kusa da Lube ya zauna ya ce" sannu kinji, Allah ya kiyaye gaba, makanta ko ta wasa ce fa baa bar so ba ce" Baba ta ce"uhumm bari kai dai Yaro bari ai gobe da sassafe zan kai kotu nasan ƴandoka ba wani abin arziki za kuyi mana ba akan nakasa yarinyar nan da aka yi, ya ce"gaskiya ne Baba ya kamata akai kotun kawai, dan nima a garinmu akwai wani yaro da ya yi ƙaryar makanta, ya rufe idonsa tsawon awa ɗaya kacal, ai ingaya miki Baba daga haka shikenan idon nan ya ƙi buɗuwa. Aikuwa sai ya fara kukan gaske yana faɗin"Allah me nai maka daga wasa sai ka rufen ido(astagfurullah).Take Lube ta buɗe idanunta sai cikin na Zayyad ta hau muzurai tana turo baki gaba.
Humaira kuwa tunda ta dawo daga duba Lube, take zaune jikinta duk ya mutu tana ta ƙara aminta da ikon Ubangiji, yanzu shikenan yarinyar nan ta makance, kai amma ancuceta innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun Allah ka rabamu da mummunar Kaddara.
Da ƙyar ta kamala dukkan shirye-shiryenta na tafiya.
JANBULU FORESTRY ESTATE KANO
Wasu ƴanmata ne suke ta gyara wani katafaran gida,Bilki ce ta fito daga toilet ɗin bedroom wanda yake mallakin Humaira ta gama gyarawa ta ce" Kulu kamar babu makullin ɗakin Officer ko?" Kulu ta ce" eh ai Hajiya bata bari a shiga ɗakin kinga duk girman gidan nan babu inda bana shiga sai can" Bilki ta ce" to ai shikenan ki je ki maida kayan kitchen ɗin nasan yanzu sun bushe ai, kinga gobe tana dawowa shikenan" Kulu ta wuce tana sauka daga stairs ɗin, Bilki ta yau yin mooping floor hatta doors sai da suka goge take gidan ya fara gyaruwa tsawon watan nin da sukayi babu wanda ke shigowa main palour, duk a kulle yake, ma'aikata ne kawai ke rayuwa a BQ ɗinsu.
Har dare masu aikin suna gyara sai da Hajiya ta kirasu a waya jin sun daɗe ba su dawo ba, dan Kulu da Bilki masu aikin Humaira ne Hajiya ta riƙesu, wai babu wacce zata koma gida, duk da auren Bilki ya kusa wacce ta kawota ta zo ta ce ansa mata rana da wanda bata sani ba, haka ake musu aure a garinsu sai an kaiki kike sanin mijin.
Take gidan ya yi haske, suka sanya turaren wuta da na ruwa komai ya dawo normal, Kulu ta ce" ashe Aunty ce kawai zata dawo, Officer ba yanzu ba" Bilki ta ce" haka na ji ana faɗa, wai gajiya tayi da garin babu ruwa ba wuta" Kulu ta ce" waii wannan wana irin ƙauye ne Allah namu yafi shi tunda mu akwai ruwa da wuta hahh. Haka suke ta hira har suka dawo gida.
"Gobe Mummy na zata dawo mu koma gidanmu ko uncle" Insaaf ta faɗa cike da murna, Fahad ya ja hancinta yana faɗin" in Allah ya yarda amma ai ta ce ke anan zaki zauna" baki ta ɓare ta hau kuka tana faɗin ni bazan zauna ana ba" hahhhh dole anan zaki zauna" ganin yanda take kuka yasa ya ɗauketa ya fara rarrashinta.
"Nima bance ki zauna ba da kike wani ɓare baki, gidan naku sai ka ce wani madina" ce war Hajiya wacce ta shigo yanzun.
"Ina mamakin yanda yarinyar nan take da wayo haka,wai tasan iyayenta haka" Hajiya ta ce" ƴaƴan yanzu kuma ai da wayonsu ake haifarsu, kaga jariri kwana ɗaya amma idanunsa tar, Allah dai ya shirya mana zuri'a.
Insaaf da ta koma gefe ya hau bacci a zaune dan kukan da tayi ya kashe mata jiki, Hajiya ta tashi ta ɗauketa ta yi sama da ita, bacci take sosai tana mafarkin wata mata da Abba ya siyo musu.
Mommyn ta na ta kuka, a baccin Insaaf ta hau kuka tana faɗin"Abba bama sonta ta fita a gidanmu" Hajiya da ke tsaye tana kallon yanda ƙaramar yarinya take mafarki har da kuka.........