Free chapter · Read without an account
Chapter 21& 22
*SU MA 'YA'YA NE*
Da
Alkalamin Ummulkhair Abba Muhammad.
*Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai*
Page 21 & 22
“Ka yi haƙ….” Tagwayen mari da na ji saukar su ya san ban ƙarashe maganar da ya fito daga bakina ba.
Cikin dashewar murya na ce. “Ka ji tsoron Allah, ka tuna ni amana ce da Allah ya ba ka, idan ka ci gaba da zalunta ta wallahi haƙƙina ba zai taɓa barin ka jin daɗin rayuwa ba. Abba da na yi abu kaɗan duka mari ba a san nagartaccen namiji da wannan muguwar ɗabi’a ba.” Ɗora ƙafarsa ya yi a gefen kujerar da nake zaune ya ɗora hannunsa a kai, cikin tsantsar tijara ya ce. “Ki fara yi wa kanki wa’azi kafin ki yi wa wani, banza jahilar kawai, kuma daga rana mai kamar ta yau, na haramta miki fita a gidan muddin kina ƙarƙashin inuwar aurena.” Ya cire belt yana wani ciccizewa kamar ɗan tauri ya ce. “Ni ba nagartaccen namiji ba ko? To me ya sa kika aure ni ba ki je kin auri nagartattu ba? Yau zan nuna miki rashin nagarta ta.”
Kafin na gama tantance komai na ji saukar belt a gadon bayana wanda har ya taɓa Sumayya da ke hannuna ta callara ihun kuka. A ƙufule na miƙe na fara ƙoƙarin kare kaina na riƙe belt ɗin, amma ya murɗe hannuna ya fizge ya ci gaba da zaula mini. Tsugunnawa na yi cikin ƙarfin hali na riƙe ƙafarsa da nufin na yar da shi, amma ko motsi bai yi ba sai ni na faɗi ƙasa ƙeyata ta bugu. Tsayawa ya yi a kaina yana huci ya ce, “Wannan shafa na yi miki, ba ki ga komai ba ma, tunda har zan gindaya miki doka ki saɓa.”
Ya ɗaga ƙafa zai yi ball da ni na gudu bedroom nasa key.
Ina sauke numfarfashi ina juyo sautin kukan ɗiyata.
Takun tafiyarsa na ji ya shiga other room ya sa sakata, na fita a hankali na ɗauki Sumayya.
Wani wahalallen bacci ya ɗauke ni da Sumayya ƙiraye-ƙirayen sallar asubahi ne ya tayar da ni na gabatar da salla na kuma kwanciya.
Ji na yi ana sheƙa mini ruwa mai bala’in sanyi. A firgice na farka ina faɗin. “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!” Tare da miƙewa cikin kyarmar jiki. Abba na gani tsaye a kaina da babban robar ruwan swan a hannunsa sai da ya karar da shi tas.
Ya nuna mini kayan da matar Hashim da mahaifiyarsa suka ba ni, “Kin je kin tallata ni ina barin ki da yunwa shi ne aka haɗa miki abubuwan nan ko?”
Ya faɗi haka cikin daka tsawa. Galala na yi ina kallonsa tare da wartsakewar da ban shirya ba, cikin karyar da harshe na ce. “Wallahi ban tallata ka ba, daidai da iyayena ba su san rayuwar da nake ba ballantana wasu. Don karan kansu suka ba ni”
Mari ya kawo mini na goce cikin sa’a tare da ja baya, ya yi mini wani irin kallo, “Za ki koma rayuwar baya shinkafa kofi ɗaya a rana sai dai a wannan karon zan haɗa ki da mai da gishiri.”
Ya nuna mini key na rufe store don na tabbatar, “Kuma wannan abu da aka ba ki kina ji kina gani zan fita da shi.” Ya juya ya fice.
Kuka na rushe da shi ko zan ji sauƙin abun da yake raina, amma tamkar ana rura garwashi haka ya ci gaba da naso a cikin raina. Ban san adadin lokacin da na kwashe a haka ba.
Ban taɓa tunanin zan tsinci kaina a irin wannan rayuwar ba ko da a mafarki, ina ta rawar kai na bar gidan iyayena na zo gidan miji na sharɓi rayuwa mai daɗi sai na ga saɓanin haka.
Anya ƙuntatawar da Abba ke yi mini ba zai sa zuciyata ta buga ba?
Juyi na yi na dawo rigingine na ƙura wa saman ɗakin ido, na rasa ina zan saka kaina, ina zan tsoma zuciyata na ji sanyi, har nauyi-nauyi na ji ƙirjina yana yi mini. Lumshe idona na yi, hakan ya ba wa hawayen da ya cika idona damar fara zuba yana ɗiga a kan pillow'n da nake kai ta gefen idona. Rayuwarmu da Abba da tun farkon aurenmu na dinga tunawa ina ƙara tisawa tsawon wannan zama ban yi wata guda da shi cikin jindaɗi ba. Me ya sa Abba ka zama daban cikin maza? Me ya sa rayuwar aure da ake faɗi mai daɗi da kwanciyar hankali ban ci karo da shi a nawa gidan auren ba?
Tabbas na yi wa kaina sagegeduwa, na cuci kaina na jefa rayuwata a cikin ƙunci da hannuna kuma ba zan iya fitar da kaina ba saboda maƙauniyar soyayya ta yi mini dabaibayi. Babu abin da ya fi tayar mini da hankali sama da duka da mari da nake fuskanta a gidan aurena da abin zai tsaya a musgunawa ma da sauki, dole na fara ƙoƙarin ƙare kaina duk ranar da Abba zai duke ni idan ko ba haka ba zai illata ni.
Wahalallen numfashi na ja ina jin kamar mafarki ne abubuwan da suke faruwa, ban san sunan da zan kiran rayuwata da shi ba, ƙaddara ko ganganci ko kuma wauta da hauka? A yadda nake jin azaba a cikin raina ba don babu kyau mutum ya yi wa kansa fatan mutuwa ba, da na lazimci addu'a ba dare ba rana Allah ya ɗauki raina saboda muddin ina numfashi ba zan iya rayuwa ba Abba ba, muddin kuma ina rayuwa rayuwar za ta wanzu ne cikin wahala. Jan majina na yi tare da tashi zaune na goge hawayen fuskata. Fuskata da idona har wani zafi suke mun saboda gajiya da kuka. Ina dafa bango na ja ƙafa da ƙyar ina dafe bango ina jin kamar zan faɗi, numfashina na fita da sauri da sauri. na je toilet na watsa ruwa.
Ajiyar zuciya na sauke na dakata da ba su labari dalilin ƙiran wayata da aka yi na ɗaga bayan na gama amsa ƙirar, sai na ga dukkaninsu suna ƙwalla, Sumayya ta miƙe na ga idanunta sun yi jajir da su don tun da na fara bayar da labarin take sharɓar kuka cikin sheshshekar kuka ta ce,
“Umma, tun daga samuwar cikina har kika haife kika rasa jin daɗi a rayuwar aurenki. Me ya sa na buƙaci sanin labarinmu? Da na san irin wannan labarin kunnuwata za su ji da ban buƙaci ji ba.”
Murmushi na yi na ce da ita, “Ai dukkaninku biyar cikin wahalar na haife ku, kuma na girmar da ku cikin wahala, Allah ya ba ku dauriya da juriyan jin labarin kawai.”
Ta haɗiye miyau da ya tsaya a maƙoshinta tare da girgiza kai, “Umma a yi mini afuwa idan har na ci gaba da sauraran labaran nan zuciyata za ta iya bugawa, yanzu ma ni kaɗai na san ƙuna da raɗaɗi da nake ji a raina.”
Na ja gauron numfashi, “Sumayya ke kika buƙaci jin labari kuma ya zama dole yadda aka fara da ke a gama da ke, zan dai ba ki kwana biyu ki samu relief a zuciyarki sai ki zo a ɗora.”
Ta fice a guje cikin gunjin kuka.
Samha ce ta miƙe tana ƙwala mata ƙira, ina Sumayya ta shiga motarta tana zuwa bakin gate maigadi ya buɗe mata ta fice.
Umma ta sauke ajiyar zuciya.
“Samha zauna, rabu da ita na san yadda zan shawo kanta.”
Ta gutsiri goro.
“ Abubuwan da ya yi mini ba ya zama tarihi ba, kuma ga shi Allah ya raya ku kun zama abin alfahari gare ni da duk duniya. To me ya sa za ta damu kanta a kai.”
Muhibbat ta goge ƙwallar da ke tsere saman fuskarta ta ce, “Umma labarin naki ne akwai taɓa zuciya, mu ma dauriya ce kawai . Tabbas kin ga jarabawa a gidan aurenki, kuma kin yi haƙuri. Allah ya samu muma mu kasance masu juriya da haƙuri a duk wani ƙalubale da za mu fuskanta a rayuwa, don ƙarshen nasara ce za ta biyo baya.”
Murmushi na yi, “Amin, tabbas haka ne. Mai haƙuri shi ke dafa dutse ya sha romonsa. Ni kam na dafa na sha, sauranku, idan mutum har yana so ya ji daɗin rayuwar duniya ya kasance mai haƙuri a duk inda yake, kuma dukkan tsanani yana tare da sauki.”
Muhibbat ta miƙe, “Wannan haka yake Umma.” Ta duba agogo “Umma zan tafi gida gobe Monday ina da shiga Court na wani case. Duk ranar da aka kuma shiryawa don ci gaba da ba mu labari sai a tuntuɓe na zo.”
Ta yafa mayafinta Minal ta ɗauko mata jaka suka mata rakiya wajen motarta ta nufi hanyar Damaturu.
Sumayya tafiya take a kan titi kamar wacce ba ta son driving domin a hankali take tukin, ƙwalla ne ya sauko daga fuskarta ta sa handikcheif ta goge.
Tana zuwa bakin gate ta yi hon maigadi ya buɗe ta shige tana parking, ta nufi falo.
Sallama ta yi Kamal na danna laptop ya amsa mata ba ta kalli inda yake ba ballantana ya samu gaisuwa ta shiga bedroom.
Rufe system nasa ya yi tare da furta,
“Anya my dear lafiyanta kuwa? Ba lau ba, don yanayin fuskarta ya nuna tana cike da damuwa.” Ya nufi inda take yana shiga fuska a murtuƙe ta ce, “What brought you here?”
What kind of question is that? Ni da gidana da matata because I came to her to be asked. Please tell me what is happening?”
A zafafe ta ce, “I don’t want to see your face, Na tsani maza!”
Ya matso kusa da ita ta ja baya ya ce, “You hate men me suka yi miki?”
Cikin fushi tana mai juya masa baya ta ba shi amsa “I don’t know.”
Ya zo gabanta ya rungume ta yana shafa bayanta, “Calm down my princess idan har za ki tsani duk mazan da ke duniya, you should not hate your husband.”
“Why shouldn’t I hate him since he is also among them.” Ta fizge jinkinta tana mai yi masa kallon tsana, “Haɗa jikina da ka yi da naka da ka san raɗaɗi da ƙunar da na ji a zuciyata da ba ka fara ba. Gwamma a jefa ni a ƙarƙashin tukuban mai tsire da fatar jikinka ya raɓa ni.”
Lallai Sumayya ƙiyayya da tsanar maza da take ikirari ya girmama, tun da suke da Kamal ba ta taɓa furta masa abu mara daɗi ba, duk da an ce zo mu zauna zo mu saɓa tun a rayuwar soyayyarsu kafin su kai ga aure ba su taɓa samun saɓani ba, haka zamantakewarsu kullum cikin farantawa da tarairayar juna suke suna gudun ɓacin ran junansu. Ran Kamal ya yi matuƙar tashi yadda matarsa lokaci guda ta sauya masa, durƙusawa gabanta ya yi yana kallon cikin kwayar idonta ba ya ko kiftawa ita ko fuskarta a haɗe tamau cikin sanyin murya ya ce. “My dear wa ya haifar da tsanata haka a zuciyarki? Anya zan yafewa wanda ya haifar da hakan? Ni Kamal kike cewa da jikina ya taɓa ki gwamma ki gan ki a ƙarƙashin tukuban mai tsire. Me ya yi zafi haka my wife? Ko kin san fushinki da ɓacin ranki su ne abubuwan da na tsani gani a rayuwata. Wa ya ɓata ran my hubaby? Tell me what is wrong with you.
Ta gefen ido ta kalle shi,
“Please go out, I want to be alone” A tsawace ta furta masa hakan.
Shi ma cikin ɗaga murya ya ce, “ I am not going anywhere utill you tell me what’s wrong with you.”
Ta miƙe tare da harararsa da murguɗa masa baki, “Haka ka ce, to bari ni na ba ka wuri.”
Wani karamar ɗaki ta shige kafin ya miƙe ta sa sakata.
Ya rafka tagumi tare da yin shiru na wasu daƙiƙu a zuciyarsa ya ce, “Allah ya kyauta! Ni dai na san gidan Umma kika ce mini za ki je, to wa ya ɓata miki rai a can? Ni Sumayya ke kora? Tana furta mini duk abin da ta ga dama, har da harara da murguɗa baki tsawon lokaci da muka ɗauka tare da ke ba ki taɓa yi mini haka ba, na yi miki uzuri my love, Allah ya yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi.”
Sumayya safa da marwa take ɗakin ta ce, “Sanadin abin da mahaifina ya yi wa mahaifiyata, ya sanya a zuciyata ina jin duk na tsani mazan da ke banƙasa.”
Zama ta yi ta haɗa kai da guiwa tana kuka.
Kamal jiyo sheshshekar kukanta sai ya ji zuciyarsa na tafarfasa ya miƙe ya zo bakin kofan da take ya ce, “My dear zuciyata ba za ta jure jin wannan sheshshekar kukan ba, zan je na tambayi Umma ita ta faɗa mini abin da ya haifar miki da wannan damuwar tun da daga gidanta kika dawo na san ba za ta rasa sani ba, idan kuma ta ce da ni ba ta sani ba, ki sani ba zan dawo gidan nan kina cikin wannan yanayi ba, sai lokacin da kika ƙira ni kika ce kin huce.”
Jin takun tafiyarsa ya sa ta yi saurin buɗe kofar cikin ɗaga murya ta ce, “Sweetheart!” Ya juyo ta ware hannayenta da ya zo gare ta, yana zuwa ta kama shi ta rungume shi cikin wani irin murya ban tausayi ta ce da shi, “Ka yi haƙuri my lovely husband, zan faɗa maka dalilin, kuma na san muddin idan ka ji ba za ka ga laifina ba don na yi maka haka.”
Ya sumbace ta, “Zan ko so na ji, duk da a jikina ina jin ba labari ba ne mai daɗi, tun da ya sa my princess kuka da furta maganganu marasa daɗi.”
Murmushi ta yi ta lumshe idanunta da suka kumbura saboda kuka ta ce, “Tabbas babu daɗi, but let me go to the kitchen and prepare food for us. Idan muka ci muka koshi sai na faɗa maka the reason that i hate men.”
Ya kai mata sumba a baki,
“Sweetheart, I have already cooked what we will eat, I said that my wife will not come back with her tiredness to cook.”
Murmushi ta yi, “Thank You my beloved husband. To bari na je na yi wanka na rangaɗa maka kwalliya.
Murmushi ya sakar mata, “Yawwa my wife ina jiranki.”
Sumayya ta yi wanka ta ci ado kamar ba ita ba, bayan sun idar da sallar isha’I ta jera musu abinci a dining table ta ba shi ya ba ta haka suka ci suka koshi, bayan sun kammala ya ɗauke ta caɗak zuwa bedroom tana kan cinyarsa ya ce ta ba shi labarin abin da ya sa ta furta ta tsani maza.
Ba ta ɓoye masa ba ta faɗa masa labarin da Umma ta ba ta, ta ce da shi duk da ba ta ƙarashe ba su labarin ba, ita kam ba za ta kuma komawa ta ji abin da zai sa zuciyarta ta buga ba. Ta ajiye maganar ƙwalla sun cika idanunta. Ya sa harshensa yana lashe ƙwallar tare da cewa, “Stop crying my wife, komai naki na da tsada a gare ni, ban son ganin ɗigar hawayen nan.”
Ya shiga rarrashinta tare da ƙarfafa mata guiwar da ta koma a ƙarasa labarin da ita, don labarin ɗauke da darasi, kuma duk yadda labarin zai zo mata da raɗaɗi ta maye gurbin raɗaɗin da abin da suka zama in sha Allah idan ta yi haka zuciyarta za ta samu salama. Ta amince da shawarar da mijinta ya ba ta.
Ya ce da ita, “Ba dukkan maza halinsu daidai ba kar ki yi mana kuɗin goro, ko don irin soyayyar da nake nuna miki ya kamata ki fahimci akwai mazan kwarai masu nunawa matayensu soyayyar gaskiya.”
Ta turo baki a shagwaɓe ta ce,, “Na sani ko kai ma za ka canja, ka zama irin mahaifina. Don shi ma ai da farkon ya nuna mata soyayya ƙin aminta da ra’ayinsa da ta yi ne ya sa shi ya sauya.”
“My wife a yadda kika ba ni labarinsa Umma ce ke mutuwar son shi ba dai shi ba, duk namijin da yake matuƙar son ka ba zai dinga furta kalmar rabuwa da abin da yake so ba akan ƙaramin matsala, tun fa suna saurayi da budurwa saɓani kaɗan ya ce zai iya rabuwa da ita, soyayyar da ta ginu ta ratsa jini da tsoka ba a furta mata kalmar rabuwa ko da da wasa ne, don haka kar ki haɗa soyayyar da nake miki da irin tasa, soyayyarmu dawwamammiya ce kuma ni da ke mutuƙaraba ne takalmin kaza.”
Ta sumbace shi tare da cewa, “I love You my beloved husband.”
“ I love you too darling.”
Sassanyar daɗi ya ji yana shiga ilahirin jikinsa, ba don komai ba saboda ya ji dalilin da ya sanya sahibarsa cikin damuwa kuma ya yi ƙoƙari ya kawar mata da damuwar. Wani irin farin ciki da annashuwa mara misaltuwa ne suka ziyarce shi.
Ya kashe hasken wutan lantarki mai haske da ya baibaye ɗakin ya kunna mara haske ya fara ƙoƙarin raba ta da suturar da ke jikinta yana mai kai mata sumba ta ko'ina.
Sai mun haɗu a next page.
Share it please