Free chapter · Read without an account
Chapter 1&2
*SU MA'YA'YA NE*
Da
Alkalamin Ummulkhair Abba Muhammad.
Burinsa idan ya yi aure su shafe shekaru biyar da matarsa suna soyayya kafin su haihu. Sai dai kash! Ita kuma ta ƙi aminta da wannan tsarin.....
Burinsa ko da zai haihu 'ya'ya maza zalla yake so, sai dai kash! 'Ya'ya mata ya dinga haifa bai san su ma 'ya'ya ba ne ya wulankanta su ya wofintar da su da mahaifiyarsu. Daga ƙarshe su suka share masa hawayen da 'ya'ya mazan ba su share ba.
*GODIYA*
Godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata’ala, wanda ya sanar da bayinsa abin da ba su sani ba.
Ya Allah ka tsarkake mini alkalamina ka sa na isar da saƙon da zai kasance shiriya ga bayinka, ka toshe mini ƙwaƙwalwata ga duk abin da idan na rubuta zai kasance fitina ga al’ummar Musulmi.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Fiyayyen halitta masoyinmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama da alayensa da Sahabbansa.
*SADAUKARWA*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ‘yan’uwana mata waɗanda ke fuskantar tsangwama wurin wasu dalilin haihuwar ’ya’ya mata zalla da suke.
Labarin ya kunshi irin tarin kalubalen da ke addabar iyaye mata da suke da 'yaya mata, inda a wasu wuraren maza ke wofintar da su. *'Ya'ya mata su ma 'ya'ya ne* suna taka matsayin da duk wani ɗa namiji zai taka.
*Ba lalle ba ne da ka fara karanta labarin ka ji daɗinsa, sai ka yi nutso a kogin sosai.*
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.
*Page 1&2*
MAIDUGURI BIRNIN SHEHU
Asibitin koyarwa (teaching hospital) misalin ƙarfe 9: 00am
A jikin kofar ofishin cikin harshen Ingilishi aka rubuta (Consultant cardiologist.) Kana shiga cikin ofishin a jikin bangon idon ka ne zai yi tozali da wannan rubutun da aka rubuta a jikin ƙarfe da ruwan gold (zinari) ‘YA’YA MATA (su ma ‘ya’ya ne)
A bangon ofishin hotunan dakta Sumayya Habib Umar ce a manne wadda ta ɗauke su ana ba ta lambar girmamawa, akwai hotonta da Gidauniyar kula da lafiyar zuciya ta Burtaniya, sai a ƙasar Saudiyya tare da Yarima Mohammed Bin Salman, da kuma wani hotonta a ƙasar Amurika tare da hukumar lafiya, sai kuma a Mumbai da ke ƙasar Indiya da wata ƙwararriyar likitar zuciya, sai kuma a nan ƙasarta Nijeriya tare da Ministan lafiya Farfesa Muhammad Ali Pate. Daga wani ɓangaren kuma hoton shugaban ƙasa ne sai kuma na gwamnan jaha da sarki, wanda yawanci jazaman ne a same su a ma’aikatu da ofishoshi.
Dakta Sumayya zaune take kan ƙayataccen kujera mai juyawa baya zuwa hagu cikin rantsatssen ofishinta ta ba wa kofar baya, sanye take da doguwar shadda gezna black blue da aka yi masa aiki zubin zamani da ratsin ruwan zaiba.
A jikin ɗan ƙarfen da ke teburin sunanta ne da a ka rubuta da ruwan gold, (zinari) DR. SUMAYYA HABIB UMAR.
Fara ce tas kyakkyawa ‘yar duma-duma saboda kallo ɗaya idan mutum ya yi mata kai tsaye ba zai ce da ita siririya ba ko ‘yar lukuta, ita dai tsaka tsaki ce.
Kyakkyawa ce dirarriya ta gaban kwatance! Doguwar fuskarta shimfiɗe take da doguwar hancinta, wanda hakan ya sake fito mata sihirtaccen kyawun fuskarta ta. Bakin kuwa jajayen laɓɓa ne masu faɗi kaɗan, wanda hakan kuwa sosai ya tafi da tsarin bakin nata idanunta dara-dara ne wanda ke ɗauke da eye lashes dogi kamar wacce ta sa mascara na asalin Fulani.
Dakta Sumayya ƙwararriyar likita ce da ta karancin ɓangaren da ya shafi zuciya ta samu lambar yabo a ƙasar ta Najeriya da ma ketare. Ƙasar Saudi Arabia ta so riƙe ta saboda wani aiki da ta yi mata ta ji daɗi amma ta ƙi ta ce ƙasarta za ta hidimtawa kuma jaharta.
Baya ga aikin likitanci da take yi tana da gidauniya da ta sa masa suna da, 'ya'ya mata su ma’ya’ya ne foundation a ƙarƙashin gidauniyar take tallafawa gajiyayyu marasa galihu da marayu, takan gina famfuna a wasu unguwanni da marasa ƙarfi ke rayuwa, tana samun tallafi sosai a wurin attajirai da 'yan siyasa.
Dakta Sumayya Habib Umar su biyar mahaifiyarsu ta haifa dukkaninsu mata, ita ce ta fari sai Muhibbat da ke bin ta sai kuma Samha sai ‘yan tagwayensu Minal da Basma su ne ‘yan auta.
Asalin sunan mahaifiyarsu Bilkisu Modibbo Giɗaɗo. Sai dai kasancewar sunan mahaifiyar Babanta ta ci sai ake ƙiranta da Ummi asalin sunan ya ɓuya. Cikakken sunan mahaifinsu kuma Habib Umar amma shi ma ana ƙiransa da Abba kamar yadda shi ma ya ci sunan Baban mahaifinsa.
‘’Ya’yan Hajya Bilkisu suna ƙiranta da Umma.
Dakta Sumayya da wuri ta tashi daga aiki yau, saboda tana so su je wani ƙauye ta rabawa mabuƙata kayan abinci kamar yadda ta saba.
Kai tsaye wurin da aka tanada don faka motoci ta nufa, wurin motarta ta tsaya ta sa mukulli tana shiga ta ja sai wurin gidauniyarta. Ma’aikatan wurin sun shirya komai tsaf da ma zuwanta suke jira, tana zuwa suka ɗunguma tare da civilian JTF guda huɗu.
YOBE STATE (DAMATURU)
Baba dattijo ne da ba zai gaza shekaru saba’in ba da ke rayuwa a wani kango wanda ke ɗauke da ɗaki biyu ginin ƙasa, ɗaki ɗaya nasa ɗaya kuma na yaransa samari biyu. Wani ɓangare daga ɗakin nasa ginin ya rufta ga saman ɗakin rufin kwano ne da ya ɓuɓɓule, hankalinsa kan tashi sosai a duk lokacin aka shiga damina saboda yadda ɗakin ke yoyo sosai wurin da zai samu ya tsuguna ma kan gagararsa.
Allah ya haɗa shi da fitinannun ‘ya’ya da yake nadamar haihuwarsu.
Kwance yake a wata jemammiyar tabarma cikin ƙwaraɓaɓen ɗakinsa, yana fitar da numfashi sama-sama, zufa na tsatssafo masa a ilahirin jikinsa, ya dafe ƙirjinsa yana juyi saboda azababben ciwon da yake masa, hatta kafaɗarsa da wuyarsa na masa ciwo. Fuskarsa duk a kumbure kana ganinsa ka san yana jin jiki.
Tari mai ƙarfi ya fara wanda ya sanya launin idanunsa suka kaɗa suka koma ja, yunƙurin tashi yake amma ya kasa kamar wanda aka yi wa ɗaurin goro haka yake jin jijiyoyin jikinsa a ɗaɗɗaure. Daga kwancen ya dinga amai kamar zai amayar da dukkan kayan cikinsa.
Ɗansa ne Kabir ya shigo yana rangaji ya haska shi da fitilar wayarsa ya ga yanayin da yake ciki, ya busa tabar da yake sha ya fesar ya ƙyalƙyale da dariya cikin muryar maye ya ce, “Kullum ina ce da kai da wannan wahala da kake ciki ka roƙi Allah ya kashe ka ka huta amma ba ka yi, ka gama wahalarka kai kaɗai.”
Ya zo daf da shi ya haske masa ido da fitilar waya, “Wai kai ba ka san mun gaji da kai a duniyar ba ne. Ka wula ka ƙi wulawa to Allah ya sa wataran idan ka fita titi tifa ta hau kanka ka mutu, kai ka huta kowa ma ya huta.”
Yana hura usur da bakinsa ya fita, ya zauna daf da bakin kofar mahaifin nasa ya kunna waƙar Davido ya ƙure murya yana saurara.
Wannan daren haka Baba ya kwana bai runtsa ba har garin Allah ya waye.
Ya fito da kyar riƙe da sanda yana tangaɗi, sai ga ɗansa Faisal ya shigo sanye da wando hands down da singileti kansa ya yi masa aski irin na nigogi, wata budurwa na bin shi a baya tana cewa, “Ba ka isa ba, ai ba haka muka yi da kai za ka ba ni ba, ai wallahi ko awowi ka yi da ni ba zan karɓi wannan kuɗin ba ballantana kwana. Na ga kuɗina cas ko kuma ka ga tujara na gogaggiyar 'yar bariki.” Ta ci kwalar rigarsa.
Jamila Shakira tacacciyar karuwa ce da ba ta gaji mutunci ba, fuskar nan tata ta koɗe saboda bilicin tana sanye da riga da siket na materiyal da suka matse ta sosai, kanta gashin attachment ne da ya zubo bayanta ɗaurin kwalin da ake ƙira ture ka ga tsiya irinsa ta yi tana tauna cingam kyas kyas kyas.
Faisal ya nemi da ta sake shi ya ji zai ba ta sauran kuɗinta.
Ta sake shi tana murguɗa baki, ya kirga kuɗi ya miƙa mata ta karɓa ta bugi cinyarta, “Ahayye! Kana iya dawowa anjima da ma shi rayuwar bariki a yi faɗa a shirya ne.”
Tana kwarkwasa ta fice.
Faisal ya ga mahaifinsa ya zuba masa ido yana kallonsa. Tsaki ya ja tare da furta, “Sa ido sana’ar banza. Ni fa ban son ana sa mini ido, idan aka ci gaba da yi zan ƙarasa laifin da ba nawa ba na aika da mutum lahira.”
Ya ɗauki buta zai zaga banɗaki, Faisal ya hankaɗe shi da gangan ya yi wucewar shi, sai ga shi wanwar a ƙasa. Wani irin takaici da raɗaɗi da ƙunci ya ji sun yi tururuwar ziyartar zuciyarsa. Runtse idanunsa ya yi tare da fatan ya haɗiyi zuciya ya mutu da wannan rayuwar, don ji yake babu wani jin daɗi ko farin ciki da ya rage masa a duniyarsa. Sai dai kuma ita mutuwa ba ta zare ran bawa face kwanansa ya ƙare.
Baba ba ya iya tsayuwar da zai shafe mintuna goma take jiri zai yasar da shi, ga idonsa ma ya samu matsala bai gani mai kyau sai ya sanya gilashi da ake ba wa masu matsalar ido ga ciwon ƙafa sai da sanda yake amfani.
Hawan jini da ciwon zuciya ke damunsa, likita ya buƙaci da yana yawaita motsa jiki a kai a kai, da yawaita shan 'ya'yan itatuwa masu gina jjik sai dai kuɗin da zai saya ma babu, don yakan kwashe kwana biyu bai ci abinci ba. Burodi da yake sayarwa a wani lokaci shi yake ci. Haka kuma likita ya shawarce shi da yana samun isasshen hutu da bacci, amma ina su ma ba sa samuwa.
A duk bayan wata guda a yadda likita ya ce da shi yana zuwa asibiti don duba lafiyarsa, amma ya shafe wata uku ba tare da ya je ba, ba komai ke hana shi zuwa ba rashin kuɗi ne, don ko an buƙaci za a yi masa gwaje-gwaje bai da kuɗin biya haka ko da magani aka rubuta, yanzu haka ma maganin da aka rubuta masa a baya wanda daga shi bai kuma zuwa asibiti ba, bai saya ba saboda suna da tsada, sana'ar da yake na burodi jarin ba nasa ba ne ana dai ba shi idan ya sayar sai ya mayar da uwar kuɗi riba tasa a hakan ma mai burodin ba kullum yake ba shi ba, zai yi ta haɗa shi da Allah da Annabi idan ya yi ra’ayi sai ya ba shi.
A hakan yaran nasa duk ranar da suka ga ya jera burodi don sayarwa za su kwasa son ransu bai isa kuma ya hana ba.
Baba bai taɓa tunanin duniya za ta juya masa baya haka ba, bai taɓa tsammanin abin da ya fi ƙarfi watarana zai zo ya fi ƙarfinsa ba, domin a lokacin da yake cikin ƙarfinsa attajirin mai kuɗi ne sosai, amma sai ga shi kamar a tarihin duniya ma bai taɓa arziƙi ba.
Ƙaramar wayar da ke hannunsa ya sayar ya je don ya sayi magani sai dai magani kala ɗaya kuɗin ya saya kuma mara tsadan cikin.
Bayan kwana biyu da ya ji jikinsa ya yi dama-dama ya tafi wurin mai burodi kamar yadda ya saba, sai ya dace aka ba shi.
Ya dawo ya jera a teburinsa yana zaune shi kaɗai ya yi jugum sai ga wani baƙar jeep ta zo ta faka daidai inda yake.
Alhaji ya fito bayan ya zo kusa da shi ya masa sallama ya amsa sai sanya hannunsa a aljihun wandonsa ya fito da kuɗi ya miƙa masa tare da faɗin, “Zakka ce nake rabawa nakan yi yawo duk mai ƙaramin ƙarfi da na gani nakan ba shi.”
Hannu biyu ya sa ya karɓa yana godiya da yi masa addu’ar Allah ya ƙara arziƙi ya sa ya gama da duniya lafiya. Ya amsa da amin ya shiga motarsa.
Kirga kuɗin ya yi ya ga dubu ɗari ce ya fashe da kukan daɗi kuɗi ya zo masa a lokacin da yake buƙatuwa da kuɗi.
Ya tattara kayan sana’ar tasa ya je ya ajiye, ya dauki katin asibitinsa ya nufi pharmacy ya sayi magungunansa gaba ɗaya ragowar canji da ya rage ya je ya sa a asusun bankinsa don idan ya tafi da shi gida bai san inda zai ɓoye ba, kuma muddin ‘ya’yansa suka kyalla ido suka gani yana ji yana gani za su karɓe.
Bayan wata ɗaya da ya gama shan magani ya je ya ciri ragowar kuɗinsa da niyyar ya ziyarci likita, bayan ya je ya ga likita sai aka sa shi da ya je ya yi gwajin jini da kuma hoton ƙirji sai ya kawo.
*Share it fisabilillahi*